Baqeer complete - Chapter 29
Baqeer complete Chapter 29: Baqeer complete Chapter 29. ****** Yau tun safe tayi wanka kai kace makaranta zata je, Zeey da aka sani da baccin safe amma yau…
3,359 words
****** Yau tun safe tayi wanka kai kace makaranta zata je, Zeey da aka sani da baccin safe amma yau ƙarfe bakwai tayi wanka, akwatinta ta buɗe bayan kanta ta shafa tana jin haushi bata wani kwaso kaya da yawa ba gashi tasan gobe dole ta koma don Daddy da kanshi ya kirata jiya yace ta dawo. Zazzage akwatin tayi ta fito da ragowar kaya kala uku da bata saka ba, ɗaya atamfa ce sai biyu laces, tunani tayi kamar Baqeer bai taɓa ganinta da lace ba hakan yasa ta maida atamfar ta fara duba ɗinkin laces ɗin, light brown riga da skirt ne sam bata son saka kayan da zai takura mata shi yasa bata sa kaya da skirt amma haka nan ta saka shi, turarenta ta fesa ta shafa mai da kwalli sannan ta ɗaura ɗankwali, cike da mamaki Nabeela dake kwance akan gado take kallonta, can ta kasa daurewa tace "Zeey ba dai wata ƙasar zaki babu labari ba?" Kallonta tayi tace "Wai kin tashi? Asibiti zani." Kallonta take da mamaki tace "Asibiti? Kina nufin duk shirin nan na zuwa asibiti ne?" Kafaɗa ta ɗaga mata tace "Nawa ra'ayin kenan." "Wai skirt ma kika sa? Kai kamar ma ɗinkin da Mummy tayi miki wanda taso kisa da taron da aka yi last year kika ce baza ki saka ba tunda skirt ne?" "To ko ma dai menene yau dai nasa zan tura mata da picture." Zeey tayi maganar tana duba agoggo. Ita gani take yi ma lokacin baya sauri "Karfe nawa zaki fita?" Nabeela ta tambayeta itama tana duba agoggo. "11am ne appointment ɗin." Nabeela bata san sanda ta miƙe zaune ba tace "11 shine kika shirya tun 8? Eh lalai wannan da alama dai zance zaku yi ke da likitan." Murmushi tayi don ita kam bata san me zata ce ba kuma, da ƙyar ta haɗo tea ta sha don sun yi da Salim 10am zasu haɗu.
***** Shi kanshi Baqeer yau da wuri yayi wanka ya gunguro kekenshi ɗaki yasa kaya, farar shadda yasa mara nauyi irin mai shara-shara ɗin nan, jin Dada tana ta fama a waje yasa ya fito, ganinta yayi tana surfa wake, yanayin fuskarshi ne ya canza yana kallonta yace "Dada me kike yi hakan?" Dariya tayi tace "Baqeeru ka fito? Ranar naji Zainabu na maganar ƙosai shine….." Ai bai san sanda ya katseta ba yace "Dada shekarunki nawa da zaki yi surfe? In tana so ki jira in tazo sai kuyi tare ko kuma in yara suka zo su tayaki, amma fisabillilahi menene hakan? Salon wani abun ya sameki kuma?" Ya ƙarasa maganar yana nufar inda take, amsar taɓaryar yayi yana kau da kai fuskarshi a ɗaure ya fara bugawa da yake ba iyawa yayi ba gashi a zaune sai turmin ke ta rawa, yanata dukan gefe, dariya tayi tace "Wai da gaske bari nayi inga ko zaka amsa ashe kuwa zaka amsan, ahh Baqeeru kaga shikenan matarka ta huta." Bai bata amsa ba sai suka ji sallamar Salim, kallon Baqeer yayi cike da zolaya yace "Shi kenan zamu fara sanar da mutane ana surfe a gidan Dada." Baqeer wanda idanunshi suka haɗu da Zeey dake shigowa kawai ya ɗan kau da kai, yanzu me Dada ta jawo musu wannan abun kunya har ina? Aga namiji babba kamarshi na surfe? Dada ce tasa dariya tace "Shi kenan ba kaga ni na huta ai, Zainabu wai ƙosai zan yi miki kafin ki dawo shine yake tayi, Baqeer ni kam an gama surfen ne? Naga ka tsaya." Kallon Zeey yayi kamar ita tayi maganar kafin ya kalli Dada kawai ya ajiye taɓaryar. Dariya tasa ita da Salim, nan suka fito Dada na zolayar shi har suka shiga mota. Baya ta zauna shi da Salim suna gaba, Baqeer kallonta yake son sake yi sai dai babu dama don tabbas gani yayi kamar yau tafi ko wace rana yi mishi kyau, to wai shi meke damunshi? Kada dai ka manta ƙawar Maryam ce. A jikin wani shago suka tsaya na ɗinki Salim ne zai amshi sako, Baqeer ne ya zubawa shagon ido yana kallon yadda suka yi kwalliya da ɗinkuna daga waje, sam hankalinshi ya tafi wurin kalin styles. Zeey idanunta na kanshi tana kallon yadda ya zubawa shagon ido cike da kokonto tace "Ya Baqeer naji ance zane kake yi, kana zanen kaya?" Waigowa yayi ya kalleta, idanuwansu ne suka haɗu da juna, idanun Zeey dake ɗauke da kwalli ya kalla, wani abu ne yake ratsa zukatansu wanda su kaɗai zasu iya kwatantawa a hankali yace "Haven't tried it yet amma ina ga I can do it, meya faru?" Ta ɗan yi murmushi kafin tace "Yauwa! Akwai ɗin kin da nakeso ne ni duk masu ɗinkin dana kaiwa teloli da yawa sun kasa yi mini abinda nake so am sure in kai ka zana zai yi." Zai yi maganar Salim ya buɗe ƙofar hakan yasa su yin shiru gaba ɗaya………
ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA TAKWAS*
{38}
Har suka ƙarasa asibitin babu wanda ya ƙara yin magana cikinsu sai Salim da jifa-jifa yake jefo musu hira ganin duk sun share shi yasa yaja bakin shi ya tsuke shima, cikin ranshi dai tunani yake to me ya faru a tsakanin su daga fitarshi da ya sakasu canjawa lokaci ɗaya har haka. Asibitin private physiotherapy clinic ne mai kyau da mahaifin Junaid ya buɗe mishi tun kafin dawowarshi ƙasar aka kuma zuba ma'aikata da kayan aiki masu kyau da inganci aka fara aiki tun Junaid ɗin bai dawo ba. Suna shiga cikin reception ta fito da wayarta daga cikin ƴar ƙaramar jakar hannunta tayi dialing number Junaid, tana fara ringing kamar wanda yake jiran kiranta ya ɗauka. "Hey babe, ya aka yi?" Ɗan yamutsa fuska tayi kamar yana ganinta jin ya ambace ta da babe, "Gamu mun ƙaraso muna reception."
"Ok, ku tambaya a nuna muku office ɗina sai ku shigo." Kashe wayar tayi ta mayar cikin jaka sannan ta ƙarasa wajen receptionist tayi mata bayanin abinda Junaid ɗin yace. Tashi tayi ta rakasu har ƙofar office ɗin sannan ta juya tana mamakin su kuma waɗannan ɗin su waye da suka shiga wajen chairman direct, ga dukkanin alamu dai VIP ne don ba kowa yake yarda ya gani ba. Sun shiga office ɗin da sallama, ya taso ya tare su yana murmushi. Hannu ya miƙawa Salim suka gaisa sannan ya bawa Baqeer hannun shima yana tambayarshi yanayin jikin shi, kamar baya so ya amsa mishi da 'lafiya' don haka nan yake jin takaicin Junaid ɗin bare daya lura da wani irin narkakken kallo da yake bin Zainab dashi. Wajen zama ya nuna musu Zeey da Salim suka zauna shi kuwa Baqeer yana zaune akan wheelchair ɗin shi dama, kallon ƙaton office ɗin Salim yayi yana jinjina tsaruwarshi da yadda aka kashe kuɗi wajen zuba kayan aiki a ciki, ya tabbata ba don Zeey ba basu isa su samu ganin Junaid ba bare har ace shi da kanshi zai ke duba Baqeer, to ai ko asibitin baya jin zasu iya zuwa saboda daga gani da ido ma an san ba wajen zuwan mai ƙaramin ƙarfi bane don zai yi muguwar tsada ko daga yawan kayan aikin daya gani kawai.
Kallon Salim yayi ya miƙa mishi wata takarda da yayi rubutu a jiki yace "Please abokina ko zaka je reception kayi musu magana a buɗe mishi file yanzu sai ka kawo min." Tashi yayi ya karɓi takardar ya fita. Sai sannan yayi wa Zeey magana yace "Ga alama dai yau nayi laifi tunda Zeey ta shigo ko kallona bata yi ba," yayi maganar yana sakar mata ƙayataccen murmushin shi mai tafiya da tunanin ƴammata. Harara ta watsa mishi haɗe da turo baki gaba ba tare data tanka mishi ba abinda ya ƙara ƙular da Baqeer don sai yaga shagwaɓa ce kawai Zeey ke yi mishi duk kuwa da bata buɗi baki tayi magana ba. Dariya ya saki yace "Hoo Zeey, wai don Allah da gaske fushi kike yi dani? To me nayi miki ne hum, faɗa min, kin san fa bana jurewa fushin ki please kiyi haƙuri ko ɗan murmushi ne kiyi min." Sai sannan ta ɗaga dara-daran idanunta ta kalleshi sai kuma taji kunyar gwasaleshi tunda dai tasan babu abinda yayi mata kawai dai tana tauna tsakuwa ne don aya taji tsoro, ita tasan Junaid da gaske yake son ta sai dai ita kuma she can't give him anything more than friendship bare a yanzu da take ƙalubalantar kanta da sabon yanayin data tsinci kanta a ciki, ba zata so Junaid ɗin ya zura jiki a sonta ba alhalin she cannot reciprocate his feelings bayan haka ma bai wani girme mata ba ita kuma tun asali bata taɓa jin sha'awar yin soyayya da saurayin da bai bata wasu shekaru da yawa ba. Murmushi ta saki tace "laifin me zaka yi mini, kawai dai i'm not in the mood ne." Tafa hannushi yayi yana dariya yace "Ashe kuwa yau za'a yi ruwa da ƙanƙara, dama akwai wani mood da zaki shiga ya hanaki surutu? Kece kuwa Zeey ɗin dana sani ko kuwa dai wata ce me kama da ita?"
Ta buɗe baki zata bashi amsa kenan Salim ya turo ƙofar office ɗin ya shigo don haka ta mayar da bakin ta rufe. Sai da ya karɓi file ɗin sannan ya juya ya kalli Baqeer daya cika yayi fam yake ganin kamar da gayya Zeey ta kawo shi wajen saurayinta suna soyayya a gabanshi, yace mishi "Ina fatan dai kana yin exercises ɗin kamar yadda na nuna maka?" A cunkushe yace mishi "eh" yana jin kamar ya janyo shi ya tsokane idanun nan masu yawan kallon mata (mu kuma muka ce masu yawan kallon Zeey dai ko Mallam Baqeer). Sai da yayi ƴan rubuce-rubuce akan folder ɗin sannan ya tashi ya zagayo wajen Baqeer bayan ya fito da wasu machines ya ɗora akan table, da taimakon Salim suka ɗora shi akan gadon da yake duba marasa lafiya sannan yaja labule ya rufe wajen saboda samun privacy, ɗaya daga cikin machines ɗin ya ɗauka yana daddana mishi akan ƙafafun nashi tun daga gadon bayanshi, haka yayi ta amfani da machina kala-kala a jikin Baqeer idan ya gama da wannan sai ya ɗauki wannan kuma har aka ɗauki wani lokaci mai tsawo, kafin kace miye wannan kuwa Baqeer ya haɗa gumi kashirɓan a dukkanin gaɓɓan jikin shi. Shi da kanshi yaji daɗi a jikinshi daga yadda treatment ɗin nasu ya kasance. Fitowa yayi ya barshi a wurin yana mayar da kayanshi don kafin a fara treatment ɗin sai da ya rage kayan jikin shi ya zama daga shi sai boxer short, wajen sink ɗin dake gefe guda daga cikin office ɗin ya nufa ya wanke hannayenshi bayan ya cire handgloves din ya zuba a dustbin sannan ya dawo ya zauna.
Har ya gama saka kayan yana tunanin ta yadda zai yi magana azo a taimaka mishi ya sauko daga kan gadon don yayi mishi tsawo ba zai iya daddafawa ya koma kan wheelchair ɗin tashi ba, jin shirun shi yayi yawa yasa Salim ya taso don yasan halin Baqeer ba zai taɓa cewa yana buƙatar taimako ba sai dai suyi ta zama a haka. Da taimakon Salim ɗin ya koma kan wheelchair ɗin Salim ya tura su zuwa gaban table ɗin Junaid a wannan lokacin kuwa hira suke yi da Zeey yana tsokanarta wai ba zai barta ta fita daga cikin asibitin ba sai yasa anyi mata allura don ya santa da tsoron allura tana kuka tun da can idan za'a yi mata sai anyi daga da ita, ita kuma tana cewa "Da kenan wallahi yanzu wuce nan na tsaya ina kuka akan allura" shi kuma yana cewa "A'a fa Zeey gara dai ki daina cika baki kada kizo kina jin kunya." "Allah ya sauwaƙe wallahi," tace tana murguɗa mishi baki. Wani abu Baqeer yaji ya tokare a makoshin shi, haka nan shi dai baya son ganin Zeey tana yiwa saurayin nan fara'a duk kuwa da bai san miye a tsakaninsu ba, bai san lokacin da ya saki siririn tsakin da a tunaninshi a cikin zuciyarshi yayi ba sai da yaga duk sun zuba mishi ido sannan yasan a fili yayi, kawar da kai yayi kamar bai lura da kallon da suke yi mishi ba ya kalli Salim da fuskar da babu ɗigo na fara'a ko kaɗan a ciki yace "Mu wuce ko?" Ɗaga kai kawai yayi alamun amsawa don haka nan yaji kamar Baqeer bai kyauta ba da yadda yake ta cika yana batsewa kamar wanda aka yiwa wani abu bayan duk ƙoƙarin da Zeey take yi na ganin ya samu lafiya abinda mahaifin da yake tutiyar yafi kowa son shi ya kasa yi mishi.
Kallon Zeey Salim yayi sai ta miƙe tana cewa "Thank you J, ka dai ƙi muyi maganar nan amma In Sha Allah ina komawa gida zan kira ka, please kada kace a'a" ta ƙarashe maganar tana langaɓar da kai gefe, shi Junaid ya fahimci maganar payment da yaƙi suyi ranar take yi mishi don haka yayi murmushi kawai yace "Waiting for your call with pleasure," yayi winking mata idonshi ɗaya. Takaici ne Baqeer yaji ya lulluɓe shi matsawa yayi kusa dashi ya ajiye wayarshi yace "Sorry ba kuɗi a hannuna ka riƙe wannan In Sha Allahu in na samu kuɗi zan kawo maka." Zeey ce tayi mishi alama wanda yasa Junaid yin murmushi yace "Kar ka damu, sabon asibiti ne sai muke trial na 30days, so after 30days in dai kazo you have to pay." Da mamaki Baqeer ya kalleshi Junaid ya nuna mishi wani flyer dake wurin wanda ya bawa Baqeer amsa, ganin da gaske yake yasa yace "Thank you" ya gara kekenshi da sauri ya bar office ɗin yana jin kamar zuciyarshi zata buga tsabar kishin da yake ji wanda tunda yake bai taɓa jinshi akan wani ba, da sauri Salim yabi bayanshi bayan ya yiwa Junaid godiya, Zeey ma tabi bayanshi suka fita tana jaddada wa Junaid zata kirashi idan ta koma gida. Bayanta yabi da kallo har ta fice yana sakin wani malalacin murmushi, har cikin zuciyarshi yasan yana son Zeey sai dai ta kasa ɗaukar shi da muhimmanci ita kallon aboki kawai take yi mishi gashi yaga alama shima wannan gurgun kamar son ta yake yi don yana lura da yadda yake harararshi a fakaice, shi dariya ma abun ya bashi don dai yasan idan har da gaske shima son Zeey ɗin yake yi to haukarshi kawai yake yi don kuwa babu abinda zai haɗata da nakasashen mutum, maza masu lafiya masu ji da class da kuɗi ma basu isheta kallo ba bare wani gurgu sai dai kuma deep down yana jin shakku na yadda Zainab ta ɗauki al'amuranshi da girma don shi dai zai iya cewa bai taɓa ganin Zeey ta damu da wani mutum kamar yadda ta damu da Baqeer ba.
***** Kamar yadda suka zo haka suka koma babu mai yin magana a cikinsu har Salim da a zuwa yake jansu da hira jefi-jefi. Motar na tsayawa a ƙofar gidan ta buɗe mota ta fice ta barsu anan Salim na kicin-kicin taimakawa Baqeer ya zauna akan wheelchair ɗin shi. Da fara'a Dada ta tareta tana cewa "Har kun dawo?" Zama tayi akan tabarma kusa da Dada tace "Wallahi kuwa Dada, mun daɗe ko?" "Kun yi sauri dai" Dada ta amsa mata tana ajiye flask ɗin data zuba mata ƙosai a gabanta. Buɗe flask ɗin Zeey tayi tana cewa "Kai Dada amma wallahi yau kin biyani, har na manta yaushe rabon da naci ƙosai." Ta ɗauki ɗaya ta dangwala yajin Dada mai ɗan karen daɗi ta kai bakinta tana lumshe ido. A daidai wannan lokacin Salim da Baqeer suka shigo, kallon flask ɗin gabanta yayi ya kawar da kai cikin ranshi dai yana tsegumin sai da Dada dai tayi mata ƙosan nan hankali ya kwanta. Gefe guda yayi da wheelchair ɗin shi a ƙarƙashin inuwar umbrella dake shigowa daga gidan maƙota. Salim ma wuri ya samu ya zauna yana cewa "Hajiya Zainab abun ƴar haka ce babu ko tayi?" Ƴar dariya tayi cikin jin kunya tace mishi "To Bismillah," Shima dariyar yayi yace "A'a ci kayanki ni bazan ci ƙosai yanzu da tsakar rana ba sai dai ban sani ba ko Baqeer zai ci."
Ɗaga kai tayi ta kalleshi sai aka yi dace shima kallonta yake yi a lokacin don haka a tare idanunsu suka shige cikin na juna. Wani irin kallo yake yi mata da ta rasa a wane aji zata fassara shi, ita ta fara janye idanunta ta mayar kan kwanon ƙosanta murya ƙasa-ƙasa tace "Idan zai ci gashi nan da yawa ai zai ishemu." Shi dai bai saka musu baki ba har ta gama cin ƙosan ta tashi ta wanko hannunta ta dawo ta zauna, sai sannan tace mishi "Yauwa Ya Baqeer zaka zana mini style ɗin?" Yi yayi tamkar bai jita ba kawai sai ya fito da wayarshi daga aljihu yana daddannawa. Haushi ne ya kama Dada don tana ganin yadda mafi yawan lokuta yake yiwa Zainab alhalin bata nufin shi da komai sai alheri don haka cikin faɗa-faɗa tace mishi "Kai kuwa dai Baqeer ban san irinka ba wallahi, Allah ya wadaran halinka na baƙar zuciya mai manta alheri, haba yarinyar nan binka take yi tana tsaye akan komai naka abinda take yi maka wani ɗan uwan na jini ma ba lallai ne yayi maka irin shi ba amma baka da abar wulaƙantawa sai ita, wallahi ka sake halinka don dai ba halin mutanen kirki bane wannan, ah to" ta tashi tayi shigewarta ɗaki ta bar su anan. Duk sai yaji babu daɗi don shi ba da nufin wulaƙanci yake yi mata hakan ba kawai dai mafi yawan lokuta bata samunshi a lokacin da yake cikin yanayi mai daɗi ne.
Ita kam Zainab bata daddara da sharetan da yayi ba cikin shagwaɓar da bata ma san tayi ba tace "Please mana Ya Baqeer" ta wani lanƙwasar da kai tana kallonshi fuska a kwaɓe kamar zata yi kuka. Sosai yaji shagwaɓar nan tata har cikin ranshi don haka ya kasa yi mata musu sai ma ce mata da yayi "Kayan suna wurin Dada," kamar baya so yayi maganar. "Yayyy" tace tana ɗan tsallen murna daga zaune tace "Amma ai zaka yi mini ko? Um?" Tana ɗan turo baki gaba irin na shagwaɓaɓɓun yara, sai yaga ta ƙara yi mishi kyau a yadda take yi kamar wata yarinya wacce bata da wata damuwa a rayuwarta don haka bai san lokacin da ya saki murmushi ba har kumatunshi na lotsawa ciki ba. Dariya tasa tace "laaa Ya Baqeer yau kai ne kake yi mini murmushi?" Da sauri Salim ya kalleshi jin abinda Zeey tace, duk ƙoƙarin shi na ganin ya gimtse fuska sai ya samu kanshi da kasawa don haka kawai ya kawar da kai bayan ya gallawa Salim harara. Shi dariya ma ya bashi don haka ya ɗaga hannayenshi sama in surrender yace "nifa babu ruwana, ah to". Bin bayan Dada tayi ɗakinta ta karɓo kayan zanen da yace suna wurinta, miƙa mishi tayi ta zauna tana kwatanta mishi yanayin style ɗin da take so. Kallonta kawai yake yi yadda take kwatance kamar wata malama a gaban aji tana bayar da darasi. Idanunshi ya rufe ya ɗora pencil ɗin akan takardar, ga mamakinshi sai yaga yadda Zainab ta kwatanta mishi style ɗin tar a cikin kanshi, da sauri ya buɗe idon shi ya ɗauki paper ya fara yin zanen sauri-sauri. Tunda ya fara sketch ɗin bai ɗago ba sai da ya gana ya miƙa mata yace "duba ki gani haka yayi?"