Baqeer complete - Chapter 26
Baqeer complete Chapter 26: Baqeer complete Chapter 26. ***** Gidan su Junaid ta nufa bayan sun yi waya bai dade ba sai gashi ya fito, tunda ya shiga mota…
3,240 words
***** Gidan su Junaid ta nufa bayan sun yi waya bai dade ba sai gashi ya fito, tunda ya shiga mota ya zuba mata ido yana jin ƙaunarta na shiga mishi rai sosai, kallonshi tayi itama tace "J kallon ya isa haka nasan baka saba ganina da atamfa ba duk shine." Ido ya lumshe sannan ya buɗe, a kyau bai kai Baqeer ba amma da yake ɗan gayu ne shi sosai mai kuɗi a haka sai kaga ya fishi, sai saje daya tara a fuskarshi dake ƙara mishi kyau, girman ido ya ɗan rage irin yanda yake jan hankalin mata yace "Zeey you just look different, sai nake jin kamar yau na soma saninki." Ido ta ɗan juya kaɗan tace "Junaid please kada ka sakani dariya ba wani different kawai dai ka ganni ne bayan shekara of course dole kaga na canza." Mota ta tada tana cewa "Ni dai Allah yasa baka ma Mamy magana ta ba." "Guess?" Harararshi tayi tace "Ya Allah ban san ya zan yi da kai ba." "Amincewa kawai zaki yi muyi aure shikenan komai yayi daidai." Murmushi tayi tace "Me nace maka?" "Sai wanda in kika ganshi zuciyarki bata nutsuwa, sai kinji butterflies na yawo a cikinki in ya matso kusa dake bla-bla-bla ba dai har yanzu yarintar na nan ba?" Kafaɗa ta ɗaga tace "Call it whatever you want ni dai haka nake ra'ayi." Idanunshi na kanta yace "Kin san in na matso kusa dake you will definitely feel it?" "Problem ɗin shine ni bazan bari ka matso ɗin ba sannan inka matso ma abotar ta ƙare daga yanzu." Dariya yayi abinda yasa yake son Zeey kenan bata shakka ba kuma ta magana don kaji dadi abinda ke ranta kawai take faɗa.
***** Baqeer wannan karon shine karo na biyar daya duba agogon hannunshi, tun jiya Dada ke cewa zata zo bai kulata ba gashi har huɗu da rabi babu ita ba labarinta, ba dai haushi taji ba akan rannan ya tafi ya nuna bai san nemanshi taje yi ba? To lokacin ai ba laifinshi bane tunda shi bai san me zai ce mata ba? Ko dai ta fahimci bata buƙatar su a rayuwa ne shi yasa ta cire su? To shi menene nashi? Sumar kanshi ya shafa yana tunani duk ya rasa me yasa hankalinshi da tunaninshi suke kan yarinyar, yana jiyo Dada tana hira da yaran dake yawan shigo mata shi sam wannan ba shine a gabanshi ba, rayuwarshi duk ta zama babu daɗi haka kawai ya fara jan kekenshi yana gyara ɗakin, kallon agogo ya sake yi biyar saura minti goma yanzu kam ya tabbatar ba zuwa zata yi ba hakan yasa ya ɗauki wayarshi kawai ya kunna karatun Qur'ani yana saurare idanunshi a lumshe. Kamar daga mafarki yaji Dada tace "Lale lale tun ɗazu nake jiranki ashe kina tafe." Sautin karatun ya rage sosai tare da nutsuwa don yaji ko itan ce tazo. Zeey ce ta rungume Dada tace "Hajiya Dada kwana biyu ne fa baki ganni ba amma duk kin yi rashina." Kunnenta ta ɗan jaa kaɗan wanda yasa Zeey yin ƙara tace "Dole inje gidanku na roƙa a bar mini ke ko a bani ke na bawa jikana." Ido Zeey ta buɗe tace "Wa? Ba dai ni ba?" "Akwai jikokina sai dai ba a Kano suke ba." Dariya kawai tasa tace "Dada kin yi mishi maganar kuwa?' "A'a yana ɗaki kin san halinshi ai tambayata zai yi wanene, kawai dai nace mishi zaki zo yau." "Hmm shiru yayi ko?" Dada tana murmushi tace "Kin san hali ai." Dada ce tayi gaba ta kamo hannun Zeey suka shiga ciki, ƙofar ɗakin ta ƙwanƙwasa sannan tace "Baqeeru?Idonka biyu?" Idanunshi ya sake runtsewa sannan ya buɗe yace "Umm!" Ƙofar Dada ta buɗe, Zeey tana jingine da bango ta juya baya, ƙamshin turarenta ne ya shiga hancinshi, kallonta yayi kaɗan yayi saurin mayar da kanshi gefe, Dada tace "Ko zaka ɗan fito akwai wanda yake son ganinka ne." Kamar zai tambayi waye sai kuma yaji bai son yin magana saboda yadda take tsaye daga waje, Dada ta juya tana saka tabarma a tsakiyar falon dake ɗauke da kujeru biyu. Keken ya turo da kanshi har yazo inda Zeey ke tsaye, kasa cigaba da tafiyar yayi ita ma bata motsa ba, a hankali ta waigo shima ya ɗago suka kalli juna, da sauri suka ɗauke kai, Zeey tace "Yau baka je yawo ba?" "Dama kullum nake zuwa?" "Au ashe fa ba kullum kake zuwa ba." Kallonta yayi itama ta kalleshi sai kuma yaga tayi murmushi ta wuce wurin Dada, Baqeer da kallo ya bita.
Waya Zeey ta yiwa Junaid ta sanar dashi ya shigo, ta fito ta wuce Baqeer tayi waje, kallon Dada yayi da mamakin kafin yace "Dada waye zai zo?" Tace "Wallahi ban gama sani ba kai dai zai zo gani." Da mamaki yake sake kallonta yace "Baki san wa zai zo ba har zaki barshi ya shigo?" Tace "To ba dai da Zainabu suke ba?" Kallonta yayi lallai Dada bata san zamani ba, waigawa yayi waje ya hangosu suna tafe a tare fuskarsu ɗauke da fara'a, kallonsu yayi yanda suka dace da juna nan da nan yaji takaici ya kamashi, kallonshi ya sake yi tun daga sama har ƙasa to kai Baqeer babh ƙafa ma me kake tunani? Menene ma naka a ciki? Wani abu ya haɗiya kamar zai koma sai yaji Dada tace "Baqeeru ina zaka? Bayan wurinka aka zo?" Haɗa ido suka yi da saurayin kafin suka ƙaraso ciki, Zeey ce tace "Physiotherapist ne zai duba ka ne kafin kuyi making appointment kaje asibiti ya sake ganin taimakon da zasu iya yi maka." Hannu Junaid ya miƙawa Baqeer wanda shima ya miƙa mishi, dukkansu fuskarsu babu walwala, Junaid zuciyarshi cike take da son sanin wanene wannan da Zee duk ta damu dashi? Hannunsu na riƙe da juna Junaid ya kalleta yace "Kamar gaske in kina magana da serious voice." Ta saki murmushi tace "Ban gane kamar gaske ba? Kai ma dai kasan in na canza yanda nake." Dada ce ta kalleshi ganinta yasa ya saki hannun Baqeer sannan ya rusuna ya gaisheta ta amsa fuska a sake sosai, nan suka shiga ciki Baqeer ya tura keke suka shiga sosai, kusa da Baqeer ya zauna sannan ya dan tsuguno yace "Sauƙe kafar daga kan keken muga." Baqeer yasa hann ya ɗaga cinyarsa sannan ya sauke, kallonshi yayi yace "Well done! Bari muga." Yayi maganar yana ɗan daga ƙafafunshi, Zeey da Dada dake tsaye suna kallonsu, ya ajiye ƙafar ya sake ɗaga ɗaya ƙafar, kallon Baqeer yayi yace "Zaka iya motsa yatsun ƙafafunka?" Baqeer duk yanda ya gwada abun bai yiwu ba ya girgiza kai zuciyarshi na wani irin zafi. Junaid yace "Babu komai dama dai gwadawa ne ai, ya sake momotsa ƙafafun yanayi yana nazari, yace "Takardun da aka baka na asibiti suna nan?" Yace "Dada takardun da Umma ta aiko dasu suna kusa?" Da sauri ta wuce don ta ɗauko, Junaid ne ya dawo inda Zeey take yace "Me kike tunani?" "Babu komai, ya kake gani?" "Haka kika yarda dani?" Murmushi tayi tace "Kaima ka sani ai." Kalaman da suke yi duk Baqeer na jinsu, wani abu ne yake ji yana tokare mishi maƙoshi wanda bai san ko menene ba, yawun bakinshi ya haɗiya yana mamakin abinda yake ji.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
#Baqeer🦼 #Zeey #RayuwadaKaddara #Hawayena #Samudarashi #UmmuAsgar #Ayushermuhd *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA HUƊU*
{34}
