Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 31

Baqeer complete - Chapter 31

Baqeer complete Chapter 31: Baqeer complete Chapter 31. Tana barin wajen tela, Mariri ta nufa don taje ta nunawa Baqeer yadda style ɗin da ya zana mata…

3,251 words

Tana barin wajen tela, Mariri ta nufa don taje ta nunawa Baqeer yadda style ɗin da ya zana mata yayi da aka ɗinka, wani irin farin ciki take ji a cikin ranta don tana ganin kamar duk wasu matsaltsalun Baqeer ɗin sun zo ƙarshe idan har ya karɓi tayin tailor nan don ta lura kamar yawan damuwarshi ta ta'allaƙa ne ga zanen da ya daina yi yanzu bayan a baya shine komai na rayuwarshi. Haka ta ɗin ga zuba gudu a titi don ta matsu taga ya reaction ɗin fuskarshi zai zama idan yaga ɗinkin. Wani ƙayataccen murmushi ta saki don tasan dole ne ma ɗinkin ya burgeshi kamar dai yadda yayi mata. Tana tsayawa a ƙofar gidan Dada ta sunkuci ledar kayan ta fice tana ji kamar tasa gudu ko zata ganta gabanshi, sai da ta shiga soron gidan sannan ta daidaita nutauwarta ta koma yin takunta a hankali ta shiga tana yin sallama kamar bata so. Daga cikin ɗaki Dada ta amsa tana cewa "Muryar wa nake ji kamar Zainabu?" "Nice Dada" ta bata amsa tana nufar hanyar ɗakin. A zaune ta iske Dada tana shan kunun kanwa da aka aiko mata daga gidan maƙwabtan ta inda aka yi haihuwa. Zama tayi akan tabarma kusa da Dada tana gaisheta. Bayan sun gama gaisawa Dada ta tura mata kwanon kunun, girgiza kai Zeey tayi tace "Meye wannan ɗin Dada?" "Kunun kanwa ne aka kawo mini daga maƙwabta anyi haihuwa." Ɗan yanutsa fuska tayi tace "Kunun gyaɗa kawai nake sha Dada ko kunun tsamiya bana so ko da azumi idan aka yi a gida sai dai na sha tea ko Mummy tasa ayi mini kunun gyaɗa." Mayar da kwanon kununta Dada tayi ta ajiye tace "Shima Baqeeru irin wannan tsirfar ce dashi komai aka yi sai yace baya so yanzu ne ma naga yana karɓar duk abinda na bashi ko baya so ya tsakuri kaɗan ya ajiye sauran." Murmushi Zeey tayi tace "Ina yake nema Dada? Wurinshi nazo daga wurin tela nake nace bazan koma gida ba sai na kawo mishi ɗinkin daya zana mini ya gani yadda style ɗin ya fita sosai," ta zazzage kayan a gabanta tana ɗagawa Dada ta gani. "La'ilahaillallahu" Dada tace tana tafa hannu, "Wannan ai irin ɗinkin da Baqeeru ya zana miki ne rannan sak kwabo da kwabo kamar hoton na takardar aka yi, amma ni ɗin kin ku ne sai naga kamar ƴar tsana za'a sawa." Dariya tayi tace "Ke kuma Dada wace ƴar tsana? Kedai kice yayi tsaf zan shige cike." Kai ta jinjina tace "Ni mamakin ma yanda yai ɗinki nake, ko ya akai ya iya zanashi haka?" "Wallahi kuwa Dada, ai ko lokacin da nake kwatanta mishi ɗinkin ban ɗauka haka zai fita ba sai da ya zana naga ya fita fiye ma da yadda ni nayi tsammani."

Tashi Dada tayi da kayan a hannunta tace "Yana ɗakin shi yau tun safe bai leƙo waje ba ina ganin ƴan miskilancin ne suka motsa gama tunda ya gamu da larurar nan ya ɗauki miskilancin dole ya ƙaƙabawa kanshi, taso muje," ta cewa Zeey tana yin gaba. Tashi tayi tabi ta a baya sai dai suna zuwa ƙofar ɗakin taja ta tsaya a wurin taƙi ƙarasa wa ta shiga, sai Dada ce ta shiga ta sameshi a zaune da takardu a gabanshi yayi sketches na ɗinkuna da yawa tun daga kan riga da skirt har zuwa dogayen riguna. "Au ashe kace zane ka samu shi yasa yau naji ka shiru" Zeey ta jiyo Dada tana faɗa daga cikin ɗakin abinda yasa ta shiga ciki babu shiri don taga zanen da Dada ke cewa yayi, a karan farko kenan data taɓa shiga ɗakin. Tsayawa tayi tana bin sketches ɗin da yayi da kallo tana mamakin irin styles ɗin daya fitar. A mamakance tace "Ya Baqeer dama ka iya zana ɗinkuna ko kuwa dai yanzu ne ka fara?" Ta sunkuya ta ɗauki takarda ɗaya tana kallon style ɗin doguwar rigar daya zana. Ai dole ne ma ayi mata wannan ɗinkin don sosai ya tafi da ita. Kallonshi tayi tana murmushi sai aka yi dace shima ita yake kallo yana ganin yadda annurin farin ciki ke fita daga fuskarta kawai don tazo ta iskeshi yana zane sai kace wacce aka yiwa wata gagarumar kyauta. Ɗan turo baki tayi gaba tana ayyana yadda murmushi yake ƙara mishi kyau amma kullum ka ganshi fuska a gimtse kamar bai taɓa dariya ba. "Ba shiryawa mukai ba ɗinki na fa nazo na nuna maka yadda yayi kyau sai nazo kuma na tarar kayi sketching waɗanda suka fishi kyau ma." Sai sannan ya lura da kayan dake hannun Dada tana ɗaga mishi, sosai shima yaji mamakin yadda style ɗin ya fita. Yasan tun daa can yana da passion for ɗinki amma koda Zeey tace ya zana mata style ya dai jarraba ne kawai ba don ya ɗauka zai iya ba ganin ko normal zanenshi da yake yi ya jarraba yin su sau babu adadi amma kamar an share ƙwaƙwalwar shi ya kasaiyawa sai gashi a gwajin farko yayi zanen ɗinkin gashi kuma kamar an buɗe mishi ƙwaƙwalwa ne sai wasu zanen yake yi har ma ya fara tunanin jarraba zana ɗinkin maza.

Hannu ya miƙawa Dada ta bashi kayan ya ɗaga yana kalla sai kuma ya waiwaya ya kalli Zeey da ita ma shi take kallo. "Good!" yace mata a daƙile kama baya so, ita dai murmushi kawai tayi sai kuma ta janyo kujerar roba guda ɗaya dake ɗakin ta zauna. Dada dai ficewarta tayi ta bar musu ɗakin don haka suka kasance shiru kamar ba zasu yi magana ba. Zeey ce ta fara kawar da shirun ta hanyar cewa "Ya Baqeer sketches ɗinnan naka sun yi kyau sosai wallahi ko dai ka taɓa yin sana'ar ɗinki ne shi yasa abun bai baka wahala ba lokacin da nace ka zana min style?" Bai amsata ba sai cigaba da yayi da jujjuya kayanta da har yanzu suke hannunshi. "Shi kan shi tailor fa baka ga yadda ya yaba da ɗinkin ba don ma sai da nayi warning ɗin shi akan bana so ya ɗinkawa kowa watakila da yanzu style ɗin ya zama uniform." Sai sannan yace mata "What's there in it don an yiwa wasu irin ɗinkin ki?" Taɓe baki tayi tace "Nop! Gaskiya ni dai bana so gara kowa yaje ya nemi style ɗin shi amma ba nawa ba." "Umhm" kawai yace ya hau tattare takardun shi daya barbaza don dama a zaune yake akan katifarshi yana zanen don yafi jin daɗin yi a haka akan idan yana zaune akan wheelchair ɗin. "Kasan wani abu Ya Baqeer" ɗagowa yayi ya kalleta sai ta cigaba da cewa "Tailor ɗin nema yace wai na haɗaku please ka ɗin ga yi mishi sketches ɗin yana biyanka to na dai ce mishi sai nayi magana da kai duk abinda ka yanke zan faɗa mishi amma ni sai nake ganin why not ka karɓi tayin shi tunda dama can sana'arka kenan yin paintings in a way wannan ɗin ma kamar yin painting ne tunda dai duk zane ne amma me kake gani?" Tun kafin ma yayi magana Dada ta shigo ɗakin tana cewa "Me zai hana kuwa yayi Zainabu tunda dama dai sana'arshi ce ai ki faɗa mishi kawai zai yi babu wani ja." Kallon Dada kawai yayi yana mamakinta yadda kawai ta yanke mishi hukunci ba tare data jira jin ta bakin shi ba. Ɗan waiwayawa yayi ya kalli Zeey sai yaga shi ta zubawa ido tana jiran jin amsar bakin shi. "I don't think if I will do it, mutanen yanzu basu da amana nafi so komai zan yi yanzu ya zamanto ban haɗa sabgata da kowa ba" yace yana ɗaga kafaɗa, tunanin Bello da abinda yayi mishi ne kawai ya faɗo a ranshi don haka yaji tayin da Zainab ɗin tayi mishi bai kwanta mishi ba. "Ba zaka yi ba fa kace Baqeeru? To idan baka yi wannan aikin ba me zaka yi tunda dai ba wata sana'a ka iya ba face zanen?" "Zan je na koyi ɗinkin da kaina sai nake yi." Salati Dada tasa tana sallallami tace "Da wace ƙafar zaka taka keken ɗinki ki akwai keken guragu ban sani ba Zainabu?" Ta juya tana kallon Zeey. Dariya ce taso suɓuce mata sai dai yadda taga Baqeer ya haɗe fuska yasa ta haɗiye kayarta bata yi ba. "Akwai keken ɗinkin mai aiki da wuta ai Dada wannan baya buƙatar a takashi da ƙafa, zai iya yin ɗinkin bawani abu bane don yana da lalurar ƙafa kawai dai ina ganin Ya Baqeer ko na wani ɗan lokaci ne kayi aiki dashi in yaso daga baya idan ka koyi ɗinkin ka ƙware sai ka koma aikinka da kanka amma dai ya ka gani?" Ɗan jim yayi yana tunani sai kuma yaga yanzu ko tailoring school ɗin zai shiga ai dole sai da kuɗi don haka yaga gara kawai yayi accepting tunda dai ma zanen kawai zai a saya a wurinshi ba wai tare zasu yi zanen ba kamar dai yadda suka yi da Bello don haka yace "Okay."

"Yayyy" tace tana ɗan tsallen murna jin cewa yayi accepting. Kallonta kawai yayi yana mamakin yadda take yin abubuwanta kamar wacce bata da wata damuwa a rayuwarta. "In Sha Allah gobe zan ɗauko shi na kawo shi sai kuyi magana har ma ya ga sketches ɗin da aka yi," tace bayan ta gama tsalle-tsallen murnar da take yi....

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce* Da *Ayusher Muhd*

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA ARBA'IN DA ƊAYA*

{41}

Karfe goma sha ɗaya na safe Zeey ta gama shirinta tsaf ta fito cikin sabon ɗinkinta don haka nan taji kayan da take so ta saka kenan, tana so taga ya Baqeer zai yi idan yaga kayan a jikinta, ta dade a jikin madubi tana bin jikinta da ɗin kin da kallo, murmushi ta saki mai sanyi dan ta tabbatar wannan ɗin kin dan ita akai jiyake kamar ta samu guri mai mahimmanci a gun Baqeer. A ɗakin Mummy ta sameta tana shirya kayanta da aka kawo daga wajen wanki a cikin wardrobe. Kallonta Mummy tayi ta mata alama da tayi kyau sosai, murmushi tai tana ɗan juya mata ɗin kin, nan da ban Mumy kuma ta canza ganin alamar shirin fita tayi tace "Yau kuma sai ina? Kin dai koyi yawo Zeey, kusan kullum yanzu sai kin fita, wai shin ina kike yawan zuwa ne?" A ɗan shagwaɓe ta hau turo baki tana bin bango tace "Yawo kuma Mummy? Please ki bari kada wancan ɗan sa idon ya jiki yanzun nan sai yaje ya haɗani da Daddy ina zaman -zamana yasa a hanani fitar ma gaba ɗaya." Dariya Mummy tayi tace "To nayi shiru amma dai don Allah kada ki daɗe sannan kuma a rage yawan fitar nan haka nan please." Rungume Mummyn tayi tace "To Mummy ba zan daɗe ba ai I promise, sai na dawo." Tana fita shagon ɗinkin ta wuce don ko yau da safe sai da tailorn ya turo mata da saƙon text yana yi mata tuni wai kada ta manta yau ne zata kai shi wajen me zane. Koda ta isa bata fita ba sai ta tsaya a mota ta danna mishi horn kawai, shima da yake dama ita yake jira tun ɗazu yana ganin lokacin da tayi parking ɗin motar ya taso da hamzari ya fito. "Ranki ya daɗe sannu da zuwa" yace fuskarshi a sake cike da nishadi bayan daya ƙaraso wurin. Buɗe mishi gaban motar tayi sai dai ya mayar da murfin ya rufe yace mata "Ai ina ganin bari kawai na ɗauko babur ɗina sai na biyoki a baya ko?"Ɗaga mishi kai tayi alamun amsawa kawai dan dama kawai dan abun ya shafi Baqeer ne amna batasa mutane a motarta. Haka suka tafi tana gaba yana biye da ita a baya har suka ƙarasa gidan Dada. Fitowa tayi daga motar bayan ta rufe ne ta juyo ta kalleshi tace "Bari na fara shiga na sanar musu zan kiraka sai ka shigo." "To" kawai yace mata yana mai ɗokantuwa da son ganin mai zanen da kuma wasu style zanen da yayi don ko waɗanda Zeey ta nuna mishi jiya sosai suka tafi dashi. A tsakar taga Baqeer shida Dada, ita tana gefe tana sauraran radio shi kuma hana zaune yana zane suna hira sama-sama, sallamarta kawai waji yaji komai ya tsayamai dakewa yai bai dago ba sai dai bai iya cigaba da zanen ba. Dada ta fara lale lale, cike da fara'a dan tana kaunar Zainab sosai, kallan Baqeer tai tana kusa da Dada jnda take gaisheta tace "Sai a ganka ai kamar ba'a ganka ba." Dagowa yai suka haɗa ido, tace "Nida tailor ɗin ne." Dada tai caraf tace "In akai kamar ba'a ganki ba ai ni na ganki ko? Kinga share wannan dukum-dunkum ɗin, yi maza kice ya shigo." Kalmar da Dada ta haɗa Baqeer dashi ne yasa yai saurin kallanta, bata ko bi ta kanshi ba Zeey ta mike tana kunshe dariyar da ke neman kwace mata suna haɗa ido da Baqeer ta kira Sani a waya tace ya shigo. Da sallama a bakin shi ya shiga gidan sai ya tarar dasu zaune a tsakar gida sai Baqeer dake zaune akan wheel chair ɗin shi don ko da Zainab tazo ma anan ta iskesu da wasu sketches ɗin ajiye a gefenshi ga wani akan cinyarshi yana zanawa ita kuwa Dada tana ƴan kaye-kayenta a tsakar gidan.

Sosai Sani tela ya kalleshi yana mamakin wai dama gurgu ne mai yin zanen? Gashi dai tabbas yaga zahiri tunda gashi nan ma wani zanen ne akan cinyarshi yana yi, Allah mai iko. Hannu ya miƙe mishi suka yi musabaha kafin yaja kujerar daya gani a gefe ya zauna yana gaishe da Dada. Kallon Baqeer Zeey tayi tace "Ya Baqeer ga tailorn da ya ɗinka mini kayan daka zana, tunda ya gani yace na haɗa shi da kai kamar dai yadda na faɗa maka na kuma faɗa mishi dama bazan yi maganar kuɗin aikinka daga ni sai shi ba sai dai yazo na kawo shi wurinka kuyi magana." Gyara zama Sani yayi yace "Yallaɓai ina faɗa maka tunda na ɗora kayan Hajjaju akan IG bayan an ɗinka mutane ke damuna gashi kuma tace bata son kayanta su zama uniform" ya ɗan yi dariya sai kuma ya cigaba da cewa "Na tabbata idan nayi amfani da designs ɗin wurinka kamar dai yadda Hajjaju ta nuna min wasu jiya ba ƙaramin alheri za'a samu ba shi yasa ma nake so mu haɗa hannu waje ɗaya ka dinga yi mini zanen tunda Allah yayi maka baiwa ta nan ɓangaren ni kuma ina ɗinkawa sai mu tsara yadda zan dinga biyanka." Sai sannan yayi shiru yana kallon Baqeer yana jiran yaji me zai ce. Bai ce mishi komai ba har sai da ya gama zana takardar dake gabanshi sannan ya haɗata da sauran waɗanda ya zana ya miƙa mishi. Karɓa yayi yana kallon styles na garari irin waɗanda bai taɓa mafarkin gani ba, tuni fuskarshi ta washe da fara'a yana jin tamkar yayi fice a harkar ɗinki ya gama idan har zai na ɗinka irin waɗannan styles ɗin. Kallonsu yake yi yana ƙarawa ya kasa daina kallon sketches ɗin , ita kuwa Zeey kallon shi kawai take yi tana murmushi sai kuma tace "Ai na faɗa maka idan kaga designs ɗin shi sai ka ruɗe."

"Ai kuwa dai gashi nan na ruɗe don na rasa ma wanda zan fitar nace yafi saura kyau," yayi maganar yana ƙara ɗaɗɗaga takardun. Da ƙyar dai ya iya ajiye papers ɗin sannan ya kalli Baqeer yace "Yo yallaɓai akan nawa zaka bani?" Kallon inda Zeey take yayi sai yaga ita ma shi take kallo, gira ya ɗage mata irin ya dai sai ta taɓe baki ta kawar da kai tana jin haushin yadda take ɓarar da ajinta idan har tana zaune a gaban Baqeer bata iya kawar da kai bata kalleshi ba. Mayar da kallonshi yayi ga telan yace "Duk da ban taɓa sayar da zane na style ɗin kaya ba bana sayar da paintings ɗina at nothing less than 100k so nawa kake ganin zaka iya biya?" Baki Sani ya saki jin manyan kuɗin daya ambata, kallonshi yayi ya marairaice fuska yace "Haba Yallaɓai har dubu ɗari bai yi yawa ba, ina ma laifin dubu ashirin haka zuwa dubu talatin?" Wani miskilallen murmushi ya saki kafin yace "Anya kuwa ka shirya yin kasuwanci dani? Daga dubu ɗari ka dawo dubu ashirin, kaso ɗaya a cikin biyar na abinda nace fa kenan?" ya miƙa mishi hannu da nufin ya bashi sketches ɗin. Ƙara damƙe su Sani tela yayi yace "Haba Yallaɓai ai ba za'a yi haka ba, yanzu dai kayi mini ragi a yadda zan iya biya amma dubu ɗari tayi yawa akan kowanne zane tunda ba guda ɗaya zan karɓa ba." Kallon Zeey yayi yana so tasa baki Baqeer yayi mishi ragi sai dai yaga ita ko a jikinta kawar da kai gefe ma tana yin game a wayarta don a ganinta wannan ba maganarta bace tunda bata da wani sani akan harkar zane da yadda ake sayar dasu shi yasa bata saka musu baki ba ta ƙyalesu suyi cinikin a tsakaninsu. Ƙara marairaice fuska yayi yace "To nawa zan biya yallaɓai?" Jin da yayi Baqeer bai ce komai ba. Shima kallon Zeey yayi sai yaga hankalinta ma baya wajensu don haka ya cewa Sani "To ka kawo 50k each take it or leave it daga haka ba zan ƙara yi maka ragi ba" ya haɗe fuskarnan kamar wanda bai taɓa dariya ba don shi sam baya so a nemi raina mishi wayo akan sana'arshi. Ko da ba irin waɗannan zanen yayi ba a baya ai yasan nawa yake sayar dasu don haka yanzu ma babu dalilin da zai sa ya sayar da zanen shi a kuɗi ƙalilan, sannan mutane sau da dama sun iya tayin wulakaanci da nuna bakasan darajar abu ba, kowa kanshi ya sani ada farkon fara zanenshi haka mutane sukai ta maidashi wawa sai dai bayan yasan darajarsa ya canza.

"To Yallaɓai nagode, yanzu bari na zaɓi kaɗan idan yaso daga baya sai na ƙara. Hajjaju ko zaki taya ni zaɓe ne don ni nama rasa wanda zan ɗauka kowanne ba baya ba wajen tsaruwa,"ya ƙarashe maganar yana kallon Zeey. Karɓa tayi tana dubawa sai kuma tace mishi guda nawa kake so?" "A yanzu dai guda huɗu nake so idan yaso daga baya sai na ƙara zuwa na karɓi wasu tunda ma naga wuri."Guda huɗu da suka fi yi mata kyau ta ware ta miƙa mishi, hannu biyu yasa ya karɓa yana ƙara kallon waɗanda ta zaɓa din. Tabbas waɗannan styles ɗin idan yayi su zasu janyo mishi customers sosai yasan kuma In Sha Allah zai samu alkhairi a ciki. Godiya yayi wa Baqeer ɗin kafin yace "Yanzu dubu ɗari ce a jikina cash da zan kai banki ko zaka karɓa in yaso idan na koma shago sai na ciro maka sauran?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull