Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 28

Baqeer complete - Chapter 28

Baqeer complete Chapter 28: Baqeer complete Chapter 28. Ƙyaleta tayi tasha kukanta ya isheta sai da tayi shiru don kanta sannan Umma tace "Sarai kin san…

3,109 words

Ƙyaleta tayi tasha kukanta ya isheta sai da tayi shiru don kanta sannan Umma tace "Sarai kin san halin mahaifinku Hadiza amma ba zaki yi haƙuri kamar yadda kowace mace take yi ki zauna a ɗakin ki ba, kun dai fi so kullum sai kun janyo mini ɓacin rai?" Wani hawayen Hadiza ta share cikin rawar murya alamun kowane lokaci zata iya cigaba da kukan tace "Umma ya zan yi? Wallahi duk haƙurina mutumin nan baya gani sannan kuma saboda Allah Umma a ina ake yin aure babu abinci, kullum fa haka yake ficewa ya bar mu da yunwa daga mu har yaran sai dai kowacce tasan yadda zata yi ta ciyar da ƴaƴanta ni kuma kin sani ba wani abu gareni ba, jiya na tashi ko ƙwaya bani da ita a ɗakina kuɗin da nazo kika bani ya ƙare a awon abincin da zamu ci da ƴan sauran buƙatu, jiya haka su Hassan suka tafi makaranta basu ci komai ba ni kuma ganin har lokacin tashin su ya kusa na rasa yadda zan yi yasa na ɗauki wata tsohuwar akwatin shi ta garwa na kaiwa ƴan gwangwan suka saya sannan na samu nayi mana abincin da muka samu muka ci, to wai akan ya dawo na sanar mishi da yadda aka yi na ɗauki akwatin da ba ma amfani yake yi da ita ba shikenan ya dinga surfa ruwan bala'i yana yi mini zagin tsame nama har yana cewa wallahi ba zai yarda ba sai na biyashi akwatin shi ko na bashi kuɗin da aka sayar ni kuma nace bazan bayar ba tunda ai hakkin shi ne ya ciyar damu amma ya fice ya bar mu babu abinda zamu ci don nayi ƴar dabara shine akan haka zai ci mutunci na, wallahi Umma har marina yayi da ace na tsaya ma nasan har dukana sai yayi ni kuma shi yasa na taho gida don wallahi na gaji da auren nan da babu abinda nake tsinta a cikinshi sai tarin damuwa da baƙin ciki," ta ƙarashe maganar tana sakin wani marayan kuka.

Ita kanta Umma kasa riƙe hawayenta tayi tana jin tausayin irin rayuwar da suka tsinci kansu a ciki ita da ƴaƴanta kowanne akwai tarin ƙalubalen dake dabibaye da rayuwarsu sai dai kuma hakan ba shine zai sa ta goyawa Hadiza baya ta kaso aurenta ba alhalin zaman gidansu ma ba daɗi gare shi ba don haka cikin tausasawa tace "ai kuwa dai haka nan zaki koma ki cigaba da haƙuri, sanin kanki ne zaman gidan nan a yanzu yafi ƙarfinki tunda dai kina jin abinda mahaifinki yace ba zaki zauna mishi a gida ba ba tare ma da ya bari yaji abinda kika zo dashi ba, dole kije ki cigaba da haƙuri ko don ƴaƴanki ki kuma nemi abun yi da zai riƙe ku ke da ƴaƴanki tunda dai kin san halin mijinki ba mai ɗaukar nauyin gidan shi bane sai dai ku kuyi mishi."

Cigaba tayi da kuka jin Umma tace sai dai ta koma alhalin zaman gidan gaba ɗaya ya fice mata akai, idan ace akwai abinci ma sauran buƙatu ne ba'a ɗauke musu da da sauƙi sai taje tayi ta haƙuri amma saboda Allah ta ina zaman aure zai yiwu babu abinci don haka tace "Yanzu Umma haka ma zaki ce na koma bayan idan na koman ma ba canjawa zai yi ba?" "Haƙuri fa zaki yi Hadiza ki koma amma ba zai yiwu na barki ki zauna a gidan nan ba alhali mahaifinki yace sai dai mu haɗu mu bar mishi gidan gaba ɗaya, ni kuwa da girmana bazan je na zaune wa Dada ba bayan ga Baqeer can na kai mata tana riƙe dashi, sana'ar dai ita zaki nema dole don haka sai kiyi tunani anan unguwarku me kike ganin mutanen wajen sun fi buƙata ko kuma me nene ba kuda yawaitar masu shi kinga daga nan sai mu san wacce irin sana'a zaki yi tunda dai akwai kuɗin kujerun nan a wajena sai ayi amfani dasu ki kafa jarin."

Ajiyar zuciya kawai Hadiza take saukewa tana share hawaye, ita dai a sonta Umma ta barta ta zauna a gida sai dai kuma bata ga alamar Umman zata ƙyaleta ba, gara ma taje ta nemi na kanta yadda zata fi ƙarfin wulaƙanci har a wurin mijin ma don yadda yake yi mata cin kashi baya yiwa kishiyarta haka saboda ita tana da abun hannunta bata neman komai a wurin shi sai ma shi da yake lallaɓawa tana bashi rancen kuɗi. Tashi tayi ta ɗauke Aydah da tayi bacci a ƙasa ta gyarawa su Hassan da tun shigowar su suka kwanta bacci kwanciya sannan ta nemi wuri kusa da ƴaƴanta ta kwanta, tasan dai dole tayi tunanin abinda zai fisheta kafin gobe ta tattara ta koma can gidan.

*****

Tunda ya shige ɗakin yake tunanin abinda ya kamata ya fara da zai taimake shi da mahaifiyar shi da ƴan uwanshi sai dai kuma duk sana'ar da tazo ranshi sai yaji anya kuwa zai iya irin wannan sana'ar alhalin shi ba ƙafa ce dashi ba a yanzu, matsalar da aka samu ita ce tun farko da zane ya buɗe ido kuma shine kaɗai abinda ya tsaya ya koya don yana tuna wani lokaci acan baya da yaso ya koyi sana'ar ɗinki Baba ya hanshi yace me zai yi da wani ɗinki shi da yake da sana'ar shi a hannu, yadda Allah ya bashi baiwar iya zane kuɗin da zai samu a harkar bai ninka abinda zai riƙa samu a ɗinki ba, yana ji yana gani ya haƙura da wannan burin nashi ya mayar da hankali akan zanen to yanzu gashi inda rayuwa ta kawo shi, bai iya komai ba sai wannan zanen da baya jin a yanzu zai iya ƙara riƙe pencil da sunan painting ko da za'a saka mishi bindiga a kanshi kuwa.

Wajen kayan zanen shi ya nufa ya ciro takarda da pencil ya saita su yadda zai ji daɗin yin zane, pencil ɗin ya ɗora akan takarda ya rufe ido yana so yayi picturing abinda zai zana kamar dai yadda yake yi a baya sai dai jin ƙwaƙwalwar shi yayi ta zama blank kwata-kwata sai yaji tamkar bai taɓa sanin yadda ake yin zanen ba, yayi-yayi ya jarraba yin zanen nan amma ya kasa. Ji yayi gaba ɗaya zuciyarshi ta ƙuntata, ta yaya abun da tun yana yaro ƙarami ya ƙware akai yanzu tashi ɗaya lokaci guda zai gudu ya bar shi tamkar bai taɓa sanin yadda ake yi ba, gaba ɗaya sai ya zama frustrated yayi jifa da takardar ya watsar da pensiran yana sakin huci. Kanshi ya kama ya rirriƙe yana jin kamar yayi ta sakin ihu ko yaji wani sanyi ko yaya ne a cikin ƙirjinshi da yayi mishi wani irin nauyi yana yi mishi zafi.

Ƙara janyo kayan da yayi watsi dasu yayi ya sake ɗaukar pencil wai ya ƙara gwada zana ko kaza ce amma duk yadda yayi tunanin ta yadda zai fara ya kasa, haka nan dai yayi ta ƙirƙirar abinda zai zana har ganye sai da yayi tunanin ya zana amma ya kasa, sai ya samu ƙwaƙwalwarshi kamar an shafe mishi sanin yadda ake yin zanen ne kawai, wata irin ƙara ya saki yana jin rashin amfanin kasancewar shi a raye tunda ba zai iya yiwa mahaifiyarshi da ƴan uwanshi maganin kukansu ba, shine babba kuma shine gatansu duk wata taƙamarsu dashi suke yi to yanzu gashi ba zai iya yi musu maganin komai ba shi yasa sam baya ganin amfanin rayuwar shi. Da hanzari Dada ta shigo ɗakin tana cewa "haba Baqeeru, ayi bawa shi dai ya kasa tawakkali kullum sai ka ɗaga mini hankali ka ɗagawa uwarka da bata da wani tunani sai naka, ai ko baka ɗauki dangana don kanka ba kayi don mahaifiyarka". Kallon tsakar ɗakin tayi taga yadda ya watsar da kayan zanenshi tace "Dole ne sai kayi zanen ne? Ba sai ka nemi wata sana'ar ba tunda dai Allah bai hana maka rai da lafiyar da zaka tashi ka nemi na kanka ba, haba. Banda dai ubanka ya kwaɗaita maka son zanen nan ni banga wani abu da mutum zai tsinta a cikin shi ba wai sai kaji an saka maƙudan kudaɗe an sayi takardar da wani ƙato ya taƙarƙare ya zana. Ai ina ga kwashe kayan zanen zan yi idan baka ganin su ai baka ce dole sai kayi ba alhalin duk ranar da ka gwada yin zanen bama zama lafiya, ƴar walwala da nutsuwar da ka samu duk sai subi su ruguje." Tana sababi tana tattare kayan haka ta kwashe su ta mayar ɗakinta tayi musu kyakkyawan ɓoyo don bata jin zata ƙara barin Baqeer ya gansu ma bare yace zai ɗauka ya gwada yin zane bayan ta lura abinda ke ƙara dagula nutsuwa da kwanciyar hankalin shi kenan.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*

*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA BAKWAI*

{37}

Da kallo yabi Dada tabbas tsanar kanshi duk ta isheshi, babu shakka shi ba kowa bane in babu zane, wace irin rayuwa yayi da bai dogara da komai ba sai shi? Idanunshi ne suka yi jaa yana tuno lokacin da yana yaro ko wasa zai fita waje Baba hanashi fita yake yi akan dole ya koma ɗaki yayi practicing painting tun yana shekara huɗu yake yi haka zai yi ta yin shirme amma Baba na yaba mishi a hankali yazo daya ƙara wayau ya fara zane abubuwa kamar dabobi da yake Allah ya bashi baiwa ga kuma Baba dake sakashi yi a koda yaushe yasa tun yana ƙarami hannunshi ya ƙware da yin zane, da ya shiga school kuwa bama a competing dashi don kowa yasan zanenshi ya fita zarra, a kuma nan makarantar ne suka haɗu da Bello wanda basu san unguwarsu ɗaya ba, yanzu shi me zai yi? Me ya iya? Hawaye ne suka cika taf cikin idanuwanshi nan ya haɗiye wani abu daya makale mishi a maƙoshi, yana jin zuciyarshi na wani irin zafi. Idanuwanshi ya rufe, kalaman Zeey ne ke sake yi mishi yawo a ƙwaƙwalwa, dole yasan abun yi ba zai bar mahaifiyarshi da ƙannenshi cikin tashin hankali haka ba. Wayarshi ya ɗauka ya kira Umma. Ringing uku ta ɗauka ganin sunan Hadiza wanda ya tabbatar mata da Baqeer ne, jiki a sanyaye yayi sallama, ta amsa cike da jin daɗi, muryarta na rawa tace "Ya jikin?" Cikin dakewa yace "Da sauki Umma, komai lafiya?" Ta sake daurewa tace "Komai lafiya Baqeer kai ne abun ji ai." Zuciyarshi ce ta sake karyewa yace "Kada ku damu dani komai lafiya, ya wurin su Hadiza da Maryam?" Umma tayi ajiyar zuciya tace "Suma duk lafiya ƙalau, Hadiza ma taso zuwa nace ta jinkirta don muzo tare." Wani yanayi ya tsinci kanshi a ciki ganin Ummanshi na ƙoƙarin ɓoye abu saboda shi, ya zai yi? "Baba fa? Ya bar takura muku?" "Kar ka damu da wannan Baqeer shima yanzu ya daina, ya Dada?" Yace "Lafiya kalau." Shiru suka yi kamar basu saba ba, jin alamun kukan Aydah yasa tayi saurin yi mishi sallama ta kashe wayar. Saman goshinta ta shafa don kanta wani irin ciwo yake yi wanda take jin har wajen idanunta yake tabawa. Haka ta kwanta sai dai har wajen ƙarfe uku bata yii bacci ba, tashi tayi kawai don tayi alwala ganin ya fiye mata kwanciya tana saƙe-saƙe. Zabura tayi a waje ganin mutum na ƙoƙarin rungumar bango, sai kuma ya girgiza kai yace "Sorry Roshni na tsaya ƙyam salute!" Ya dan buga ƙafa yana daidaita tsayuwarshi, kafin yayi hanyar shiga ɗakin Kamalu, Umma tsorata tayi ta fara neman son yin ƙara taji yace "Shhhhh! Malama nine." Kallonshi tayi da mamaki tace "Kamalu? Me kake yi a waje a daren nan?" Cike da takaici ya ƙaraso yace "Wannan kuma ba damuwarki bace ke da kike waje yanzu me kike yi?" Mamaki me ya hanata magana don daga yanda yake magana ma ba wai kanshi ƙalau bane, ba dai zargin da ake yi mishi na yana shaye-shayen kayan maye da gaske ba ne? Tana ganinshi ya shiga ɗaki. Alawala tayi ta koma ɗaki, a iya saninta Baba da wuri yake rufe ƙofa to tabbas ta katanga ya sauko kenan, Innalillahi lallai Kamalu bashi da kai dole a dage da yi mishi addu'ar shiriya, tasan yanzu tana yin magana za ace din taga ɗanta ya rasa ƙafa ne take neman ƙaƙabawa Kamalu laifi.

