Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 27

Baqeer complete - Chapter 27

Baqeer complete Chapter 27: Baqeer complete Chapter 27. Ɗan jim yayi kafin yace "ai shikenan tunda Bellon kika zaɓa, kin dai tabbatar kina son shi ko?"…

3,358 words

Ɗan jim yayi kafin yace "ai shikenan tunda Bellon kika zaɓa, kin dai tabbatar kina son shi ko?" Ɗaga kai tayi alamun amsawa tana murmushin farin cikin ganin Baban bai bata wata matsala ba ya amince, sai Innarta ce tace "amma Mallam sai ka biye mata bayan kasan yaron nan Baqeer yayi wahala da ita ba kuma shi yace ya fasa ba sai ita da taƙi shi saboda kawai Allah ya jarabce shi da larura". Sai ce mata yayi "to in banda abunki shi da ya nakasa yanzu wane batun aure zai yi? Ai sai a bawa mai lafiya dama tunda kuma Allah ya kawo mijin ai ba zamu ƙi aurar da ita ba saboda wani dalili can". "Haka ne" kawai tace ba don ta gamsu da bayanin da yayin ba. Haka nan ya koma wajen iyayen Bello ya karɓi kuɗin aurensu nan dai aka tsayar da magana aka sa rana watanni uku masu zuwa. To sai muce Allah ya tabbatar da alkhairi....

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*

*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA BIYAR*

{35}

Da mamaki Zeey ke kallon motar da aka yi parking a harabar gidan, in har ba wai tayi kuskure ba motar Mummy ce, to yaushe tazo? Tambayar data faɗo mata cikin rai kenan, da sauri ta ƙarasa ciki fuskarta ɗauke da fara'a don tasan Mummy missing ɗinta ne yayi mata yawa, harta shiga falon bata ga kowa ba, hakan yasa ta nufi ɗakin Inna kai tsaye don daga cikin falon tana iya jiyo magana na fitowa daga sama-sama don dama ta gaji da takurar Inna gwara ta bita su koma gida gashi kuma ta samu Junaid zai dinga taimakawa Baqeer. Hannu tasa zata ƙwanƙwasa taji muryar Inna na cewa "Ke sam kamar ba uwa ba baki san me ya kamata ba? Wannan wace irin rayuwa kika ɗaukar wa kanki? Kenan ke baki san abinda ya kamata ba? Ko ce miki aka yi ita ba....." Ƙofar ta buɗe wanda hakan yasa su kallonta da sauri, ajiyar zuciya tayi zuciyarta na tafasa idanunta a kansu tace "Ni kam don Allah sai yaushe zaku daina faɗa a kaina? Wannan wace irin rayuwa ce?" Mummy ce ta taho tana neman riƙeta ta ɗaga mata hannu tace "Mummy please ki bari, ni yarinya ce? Ko kuwa shi kenan ni ban isa nace zanyi abu ba? Gidanku ne fa ba wai wani wurin naje ba amma sai kin nuna kamar ana wahalar dani?" Inna ce tayi tsaki tace "Ba sai tai tayi ba ni dai na faɗa ban gayyaceki ba don haka babu wanda zai zo ya ɓata mini rai a cikin gida don haka ki tattara ki bita." Takaici ne ya rufe Zeey kawai ta wuce ɗakin su da gudu, kan gado ta faɗa tana kallon Nabeela dake zaune tana karatu cike da shagwaɓa kamar mai shirin yin kuka tace "Aunty Nabs wai haka zamu zubawa Mummy da Inna ido? Shi kenan su daga sun haɗu sai faɗa, ba zaka taɓa ganinsu suna hirar arziƙi ba? Wannan wace irin rayuwa suka ɗaukarwa kansu? Ƴa da uwa kamar wasu maƙiyan juna? Kuma babban takaicina duk a kaina suke wannan abun?" Jiki a sanyaye Nabeela ke kallonta tace "To ya zamu yi dasu? Ni shi yasa muna gaisawa na bar musu falon don nasan dama raina ne kawai zai zo ɓaci." Kanta tasa a saman pillow cikin takaici tace "Ni wallahi na gaji da wannan abin nasu haba! Da zan bi Mummy mu koma gida amma yanzu Allah babu inda zani." Ta faɗa tana juya baya zuwa saitin Nabeela tana tunanin wannan rashin jituwa ta Mummy da Inna. Ita dai Nabeela kai kawai ta girgiza ta cigaba da karatunta don bata shiga wannan case ɗin. Mummy ce ta shigo ɗakin tana yiwa Nabeela alama da tayi shiru har ta ƙaraso ta zauna kusa da Zeey, hannu tasa ta ɗan mintsineta kaɗan, Zeey ta juyo da sauri rungumeta tayi tace "Mummy please!" Nabeela ce ta tashi ta bar musu ɗakin hakan yasa Mummy shafar bayan Zee tace "Naji ya isa am sorry shikenan?" Kallonta tayi tace "Bana son ku dinga faɗan nan, especially a kaina don Allah!" Jinjina kai tayi cike da fahimta tace "Naji to tashi mu wuce." Ajiyar zuciya ta saki tace "Please Mummy ki bar ni zuwa jibi, abubuwa ne a kaina wallahi gaba ɗaya ni kaina ban san meke damuna ba, watakila faɗan Inna zai sa na dawo hayyacina." Cike da mamaki take kallonta tace "Har akwai wani abu da zai hanaki sukuni a duniyar nan Zeey? Dad ɗinki yafi sonki a gida kema kin sani kaf duniya yafi ji dake sama da komai." Fuska ta tsuke sosai tace "Kema kin san zolaya kike Mummy ni gaba ɗaya……." Ta maida kanta kan cinyar Mummy cike da damuwa tace "Ban san ya zanyi ba sam haushin kaina da damuwar halin da nake ciki ya isheni." Shafar kanta tayi tace "Koma menene kar ya dameki, a duniya mahaifinki ko me kike so zai tsaya miki ki samu, haka duk wani abu da bai fi ƙarfina ba kema kin san zan tabbatar kin samu abun nan, don haka ki sanar dani koma menene, na gaji da ganinki cikin wannan halin." Tace me to? Bayan ita kanta bata san mazaunin da take ba? Mikewa tayi ta zauna a gaban Mummy ta lanƙwashe ƙafa a kan gado tace "Mummy mutum ne ya shiga raina, komai nake yi da tunaninshi nake yi bayan na kuma san bani da haɗi dashi to cut it short ma ni dashi enemies ne wanda am sure ko sunana yaji ya ganeni kallona ba zai sake yi ba, sai dai ban san meke damuna ba." Da mamaki take kallonta tace "Son shi kike yi?" Kai ta girgiza da sauri tace "No of course not! Sannan ba ma lafiya gareshi ba kina ganin tausayi ne yasa nake jin hakan?" Shiru tayi tana nazari na wajen minti uku kafin tace "Ban san meke ranki ba Zeey sai dai nasan koma menene na baki damar kiyi abinda hankalinki ya kwanta dashi, a koda yaushe ina bayanki." Rungumeta tayi tace "Mummy I love you so much, zan yi ƙoƙari nayi sorting tunanina kafin jibi in na dawo zan sanar dake komai." Kai ta jinjina cike da gamsuwa sannan tace "Kuɗi fa kina bukata?" Kai ta girgiza tace "Har yanzu wanda Dad ya bani ban ma ci ko rabi ba." "Bari na wuce." Saukowa tayi daga kan gadon suka fito falo, har yanzu Inna bata fito ba da alama Nabeela na wurinta don suna iya jiyo dariyarsu ita da Nabeela daga falon, Zeey na mamakin wannan abu a koda yaushe Inna bata fushi da Nabeela amma baka taɓa ganin fara'arta da Mummy. Haka Mummy ta wuce ita kuma ta koma ɗaki, zuciyarta na tunanin ko Baqeer yana can yana exercise ɗin kuwa? Haka kawai sai taji murmushi ya kamata.

****** Washegari…….

Umma tana gugar kayan Baqeer ragowar da aka bari a gidan tana so ta tattara ta samu taje ta ganshi, ita dai fatanta Allah yasa ya barta taje, tana mamakin yadda duk kwanakin da Baqeer yayi a gidan Dada har yau Badaru bai tambayi ina aka kai shi ba bai kuma tambayi lafiyarsh ba, ita sam dama bata damu da sai dole yazo ɗakinta ba amma a ƙalla soyayyar da yake nuna wa Baqeer bai ci ace ta gushe lokaci guda ba. Kamar daga sama taji ance "Hadiza? Uban me kike mini a gida har da ƴaƴanki da ƙatuwar jaka?" Garin razana da Umma tayi bata san sanda dutsen gugar ya ɗan shafeta ba, da sauri ta ajiye a gefe tunda na gawayi ne ta fito cikin sauri tana addu'ar Allah yasa ba Hadizanta bace yake magana akai. A tsugune taga Hadiza tana share ƙwalla tana gaida mahaifin nasu. A fusace ya nuna mata hanyar waje yace "Wallahi tun kan ranki ya ɓaci ki tashi ki bar mini gida, bana son haukar banza da wofi, bazan aurar da ƴara ba sannan su dawo mun gida da jaka don wannan jakar ko ban tambaya ba nasan ta yaji ce, ko ƙarya nayi?" Hawaye ta share tace "Baba don Allah ka tsaya ka saurareni wallahi auren nan sam……" "Kina sake magana zan sallami uwarki kuje can ku ƙarata, yau naga shirmen banza da wofi ni dama yanzu na cire rai da yaran Fatima amma babu ƙatuwar macen da zata dawo mini gida bayan ta cinye kayan gara da kayan ɗakin da na kashe kuɗi nayi mata." "Ai dai gidan mahaifinta ne ko? To in ma komawar ne ba dai yau ba, don kuwa babu inda zata". Cike da dakiya Umma ctayi maganar duk kuwa da irin faɗuwar da gabanta yake yi. Salati Abu ta saka tana tafa hanu tace "Fatima? Wai Mallam kike yiwa magana haka gatsal? Ba tarbiyya babu biyayya? Tab lallai kin riƙa, wannan ai tarbiyar da take amfani da ita kenan shi yasa aka korota." Nan da nan kuwa Badaru ya sake tunzura yace "Ki kwashi shirginki kibar mini gida kema, sai kuje can kuyi yawin tare tunda iskancin naku ya isa." Umma bata tanka mishi ba tasa hannu taja Hadiza da ƴaƴanta suka shiga ɗaki tasa makulli ta rufe, suna jiyoshi yana zazzaga masifa amma babu wanda ya tanka a cikinsu sai Abu dake ta sake tunzurashi, Jamila mamaki duk ya rufeta wai yaushe Abu ta kile har haka? Bayan aurenta ne ta koya mata maida martani? Umma suna shiga ta kalli Hadiza dake ta kuka ga Aydah a bayanta itama kamar tasan me ake yi kawai kalle kake take yi ga ƴan biyu da alama bacvi ma suke ji, kuka sosai take yi Umma tayi shiru ita ma tana matsar ƙwalla a fakaice, wannan wani irin bala'i ne.

