Baqeer complete - Chapter 35
Baqeer complete Chapter 35: Baqeer complete Chapter 35. Tun da suka rabu da Zainab yake tunanin ta yadda zai yi ya faɗaɗa sana'arshi, ba zai yiwu ace yana…
3,027 words
Tun da suka rabu da Zainab yake tunanin ta yadda zai yi ya faɗaɗa sana'arshi, ba zai yiwu ace yana daga zaune komai sai tayi mishi ba. Ta dai yi mishi hanyar yadda zai kafa tubalin business ɗin shi amma dole yayi komai da hannunshi, dole yasan yadda zai yi ya nemi customers da kanshi kafin ya nemi tailoring school ya shiga don a yanzu yaji babu abinda yake da bukatar yi irin sana'ar ɗinki, dama can yana da passion for ɗinkin harkar zanen nan ce ta ɗauke mishi hankali da kuma Baba da ya hana mishi damar da zai koyi ɗinkin don a cewarshi babu abinda zai yi dashi bayan yana da sana'ar da tafi ɗinkin da yake so daraja da kawo kudi. Wayarshi ya ɗauka ya kira Salim yace idan ya samu dama yazo yana nemanshi, dole yana da buƙatar mataimaki a yanzu kuma da Salim kaɗai ya yarda shi yasa ma zai janyo shi suyi harkar tare. Kafin gari ya waye yayi duk wasu tsare-tsare na yadda zai faɗaɗa kasuwancin nashi akan takarda, zuwan Salim kawai yake jira ya nuna mishi abinda ya tsara zasu yi. Da wuri kuwa Salim yazo don tun da yaga kiran wayar Baqeer jiya bayan har ya kwanta yasan cewa abu mai muhimmanci yasa yake neman shi. Tare suka karya sai da suka gama sannan Baqeer ya ɗauko takardar nan ya nuna mishi. "Yanzu dai dole mu nemi masu sayen sketches ɗin idan anyi don ba zai yiwu muce yarinyar can ce zata samo mana masu saya ba, ta dai kafa mini tubalin kasuwancin and I really appreciate her for that amma ya kamata ace na karɓi komai ya dawo hannuna ba wai ina daga zaune komai sai anyi mini ba, tana da rayuwarta kaga bai kamata mu dogara da ita ba, sannan tana mace bai ma kamata ta dinga bin mutane saboda mu ba." Salim ya jinjina kai yace "Wannan shawara ce mai kyau Baqeer its high time dama ka tashi ka gyara rayuwarka ka sani cewa babu mai taimakonka sai har idan kai ka taimaki kanka, babu wani dalili da don Allah ya jarabce ka da disability shikenan kace rayuwarka ta kare bayan yayi hakan ne don ya jarrabi imaninka. wannan tsarin da ka kawo mai kyau ne kuma In Sha Allah zan tuntubi wasu tailors dana sani akan sayen sketches din namu duk da dai ba directly zamu nemesu da su sayi kayanmu bane zamu ɓullo musu ta yadda Zainab ta yiwa wancan telan sai mu haɗa dasu Maryam idan zasu yi dinki a basu sketch din su kai daga haka idan har suna buqata su zasu kawo kansu da kansu ba sai mun bisu ba, sai kuma sabon page da zamu bude a ig da zamu dinga ɗora hotunan sketches din idan anyi sai kuma mu ƙirƙiri sunan da za'a sakawa business ɗin sai kuma muyi logo da zamu dinga ɗorawa a jikin sketches ɗin saboda masu satar fasaha". Haka dai suka zauna suka yi ta tsare-tsare har wani lokaci, basu tashi ba sai da Dada ta gabatar musu da abincin rana sannan suka yi akwala suka fita masallaci suka yi sallah sai da suka dawo ne suka ci abincin. Da Salim zai tafi ya karbi wasu daga cikin sketches ɗin akan zai kaiwa Maryam ta kaiwa telanta ya ɗinka yasan zai yi wuya shima bai biyosu ba kamar dai yadda wancan telan yayi. Akan haka suka rabu Baqeer ya koma ya kwanta yana jin wata irin nutsuwa na sauka a cikin zuciyarshi, dama can har da rashin abun yi yasa damuwarshi ta yawaita amma yanzu ya samu nutsuwa tunda ya samu wani abun yin da ko bai sayarwa da wani ba zai iya yi da kanshi don a yanzu nema yake ƙara jin son koyon ɗinki fiye da shekarun baya da sha'awa kawai yake bashi.
*****
Lokaci zuwa lokaci Zeey ke sakin murmuahi idan ta tuno da kyautar da Baqeer yayi mata, duk da turaren bai kai tsadar wanda take amfani dashi ba amma sosai taji daɗin kyautar kuma take jin son turaren cikin ranta bare idan ta tuna da rose flower ɗin daya haɗa mata dashi sai tace anya kuwa shima baya jin irin yadda take ji a kanshi a kanta? Idan ta tuna da cewar da yayi kuma wai taje wajen saurayinta yayi mata allura sai taji wata dariya ta kamata. "Is he jealous?" ta samu kanta da yiwa kanta wannan tambayar sai kuma tace kai a'a zai yi wuya ace kishi yake yi bayan ko damuwa bai yi da ita ba idan har ba ita ta nemeshi ba shi sam baya nemanta, gaskiya bata zaton yana jin irin abinda take ji a kanshi tunda gashi ita bata iya yin dogon fushi dashi ko tayi ma da kanta take bawa kanta haƙuri ta huce amma shi yana iya shareta idan har bata nemeshi ba baya iya nemanta. Bedside drawer dake gefenta ta janyo ta fito da rose flower ɗin ta shinshina tana lumshe ido tana jin wani shauƙi da farin ciki na kamata duk ta tuna wannan kyautar daga hannun Baqeer ta fito, wani ƙwayar mutum guda ɗaya da a yanzu take jin dukkanin wani farin cikinta ya ta'allaƙa ne da kasancewarshi cikin farin ciki da walwala, har mamakin yadda ta damu dashi da yawa har haka take yi bayan tasan a daa can babu wani shiri a tsakaninsu, koda yake tafi danganta rashin jituwar tasu ta wancan lokacin da yarinta.
***** Tun safe yau gidan babu kowa, Abu ta fice kasuwa sayen kayan magungunanta ita kuma Jamila ƴar ƙanwarta ce ta haihu yau suna don haka ta fita da sassafe. Ita kaɗai ce a gidan tana zaune tana hutawa bayan gama dukkan wasu ƴan hidindimunta, Baqeer ne ya faɗo a ranta tana jin daɗin yadda rayuwarshi ta fara samun saiti, duk wannan ƙuncin da rashin walwalar ya tafi duk kuwa da bata je ta ganshi ba har yau tun bayan barinshi gidan amma tasan daga yanayin yadda take jin muryarshi a waya al'amuranshi sun fara daidaita. Tunaninta ne ya ƙara komawa kan takardun filinshi da suke hannun Mallam da tasan ko sama da ƙasa zata haɗe ba bayarwa zai yi ba, idan tace zata tambayeshi ma tasan ranta ne kawai zai ɓaci ya kuma zo bai bata ba. Kallon ƙofar ɗakinshi tayi sai taga ɗakin a buɗe ga alama mantawa yayi ya fita bai rufe ba don ba sabonshi bane barin ƙofar a buɗe saboda rashin yarda. Wani tunani ne ya ɗarsu a cikin ranta ai kuwa zuruf ta miƙe ta nufi ɗakin, tura ƙofar tayi ta shiga ta janyo akwatin data san yana ajiye dukkanin wasu muhimman abubuwa nashi. Buɗe akwatin tayi ta fara fitar da kayan ciki tana duba duk wata takarda da hannunta zai kai akai, cikin sauri take komai don bata so wani ya dawo ya isketa a ɗakin so take yi tayi abinda zata yi ta fita ba tare da wani mahaluki ya ganta ba. Sai da ta kusa gama fitar da kayan cikin akwatin Allah ya bata sa'a taga takardar da take nema. Hannunta har rawa yake yi data warware takardar taga itace dai wadda take nema, haka ta ajiye ta a gefe sannan ta mayar da sauran kayan data fitar cikin akwatin har ta gama ta ɗauke ta mayar dashi inda yake kamar bata yi komai ba ta fita ta janyo ƙofar ta rufe kamar dai yadda ta ganta, tana shiga ɗakinta ta samu wuri tayi mata kyakkyawan ɓoyo sai ranar da zata je ganin Baqeer zata tafi mishi da ita ta bashi tasan idan ya sayar da filin ba ƙaramin taimako kuɗin zai yi mishi ba, sai sannan ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciyar da bata san tana riƙe da ita ba don fa har ta shiga ɗakin Badaru ta fito zuciyarta na bugawa don tsoro kasada kawai tayi ta shiga ɗakinshi ta ɗauko takardar nan amma tunda Allah yasa har tayi ta gama babu wanda ya ganta ta godewa Allah. Da yake yau ita ce da girki sai ta tashi ta cigaba da ƴan kujiba-kujibarta, ta ɗora sanwar abincin rana har ta gama babu wacce ta dawo. Har yaran ma yau babu wanda ya shigo, haka ta gama ta rarraba ta ajiyewa kowa nashi sannan ta gyara wurin, Fatima ba dai tsafta ba, duk cikin matan Mallam Badaru ita kaɗai ce bata barin wuri da datti ko tace sai tayi aikin yamma zata haɗa ta gyara, tana gama girki zaku samu ta gyare wurin tsaf kamar ba a nan aka yi aiki ba. Sai wuraren la'asar sannan Abu ta dawo niƙi-niƙi da buhun kayayyakin da take haɗa magunguna dasu, anan tsakar gidan ta dire buhun ta zauna tana sauke numfashi don sosai ta kwaso gajiya. Sannu da zuwa Fatima tayi mata, kai kawai ta iya ɗagawa sai faman haki take yi. Ita dai Fatima bata ƙara bi ta kanta ba sai ma cigaba tayi da aikin girkinta, dama can babu wani sakewa a tsakaninsu saboda haɗe mata kan da suka yi suka wareta a cikinsu shi yasa itama ta fita sabgarsu ta kama ƴaƴanta kawai take hidimarta dasu. Sai da ta gama hutawa sannan ta tashi ta shiga kitchen ɗin ta ɗauko kwanon abincinta na rana. Anan tsakar gidan ta zauna taci sai da ta ƙoshi tayi hani'an sannan ta kora da ruwa ta tashi tayi alwala ta shige ɗakinta don ko sallar azahar bata yi ba tana can tana bulayi wajen masu haɗa mata maganin mata.
***** Baqeer yayi nasarar ɗora sketches ɗin shi akan sabon page ɗin daya buɗe akan IG da facebook har ma da tiktok da twitter. Cikin hukuncin Allah cikin kwanaki biyu da ɗorawa akan shafukan nashi sai gashi yaci karo da saƙonnin mutane masu son designs ɗin nashi, godiya yayi wa Allah domin kuwa ba iyawarshi bace ko dabararshi tasa mutane suka nuna sha'awarsu ga kayan nashi. Tuni ya fara neman makarantar koyon ɗinki mai kyau inda yake so ya fara cikin ƙanƙanin lokaci. Da taimakon Salim ya nemi makarantar har ya sayi form ya cike ya mayar, a yanzu matsalarahi kawai kuɗin makaranta da zai biya, yana da kuɗaɗe a account ɗin shi amma ba wasu masu yawa bane ga baya son ya faɗawa Umma tunda yasan ba shi gareta ba kawai zai ɗaga mata hankali ne, gaba ɗaya ya damu don bai san yadda zai yi ya samu kuɗin ba, dama ya saka rai ne da samun kuɗi saboda wasu da suka ce suna son zai yi musu designing wasu kaya amma su zasu bayar da description na kayan sai ya zana to ya basu address ɗin gidan Dada akan zasu zo tun kwanaki biyu da suka wuce har yanzu shiru kake ji kuma basu ƙara nemanshi ba. Shigowar Dada ce ta katse shi daga tunanin da yake yi tace "Tanimu yazo fa tun ɗazu kai yake jira." Ajiyar zuciya ya sauke ya gunguro wheelchair ɗin tashi ya fito, anan tsakar gidan yaga Tanimun ya tambayeahi ko ya samo musu mai adaidata sahu? Yace "eh" Sallama yayi wa Dada suka fice daga gidan Tanimu yana tura shi. A ƙofar gida mai adaidaitan ya tsaya Baqeer ya faɗa mishi inda zai kai su ya kuwa yanka musu kuɗi, babu wani jaa Baqeer ya amince suka taimaka mishi ya shiga ciki sannan Tanimu ya naɗe wheelchair ɗin ya shiga suka tafi. Suna tafe Tanimu nayi mishi hira yawanci labarin garinsu ne da Innarshi sai ƙannenshi mata guda huɗu, mahaifin shi ya rasu shine wan uban ya kawo shi almajiranta wai a rage mishi nauyi. Jefi-jefi yake amsawa don hankalinshi ya kasu kashi biyu, ɗaya yana tunanin yadda zai yi mutane su san shi da sabuwar sana'arshi ɗayan kuma yana wajen tunanin Zeey da a ƴan kwanakin nan ta koyi shariya don ko gidan tazo sai tayi ta wani sha mishi ƙamshi tana basar dashi sosai hakan ke damunshi kawai dai yana dannewa ne kada ya nuna mata don bai cika son ya zura jiki ba kada yaje yayi nisan da zai kasa dawowa alhalin tafi ƙarfinshi ba iya samunta zai yi ba. Har cikin asibitin mai adaidaitan ya shigar dasu, da taimakon Tanimu ya zauna akan wheelchair, sai da ya sallami mai adaidaitan sannan suka shiga cikin asibitin. A reception ya faɗi number folder shi da kuma wurin wanda suka zo. "I know" kawai tace don tasan duk zuwan da suke yi Junaid ɗin suke gani. Sai da ta miƙa mishi folder sannan ta basu izinin shiga. Shi kuwa Junaid yana ganin folder Baqeer wani farin ciki ya lulluɓeshi nan ya fara gyara zaman rigarshi yana murmushi don ya kwana biyu bai ga Zeey ba kuma ko a waya ba sosai suke magana ba sai dai suna shiga sai yaga wani saurayin yaro ne ya rakoshi babu ma abokinshi da suka saba zuwa bare Zeey da ita yake sa ran fara gani. Fara'ar fuskarshi ce ta ɗan ragu yace "ina kuma Zeey ɗin yau baku zo da ita ba?" Wani malalacin murmushi Baqeer ya saki don haka yaji daɗi da Junaid ya zama disappointed da rashin ganin Zeey. Yaga murmushin da yayi sai kawai ya basar cikin ranshi yace "Wannan gurgun fa na lura har wani gani-gani yake yi mini akan Zeey sai dai kuma duk abun shi bai isa na bar mishi ita ba ko yana da lafiya kuwa bare a yadda yake da disability." Haka dai aka yi session ɗin ranar zuciyar Junaid a cunkushe shi kuwa Baqeer sai daɗi yake ji, har da haka yasa ya hana Zeey yi mishi rakiya kamar yadda taso ta cigaba da kawo shi.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ARBA'IN DA BAKWAI*
{47}
Suna fita Junaid ya cillar da file ɗin Baqeer ƙasa, yau yaci burin ganin Zeey da soyayyar da zasu ci amma sai gashi komai bai tafi daidai ba, secretary ɗinshi ce ta shigo tace "In kawo tea ɗin?" Rai a ɓace yace "Mai tea ɗin zaki kawo." Yayi maganar tare da cigaba da aikinshi a computer cike da ɓacin rai, fitowa tayi tai shiru tana tunanin ina zata ga mai tea, da sauri ta fito bakin gate ta sanar da mai gadin rehab centre ɗin nasu akan ya kira mai shayin dake ƙasan layinsu tana tunanin ko yunwa yake ji yana son a bashi wani abun. Babu dadewa kuwa sai ga mai shayi nan tace ya biyota, office ɗin Junaid suka nufa, yana zaune yana rubuce-rubuce, izini ya bata ta shiga shi kuma yabi bayanta, wani kallo Junaid yayi mishi yace "Waye?" Hankali a kwance tace "Mai shayin ne don bansan me kake so ba." "Shayin me kuma?" Ya tambaya cike da mamaki, ta ɗan kalli mutumin dake tsaye sannan tace "Ɗazu kace in kira mai shayin?" Wani kallo yayi mata yace "Nafisa ni kam hausa ce ba kya ganewa?" Da yake yoruba ce zaman Kano ne yasa ta iya hausa yasa tace "Ba haka kake nufi ba?" Kai kawai ya girgiza ya sallamesu ya cigaba da aikinshi.
******* Bello tare suka je Abuja da Asiya wurin visa ɗinshi, a jirgi suka je zasu yi a ranar su dawo, tunda suka je Abuja suke yawon restaurant bayan an gama application ɗin babu abinda take yi sai ɗaukan pictures tana ɗaurawa a IG ɗinta, suka sayi zobe iri daya suka saka sannan tayi caption a ƙasa wai 'His wife!' Nan fa kan Bello ya ƙara fasuwa don tabbas yana son Asiya, bayan sun dawo sun je gidan da zata zauna ƙaton apartment ne, don su mahaifiyarta da Habi da suka zo ganin gida sai baki suka sake, Habi tace "Asiya ina Bello yaga kuɗin biyan wannan ƙaton gidan?" Wani mugun kallo ta zabga mata tace "Bana jin wannan damuwarki ce ke dai kiji da naki ruɓaɓɓun samarin in kuma kishi kike yi to." Dariya Habi tayi tace "Akan me zan yi kishi ni kuwa? Bayan banga abin kishin ba?" Fusata Asiya tayi tace "Ke in baki gani ba ni na gani." Ran Habi ne ya ƙara ɓaci tace "Ko banza dai Baqeer yafi shi komai wallahi kuma dai a dinga tsoron Allah." Tana kaiwa nan ta fito cike da ɓacin rai, ita ma Asiya takaicin Habi ne ya hanata binta, kwanan nan sam basa jituwa, to dole ne? Tace bata yi da Baqeer in ita ta damu taje ta aureshi mana. Nan tayi tsaki ta sanarwa iyayensu akan wai taje wani wurin, su kansu mamakin gidan ya ishesu Baban Asiya yace "Gaskiya ba zai iya gyara ɗaki uku ba shi ko biyu ma ba zai iya ba don haka ɗaki dayan nan da falo kawai zai gyara in su suna da hali nan gaba sayi amma ba zai kwashe komai yayi mata kayan ɗaki alhalin Habi na tasowa ita ma. Kalmar nan ta ƙonawa Asiya rai tace "To ita a kwashe ayi mata in yaso in auran Habi yazo ita zata sa Bello yayi mata." Shi dai yace a'a babu ruwanshi da wannan gangancin, da haka suka fito ta rufe gidan ranta duk ya gama ɓaci don ita gaskiya kayan ɗakin da take so masu tsada ne tafi so a zo biki kowa ya koma da mamakinta a ranshi, dole tasa Bello yayi mata wani jeren amma ba za'a zubar mata da class ba haka kawai.
****** Baqeer kam har ya isa gida ƙasan ranshi wasai ko banza ya san Junaid yau yaji a salansa, haka yayi ta duba wayarshi amma babu message akan designs ɗin daya ɗaura, sake gyara profile dinshi yayi akan duk hotunan da ya saka basu zai bada ba sai dai duk da haka shiru har ya kwanta yayi bacci.