Ya ɗauki wani lokaci yana duba takardun kafin ya ɗago kai ya kalli Baqeer yace "naga anan ance accident kayi shine cause na paraplegia ɗin ko?" Ɗaga kanshi kawai yayi alamun amsawa ba tare daya buɗe baki yayi magana ba don baka nan tsayuwar Zeey a kusa da saurayin ke saka mishi ɓacin ran da bai san dalili ba. Kallon Zainab Junaid yayi yana murmushi yace "In Sha Allah with proper care and treatment ko bai taka ba zai samu ya iya motsa ƙafafun da kanshi sai dai kuma kin san ciwo ke shiga farat ɗaya sauƙi sai hankali, ba wai daga fara session ɗin mu zai warke ba, it will take time before we can be able to see some changes". Daɗi ne ya kama Zeey jin cewa Baqeer ba zai dawwama a haka ba akwai yiwuwar ya warke, mutane su daina wulaƙanta shi saboda nakasar shi. "Thank you J, i really appreciate it" tace tana murmushi. Daɗi Junaid yaji yana ganin yayi wani abu daya faranta ran Zeey duk da bai san alaƙarta da patient ɗin ba, sanin wacece Zeey ɗin mai lafiya ma ba kowa take so ba bare nakasashe yasa yake danne abinda yaje ji yana mintsinin zuciyarshi akan Baqeer ɗin. Murmushin ya mayar mata shima yace "it's my pleasure".
Kallon Dada tayi tana yi mata bayanin abinda Junaid yace, itama sosai farin ciki ya kamata jin akwai yiwuwar warkewar Baqeer ɗin, sai ga Dada na share hawayen farin ciki don sosai take jin tausayin Baqeer da yadda mahaifinshi ya juya mishi baya saboda ƙaddarar data sameshi. "Da kanka ma zaka iya yin exercises ɗin zan nuna maka yadda zaka yi kana daga zaune da hannayenka, In Sha Allah with time komai zai zama tarihi amma sai kayi haƙuri ka sakawa ranka juriya don irin wannan abun is very tiring" Junaid yace yana kallonshi. Ciki-ciki ya amsa mishi da "to" don yana lura da wani irin kallo da yake jifan Zeey dashi wanda yake ƙara saka mishi nauyin zuciya, haka nan yaƙi jinin yaga Zeey ɗin a tsaye a gefenshi, shi sai yaga ma kamar yau tafi koyaushe fara'a saboda tana tare da saurayinta.
An ɗauki tsawon lokaci yana exercising mishi ƙafafun sannan ya nuna mishi yadda zai dinga mommotsa ƙafafun da hannayenshi yace "wannan exercise ɗin zai taimaka wajen tada jijoyoyin da suka mutu su koma aiki, Allah ya baka lafiya". Dada ce ta amsa da "Ameen" sai faman washe baki take yi tana saka mishi albarka daga shi har Zainab data kawo shi. Sun yi mata sallama suka tafi Zainab nace mata sai sun dawo ƙara dubashi don yace ba kullum zasu dinga yin treatment ɗin ba za'a na yin tsallaken kwana ɗaya idan anyi yau gobe ba za'a yi ba sai kuma jibi. Bayan fitarsu Dada ta kalleshi tace "Allah dai ya yanke maka wahala Baqeeru yasa a dace". A cikin zuciyarshi ya amsa da 'Ameen' don bai ji zai iya buɗe baki yayi mata magana ba saboda hatta ita haushinta yake ji ganin yadda take ta wani nan-nan da Junaid.
***** Yau ta tashi ɗakinta babu komai ko ƙwayar shinkafar da zata dafa babu, ƴan kuɗaɗen da ta samo wurin Umma tuni suka ƙare. Kallon ɗakinta tayi tana tunanin abinda zata ɗaga ta sayar ta samu ta saya musu abinci, ita yunwar cikinta ba damunta ma take yi ba don idan da sabo zata iya cewa har ta saba da ita to amma yaran fa ya zata yi dasu su da basu san babu ba. Fitowa tayi tsakar gida ta kalli uwargidanta dake tsugunne a gaban murhu tana girki. "Sannu da aiki Maman Aisha" ɗagowa tayi ta kalleta ta watsar don tasan wani abun zata tambayeta ganin yau tunda ta tashi bata ɗora sanwa ba tasan bata da komai ne ita kuwa kayan abincinta nata ne da ƴaƴanta ba zata iya ɗauka tayi neman suna ba alhalin itama nema take yi. Duk da taga kallon wulaƙancin da tayi mata sai tayi kamar bata gani ba tace "don Allah ko zan samu aron dubu ɗaya a wurinki? Wallahi yau na tashi bani da komai ga yara sun kusa dawowa daga makaranta bani da abinda zan basu". Mafici ta ɗauka ma ta hau fifita wutar girkin da take yi tayi kamar bata ji abinda Hadizan tace ba. Duk da taji haushin ƙyaletan da tayi bayan tasan sarai taji ta tsabar wulaƙancinta ne ya tashi amma sai ta haɗiye fushinta tunda tasan idan ba wurinta ba bata da inda zata je ta samu, idan ma tace ta tafi gida wajen Umma kafin ta ƙarasa ma yaran sun dawo gashi haka nan ta turasu makarantar ko ɗan kokon ma yau basu samu ba. Kwantar da murya tayi tace "don Allah Maman Aisha kiyi haƙuri ki bani aron wallahi ba zanyi miki wasa da kuɗinki ba zan baki". A fusace ta ɗago tana nunata da yatsa tace "bafa na son rainin da kike neman kawo mini Hadiza, da can ni nake baki abincin da zaki nemi ki takura mini ko kuwa ni na ajiye ki, ha'an haka kurum mace baki san ki tashi ki nemi na kanki ba sai dai a ɗauko kina daga kwance a baki idan ya ƙare ki nemi takura mini kamar nj na ajiye ki". Kamar tayi kuka haka take ji sai dai bata da yadda zata yi don haka ta ƙara cewa "kiyi haƙuri don Allah wallahi zan baki". Tsaki taja ta juya ta cigaba da aikin girkinta tana barta anan a tsaye tana jin takaicin rashin tashi ta nemi na kanta tun da gatanta sai kawai tayi kwance duk wata Ya Baqeer na ajiye mata kayan abinci don haka bata da wata damuwa a lokacin gashi yanzu tazo abincin da zasu ci ita da ƴaƴanta na neman yafi ƙarfinsu, shi dama maigidanta babu abinda ya dameshi idan yayi ficewarshi tun safe baya ƙara waiwayarsu sai lokacin kwanciya bacci yayi acan inda yake fita yake cin abinci don haka bai damu da ko suci ko kada suci ba.
Ɗakinta ta koma tana share hawaye, tunaninta ɗaya yanzu idan yaran suka dawo daga makaranta me zata basu? Ɗakin kawai take bi da kallo tana tunanin ita yanzu ba wani abu gareta ba bare ta ɗaga ta sayar ta samu abinda zasu ci abinci, idanunta ne suka kai kan wata tshowar akwatin garwa ta maigidan da ta daɗe a ajiye a ɗakin nata, ba komai yake yi da ita ba sai haɗa ƙura don haka ta tashi ta janyota ta karkaɗe ƙurar kai tasa hijabinta ta sunkuci akwatin ta fice ta kaiwa ƴan gwangwan, ko ɗari biyar suka bata ai dai ta isheta ta samar musu da abinda zasu ji, da kallo kishiyarta ta bita tana ayyana lallai yau akwai bala'i a gidan don kuwa tasan ba ƙaramin ɓaci rayuka zasu yi ba akan wannan matacciyar akwatin.
*****
Tunda suka bar gidan babu wanda yayi magana har sai da suka hau titi sosai suka yi nisa da unguwar ta mariri. "Who is he to you?" Ya tambayeta. Waiwayowa tayi ta kalleshi tace "na'am J, magana kake yi?" Ƙara maimaita tambayar yayi yace "Who is he to you? naga kin damu sosai da al'amuranshi". Shiru tayi ta kasa amsa mishi don sai ta samu kanta itama da yiwa kanta makamanciyar tambayar da yayi mata "waye shi a wajenta? Akwai wata dangantaka ne a tsakaninsu bayan kasancewar shi yaya ga ƙawarta Maryam?" Kasa bawa kanta amsa tayi don haka tayi shiru bata amsa Junaid ɗin ba, shima sai bai ƙara tambayarta ba jin tayi shiru sai dai yana jin fargaba akan abinda zuciyarshi ke neman saƙa mishi sai dai kuma idan ya tuna wacece Zeey ɗin da yadda take kallon maza ƴaƴan manya masu ji da kyau da class a ba komai ba sai ya samu ƴar nutsuwa kaɗan don yasan babu abinda zata yi da gurgu sai dai kuma tambayarshi anan itace waye shi a wajen Zeey ɗin data damu dashi da yawa har haka?
Har suka ƙarasa gidansu babu wata hira a tsakaninsu kowa da abinda yake saƙawa a cikin zuciyarshi, sai da zai sauka nema tace mishi "nagode sosai J, please ka gaishe mini da Mami kace ina sauri ne shi yasa ban shigo na gaisheta ba amma takanas zan zo na gaisheta, sai kuma batun payment ɗinka ban ji kace komai ba". Harararta yayi yace "ai bakin ki ne payment ɗin" ya mayar da ƙofar motar ya rufe ya wuce ba tare da ko waiwayowa yayi ba. Bin bayanshi tayi da kallo har ya shige cikin gidansu sannan taja motarta ta bar wurin cikin ranta tana jin ina ma zata iya mayar mishi da martanin soyayyar da yake yi mata don tasan J yana sonta shi yasa yake ɗaukar duk wasu al'alarta sai dai kuma ba zata iya ba don ba wani girmarta yayi ba beside that bata jin shi har ƙasan ranta a matsayin wanda zata iya spending the rest of her life with. Girgiza kanta tayi kawai ta kawar da wannan tunanin daga ranta, haka nan ta samu kanta da yawatawa akan titi don bata ji tana son komawa gidan Inna ba taje suyi ta faɗa tana sakar mata baƙaƙen maganganu don ma dai tana kawarwa tana mayar da abun wasa amma abun yana yi mata ciwo yadda Inna take treating ɗinta sam baya yi mata daɗi. Sai can goshin magriba ta gaji da yawon a titi ta ɗauki hanyar da zata sadata da gidan Inna tana jin koma zuwa zata yi ta tattara kayanta ta koma gida ne.
*****
Shi kuwa Bello ganin da yayi iyayen shi sun ƙi su goya mishi baya aje gidansu Asiya a nema mishi aurenta daya ɗauki dukkanin buri ya ɗaura akai yasa shi niƙar gari ya tafi garin Rano inda Baffanshi babban yayan mahaifin shi yake da zama ya kai mishi ƙarar su Baban akan ya samu yarinya har sun daidaita kansu amma su Baba sun ce ba zai aureta ba. Nan fa Baffan ya rufe ido yayi ta faɗa yana cewa "don me yaro ya girma ya kai munzalin ajiye iyali zasu ce ba zai yi aure ba, to shi ba zai lamunci wannan ba dole aje a nema mishi auren tunda dai ya nuna buƙatar hakan kuma yana da abinda zai riƙe matar dashi". Haka nan Bello ya ɗauke shi a sabuwar motarshi daya saya don ba ƙaramin alheri ya samu ba a gasar nan da yaje suka tafi Kano. Duk yadda Baban Bello yaso yayi wa ɗan uwanshi bayanin dalilin da yasa suka ce Bello ba zai auri Asiya ba ya toshe kunne yaƙi karɓar uzurin su don kafin tahowarsu sai da Bello ya jiƙa shi da kuɗi don haka yace tunda dai yaji ya gani kuma yana da abinda zai riƙe matar to su ƙyale shi ya aureta, haka nan dai ba don su Baban sun so ba aka je gidansu Asiya aka nema mishi aurenta, shi kanshi Babanta da yaga iyayen Bello ne suka zo neman auren nata sai da yaji mamaki don yasan dai Bello abokin Baqeer ne asalin manemin auren ƴar tashi sai kuma yanzu iyayenshi suzo da wani zance na daban kuma don haka ya dakatar dasu sai da ya shiga gida ya kira Asiya ya tambayeta da saninta iyayen Bello suka zo neman aurenta? Babu kunya Asiya ta amsa mishi da eh, "to ina maganar Baqeer ta kwana da zaki sa abokinshi a nema mishi auren ki?" Sai cewa tayi "Baba Baqeer fa ya zama gurgu ta yaya za'a yi na aureshi?"