***** Kamalu dake ta shiri zai fita ya fito yaga Baba na zabgawa Hadiza faɗa shi abun dariya ma ya bashi yayi waje yana fito don abinda babu ruwanka daɗin kallo gareshi. Salim ya hango tsaye jikin mai baron sayar da yalo, kusa dashi ya ƙarasa yana tafiya yana cigaba da fito har yazo inda yake ya kalleshi yace "Kana dai da kuɗin yalon ko ba sata kazo yi ba?" Cike da takaici Salim ya kalleshi kawai ya kauda kai, Kamalu ne ya kalli mai yalon yace "Ka tabbatar ya baka kuɗin ka don ɓarayi ko a ina suke sai sun nuna halinsu." "Wai ni kam Kamalu meye damuwarka dani?" "Damuwata ka fita hanyar Roshni yanzu ma can zani zance ko baka ga gayun da nayi bane? Irin babban yaro da babbar yarinya ba wai kai maloho ba, sannan ka sanar da abokinka yazo ya kwashe tsohuwar shi da ƙanwarshi dan tsoho ya sallamasu." Gaban Salim ne ya faɗi hankali a tashe ya riƙoshi yace "Me kake nufi?" Fizge rigarshi yayi ya nunashi da yatsa yace "Wallahi kaji na faɗa maka ka shiga hankalinka dani inba haka ba na fasa ma baki." Yana kaiwa nan ya ɗauki yalo ɗaya babu alamun zai biya kuɗin yayi gaba, haka Salim ya biya kuɗin haɗe da nashi, hankalinshi kasa kwanciya yayi tunda Baba na gida yasan bai isa yaje gidan ba don haka dole ya kira Baqeer ba don yaso ba. Baqeer na zaune a ɗaki yana ta gwada exercise ɗin da Junaid ya koya mishi, ajiyar zuciya yayi a fili yace "Kamar wani yace ta kawo mana saurayinta har gida." Sai kuma yayi shiru tunda yasan taimakon shi aka zo yi, shi dai sam ya rasa me yasa zuciyarshi ke sake hango mishi Junaid da Zee tsaye kusa da juna, tsaki yayi ya cigaba da exercise ɗinshi, jin wayarshi na ƙara ya ɗaga da sauri ganin Salim ne. Tun daga yadda Salim ya amsa mishi sallamar yasan akwai matsala, jiki a sanyaye yace "Salim wani abu ya faru ne?" Kamar yace a'a sai dai yasan ba lokacin ƙarya bane in wani abun ya samu su Umma fa alhalin ya sani? Cike da sanyin jiki ya sanar dashi abinda Kamalu yace. Hankalin Baqeer ba ƙaramin tashi yayi ba nan da nan idanunshi suka canza kala sosai, wayar ya kashe a fusace ya fara tura kekenshi yana jin zuciyarshi na wani irin zafi, har ya gama sanin meya faru in dai Hadiza ce tayi yaji "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" abinda zuciyarshi kawai ke faɗa kenan, matsalar nan dai ta kuɗi ce yanzu kam ko aikin ƙarfi ne tabbas zai yi in dai zai fitar da ƴan uwanshi daga halin da suke ciki, wani yanayi yake ciki mai wuyar fassarawa, sam bai ji kiran da Dada ke kwaɗa mishi ba ganin yana tura keke yayi hanyar waje, ita kuma ganin bai dawo ba yasa ta ɗauka fitar da yake yi kwanan nan ita ce yake son sake yi, hakan yasa ta koma ta cigaba da aikinta tana cewa "In zaka fita ai ka sanar mini banda dai Baqeer kai ma halinka sai kai." Baqeer huci kawai yake yi, yau tana daga cikin rana mafi muni da wannan rashin ƙafar ta janyo mishi don gashi a titi amma bai san me zai yi ba.don duk hannun da yake ɗagawa babu mai adaidaitan daya tsaya mishi, waigawa kawai yake yi idanuwanshi na sake yin wani jaa, takaicin wannan rayuwar duk ta gama isarshi. A hankali motar ta tsaya a gabanshi, kallon motar kawai yayi yasan ta wacece don kuwa ya ganta a ciki kwanan nan, sauka daga titi tayi tare da yin parking idanuwanta kawai ta samu suna zubar da ƙwalla, ta fito zata kawo ma Dada irin abin motsa jiki data sayawa Baqeer a daren jiya kawai ta hangoshi a titi, ita da tayi niyyar bawa Dada ta koma ba tare da ta ganshi ba sai gashi a titi gwanin tausayi, share ƙwallarta tayi sannan ta fito daga motar, bata ce komai ba har tazo kusa dashi, hannun keken ta baya kawai ta riƙe ta fara turawa, yanzu kam ta tabbatar akwai abinda zuciyarta ke auna mata akan Baqeer don sam idanunta neman cigaba da zubar da ƙwalla suke yi sai ƙoƙarin maidasu kawai take. Shi kanshi Baqeer tunda ya ganta ya kasa magana, har wannan lokacin da take turashi kasa magana yayi, sai da suka bar kusa da titi yace "Zan iya." Bata tanka shi ba ta cigaba da turawa har suka shiga wani kwana da zai sada su da gidan Dada. "Zan iya!" Baqeer ya faɗa cikin yanayi na jin haushin rayuwarshi, yanzu kam ya tabbatar yasan dalilin da yasa Asiya ta gujeshi. Tsayawa tayi a ta bayanshi tace "Meya faru?" Wani abu ya hadiya zuciyarshi na zafi yace "Ba komai." Cikin wata kasalalliyar murya tace "Ya Baqeer haka zaka cigaba da rayuwa?" Damm gabanshi ya faɗi, Ya Baqeer? Yaji tasan sunanshi amma haɗashi da Yayan na menene? Don tana ƙawar Maryam? To amma damuwa dashi fa? Ko bai waiga ba muryarta cike take da tausayin shi. Zeey kuwa ji take yi ina ma zata san yanda zata yi taga ya miƙe? Bata son ganinshi cikin wannan halin, zuciyarta zafi take yi…… Waigowa yayi ya kalleta itama idanunta ta sauke cikin nashi, idanunsa sun yi jaaa ita kuma idanunta ciki suke taf da ƙwalla dake ƙoƙarin saukowa saman kuncinta, wani yanayin kallo suke yiwa junansu ko wane da abinda yake ayyanawa a cikin ranshi.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*

*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA SHIDA*

{36}

Shi ya fara kawar da kanshi yana ƙoƙarin danne abinda yake ji yana neman taso mishi. Cikin dabara tasa hannu ta ɗauke ƙwallar data taru a cikin idanunta tana kawar da fuskarta daga kanshi itama tana mai jin kunyar dogon kallon da suka yiwa juna, hannu tasa ta cigaba da turashi har suka isa gidan Dada kowa da abinda yake saƙawa a cikin zuciyarshi. Sai da suka isa ƙofar shiga gidan sannan ta saki keken ta gewaye shi ta shige cikin gidan ta bar shi anan, bin bayanta yayi da kallo yana mamakin yadda take neman shiga cikin rayuwarshi ta ƙarfi don a yanzu in har bai ganta ba sam baya jin daɗi. Tana shiga Dada dake zaune ta tadda a waje tana gyaran waken da zata yi musu fate, tana ganinta ta fara yi mata lale maraba fuskarta ƙunshe da fara'a don tayi wani irin sabo da Zainab ɗin da idan ta kwana biyu bata zo ba zata yita cigiyarta tana jin kewarta. Itama murmushin ta saki duk kuwa da bata cikin yanayi mai daɗi ta soma gaisheta. Hannu tasa tana tayata gyaran waken tace "Yau gidan shiru Dada, sai ke kaɗai?"

Kafin Dada ta buɗe baki ta bata amsa har ya gurguro kekenshi ya shigo gidan, bin bayanshi suka yi da kallo har ya shige ɗakinshi ba tare da ko kallonsu yayi ba, wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Zeey ta saki tana jin wannan baƙon yanayin yana sake ziyartar ta, taɓe baki Dada tayi tace "Ashe yawon naka ba mai tsawo bane, ai ni a yadda naga ka fice na ɗauka yau ma sai na ganka."A surutu irin na Zeey a yau sai ta samu kanta da kasa amsawa Dada duk hirar da take yi mata har Dadan ta tambayeta "Lafiyarki ƙalau kuwa ƴar nan?" A ɗan firgice ta kalli Dada tace "Me kika gani?" Don duk a zatonta ko ta fahimci halin da ta samu kanta a ciki ne. Girgiza kai kawai Dada tayi tace "Ganinki nayi ba a yadda na saba ba shi yasa na tambaya ko ba kya jin daɗi ne?"

Dariya tayi duk don ta kawar da tunanin Dadan tace "Da a yaya kike ganina?" "A yaya nake ganinki kuwa banda a yadda na sanki, sam ba'a raba fuskarki da walwala da fara'a gaki da yawan son barkwanci da hira yau kuwa duk kin yi wani sukuku dake tamkar ba ke ba shi yasa kika ji ina tambayar ko ƙalau kike."

Ƙoƙarin danne wani abu da taji yana neman taso mata tayi cikin muryar dake ɗan rawa tace "Lafiyata ƙalau Dada kawai dai ƴan maganar ne basa kusa ina jin shi yasa kika ganni a hakan." "To Allah ya kyauta muku, kema kin koyi irin na Baqeeru kenan haka nan ana zaune dashi lafiya-lafiya gabaki ɗaya kuma sai kiga ya birkice sai kace wani mai jinnu." Dariya ta saki tace "Kai Dada, Ya Baqeer ɗin ne mai jinnu, maza dai yaji ki wallahi babu ruwana." Dariya ita ma Dada tayi tace "Yo sai me idan yaji ni, ko a gabanshi ma sai na faɗa tunda dai ba tsoron shi nake ji ba." "To shikenan ni dai babu ruwana, ato." Bata wani jima sosai ba ta tashi ta yiwa Dada sallama ta tafi, cikin zuciyarta ji tayi kamar ta leƙa ɗakin shi ta ƙara ganinshi sai dai kuma tayi wa kanta faɗa tace ki leƙa ɗakin shi kice mishi me? Don haka ta wuce ba tare da ko kallon ƙofar ɗakin tayi ba. Shi kuwa har ta bar gidan yana jikin ƙofa yana sauraren su duk da rabin hirar ba jinta yake yi ba sai dai jin tana dariya yasa yaji wata irin nutsuwa na saukar mishi.

*****

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull