Baqeer complete - Chapter 34
Baqeer complete Chapter 34: Baqeer complete Chapter 34. Tunda ta samu Umma ta bata kuɗi ta sayi injin markaɗe shikenan aka daina jin kansu da maigidanta…
2,886 words
Tunda ta samu Umma ta bata kuɗi ta sayi injin markaɗe shikenan aka daina jin kansu da maigidanta don yanzu ta daina damunshi da bani-bani akan abinda zasu ci. Har wani ƴar daɗi suke yi bare idan yazo yaga ta shirya mishi abincin da bai san yadda tayi ta samu ta girka ba, haka zai zauna yaci yana washe baki yayi tayi mata kame-kamen zancen abinda bai shafeta ba. A yanzu bata da wata damuwa don tana samu tayi duk wasu ƴan hidingimunta a cikin ɗan abinda take samu duk da har yanzu cinikin bai zauna ba soaai saboda ba kowa yasan tana markaɗen ba duk da lokacin data fara ta tura ƴan biyu makwabtansu na kurkusa duk sun sanar cewa ta fara yin markaɗw na kuɗi idan suna buƙata, to amma ko a haka babu abinda zata ce sai gidiyar Allah domin kuwa sun daina zama da yunwa tunda duk tsiya bata rasa abinda zata girka musu abincin da zasu ci kullum har ma ta samu na sayen sabulun wanka da omon wanki. Wai kuma sai da kishiyarta taga ta samu canjin rayuwa tunda ta fara markaɗen sai ta tsiro da tsurfar wai ƙarar injin tana damunsu tana hanasu walwala a cikin gida markaɗen da ba kowane lokaci take yi ba amma shine ganin tana samun na rufin asiri take neman rabata dashi, sosai suka yi rigima har sai da maigidan ya saka baki sannan ta haƙura ta ƙyaleta ta cigaba da yi anan soron gidan nasu don da cewa tayi sai dai ta fitar dashi ƙofar gida don haka nan ba za'a kashe musu kunne da ƙarar inji ba.
***** Kabir bai shigo gida ba sai wajen ƙarfe sha ɗaya na dare bayan kowa ya tafi ya kwanta, tun Daddy na tambayar ina yake Mummy na kakkarewa har ya haƙura yayi ahiru ya daina tambayar. Cikin sanɗa yazo zai shige ɗakinshi don baya so aji motsin shigowarshi har Daddyn da baya son yasan bai yini a gida ba ya fito ya ganshi a yanayin da yake ciki. Ya kai tsakiyar parlourn kenan yaji ansa hannu an riƙo shi, sai da gabanshi ya faɗi don baya son ganin kowa a wannan lokacin. Ƴar nutsuwa ya samu da yaji kaurin hannun alamun na mace ne. Fitilar wayarshi ya kunna yana fatan ace ba waccan ƴar sa idon bace ta zauna zaman jiranshi don yasan idan har ita ce to asirinshi ya gama tonuwa. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke da yaga Nabila a zaune tana yi mishi wani narkakken kallo. Ƙwace hannunshi yayi ya haɗe rai don kada ma tace zata kawo mishi raini yace mata "Me kike yi har yanzu baki je kin kwanta ba?" Narkar da fuskarta tayi tace "Taya zan iya bacci alhalin baka dawo gida ba har wannan lokacin, wai shin ina kaje nema Kabir tun rana fa Daddy yake tambayarka."Tsaki yayi yace "Koma ina ne ina ruwanki da inda naje, kin san sarai dai bana son yawan sa ido." Yayi wucewarshi ya barta a wurin, yasan dai ba zata faɗawa kowa ba amma ya lura sai ya taka mata burki don yaga alama nema take yi ta takura rayuwarshi akan abinda daga shi har ita sun san ba mai yiwuwa bane. Sai da ya shige ɗakinshi ya mayar da ƙofar ya rufe sannan ta tashi ta bar wurin zuwa ɗakinta tana share hawaye.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ARBA'IN DA BIYAR*
{45}
Yau kwana biyu kenan Zee bata zo ba gashi ko waya taƙi yi mishi, sam komai yaji ya fita daga kanshi, haka kawai inya kalli turaren da rose flower ɗin daya siya sai yaji ranshi ya ɓaci, Dada tana lura da duk wani ɓacin ran da yake ji dashi kwanan biyu, don ko waje baya fitowa sai in abu yake so, zanen ma da yake na ɗinki ya ajiye tunda yana jiran a gama sayar da wancan kafin ya sake wani. Yanzu shine karo na takwas daya ɗauki wayarshi yana ajiyewa, tsaki yayi ya cilla wayar kan gado, sallama yaji daga ciki hakan yasa ya ɗan gunguro kekenshi zuwa jikin ƙofar ɗakin shi. "Talatu kece?" Abinda ya jiyo Dada tana faɗa kenan hakan yasa ya maida kekenshi ciki takaici duk ya ƙara kamashi, exercise na kafarshi ya shiga yi sannan ya ɗauki wani littafi yana karantawa na fashion and design, "Me zai dameshi bayan mahaifinshi ma tunda ya koreshi ko waya bai taɓa yi ba yaji ya yake? Ai duk da bai san inda yake ba ya tabbatar daya tambayi Umma zata sanar mishi." Rufe idanuwanshi yayi yana tunanin meke damunshi akan Zainab? Me yasa yake ji kwana biyun nan kamar wata guda? Wayarshi ya janyo ya rubuta 'Hope kina lafiya?' Gogewa yayi ya sake rubuta 'Zaki zo?' Ido ya zaro yace zamana take yi ashe? Nan ya goge ya rubuta 'Nace ba?' Nan ma ya goge cike da takaici ya rufe wayar yana jin haushin kanshi. A haka yayi sallar azahar, ko da Dada ta bashi abinci ma tsakura yayi ya ajiye yace ya ƙoshi, ita dai bata kulashi ba ta shirya ta fita gidan mai jego inda aka yi haihuwa kusa dasu. Haka yayi sallar la'asar ya fito waje yana neman fita waje wurin wannan makahon haka kawai yake ji yana son bashi ko dubu biyar ne a cikin kuɗin shi, turus ya tsaya jin ƙamshin turarenta, baya yayi da keken ya koma tsakar gida yana ɗan gyaggyara zaman rigarshi, sallama tayi ya amsa ciki-ciki, da mamaki ta shiga tsakar gidan yi tayi kamar bata ganeshi ba tace "Dada fa?" Mamakin kalamanta ne ya sakashi waigowa, kallonta yayi sanye take da doguwar rigar abaya sabon yayi, a saman abayar aka yi hula sai ta ɗaura ɗankwali tasa hular a sama, tayi kyau sosai sai yaga ma kyaunta kamar ƙaruwa yayi, kai ta ɗan karkatar tace "Tana ciki?" "Ban sani ba." Amsar daya bata kenan ba tare da yasan ya furta ba. Ga mamakinshi sai gani yayi zata juya ta fita da sauri yace "Ina zaki?" Waigowa tayi tace "Gida." "Gida?" Ya tambaya fuskarshi a tamke tace "Eh, ko da wani abun ne?" Kasa magana yayi sai kallonta da yake tace "Meye amfanin zuwa inda in aka ji kwana biyu kayi shiru ba za'a yi maka waya ko a tambayi lafiya ba ina ganin ba amfanin zuwa." Kallon juna suka yi, juyawa tayi zata wuce sai ga Dada ta shigo, dariya suka saki ta gaisheta tana cewa "Haba duk kwana biyu gidan babu daɗi ba kya nan shi kuma o'o sai ƙuncini da cin magani." Ta gefen ido ta kalleshi shi dai duk bai jin daɗi yaso yayi mata magana kuma sai ga Dada ta shigo, da alama ma bata ji daɗi bane, duk sai yake jinshi babu dadi. Wayar Zee ce tayi ƙara kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗaga haka kawai taji zuciyarta na ingizata yin abu, tace "J haba ai ni nayi fushi." Kalmar J data furta ne ya sakashi kallonta, nan da nan takaici ya kamashi Junaid fa kenan, shine basu tashi yin wayarsu ba sai da tazo nan gidan? Junaid yace "A'a fa nine zan yi fushi, sau nawa ina kira baki ɗauka ba." "Wai ka kira sam ban kula ba ban ɗan ji daɗi bane kayi hakuri." Kallon Baqeer tayi shima kallonta yake yi sai yaji ranshi duk babu daɗi, to wai shi menene nashi? Yasan bai kyauta ba amma wayar da take yi da Junaid haka ji yake yi kamar ya kwace wayar ya hanata magana. "Allah a'a kaima kasan ba haka bane." Shagwaɓar da yaji tana yiwa Junaid kenan, wani abu yaji ya sake tokareshi nan ya kauda kai. "Okay to shikenan zan sanar mishi sai muzo kasan ni na ɗauka kaine zaka bamu appointment ai." Sallama suka yi ta kashe wayar sannan ta kalleshi tace "J yace ya kamata ka koma." "Na dauka Junaid sunanshi?" "Eh amma J nake ce mishi." Wani kallo ya maka mata ta kauda kai tana cin magani. Bata jira me zai ce ba tace "Yaushe zamu je?" "Zamu je da Salim." Wani kallo tayi mishi ranta ya ƙara ɓaci sai dai shi haka kawai baya son ya dinga sakata wahalar yawon nan sannan baya son ma ya dinga haduwa da Junaid.
Dada ce ta sake dawowa tace "Zo mu shiga ciki kin ji waje akwai ɗan sanyi." Zeey wucewa ciki tayi suka barshi a waje takaici duk ya isheshi, shigowa yayi ya kalli jakar turaren daya siyo mata sannan yasa hannu ya ɗauka, fitowa yayi yaga Dada tana waje da alama banɗaki ta shiga, Zeey na zaune tana daddanna waya, kusa da ita ya nufa ya miƙa mata gift bag ɗin, ɗagowa tayi ta kalleshi tace "Na menene?" "Ki amsa." Kamar ba zata amsa ba sai kuma ta amsa tana kallonshi, shagwaɓewa tayi tace "Allah fushi nake yi." Wani irin yanayi ya shiga ya ɗan dake yace "Zazzaɓi?" Kai ta girgiza alamar a'a yace "Ciwon ciki?" Nan ma kai ta girgiza yace "Me ya sameki?" "Kawai." Maimaita kalmar yayi yana kallonta, ta turo baki kaɗan tace "Kawai babu abinda ke mini daɗi ne." Wani murmushi ne yazo mishi wanda shi kanshi bai san yayi ba, kallonshi tayi tace "Allah da gaske nake yi." Kai ya ɗaga alamar eh sannan yace "Sai kije saurayinki yayi miki allura." Yana faɗar haka ya fara tura keken, kallonshi tayi sannan ta buɗe jakar, flower ɗin data gani da turare ne yasa ta miƙe da sauri tace "Ka san mai bada rose flower dai yake nufi ko?" Kallonta yayi daidai ƙofar shiga ɗaki yace "Me yake nufi?" Kafaɗa ta ɗaga tace "Ka bani baka san ma'anarshi ba?" Kai ya kauda yace "Ni dai ban fassara ba." Zai rufe ƙofar ɗakin tayi saurin cewa "Thank you!" Kallonta yayi yace "Nima." "Ban ji ba Allah me kace?" Gyaran murya yayi tace "Yauwa me kake gani in muka nemi wasu masu ɗinkin suma kana musu zanen?" Kallonta yayi yace "Hmm idea ce mai kyau, zan….." Da sauri ta katseshi tana cewa "Zan je na kai ɗinki kamar yadda muka yi wannan am sure zasu zo da kansu gwara suzo da kansu da ace mu muke nemansu." Murmushi ya saki yana jin daɗin yadda komai take faɗarshi duk da wani sa'in ya kula bata iya magana ba amma a ƙalla abinda ke ranta take faɗa. Itama murmushi tayi tace "Ya Baqeer yaushe zamu duba school ɗin ɗinkin?" "Kada ki damu zan duba zan faɗa miki yadda ake ciki." "Hmmm sai kayi mini alƙawarin in ka jini shiru zaka dinga kirana Allah bana son a shareni sai naga kamar ba'a damu dani ba." A ranshi yace ke kuwa aka damu dake amma a fili murya kawai ya gyara. Dada ce ta shigo hakan yasa ya rufe ƙofar ɗakin, wayarshi ya tadda tana ƙara ya ɗauka da sauri ganin Umma ce, tambayarshi tayi jiki nan yake sanar da ita makarantar da yake son shiga, tayi farinciki sosai sai dai tunda makaranta mai tsada ce sannan kafin ya gama ya buɗe shago tasan zai ji jiki nan suka ɗan yi hira sannan ta kashe.
***** A fusace Badaru ya fara kiran sunan Kamalu kana ji kasan ranshi a ɓace yake, Abu ce ta fito da sauri har zaninta na neman kwancewa, tace "Malam me yayi?" Yatsa ya nuna mata yace "Wallahi in ba so kike yi nasa a kulle ɗanki ba kice kada ya kuskura ya ƙara zuwa mini shago ya ɗauki abu, don asara da rashin hankali satar ma a shagona zai yi? To daga ke har shi zan iya sallamaku ke kin san ba damuwa ta bane." Jiki a sanyaye tace "Mallam anya kuwa shine zai ɗauka duk fa fitinarshi baya halin ɓera kasan wannan Bashir ke yi." Salati Jamila tasa tace "Bashir? Ahir ɗinki ko tsinke bai taɓa dauka ba tare da izinin mahaifinshi ba ehe." Badaru cike da takaici yace "Ni dai banyi sa'ar ƴaƴa ba kaf cikinsu kowa da ɓacin ran da yake ƙunzuga mini, to wallahi ni daidai nake da kowani ɗan iska kun ji na faɗa muku." Ɗakin Fatima ya shiga yana sababi, haushi ne ya ƙara rufeshi da yaga babu kujeru ya wuce ɗakinta ya kwanta akan gado. Jamila ce ta kalli Abu tace "Kin dai yi asara wallahi a gidan uban wa Bashir ya taɓa sata? Amma Kamalu fa? Sai dai kar ki faɗa amma kowa yasan yana ɗauke ɗauke." Harararta Abu tayi ta shiga ciki tana masifa itama. Ita dai Fatima tana kallonshi don yanzu tunanin yadda zata tunkare shi ya bada filin Baqeer take yi, gani take in aka sayar da filin tabbas zai ishi Baqeer biyan kuɗin makaranta ya kuma buɗe shago sai dai taya zata amshi takardun fili a wurinun Badaru? Sannan inya tambayeta wace ƙaryar zata yi?
****** Zeey da tsantsar farin ciki ta shigo gida, parking tayi mai gadi ya taho da sauri ya miƙa mata leda yace "Hajiya gashi wai inji Sadaath wai ku hadu ko a menene din soyayya?" Wani banzan kallo ta yiwa ledar tace "Waye hakan?" Yace "Wannan dai yaron da yake zuwa nemanki." "Ban san shi ba ban kuma san daga ina yake ba, ka ajiye in ya dawo ka maida mishi bana son hauka please." Tana kaiwa nan tayi ciki, ɗakin Mummy tayi tana ganinta ta rungumeta ƙam tana cewa "Mummy na kalli." Amsa tayi ta buɗe jakar, nan ta zaro ido tace "Inji wa?" Shigewa jikinta tayi tace "Wanda ya sakani jin duniyar babu daɗi kwana biyu." Dariya tayi tace "Wai harda rose? ashe kun fara dating?" Kai ta girgiza tare da sauke ajiyar zuciya tace "Wannan clueless man ɗin kawai siya yayi ba da wata manufa ba, Mummy kina ganin so ne ke damuna ko?" Kuncinta ta ɗan jaa tace "ɗari bisa ɗari kawai dai tsorona mahaifinki, kinga Junaid yake son baki bana son ku samu matsala." Baki ta taɓe tace "Nifa kin san babu mai takura mini nayi abinda bana so, sannan Daddy fa don siyasarshi yake son aurar dani ga Junaid kema kin sani." Riƙo hanunta tayi tace "Kada ki damu kisa a ranki ni ina bayanki a koda yaushe." Kai ta ɗaga cikin jin daɗi tace "Shi yasa nake sonki Mummy na." "An dai girma ba'a san an girma ba." Nabeela ta faɗa tana daga tsaye jikin ƙofar, Zeey ta ƙara ƙanƙameta tace "Ke dai Aunty Nabs ko kishi kike? Ko muje ki rungumi Inna hankalinki ya kwanta." Maimakon ta bata amsa kawai juyawa tayi, abincin Kabir ta ɗauka tayi ɗakin shi, bata ko ƙwanƙwasa ba ta shiga, ya fito daga wanka kenan da towel a ƙasan shi sai kuma ƙarami yana goge kanshi, a zabure ya kalleta yasa hannu ya rufe ƙirjinshi yace "Meye hakan?" Juya baya tayi da sauri tace "Sorry KB ban kula ba." Riga yayi sauri ya zura yace "To ba sai ki fita ba me kike yi anan?" Waigowa tayi ta tako har inda yake tana murmushi tace "Plz Kabir ka canza tunaninka, wallahi it's not a big deal." Matsawa yayi ya juya mata baya, da sauri ta saƙalo hannunta ta kwantar da kanta saman kafaɗarshi, gabanshi ne ya shiga faduwa don duk rigimar Kabiru baya harkar mata ba kuma ya shaye-shaye tace "Baka so na kasance kusa dakai?" Waigowa yayi yace "Nabeela please!" Yayi maganar yana janye jikinshi, idanunta ne ya cicciko tace "Allah ne ya ƙaddara mini nima ba ni nasa wa kaina ba." "Please enough don Allah! Ke wai me yasa kike yin abu babu tunani? Don Allah kada ki sake yi mini haka, ya isheni haka nan bana son shirme please." Yana kaiwa nan ya fita ma ya bar mata ɗakin, hawayenta ta share ta fito, Mummy ce ta ganta tana shiga ɗakinta ita ma ta shiga tace "Me nace miki? Wai uban me kike zuwa yi ɗakin Kabir?" Kai ta kawar tana ƙoƙarin zama tace "Abinci na kai mishi." "Yaushe kika zama mai kai mishi abinci? Ha'a wallahi zaki tattara ki koma gida wannan shine last warning da zan miki tana kaiwa nan ta fito.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ARBA'IN DA SHIDA*
{46}