***** Wayarta ta ɗauka tana jujuyata, jibi zasu je asibiti wurin Junaid sai dai tun yanzu tana ji zuciyarta baza ta iya haƙuri da rashinshi ba, ido ta runtse tare da jan bargo ta lulluɓe fuskarta, Nabeela ce ta girgiza kai tace "Allah Zeey akwai abinda ke yawo akan ki, anya kuwa." Juyowa tayi dukanta tace "Aunty Nabs ya zaka yi ka cire mutumin da kake tausayi daga ranka?" Kallonta tayi tace "Ya zaka yi dai ka cire wanda kake so a ranka?" Tsaki tayi tace "Ke fa matsalarki kenan sam baki fahimta to mu bar maganar." Sauka Nabeela tayi ta fito daga ɗakin hakan yasa Zeey sauke ajiyar zuciya, waya ta ɗauka ta kira Salim nan ta sanar dashi zuwan da zasu yi asibiti yace to zai zo da safe, tace "Yauwa bani number shi zan tura mishi text na abubuwan da zamu tafi dashi." Salim yace "To shikenan." Zata yi magana taji muryar mace tana cewa "Waya kake yi?" Zee cike da tsokana tace "Wacece?" "Habi ce ƙanwar Asiya saƙo na kawo mata." Da mamaki tace "Asiya?" Gyaran murya yayi yace "Budurwar Baqeer tada." Mamaki ya kama Zeey tace "Me kake yi tare da kanwarta?" "Saƙo kawai zan bata na juya, sannan ita babu ruwanta kinga duk abinda ya faru ma daga wurinta muka ji." Murmushi tayi tace "Anya kuwa saƙo ne kawai?" Yasa dariya yace "A'ah fa ba komai tsakaninmu." Nan suka yi sallama ya tura mata number Baqeer. Sa wayar tayi a ƙasan pillow ta daki saman goshinta tace "No babu abinda zan yi, Zeey calm down and take a deep breath." Nan ta fara breathing in and out tana cewa "Ba komai a raina, tausayi ne, tausayi ne, da kuma zumuncin Maryam." "Yaushe kika je gidan Maryam? Yaushe kika kirata ko a waya? Yaushe ma kika nemeta?" Kai ta girgiza ta fito daga ɗakin da sauri babu kowa a falon, baki ta taɓe sam Inna babu ruwanta da ita, ƙofar ɗakin Inna taje ta ƙwanƙwasa. Suna zaune ita da Nabeela suna hira suna dariya, kallon Inna tayi a shagwaɓe tace "Inna a dai dinga yi mini kara." "To ai ko ban miki ba kina yiwa kanki." Zama tayi kusa da ita tace "Hirar me kuke yi ni aka warenj?" "Ba ji zaki yi ba, ke ni kam me yasa kike da son jin abinda bai shafe ki ba." Shiru tayi don tasan Inna dama baƙar magana zata faɗa mata, ga mamakinta shiru ɗakin ya koma, jiki a sanyaye ta miƙe ta bar musu ɗakin tunda babu amfanin zaman nata. Wayarta ta kalla ta kalli number Baqeer, taɓawa tayi nan da nan wani abu yazo mata hankali a tashe ta ɗauki wayar zata kashe, tana kai hannu zata kashe shi kuma ya kai hannu ya ɗauka, ido ta runtse da sauri ta kara wayar a kunnenta. Baqeer wanda ke zaune a ɗaki wayarshi ce tayi ƙara, kallon sunan da yayi saving number yayi 'ƙawar Maryam' kallon wayar ya sake yi yana mamakin ashe tana da numbershi? Kenan tasan lokacin da ya kirata? Nan ya ɗauka yana son tabbatar da itan ce ko a'a don in haka ne lallai yayi abun kunya. Zeey ganin ya ɗauka yasa ta zaro ido tare da sauke ajiyar zuciya, shiru yayi shima don bai san me zai ce mata ba. A hankali tayi gyaran murya tace "Hmm nace na kira Salim." Yace "Toh!" Toh? Ta maimaita a ranta sannan tace "Na sanar dashi maganar zuwa asibitin shine nace zan kiraka don na faɗa maka ka taho da takardun da aka baka a Aminu Kano." Ga mamakinta yanzun ma toh kawai yace, takaici ne ya kamata tace "Toh toh bye." Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta kifa kanta akan pillow sai kuma ta ɗauki wayar tayi saving ɗin numbershi da 'Toh' Baqeer kuwa tana kashewa ya kalli wayar yace "Meye abun fushi to? Ba dai nace toh ba?" Ya ajiye wayar yana mamakin fushin na menene.

****** Washegari Umma ta bawa Hadiza dubu uku a cikin kuɗin nan sannan tace "Kije in muka yi magana da Maryam sai ki samu ko injin markaden ne ki siya ki fara sana'a don zamanki haka babbar illa ce." Ita dai Hadiza taso ta sake kwana ɗaya amma babu halin yin hakan don ita kanta tsoron Baba take kada ya dawo yazo ya tarar da ita ga kuma karatun yara da babu yadda zata yi, takaicinta ɗaya ko waya bai yi ba balle ma ya nuna yayi dana sanin abinda yayi. Haka ta fito riƙe da yaranta idanunta fal da kwalla, Jamila ce ke shara a tsakar gida, ganin Hadiza yasa tace "Dije tafiyar zaki yi?" Kallonta tayi dao sam bata ma san me zata ce mata ba, Abu ce ta leƙo tace "Dije to kinga dai kafin ki maida ku zawarawa daga ke har uwar taki gwara ki lallaɓa ki riƙe aurenki da daraja, in kuma ba gidan Maryam zaki tare da zama ba ayi abun kunya." Mamakin kalamanta ne yasa Hadiza kallonta tace "Dadinta dai kema kin taɓa yin yajin." Baki Abu ta saki, ai kuwa kamar an tsungunota cike da masifa tace "Uban wa kike faɗawa haka? Ni? Eh lallai kam wuyanki ya isa yanka, lallai yarinyar nan, ba dai zugoki aka yi a ɗaki don kiyi mini rashin kunya ba ko?" Ita dai Umma tana jinsu bata san magana don maganar ma ƙara tada husuma zai yi, daga ciki tace "Hadiza bana son shirme fa ki wuce ki tafi gidanki." Fita tayi ranta a matukar ɓace, ta tsani cin kashin da suke yi musu kwanan nan don kawai Ya Baqeer ya samu nakasa shikenan sai a maidasu kamar ba yaran gidan ba? Ita dai ko ina babu daɗi, wannan wace irin rayuwace?

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull