Baqeer complete - Chapter 30
Baqeer complete Chapter 30: Baqeer complete Chapter 30. Wani ɗan ihu Zainab ta saki tana cewa "Wow! Ya Baqeer haka kake da talent dama? Don Allah duba…
3,303 words
Wani ɗan ihu Zainab ta saki tana cewa "Wow! Ya Baqeer haka kake da talent dama? Don Allah duba yadda style ɗinnan ya fita kamar yadda na kwatanta mishi abinda teloli da yawa suka kasa yi shi a cikin ƴan mintuna yayi" ta miƙawa Salim takardar, karɓa yayi ya duba sai yayi murmushi don dai bai yi mamaki ba a irin baiwar da yasan Allah yayi wa Baqeer ɗin ta fitar da zane duk da ba zanen kaya yake yi ba. Fitowa Dada tayi daga ɗakinta tana cewa "Kai lafiya kuke yi mana ihu?" Itama sakin baki tayi tana kallon ikon Allah ganin yadda Baqeer yayi zanen ɗinki kamar dama can irin zanen da yake yi kenan.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar CE* *Da* *Ayusher Muhd*
*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA TARA*
{39}
Zeey cike da zumudi tace "Dada kalla ki gani?" Amsa tayi cike da mamaki tace "Baqeeru yaushe ka iya zanen ɗinki haka?" Kallon Zeey yayi kaɗan ƙasan ranshi yana jin wata irin nutsuwa, ashe dai yana da amfani? Ya ɗan kawar da kai yace "Ita ta faɗi ya take so ayi." Dariya Zeey tayi tana kallon Dada tace "Dada don na faɗa ai mai zanawa shine mai ƙoƙarin ko?" "Dukkanku dai kun yi ƙoƙarin kai Masha Allahu." Tayi maganar tana komawa ciki zuciyarta na wani irin sanyi da nutsuwa. Zeey ce ta kalli Baqeer ta ɗan karkatar da kai tace "Tukuicin aiki fa?" Kallonta yayi fuskarshi sam babu alamun fara'a yace "Ki bawa saurayinki." Yana kaiwa nan ya fara tura keken yana jin wani irin yanayi da bai taɓa ji ba, me yasa take karkatar da kai a gabanshi gashi tana neman ja mishi ciwo a zuciyarshi da yadda take bugawa da ƙarfi. Har ya shiga ciki Zeey tana kallonshi murmushi ya kasa barin fuskarta, wai saurayi? To wa kenan? Da yake ba shine a gabanta ba hakan yasa bata kula ba, sallama ta yiwa Dada tana jiyota daga ciki ta fito, wata irin nutsuwa take ji wacce ita kanta bata san daga ina take saukar mata ba, anan ta bar Salim don yace shi ba yanzu zai tafi ba. Kai tsaye wurin tailor dinta ta wuce, ta kai mishi dinki tace ya sayi atamfar da zata yi kyau da ɗinkin, don ita yawanci kayanta sai dai ko Mummy ta ɗin ka mata amma sam bata iya zuwa shopping ta sayi kayan mu na hausa ta kai a ɗinka don ita a ganinta babu abinda ya kai hakan ɓata lokaci da wahala, yanayin sa ne ya canza ya sake kallon takardar sosai yace "Hajiya waye yayi wannan zanen?" "Menene?" "Ai tun kafin a ɗinka ma hankalina ya tafi kai na tabbatar in aka yi ɗinkin nan tabbas zai yi kyau sama da yadda kike tunani." Murmushi tayi tace "Ka fara ɗinkawa sannan ni na kawo style ɗina ba kuma naso wasu su gani suce kayi musu irin shi, na dai yadda kayi tallan shagonka dashi amma ba ka ɗinka irinshi ba." Kuɗi ta bashi sannan ta fita hankalinta ya ƙara kwanciya jin yaba ɗinkin daya yi in har masu abu sun yaba alamu ne na komai yayi yanda ya kamata. Wayar Mummy ce ta shigo wayarta wanda hakan yasa ta gangara gefen titi ta ɗauka cike da shagwaba tace "Mummy na!" Maimakon Mummy ta amsa sai tayi ajiyar zuciya wanda hakan yasa jikin Zeey yayi sanyi, kashe wayar tayi kai tsaye ta nufi gida maimakon ta koma gidan Inna. Kabir ta gani a falo yana cin abinci ta jefa jakarta kan kujera tana tambayarshi inda Mummy take, wani kallo ya watsa mata yace "Sai yanzu kika tuna da ita sai da kika gama yawon gantalinki?" Tsaki tayi tace "Matsalarka kenan kai maganar arziki ma baza ayi da kai ba, tayi ɗakin Mummy da sauri, a kwance ta ganta cikin bargo hakan yasa ta ƙarasa da sauri tana bin ɗakin da kallo wanda mai aiki ke ta faman gyarawa, kallonta tayi wani abu yazo mata tace "Ɗan bamu wuri." Fita tayi hakan yasa ta ɗago Mummy, da sauri Mummy ta share ƙwallarta ta rungumeta tace "Baby kin dawo?" Idanun Zeey ne suka fara canzawa sosai nan da nan ƙwalla suka cika taf a cikin idon tace "wani yazo daga Ɗambatta ne?" Kai Mummy ta girgiza mata alamar a'a, Zeey baƙin ciki ne ya isheta ta goge ƙwalla tana sauke huci tace "Ba Daddy ya hanasu shigowa ba?" "In Daddy ya hana ni na isa na hana ne? Haka kuma rayuwar zata kasance?" Cikin takaici tace "Mummy please ki daina magana haka, sai yaushe ne zaki ƙwatarwa kanki ƴanci? Haka zaki zauna suna abinda suka ga dama? Kiyi hakuri Mummy tsautsayi ne yasa nima nace zanje wurinsu kwanaki na tuba bazan sake ba………" kuka ne yaci karfinta wanda ya hanata karasa maganar, Kabir ne dake tsaye jikin ƙofa shima tun dazu ranshi a ɓace yake yace "Mummy daga yau kema kar ki sake bari a buɗe musu ko gate ne sannan har Ɗambattan zan je wallahi enough is enough bama son akuyanci." "Akuyanci?" Mumy ta maimaita fuskarta a matukar ɓace, kai ya kauda kawai ya bar ɗakin don duk wanda zai taɓa Mummy to fa baza su yarda ba. Mummy ce tasa hannu ta ɗago Zeey ta rungumeta tace "Ya isa haka nan please ba gashi kun zo ba? Ni ku kaɗai kun isheni rayuwa." Hawayenta itama ta goge tana kallonta cike da tausayi sam basa shiri da mahaifiyarta sannan ga mutanen can na Ɗambatta da suke kara takurawa rayuwarta, ya zata yi ta sanyaya ran mahaifiyarta? "Mummy in dawo gida?" Kai ta ɗaga da sauri tana riƙeta, murmushi tayi tace "Zan yiwa Aunty Nabs magana tazo in kuma bata zo ba bazan ƙara bin ta ba nima." Cike da jin daɗi Mummy ta ɗaga kai tana sake rungume Zee rungumar da sai ka ɗauka wani ne zai ɗauke mata Zee ɗin. Waya ta yiwa Nabeela ta sanar da ita ta dawo gidan don Mummy bata jin daɗi, jin haka yasa tace zata zo itama, tana kashewa ta ƙira Daddy wanda yaje Abuja yau saboda wani taro. Yana ɗauka Mummy tayi saurin ƙwace wayar daga hannunta ta kashe tace "Zeey me kike yi haka?" "Sanar dashi zan yi yayi musu magana." Ido Mummy ta zaro tace "Baki san yanzu akan haka tashin hankalin da zai sake faruwa yafi wanda ya faru ba? Bafa wani abun bane ya faru sosai." Cikin ɓacin rai tace "Mummy please! Nifa bazan bar wani abu ya sameki ba yanzu kalli har kwalbar turaren wuta an fasa nan gaba in wani abun ya sameki fa?" "Babu abinda zai faru In Sha Allahu, ba dai gaki ga Kabir ba babu komai In Sha Allahu." Rungume Mummyn tayi tausayi na sake shiga ranta, dole ta kula da Mummy don bazata bari a cigaba da sa musu ita kuka ba da girmanta. Nan ta kira mai aiki ta gyara wurin don Zee ko gyaran gadonta ba yi take ba sanda taje karatu sai dai in ɗakinta taga ya gaji da datti ta kira cleaner ta mata deep cleaning amma sam bata son aiki bare shiga kitchen, taɓ ai iya kacinta da kitchen to fa ruwan zafi zata dafa a kettle ko kuma abinci zata yi warming a microwave haka tayi rayuwa a school nan kuwa ruwan zafin ma sai dai tasa a dafa mata. Ɗaki ta wuce ta kwanta tana jin zuciyarta har yanzu tana zafi, waya ta ɗauka ta kira Baqeer, yana zaune haka kawai yake sake auno Zee yana sake yin wani zanen ɗinkin mamaki yake yi yadda idea ta ɗinkin ke sake floating cikin mind ɗin shi, yana gamawa yaji wata idea ɗin ta sake zuwa, nan ya sake ɗaukan pencil ya fara, wayar Zee ce ta katseshi ya kalli sunan da yasa mata a hankali yayi smirking sannan ya ɗauka. Shiru yayi itama shirun tayi kafin tace "Raina a ɓace yake." "Why?" "Hmmm family issues." "Umm!" Gyara kwanciyarta tayi tace "Shikenan abinda zaka ce?" "Umm!" Baki taɗan turo tace "Mutum ba kara, tambayata ya kamata kayi ko am alright?" "And then?" Ta ɗan yi jim kaɗan tace "Sai nace maka eh." "And?" "Hmm sai ka tambayeni ina ina?" "And then?" "Sai ince ina gida." "And?" Shiru ta ɗan yi kafin tace "Sai na tambayeka ni kuma, me kake yi?" "And?" Cike da shagwaba tace "And ɗin me? Allah ni har kasa ma naji bana son kalmar." Shiru yayi tace "Ka tambayeni to." "Ai kin bada amsa." Shiru tayi can tace "Allah wayau akayi mini ban yarda ba a sako daga farko." Bai yi magana ba hakan yasa tace "Kaji?" "No!" "Allah in nayi fushi baza ka ƙara ganina ba, in baka yi mini magana ba naiy counting 5 bazan sake nemanka ba nima." Nan ta fara "5,4,3,2,1,1,1,1" Zata kashe yace "Okay!" Cike da takaici tace "Shiyasa ma budurwarka ta gudu ta barka." Tana kaiwa nan ta kashe wayar, kan gado ta cila ta don ita bata tauna magana ma take faɗa, haka Allah yayi ta komai ya fito bakinta faɗa take yi. Baqeer ne ya kalli wayar maimakon yayi fushi sai murmushi ya suɓuce mishi, idanu ya rufe yanayin yanda ta langwaɓar da kai dazu kawai yake hangowa, shi kam bai san meke kanshi ba. Zeey kuwa pillow ta cillar ƙasa tace "Allah nayi fushi."
***** Nabeela sai dare ta samu ta iso, Zeey da kanta ta kaiwa Mummy abinci a ɗaki, tana jinsu suna waya da Daddy kamar babu wani abu da ya faru da ita da rana, itafa ko aure tayi gaskiya bazata ɓoyewa mijinta komai ba dole yasan duk abinda ke faruwa ya kuma sanar da ita itama don bata son sirri a aurenta. Jin muryar Nabeela yasa ta leko tace "Aunty Nabs ina wurin Mummy." Shigowa tayi ta dubata sannan ta fito ta bar Zeey a ciki, ɗakin Kabiru ta nufa fuskarta ɗauke da murmushi, yana zaune yana game a PS5 ɗin shi da yake ɗakin shi nada girma sai akayi mishi sitting area daga gefe kaɗan, knocking tayi ya amsa sannan ta buɗe. A jikin kofa ta tsaya tace "Dama nayi tunanin game kake yi." Bai kalleta ba yace "Kin dawo?" Kai ta ɗaga tace "Kayi tunanin abinda na faɗa maka kuwa?" Kallonta yayi kaɗan ya ɗauke kai yace "Ba sai nayi tunani ba don its a big NO." "Ka tabbatar?" Yana kallonta yace "Yes!" Murmushi ta sakar mishi tace "Shall we make a bet?" Kallon mamaki yayi mata yace "Na me?" Tace "Na maganar mana, mu sake magana in 2months." Tana kaiwa nan ta juya, ɗakin Zainab ta fara shiga ta gyara sannan ta koma nata ɗakin, exams ne da ita hakan yasa ta ciro books ɗinta ta fara karantawa.
****** Yau Maryam tun safe ta tashi ta fara shiri, babu shakka yau duk yadda zata yi sai ta lallaɓa Baban Areef ya barta taje duba Ya Baqeer, cike da salonta ta shirya tun yana kan gado ta kwanta ta shige jikinshi, a hankali ta gangara ta fara yi mishi wasu salon wasanni da suka janye hankalinshi gaba ɗaya, wani irin nishi kawai yake saukewa yana gurnani, wani irin salo ta shiga yi mishi daya rikitashi nan da nan ya fita daga hayyacinshi, nan suka shiga nunawa juna ƙauna. Tare suka yi wanka ya rungumeta yana sumbatarta. Saman fuskarshi ta shafa tace "Bae please inje wurin Dada?" Kai ya ɗaga mata yace "Kije zan sanar da Baffa kawai dai ki dawo daidai lokacin ɗauko Areef daga school." Sumbatarshi ta sake yi tace "Haka zan je bazan riƙe musu komai ba?" "Fitowa yayi ya ɗauki wallet ɗin shi ya miƙa mata dubu biyar yace "Ki saya musu wani abu, nima zan samu lokaci naje na gaishe su." Murmushi tayi sannan suka shirya suka fito, breakfast ta haɗa suka zauna dukansu akan dining table, bayan sun gama ya shiga gaida Baffa nan yake ce mishi yana son kuɗi da zai riƙe a hannun shi, ganin babu kuɗi ya shigo gidan sai ya fito yazo wurin Maryam ya kalleta yace "Kuɗin da na baki ko zaki bani na bawa Baffa ke sai na tura miki ta account?" Mamaki ne ya rufeta tace "Ko shi zaka turawa ta account ɗin ni kaga wurin masu fruit ba kowa ke amfani da POS ba." "Bani please ai dubu uku ma yake so Baffa yace kema dubu biyu ta isheki." Kamar zata yi magana ta fasa don tasan komai ta faɗa komawa zai yi ya sanarwa Baffan amma in banda haka dubu me zata yi mata, haka ta ciro ta bada ita kuma ta riƙe dubu biyun, zuciyarta duk babu dadi haka ta ajiye Areef a makaranta sannan ta wuce gidan Dada bayan tasa yi kayan marmari ƴan kaɗan don ba zai yiwu taje musu gida hannu na dukan cinya babu wani ɗan alheri ba.
+******* "Lale-lale maraba da Maryamu Daso, yau kece a gidanmu da safen nan?" Maryam ta gaisheta tare da ajiye ledojin hannunta tace "Dada ni kam har yanzu ana yin tsame?" "Ana yi mana a gidan Talatu ko dai Areef zai yi kanwa ne?" Murmushin yaƙe tayi don ita kanta cikin take so ta samu amma har yanzu shiru, nan ta bawa wata yarinya data shigo wurin Dada 200 ta siyo mata, suka shiga ciki. Ƙofar ɗakin Baqeer ta ƙwanƙwasa, ya buɗe yana kallonta, wani sanyi ne taji ya ratsata ganin nutsuwa a tattare da Baqeer tabbas bata taɓa zaton zata zo ta ganshi haka ba ta ɗauka in tazo zata ga ya rame sai gashi ta ganshi kamar da harma yafi da samun nutsuwa a fuskarshi. Haka suka fito falo suna hira da Dada shi kuma yana daga gefe sai jefi-jefi yake saka musu baki, anan aka kawo tsamen suna ci ana cigaba da hira. Shi dai duk hirarsu ba itace damuwarshi ba so yake ya tambayeta game da kawarta Zainab, wacece ita? A ina suka haɗu? To amma ta ya zai fara tambaya? Dada ce ya kamata tayi maganar amma yaga sam bata da alamar yin hakan sai wani zancen ma da suke yi wanda shi duk ba shine a gabanshi ba. Ya tambayeta ne? Ko kuwa dai yayi shiru? To in zai tambaya yace me? Menene haɗinshi da ita da ya damu da sai yaji ita wacece?
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*
*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA ARBA'IN
{40}
Har Maryam ta mike zata tafi Baqeer bai iya tambayarta komai ba game da Zainab. Haka suka fito Dada ta rakota sai da zata shiga mota Dada tace "Maryam nikam ki mana godiya gun kawarki." Da mamaki Maryam ta kalli Dada tana ƙoƙarin bata amsa waya ya shigo cikin wayarta hakan yasa ta ɗaga tare da ɗagawa Dada hannu. Nan ta shiga mota ta bar gun. ****** Ranar da Zainab taje ta karɓi ɗinkinta ita da kanta tayi mamakin yadda style ɗin ya fita fiye ma da yadda tayi zato gashi kuma sosai ya dace da atampar da telan ya zaɓa mata, sai zuzuta haɗuwar kayan take yi tana jin daɗi. "Ai Hajiya idan kinga yawan mutanen da suka ce nayi musu irin ɗinkin nan wallahi zaki yi mamaki bare ma dana ɗora a shafin mu na IG da facebook baki ga yawan likes da comments ɗin da muka samu ba, sai dai haƙuri kawai nayi ta bawa mutane nace mai kayan tace bata son ganin irin style ɗinta a jikin kowa." Wata dariyar farin ciki ta saki tana jin daɗin yabon da kayan nata da ya samu, tana kuma daɗa jinjinawa Baqeer don shi ya fito da zanen style ɗin fiye ma da yadda ta kwatanta mishi, tana wannan tunanin ne taji telan ya ƙara cewa "Da zaki daure sai ki haɗani da wanda yayi miki wannan zanen Hajiya don naga ya iya tsara style ɗin ɗnkuna masu kyau dan kuwa nasan ba ƙaramin ciniki zamu samu ba." Kallonshi tayi tana jinjina abinda yace cikin ranta, tabbas idan Baqeer zai yarda yana daga zaune ya samu sana'ar yi tunda dama bai san wani abu ba bayan harkar zane watakila daga zanen kayan sai kaga ya koma wa harkar paintings ɗin shi cikin ƙanƙanin lokaci don haka ta cewa telan "Zan yi mishi maganar muji me zai ce amma fa kasan zaka yi mishi biya me kyau ne idan ya amince ko?" Ai tuni ya fara washe haƙora yana murna yace "Haba Hajiya me zai hana kuwa na biyashi idan har irin waɗannan styles ɗin yake zanawa da ba ko ina za'a iya ganin su ba, ai ko ace wasu sun kwafemu sun yi irin su to a wurin mu dai za'a fara gani kinga kuwa ko wannan ai riba ce a karan kanta bare kuma nasan zasu ƙara janyo mana customers." "Haka ne" tace tana mayar da kayan cikin ledar su. "To muyi maganar price tun yanzu yadda idan naje zan faɗa mishi, nawa zaka na biya akan kowane sketch?"
Tsayuwar shi ya gyara yace "Eh to ina ganin zan dinga biyanshi kaso ɗaya cikin huɗu na abinda na samu."Wani irin kallo tayi mishi "You're not serious at all, to zaka biya shi akan kowanne ɗinki ko kuwa a guda ɗaya? Kenan idan kayi ɗinki akan dubu ashirin dubu biyar ne nashi, bari kaga tafiyata don naga alamar ba da gaske kake yi ba, ka dai san ba kai kaɗai bane telana zan iya neman wani telan muyi ciniki ba sai na tsaya kana raina mini wayo ba," ta suri ledarta ta nufi ƙofar fita daga shagon. Da sauri ya dakatar da ita yana cewa "Haba Hajiya kada muyi haka dake mana, duka abun ai bana zafi bane, kawai tsayawa zaki yi mu daddale akan nawa zan dinga biya kinga idan na biya shi shikenan ni style ɗin ya zama nawa." Murmushi ta saki tace "To yanzu naji magana amma ina jin barin maganar price ɗinnan zamu yi har sai naje mun tattauna dashi don kasan fa harkar paintings yake yi zai fi kyau ma ya yanke kuɗin da kanshi don shi yasan a yadda yake sayar da kayanshi." "Amma Hajjaju style ɗin ɗinki daban painting daban ba zai yiwu ayi musu kuɗi iri ɗaya ba," yace mata don baya so aje a tsuga mishi kuɗi da yawa tunda yasan paintings suna da tsada sosai." Harararshi tayi tace "Duk ba zane bane kuma ƙwaƙwalwa ke ƙirƙirarsu to don me kuɗin su zai bambanta? Kai dai kada ka samu damuwa I assure you sketches ɗin da zai yi maka har matan gwamnoni sai sun nemeka don ka zama telansu, ai dai ka gani wannan kaɗai daka ɗinka mini yadda mutane suka yaba dashi." "Haka ne kuma Hajjaju, to sai na jiki dai kenan ko?" Tace "In Sha Allahu, kada ka samu damuwa."