Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 32

Baqeer complete - Chapter 32

Baqeer complete Chapter 32: Baqeer complete Chapter 32. "Hakan yayi" Zeey tace "Amma me zai hana ka saka mishi sauran ta account ai kamar zai fi ko?" Ta…

3,238 words

"Hakan yayi" Zeey tace "Amma me zai hana ka saka mishi sauran ta account ai kamar zai fi ko?" Ta kalli Baqeer don son jin me zai ce. Ɗaga mata kai yayi alamun amsawa don haka Sani ya fito da kuɗi cash dubu ɗari daga aljihun shi ya miƙa mishi. Karɓa yayi ya ƙirga yaga sun cika cif, account number ya bashi a take a wurin ya tura mishi sauran kuɗin sai gashi da dubu ɗari biyu cif nashi na kanshi. Wani irin daɗi Baqeer yaji ya mamaye zuciyarshi, a tunaninshi tunda larurar nan ta sameshi ya tashi a aiki kenan ashe dai yana da sauran amfanin da zai yi da rayuwarshi. Sallamar su Sani tela yayi ya tashi ya tafi. Yana fita Baqeer ya miƙawa Zeey kuɗaɗen gaba ɗaya. Tsayawa kawai tayi tana kallonshi, "Amsa" yace mata shima idanunshi a cikin nata. "Me zan yi dasu ni da zaka bani, ba kuɗinka bane?" tace tana turo baki gaba abinda ya kula kamar ya zame mata jiki tsabar shagwaɓa. Ganin ba zata karɓa ba ya ƙirga dubu ashirin ya miƙa mata. Noƙe kafaɗa tayi taƙi karɓa sai ma tashi da tayi ta shige falo gun Dada ta bar shi anan wurin. Da kallo ya bita kafin kuma ya tattare sauran sketches ɗin shi ya gara keken nashi ya bita cikin falan. Tana kishingide akan kujerar ƙarfen Dada ita kuma Dada tana zaune akan tabarma suna hira. Gefen kujerar ya ƙarasa ya miƙa mata kuɗin, sai ma kawar da kai tayi kamar bata ganshi ba.

Kallon Dada yayi yace mata "Dada yi magana."?Baki Dada tasa tace "Ke kuwa Zainabu ki karɓa mana, ai ba'a mayar da hannun kyauta baya." Tashi tayi zaune tace "Allah Dada ba zan karɓa ba, ya daga fara abu kawai zai ɗauki kuɗi ya bani ya bari a gaba na karɓa amma dai ba yanzu ba." Bai ƙara jan maganar ba sai ma ya miƙawa Dada kuɗin hannunshi. Karɓa tayi tace "Na miye wannan ɗin?" Sai da ya kawar da fuska sannan yace "Naki ne." "To daga farawa kai kuma Baqeeru sai ka cire iyayen kuɗi kamar wannan ka bani, da dai ka rage." Ƙin amsa yayi sai ma ya cire dubu goma a sauran kuɗin ya saka aljihun shi ya miƙawa Zainab sauran dubu saba'in ɗin yace "Please ki kaiwa Umma kice ta ɗauki 30k sauran ta bawa Hadiza da Maryam" karɓa tayi tasa a jakarta tana godiya kamar ita aka bawa. Dada ce tace "to kai kuma haka ake yi duk kabi ka rabar da kuɗaɗen naka?" "Saboda ku nake neman ai Dada" abinda yace kenan kawai yace ya gungura kekenshi zuwa ɗakin shi.

*****

Bello da Asiya kuwa saboda tafiyar shi data matso kusa yasa aka dawo da bikinsu baya don a samu ayi bikin kafin lokacin tafiyar tashi yayi, shi zai fara tafiya daga baya sai Asiya ta bishi don aƙalla zai yi shekara uku zuwa huɗu acan ƙasar da aka turashi. Tsare-tsaren biki kawai suke yi Asiya ana ta iyayi da gwalli ita a dole ta zama big babe tunda zata fita ta bar ƙasar ƙawayenta na ƙara zugata suna fasa mata kai. Gida ma da Bello zai kama haya cewa tayi bata son mai tsakar gida sai dai ya nema mata gida me gate gashi duk inda suka je neman irin gidan da take so sai suji yayi tsada don kuɗinsu daga dubu ɗari takwas zuwa miliyan ɗaya ne har da inda aka ce musu miliyan ɗaya da rabi. Da ƙyar suka samu wani three bedroom flat a tarauni, gidan sama da ƙasa ne na saman suka samu. Sai da Bello ya jinjina yawan kuɗin gidan amma da ya tuna ba wani daɗewa zasu yi a ciki ba su tattara su bar ƙasar sai yaji ba wani abun damuwa bane don haka ya kama yana murna burinshi ya kusa cika. Events kala-kala ta tsara da zasu yi shi kuma yana biye mata idan Habi tayi magana tace ya kamata ta rage ƙaryar data ɗaukarwa ranta ta tuna ita ba ƴar kowa bace iyayenta basu ajiye ba basu bawa wani ajiya ba sai ta hayayyaƙo mata da masifa tace tana yi mata baƙin ciki don taga Allah ya ɗaga darajarta ya kusa rabata da ƙangin talauci.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA ARBA'IN DA BIYU*

{42}

Dada ce ta fita jin sallama daga waje, Zeey a hankali ta kalleshi sai kuma ta canza yanayin fuskarta ganin kallan da yake mata, takardun ta kwasa sannan ta miƙe ta koma jikin ƙofa tana sake kallansu, yana daga zaune yake binta da kallo, gyaran murya yai yana ɗan kauda kai. Ta kalleshi tace "Ya Baqeer karma ka fara." "Me?" Ya tambaya yana kallanta, tace "Wai karma ka canza magana kaga dai magana ɗaya kake yi." Bai san sanda ya ɗan murmusa kaɗan ba, kanta ta kwantar jikin bango tana kallanshi, ba shakka itadai yanzu kam ta tabbatar san Baqeer nada mahimmanci arayuwarta wanda murmushinshi kaɗai nutsuwa take saka mata. Yanda ta kalleshi ne yasa yace "Kallan na menene?" Kai ta girgiza alamar a'a tace "Hakuri na nake jira ka bani?" "Name kenan?" Ajiyar zuciya tai idanunta na kanshi tace "1?" "Zero ɗin fa ina aka kaishi?" Tasan halinshi sarai kwanan nan, yanzu har kalamansa sun daina bata haushi, kallan zanen ɗinkuna dake hannunta take tabbas Baqeer Allah ya bashi basirar zane taya mutumin da bai taɓa ɗin ki ba zai zane ɗin kuna haka? Kallansa tai shima daidai nan ya ɗago yana kallanta, ya zaiyi da abinda ke ransa? Wai yau shine ya wuni yana zanen kayan da Zeey zata ɗin ka tasa, haka kawai in ya ajiye sai yaji kwakwalwarshi na auno mai ita cikin wata shigar wasu kayan, idea na sake saukar mai wanda hakan zaisa ya zauna ya sake yin zanen, sannan abinda ke ɗaure mai kai yanda zanen kayanta ke sashi farinciki da nutsuwa a cikin ranshi. Yasa a ranshi ko keken electric ɗin bai fara amfani dashi ba zai fara yanka dan yanzu ji yake yana san ɗin ka mata abinda zata sa. "Zaka min sketch na maza?" Kallanta yai da mamaki sai kuma ya tuno Junaid badai so take tace ya zana mata saurayinta ba? Nan danan fuskarsa ta canza, ya kauda kai tace "Hmmm a tsayi bai fika ba, sannan a jiki ma haka, ashekaru ma ina ga bai fika ba." Fuskarshi ce ta murtuke sosai dan yanzu kam ya tabbatar da Junaid take duk da basu gwada tsayi ba amma yana tunanin kansu ɗaya sannan jiki ma da kadan Junaid ya fishi kenan ko kaya ne zasu iya sawa, mamaki ne ua kama Zee ganin yanda ya canza fuska lokaci ɗaya. Tace "Me kuma nai? Ko bazaka dinka ba?" "Eh!" Kalmar dayaji ta fito daga bakinshi kenan shi kanshi bai sani ba "Meyasa?" Nan ya fara tambayar kansa dan shi kanshi baisan amsar da zai bata ba, yana ƙoƙarin yin magana Dada ta dawo tana cewa "Baqeeru almajirincan ne Tanimu wai gaisheka yazo yi." Ja mishi ƙofa sukai suka bashi guri dan ya hau keken guragun, haka ya hau ya turo keken zuwa jikin ƙofa yana buɗe wa suka ƙara kallan juna, wani yanayi ne ke ratsa zuciyar ta da ita kanta batasan sanda ta canza yanayin kallan da take mai ba, wani abu ne ya tsayamai wanda yai saurin kauda kai yana cewa "Tanimu?" Da sauri yaran ya taso da bai wuce shekara 16 ba yana gaida Baqeer, tana daga ciki tana kallan yanda suke magana fuskar Baqeer a sake, hakan yasa ta kasa ɗauke idanunta daga kanshi. Mikewa tai ta ɗau dinkin ta sannan tawa Dada sallama. Yana kallan sanda ta fita ganin taki mai magana yasa ya rasa ta yanda zai mata magana harta kai bakin ƙofa idanshi na kanta, takardun hannunta ta ɗaga mai sama kaɗan, kai ya ɗaga mata alamar to tana murmushi tace "Zan kawoshi." Nan ma kai ya ɗaga mata, ta kalli Taminu sannan tace "Bazan ƙira waya ba." Yanzun ma kai ya ɗaga mata, fuska ta canza sannan ta fita waje, mota ga shiga tasa hannu saitin kirjinta tana fitar da wani irin numfashi sama-sama nutsuwa ce take saukar mata ta sake kallan sketch ɗin tana cewa "Duk ni zan fara ɗin kunan nan." Baqeer kuwa samun kanshi yai kamar wanda bashi da damuwar komai, yana mamakin yanda ta shigo rayuwarshi har ta cire duk wani duhu dake baibaye dashi. Tanimu ya daɗe a gidan dan har gyaran ɗakin Baqeer, Dada tace ya jira yaci abinci yace a'a zaije kasuwa ne yin dako sannan ya tafi.

***** Bashir ne ya fito hannunshi ɗauke da kofin shayi ya ajiye sannan ya fita, Abu na zaune sai sake cika da batsewa yau tun safe ranta a ɓace yake sakamakon kwanan da Alhaji yai a gun Jamila, tana zaune tana jujuya kazar amarya da aka aiko mata ta dafa, Jamila ce ta fito sanye da atamfa tasha kwalliya kai kace wata yan mata, an dambara hoda da jambaki tana tauna chewing gum, kanta ta turo ɗaurin ture kaga tsiya zama tai a waje tana wani kale-kale da muzurai har Bashir ya gama ya fita, can ta dau waya ta kira tana cewa "Ah to mu namu kunsan ba irin nasu bane, mu har a nuna mana sanabe? Mutum ya girma wai shi a dole maida tsohuwa yarinya? Yo ta ina ka tsufa zakace zaka dawo yaro? Gane mun hanya abinka da wacce bata waye ba kinsan kan nan ba komai a ciki sai tunanin kayan mata, to ya girma yana san hutu an sha magani an hanashi bacci ba dole ya gudo ba?" Ai Abu dake saurarenta ta gama kaiwa bango a fusace ta matso inda take tana nunata da ludayin hannunta tana cewa "Jamila na rantse da Allah zaki jawo ai abin kunya dan wallahi banki na kwabe mu daky ba kiga waye tsohon." Ajiye wayar tai dan dama wayar ma ta karya ce tace "Kinga ni bansan tashin hankali ke wai sai yaushe zakisan ni na finkarfin yin dambe? Yarana na aure a ganni ina dambe ai wallahi nafi karfin wannan, shayi ne dai an hana ku ke sanda kuke ci kuke cinyewa a ɗaki wani ne ya sa muku ido?" Fatima ce ta fito daga ɗaki buta ta ɗauka ta nufi bandaki kamar batasan sunayi ba, ta dawo tana kallansu duna cece kuce sai dataje wajen ɗakinta sannan tace "In kun tashi fadanku nan gaba ina ganin ku yishi in yana gidan matsalar kai abu ba'asan kanayi na kenan." Tana kai nan ta wuce ciki dan ta kula rashin hankalinsu karuwa yake maimakon angirma asan an girma.

***** A bangaren Zeey kuwa kai tsaye gun mai ɗinki ta koma ganin yanda Baqeer yai zane yasa mamakinshi ya kara karuwa, kallanta yai yace "Hajiya dan Allah zan iya ganinshi gobe?" "Eh zan ƙira shi naji lokaci sai mu hadu dakai a gidan." Daɗi ne ya kamashi yace "Kai nagode lalai inaji a jikina alkairi ne ya zo gareni." Haka ta kwashe takardun tace "In kun gama yanke yanda zakuyi business ɗin na dawo maka dashi." Ba yanda zaiyi haka yana gani ta tafi dasu, ji yake harya kosa gobe tai, nan ya dinga kallan shagonshi yana tunanin da alama dole ya ƙara fadada shagon tunda alkairi ne ya zo musu. A hanyarta ta komawa sau hudu tana ɗaukan wauarta tana ajiyewa tana kwaban kanta akan itama taɗan ja aji irin na mata, har mamakin kanta take yanda take da jan aji wai akan Baqeer sam bata iyawa, harta isa gida bata ƙira shi ba. Mumy ta tarar a kitchen tana bada umarnin girku, a shagwabe tace "Mumy ruwa." Kallan ɗaya daga cikin masu aikin tai nan ta miko msta da sauri, Zeey ta amsa tai daki tana tafe kamar ba laka a jikinta duk zuciyarta nemab kin hakura da ƙiran Baqeer take. Binta Mumy tai tana shiga itama ta shigo tace "Suta lafiya?" Huci ta sauke sau uku sannan tace "Mumy waya nake san yi kuma bana san yi." "Me kenan? Kinaso kuma bakyaso?" Ta ɗaga kai tace "Banaso ya rainani kuma na kasa hakura." Kallan mamaki ta mata, tace "To ni bansan meke faruwa ba ina na isa bada shawara?" Jawo jakarta tai ta ciro takardun tace "Yauwa Mumy kalla?" Amsa tai tana kallo mamakin yanda Zeey ta koma farinciki take, sai sa ta gams dubawa sannan tace "This is incredible waye yai?" Amsa tai daga hannun Mumy tana dariya tace "Dan baiwa." "Mai disability ɗin da kika ban labari?" Kai ta ɗaga a hankali tace "Mumy karki manta sirrin mu ne." Kanta ya shafa tana cewa "Karki damu sannan karki manta na ce miki ina bayanki duk abinda kika zabarwa kanki ina tare dake." Kai ta ɗaga a hankali taee da rungume Mumy wata nutsuwa ma saukar mata, Mumy na fita ta jawo wayarta, sako ta turamai 'Ka kirani' Shima maida mata yai yace 'Why?' 'Kawai nidai ka ƙirani so nake naga ya receiving call ɗinka zai kasance.' Kai ya girgiza kamar bazai kiraka ba har na wajen minti biyar, dan Zee har ta ajiye wayarta tare da jan tsaki tace "Na sani dama ai." Karar wayarta ce yasa ta mike zaune da sauri ta jawo wayar tana jin wani sanyi cikin ranta, ringing biyu ga daure akan bazata dauka ba, tana jiran na ukun da zata dauka kawai taji ya kashe, wayar ta cilar kan hado sannan ta kwanta, cike da takaici ta ƙira yana daukar tace "Ringing uku ma baza'a bari yai ba?" "I thought bakyajin yin wayar ne." "Bayan ni nace ka kirani?" "Then?" Baki ta turo kafin tace "Naje gun tailor ɗin, nan ta zayyane mai abinda ke faruwa, Baqeer da ɗi ne ya kamashi cikin kakkausar murya yace "Thank you!" Gyaran murya tai tace "Ni sam banji me kace ba me kace?" Mamaki yake yanda sam batada damuwa ko ɓacin rai bai taɓa gani ba a idanta, sai dai tai na wasa, shiru suka ɗan yi kowa da abinda yake sakawa a ransa kafin yace "Bye!" Tace "Bye." Kace wayar yai tabi wayar da kallo tare sa jan bargo ta rufe fuska, kafafunta tadan bubuga sannan ta ɓoye takardun cikin drawer, alwa tai ganin la'asar tayi sannan tai sallah, rabin addu'arta Baqeer takewa akan Allah ya kara mai lfy yasa taga ranar da zai taka da kafafunsa, Allah ya bashi ikon fara yin sana'arnan lfy."

***** Fatima yau kunnenta na waje dan tun jiya wayarta ta mutu taki tashi gaskiya Baqeer takesan dubawa dan haka hankalinta na kan shigowar Malam. Cikin faɗa yake magana "Wallahi Abu kinji na faɗa miki in bakiwa Kamal magana ba zan tattarashi shima na koreshi, gıdana ne nan ba uban daya isa ya jamin ɓacin rai, yanzu na gama da takaicin Baqeer har zan fita wani banza ya tareni yana wai ban shawara akan insa ido a kan Kamal? Wuya zansa ba ido ba kindai ji na faɗa miki, a kalla su Bashir makaranta ne kawai basa zuwa amma yanzu tunda na musu magana sunji shifa? Shi ba karatun ba sai ja min magana? To ni ba uban da zai samun hawan jini kinji na faɗa miki." Ajiyar zuciya Fatima tai dan tasan tana tambayarshi cikin wannan halin ma wani tashin hankali zata jawa kanta dan dama a san samunta ma ba cemai zatai gun Baqeer ba, cewa zatai zata barka ko biki." Haka ta koma ta zauna ranta na sake ɓaci, cike da mamaki taga an buɗe labule, Mallam? A bangarenta? Mamaki ne ya kamata ta mike tace "Mallam kaine? Sannu da dawowa." "Ba ni bane aljanina ne, ke wai nikam meke damunki? Dama lekowa nai na amshi kuɗin da nake binki." Kallansa tai tace "Wane kenan?" "Wanda nasa na sai kujeru kika haɗa kika cinye, same mace ace Allah ya yiki ba imani?" Kai ta kauda tace "Mallam na ɗauka mun yi maganwf kujeru kuma ka fahimceni?" Zagaye ya fara a ɗakin wanda hakan ya tabbatar mata dama ba zancen kudin yazo ba bincike yazo mata, yana tafe yana cewa "Na fahimceki kamar ya? Ke ai na dade da daina fahimtarki daga ke har ƴaƴanki, Maryam ma dana aurar gidan dauka na ɗauka za'a samu a amfana ashe fankan fayau ce." Yaja tsaki sannan yabar ɗakin, ba ta da niyyar kuka dan yanzu ba shine a gabanta ba, tunda sukai magana da Baqeer taji muryarshi wasai ta tabbatar komai lfy kawai dai ganinshi take san yi sai dai in haka zai sake jawo matsala gwara ta jinkirta.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Muhd Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA ARBA'IN DA UKU*

{43}

A duk sanda Habi taga Asiya na wannan zumudin kasa ɓoye mamakinta take, yanzu ma tana kwance bayan sallar asuba take juyo kunkunin Asiya, farkawa tai ta ɗan juyo tana cewa "Yau kuma menene da sassafan nan ke da bakya rabo da neman magana?" Asiya tsaki tai tace "Ni dasu Inna ne wallahi badai ni za'awa kayan ɗakin dubu dari biyar ba kamar wacce wace ba tada gata? Ai ko miliyan biyar ni yamin kaɗan a jeran gidana." Sake baki Habi tai tana kallanta tace "Miliyan biyar? Asiya kanki kalau dai ko?" Wani mugun kallo ta mata tace "Banasan iskanci ke in bikinki yazo kice kin yafe kayan ɗaki ku zauna a tabarma, aikin kawai tun yaushe ma aka daina kayan ɗakin 700k? Na tabbatar ko mutanen kauye yanzu suma sun waye." Daga waje Habi ta juyo Inna tana ƙoƙarin haɗa murhu, ta mike tana gyara inda ta kwanta tana cewa "Su masu miliyan biyar ɗin rainan gas ne ke kuwa rainan itace ce ko gawayi sai ai sati ba'ai amfani dashi ba a gidan da kika taso." Ai da sauri ta mike tana neman jawo Habi, ganin haka yasa ta ruga waje da gudu tana ma Asiya gwalo wanda ba karamin ɓata mata rai yai ba. Kwafa tai tace "Zaki dawo wlh." Habi kuwa tana fita tai tsaki tace "Auren cin amana akewa zumudi haka, mutum sai karya kamar ɗan wani? Kawayenta har yau ba wanda ta taɓa bari yazo gidansu amma dan san a sani harta bisu ta sanar dasu zatai tafiya." Muryar Inna ce ta katseta "Habi shine ke baki ɗan kwanta ba zaki fito da safen nan?" "Ke kika fito bare ni Inna?" Ta faɗa tana ƙarasa was tare da ɗaukan abin tatar koko.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull