Baqeer complete - Chapter 33
Baqeer complete Chapter 33: Baqeer complete Chapter 33. **** Zeey a ƙofar gidan Umma tai parking, kallan kanta tai a madubi wai yau itace take bin namiji?…
3,368 words
**** Zeey a ƙofar gidan Umma tai parking, kallan kanta tai a madubi wai yau itace take bin namiji? Itadai sam tasan wannan rayuwar ba tata bace, gabanta ne ya ɗan faɗi kadan ya Baqeer zaiyi in yasan itace Zainab? Wani yanayi ne ya bayyana a fuskarta ta daure ta buɗe ƙofar mota ta fito. Jamila na waje ta shimfida tabarma tana yanke farcen kafarta, yau sau ƴan harare-harare sukeyi uta da Abu dake busar da aya zatai sana'ar data saba. Zainab ce ta shigo ko kallan inda suke batayi ba ta fara neman wucewa bangaren Umma. Abu a kufule tace "Ke cokal? Kin wani cokalo takalmi mai tsini kinzo mana gida kina neman shigewa ciki? Hala dangin mijin Maryam ce? Dan nasan kaf zuri'arsu Fatima ba wanda zai sa atamfar jikinki." Duk yanda sukeji da faɗa ita da Jamila sai ji mukai Jamila tasa dariya tace "Yoo wannan ma dangin nata da su ai da babu duk daya, uwar ma bakiga ba ganinta zuke zuwa yi ba." Zainab ce ta waigo tana murmushi tace "Dama aiko ni akai naga yawanku dan shugaban mu yace zai fitar da zakka amma da akama mace ɗaya ce a gidan." Jamila ce tai zuruf tace "Shareta ƴar nan wannan fa dama haka take duk wani kursusun gulma daga gunta yake fitowa nace wanene shugaban?" Abu ce tai tsaki tace "Andaiji jiki wlh mutum ya nemi sana'a yaki sai yaji za'a raba ɗari biyar ya hau bin layi." Zeey kam ganin suna masufarsu yasa ta shiga ciki ta barsu, Umma na ɗaki tun safe take jin kanta babu daɗi ga wayarta ta kunnu amma tana tsoron ƙiran Baqeer kar ya gane halin da take ciki daga muryarta. Sallamar Zainab ce yasa ta miƙe tana amsawa, ganin Zainab yasa fara'arta ta ƙara faɗa da tace "Zainab kece?" Zama tai ta gaisheta sannan tace "Daga ina haka?" "Dama nakaiwa Dada sako ne Ya Baqeer ya aikoni gunki." "Baqeer? Ya yake? Ya jikin naashi? Ya yake rayuwa?" Umma tai tambayar a jere idanunta na cikowa da kwalla, murmushi Zeey tai tace "Umma yanzu komai ya daidaita?" Kai ta jinjina tana murmushin yake tace "Indai har su yaran suna zaune lafiya ni ko ma menene bakomai." Tausayin Umma ya kamata dole ta taimaki Baqeer ko dan ya ƙara tsayawa da kafarsa, hannu tasa cikin jakarta ta ciru kuɗin ta ajiye gabanta, Umma da mamaki ta zaro ido kafin ta tamke fuska tace "Kindai san bazan karbi kuɗin iyayenki ba, ban rikeki ba abaya ban kuma......" Da sauri Zeey ta katseta tace "Inji Ya Baqeer sakon ne." Mamaki ne ya hana Umma magana tace "Baqeer?" Kai ta ɗaga zatai magana wayar Nabeela ta shigo kamar bazata ɗauka ba saboda tunanin kar a gane inda take sai kuma ta daure ta ɗaga. Nabeela tanaji ta ɗaga tace "Zeey kina ina? Dady ya kusa isowa, yana Kano." Da sauri ta mike tace "Okay, nagode Aunty Nabs." Kashewa tai sannan ta kalli Umma ta mata bayanin yanda Baqeer yace a kasafta kudin sannan tace "Zan wuce Umma ana nemana." Harta fita Umma na riƙe da kuɗi mamaki ya gama rufeta, ina Baqeer ya samu kuɗi? Kuɗin ma har haka? Wayarta ta ɗauko tadan bubuga bayan sannan ta tashi, ƙiran Baqeer tai ta ɗau kudin ta shiga dashi ɗaki ta zauna a bakin gado, karin mamakinta ma ya akai Baqeer yaba Zee sako?
Zeey cikin sauri ta fito tana ji su Jamila na gulmarta itada Abu itakam ko ta kansu batai ba tai waje, dan tasan in Dady ya san yawo take tabbas hanata fita ma zai gaba ɗaya ita kuwa yanzu aka hanata ganin Baqeer to fa an mata giɓi sannan batajin zuciyarta zata iya dauka. Kamalu ne ya sauka akan babur da mamaki yaga wata kamar Roshni ta shiga mota, cikin sauri ya ke tahowa yana hadawa da ɗan gudu-gudu, sai dai kafin ya iso taja motarta ta tafi, motar da take hawa ne sai dai bayaji Roshni zatazo gidansu, gida ya shiga ya nufi gun Abu wacce ganinshi yasa tace "Kamalu? Hala yunwa ta koroka?" "Roshini ce ta shigo gidan nan?" Da mamaki tace "Rasheeda? Au wai sunanta kenan? Yo ai ni ban sani ba." Da takaici cikin dan ɗaga murya yace "Wace wata Rashida? In ma Rabi ce ni bai damenba." A fusave Jamila tace "Karka sake kiran sunan mahaifiyata in zakai zagi ko magana ku kare can tsakaninku. Tsaki yai yana kumboro baki kawai ya fita daga gidan, ya banko ƙofar gida kai kace ɓalata zaiyi. Da gudu ta shiga ciki, saura kiris ta buge Kabir da ya nufi hanyar waje, tace "Oops! Sry." Kai ya girgiza ya bita da harara sam yarinyarnan ta rainashi wato ko dawowa ma ya bata hakuri baiyi ba? Duk an bari ta rainashi saboda bin bayanta da kowa yakeyi. Muryar Nabeela ce ta katse shi tana cewa "Are you alright?" Kallanta yai ta sakar mai murmushi, kai ya girgiza kawai ya fita dole ma yaje gun abokansa suje club, waya ya ɗauko bayan ya shiga mota ya ƙira Mumy. Ta dauka tana cewa "Abu kake so?" "No Mumy please fita nakesan yi zanje gun wani friend dina ne in Dady ya dawo kice ina bacci, ba dadewa zan ba." Kafin tai magana ya kashe wayar ya shiga motar ya bar gidan. A ɗaki ta ajiye jakarta sannan ta cire mayafi ta fito gun Mumy inda take shiryawa Dady abinci.
***** Baqeer ne ya ɗaga ƙiran Umma, bayan sun gaisa tace "Baqeer meke faruwa? Ka barni riƙe da kuɗi ina kokonto." "Umma badai so kike kice baki yarda da ɗan ki ba wanda kika haifa kika kuma raina, kindai san bazan yi abin banza ba." Ajiyar zuciya tai tace "Bawai abin banza ba kawai tsoro abin yaban." Jiki a sanyaye yace "Umma insha Allahu Allah bazai wulakanta mu ba, Allah zainzama gatan mu, kedai ki cigaba da mana addu'a." A hankali tace "Allah ya dafa mana Baqeer sai dai nayi mamaki sannan yaushe kuka……" sai kuma tai shiru a matsayinya na mahaifiya da dama batasan wannan gabar tun shekarun baya me zai sa ta tambayeshi har ta kara taso da abin? Haka sukai sallama yana Dada wayar. Dada fitowa tai waje dan ta bata labari ta kuma san yanzu Baqeer zai kwafsawa hirarsu. Umma ce ta katseta da cewa "Dada nikam Baqeee yasan Zainab ne?" Dariya tasa tace "Sani kai ai duk wannan abin da taimakonta ya tabbata." Mamaki ya kama Umma sai dai Alhamdulila da Baqeer ya cire wannan mumunan abin a ransa ya saki jiki suke gaisawa da Zainab, sai dai kasan zuciyarta na tsoro kar abinda ya faru baya irinshi ko shigenshi ya ƙara faruwa. Kai ta girgiza sannan tace "Dada dan Allah kar wanda yasan sana'ar da Baqeer yakeyi yanzu, mu barshi a matsayin sirri ina tsoro kar tsautsayi yasa mahaifinshi yaji labari. Kai Dada ta jinjina alamar hakan yayi nan suka ɗan yi hira kaɗan da Dada sukai sallama.
Ba shiri Umma ta fito tai alwala ta koma ɗaki tai sallah tanawa Allah godiya akan abinda ya faru lalai babu shakka Allah shine maj bayarwa kuma shine mai hanawa.
******* Plate kowa yaja yasa abinci a falo da Dady, kallan Zeey yai yace "Ƙira Kabiru mana." Kallansa tai tace "Anya ma yana gidan kuwa bari dai na duba." Mumy ce tai saurin rikota tana cewa "Baya ɗan jin dadi shine nace ya kwanta." Da mamaki tace "Yanzu fa na ganshi da zan…." Sai kuma tai shiru kar ya gane yanzu ta dawo ta wayance tace "Allah Mumy ba wani bacci kawai gulma ce." Rikota Mumy tai tana cewa "Bari ni na duba." Bata musa ba ta koma ta zauna ta kalli Dady tace "Dady bari na ƙira Nabeela." Hannu ya mata alamar ta dakata sannan yace "Magana nakeso muyi shiyasa bance tazo ba, mahaifin Junaid yace kun haɗu ko?" Nan danan yanayin fuskarta ya canza tace "Eh amma Dady kasan ba wani abu tsakanin mu." Kai ya jinjina yace "First step ne so babu matsala, Mumy fa? Da na tafi batajin dadi ne naga duk tayi sanyi." Kai tsaye ta buɗe baki tace "Mutanen Dambatta ne……" Cikin hanzari Mumy wacce ta taho tace "Zee zo kiyi maza ki dubamin Nabeela." Kallan Mumy tai da mamaki sai dai ganin yanayinta yasa ta tashi da sauri, tana zuwa inda take ta ja ta sukai falan ciki tace "Zeey kin manta nace mu bar maganar nan?" Baki ta turo tace "To gashi nan abin yana damunki har Dady ya gane."- "Please Zeey ya isa nima na ware banasan na zama sillar mai raba alakar da Allah ya haɗa ." Jiki a sanyaye ta kalleta sannan tace "Shikenan na bari Mumy." Haka suka koma Mumy tace Kabir ma wanka, sukaci abinci ta koma ɗaki tai salla sannan ta faɗa gado. Kwanciya tai zuciyarta na tuno mata yanayin Baqeer nan ta ɗau waya tamai text tace 'Me kakeyi?' Baqeer dake zaune yana addu'oi sai daya shafa sannan ya ɗau wayar maida mata yai da '?' Baki ta taɓe tace "Oh ni!" Zata ajiye wayar wani sakon ya shigo 'Thank you' kallan sakon tai zuciyarta na ji kamar tafi kowa farin ciki, rungume wayar tai a ƙirjinta taɗan yi juyi tana lumshe ido. Zata mai reply kenan Nabeela ta shigo da sauri ta rufe wayar tace "Aunty Nabs." Karasowa ciki tai ta zauna tana cewa "Ɗazu kinwa Kabir laifi ne?" Ido taɗan juya kaɗan tace "Allah ni na ɗauka ma wani abin ne, kinga Allah ki kyale shi yai abinda yaga dama nifa a iya sanina ba abinda namai kawai kinsanshi sam baya rasa abin cewa." Jiki a sanyaye tace "Kinsan dai kaf duniya baki da kamar shi dan Allah Zee ki daina ɓata mai rai." "Wai ke kullum a bayanshi kike bakya taɓa ganin laifinshi?" "Ke kuma kullum su Mumy da Dady a bayanki suke ai." Kallan Nabeela tai cike da zargi tace "Bayan gaskiya dai ke kanki dan dai kina san biye mai ne amma kema kinsan neman faɗa yakeji dani ko da yaushe." Kawar da maganar tai da cewa "Abinci fa? Kinci?" "Umm!" Kawai tace dan tabbas tana jin ba da ɗi, mikewa tai da sauri Zee ta ɗago ta kalleta har tabar ɗakin. Dakinta ta koma ta kwanta zauna tana tunani, ya zatai da abinda ke ranta? Bayan tasan ba laifi bane amma ba wanda zai yadda da ita? Hannu biyu tasa ta shafi fuskarta.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ARBA'IN DA HUƊU*
{44}
Da sassafe ya tashi ya shirya don baya so Salim yazo ya samu bai gama shiryawa ba, tun jiya dama ya faɗa mishi yazo yau da safe zai yi mishi rakiya wani wuri, Salim ɗin bai bi ba'asin inda zai raka Baqeer ɗin ba sai ma daɗi da yaji na ganin ya fara warewa ya fara dawowa da walwalarshi, rayuwarshi ta fara hawa kan saiti kamar yadda take a daa ba kamar yadda ya ƙuntata rayuwarshi tun bayan da ya gamu da larurar nan ba. Ita dai Dada tana kallonshi ƙanzil bata ce mishi ba, tana kallon lokacin da ya haɗa wuta sannan ya ɗebo ruwa a randa ya zuba a tukunya ya ɗora ruwan wanka, bayan yayi zafi da kanshi ya sauke ya juye a bokiti sannan yaja boktin a hankali ya kaishi har wajen randar ya surka, a hankali ya dinga tura bokitin yana kan wheelchair ɗin shi har ya kai banɗakin, bai nemi taimakon Dada ba ita ma bata ce zata taimaka mishi ba kamar yadda take yi a mafi yawan lokuta da idan taga yaje zai yiwa kanshi wani abu zata tashi ta karɓa tayi mishi ko bai ce ba. Haka yayi tara-tara da dabara ya kai ruwan wankanshi da kanshi ya tuɓe yayi wankan bayan ya gama ya fito ya shirya cikin wasu kayanshi wankakku sai dai babu guga. Kallon kanshi yayi yana tunanin wai shine Baqeer wannan ɗan ƙwalisan saurayin da komai nashi ya fita daban dana matasa ƴan uwanshi gashi yau ko ɗan turaren da zai fesa a jikinshi baya dashi, shine yau yake saka sutura babu guga, tabbas dole ya saita rayuwarshi ta koma daidai ya tsaya da ƙafafunshi ya nemi abinda zai rufawa kanshi asiri ba zai yiwu ya cigaba da zama a haka ba yana ƙuncin zuciya kawai don Allah ya jarabce shi da wata larura ya mayar da kanshi mara amfani ba, bai ma ƙara tabbatar da nakasa ba kasawa bace sai da yake ɗan fita waje a yanzu yana ganin yadda mutane suka tashi tsaye da neman na kansu, akwai wani makaho anan inda yake yawan zama yake ganinshi yana sana'ar gyaran takalma har yana mamakin ta yadda yake iya yin gyaran alhalin baya gani, ranar daya fara ganinshi sosai abun ya tsaya mishi a rai don yaga dai ga wanda yafi shi zama nakasashe tunda shi ko ganin ma baya yi amma bai zauna ya dogara da kowa ba ya fito yana neman na kanshi to ahi kuwa don me yasa don ya gamu da larurar ƙafa kawai zai koma ya zauna yana jiran komai sai anyi mishi.
Salim bai zo ba sai can wajen ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe. Yana jin muryarshi suna gaisawa da Dada yayi zuruf ya fito yana maka mishi harara. "To ko dai na koma don naga kamar baka yi maraba da zuwana ba, daga ganina kawai sai ka riƙa aiko mini da harara?"Hararar tashi ya ƙarayi yace "Tun ƙarfe nawa nace maka kazo shine baka tashi zuwa ba sai yanzu?" Shima hararar tashi yayi yace "Anƙi azo da wurin Mallam daga zuwana zaka wani tareni da faɗa ko tambayar abinda ya tsayar dani baka yi ba?" "Au haka ma zaka ce?" "Eh ɗin" Ita dai Dada tana jin cacar bakin da suke yi tana dariya sai da suka gaji suka bari don kansu sannan suka yiwa Dada sallama suka fita. Sai da suka fita waje Salim ke tambayarshi inda zasu je, sai sannan yayi mishi bayanin zanen da yayi wa Zeey ranar nan bayan ta kaiwa telan ya ɗinka mata ya nemi da yayi mishi wasu ya saya da duk yadda aka yi dai har ma da kuɗin daya samu shine yake so ya rakashi kanti ya sayi ƴan abubuwan buƙata. Jinjina kai Salim yayi kafin yace "Kai amma nayi maka murna abokina, wallahi sosai nayi farin ciki, don baka san yadda zamanka a haka yake damuna ba don nasan har da hakan yake ƙara maka yawan damuwa tunda ba sabawa kayi da irin wannan zaman ba, tun baka gama mallakar hankalinka ba kasan neman na kanka to yanzu kazo baka iya yin komai kaga kuwa ai dole ka shiga damuwa amma yanzu Alhamdulillah da Allah ya kawo maka wani abun yin cikin sauƙi, Allah ya sanya alkhairi yasa wannan shine silar warwarewar duk wasu matsaltsalunka."
"Ameen Ya Rabb, nagode Salim. Ka tabbata aminin ƙwarai, kai kaɗai ne baka gujeni ba tun bayan da iftila'in nan ya afko mini, da yawa daga cikin abokanmu ma ko dubani basu zo sun yi ba bare su tausayawa halin da nake ciki, kai kaɗai ne ka tsaya tare dani ka kula dani da jikinka da aljihunka, nagode ƙwarai Allah yayi maka mafificin sakamako da aljannarshi da yayi tanadinta wa masu yin abota domin shi" haka nan yaji ƙwalla na taruwa a idanunshi, ƙoƙari yayi ya mayar da ita bai barta ta zuba ba. Shi kanshi Salim sai da jikinshi yayi sanyi da abunda Baqeer ɗin yace don shi shaida ne yadda abokansu duk suka juya mishi baya shi kuwa Bello ma sai ya haɗa da cin amana mafi muni bayan duk a cikinsu tasu tafi zuwa ɗaya shi da Baqeer saboda ra'ayinsu da yazo ɗaya na yin zane. Mai adaidata sahu Salim ya tarar musu ya faɗa mishi inda zai kai su, da taimakon mai adaidaitan suka saka Baqeer a ciki ya zauna sannan Salim ya naɗe wheelchair ɗin ya shigar da ita shima ya shiga ciki ya zauna. Suna tafe suna ƴan hirarrakinsu har suka ƙarasa wani store anan kan titin hotoro. Salim na tura wheelchair ɗin suka shiga cikin kantin bayan sun biya mai adaidata kuɗin shi. Kayan amfanin shi ya saya irinsu sabulun wanka, toothpaste da brush, man shafawa, hair cream sannan suka ƙarasa ɓangaren turare. Kallon wajen yayi idanunshi suka kai kan turaren intense oud (Gucci) da yake amfani dashi tunda ya fara riƙe kuɗi na ƙashin kanshi sai dai yanzu yasan bai isa ya iya saye ba tukuna, ɗauke kanshi yayi ya cigaba da duba turarukan mata yana so ya sayawa Zainab. Yana son saya mata turare mai tsada sai dai kuma yana jinjina kuɗaɗen su gashi shi ba wani kuɗi bane dashi masu yawa, dubu ɗarin da akatura mishi ce a account jiya, haƙuri yayi ya ɗaukar mata turaren da bai haura dubu ashirin ba ya nemi wanda bai gaza dubu biyar ba ya ɗaukarwa kanshi. Yanzu ba lokacin sayen abubuwa masu tsada bane lokaci ne da zai yi ƙoƙari ya gina kanshi in yaso komai yake son yi yayi daga baya. Kallon Salim yayi yace shima ya ɗauki turaren sai yace a'a ya saya mishi wata rana amma ba yau ba. Harara ya watsa mishi sai ya ɗaukar mishi irin wanda ya ɗauka yace "Gashinan sai muyi anko." Dariya kawai Salim yayi sai dai bai ce mishi komai ba, har sun juya zasu bar wurin idanunshi suka sauka akan wata rose flower me kyau an sakata a cikin wata garai-garai ɗin roba. Tsayawa yayi yana kallon rose ɗin yana tunanin ya dace ya haɗa mata da ita to show his appreciation. Salim dai na kallonshi bai ce mishi komai ba sai da yaga baya da niyyar barin wurin yace "Malam idan saya zaka yi ai gara ka ɗauka mu tafi mu bar ɓata lokaci rana tana ƙara yi idan kuma ba saya zaka yi ba to mu tafi don ina so naje kasuwa bayan na mayar da kai gida."
Kallon Salim yayi ya haɗe fuska don baya so ya kawo wani abin a ranshi sannan ya ɗauko flower ya saka a cikin basket ɗin suka bar wurin. Dariya ce ma taso kama Salim ganin yadda ya ɓata rai wai shi a dole kada ya kawo mishi wasa sai kace idan yayi niyyar tsokanarshi shan ƙamshin shi zai hanashi ne, ai ba wannan ne lokacin tsokanarshi ba don yasan yanzu yana buɗe baki yace zai yi magana fasa sayen flower ɗin zai yi shi kuma ba zai so ya fasa abinda yayi niyya saboda shi ba, shi yasa yayi shiru ya ƙyaleshi. Haka suka je wajen cashier aka buga musu kuɗi ya fito da atm card ya biya. Sai da suka fita har sun hau adaidaitan da zai mayar dasu gida sannan ya cewa Salim "Dan Allah idan ka samu lokaci kazo ka rakani banki nayi updating account ɗina kasan tunda na rasa wayata ban yi welcome back na layina ba don haka bana ganin alerts idan anyi min." "To sai nazo wajen jibi In Sha Allah" sai kuma ya kalleshi yana ƴar dariya ƙasa-ƙasa yace "Shi turaren da rise flower wa ni aka sayawa?" Harararshi yayi ya ɗauke kai bai amsa mishi ba, shi dama yasan ba ƙyaleshi Salim zai yi ba sai yayi ta tsokanarshi akan wannan flower ɗin da yaga ya saya. "Ah to nidai na mata na gani kuma ni namiji ne amma ba matsala zan iya amsa na kaiwa crush dina." Wani kallo Baqeer yamai yace "Hala Habi ce crush ɗin?" Salim yai gyaran murya yace "Nidai ban ce ba, kaine ma za'a tambaya tunda kai ka siya." Gefe ya kalla baice komai ba dan dama sun saba haka da Salim indai cacar baki da zolaya ne.
*****