Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 25

Baqeer complete - Chapter 25

Baqeer complete Chapter 25: Baqeer complete Chapter 25. *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

3,095 words

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

#Baqeer🦼 #RayuwadaKaddara #Hawayena #Samudarashi #UmmuAsgar #Ayushermuhd

*BAQEER*🦼 *NA*

*UMM ASGHAR* Da *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA BIYU*

{32}

Cakuma ya kaiwa wuyan rigarshi ya shake shi yana cewa "Dan uwarka ba zaka bayar ba fa kace? Ni kake faɗawa ba zaka bayar ba don ka raina ni ko kuwa don kana ganin kayi tsawon ƙafa ka kere ni a tsawo? Idan da wancan nakasashen ne yace ka bashi kuɗin hannunka zaka faɗa mishi haka ne?" Da ƙyar ya iya ɓanɓare hannayen Kamalu daga wuyanshi domin kuwa ba ƙaramin shaƙa yayi mishi ba. A sakarce ya kalleshi yace "An hana ka ɗin sai dai kayi duk abinda zaka yi amma ba zan ɗauki kuɗina da zan tafi makaranta ba na baka alhalin ba wani abu zaka yi dasu ba watakila ma sigari zaka saya, kuma da kake cewa da Yaya Baqeer ne bashi zan yi ai shi Yaya Baqeer sai dai a ƙi shi don wani abu amma dai ba don halin shi ba don kuwa kowa a gidan nan ya sani abun hannunshi bai rufe mishi ido ba kuma babu ruwanshi da bambancin da Baba yake nunawa idan ya tashi alherin shi gaba daya yaran gidan nan yake hadawa yayi wa kowa shine har kake haɗa kanka dashi bayan kai baka taɓa iya morawa mutum da ko sisi sai dai ma kai ayi maka."

Ai kamar ya tunzura Kamalu ya kuwa hayayyaƙo mishi yana ƙoƙarin kai mishi duka yana cewa "Ni kake faɗawa wannan maganar don uban uwarka?" Cikin hanzari Jamila ta fito daga ɗakinta tana cewa "Rashin mutuncin naka har ya kai ka zagi ubana Kamalu? Akan ya hanaka kuɗin shi kake yi mana wannan ɗiban albarkar?" A fusace yace "Shi baki ji abinda ya faɗa mini ba sai ni don na rama zaki taso ki shigar mishi." Ƙwafa tayi tace "To uban uwarka Abu ka zaga ba dai ubana ba ato." Abu naji an haɗa da ubanta ta taso da tata masifar itama alhali da tana zaune a gefe tana kallon rashin mutuncin da Kamalun yake yi bata hanashi ba.

"A'a fa Jamila wallahi banda tsikarin uwar miji da taɓarya, saboda me zaki sako da ubana ko kin ji na saka musu baki tunda suka fara abinsu da zaki sako dani?"

"Au ashe babu daɗi, ba'a gabanki ɗanki ya zagi nawa uban ba kin hanashi ne? Ko kin yi mishi faɗa, to wallahi ba ubana ya zaga ba sai dai naki, haka kurum don yana ji da tijara sai ya huce akan yarona ko kuwa sai kada yaje makaranta tunda ɗan gwal wanda bai san daɗin ilimi ba ya buƙaci ya bashi kuɗin?" A take faɗa ya kaure a tsakaninsu har suna nema su kaiwa juna duka, sai Umma ce ta fito daga ɗakinta ta rabasu jin hayaniyar tayi yawa, da ƙyar suka haƙura kowacce ta koma ɗakinta suna faman zage-zage. Komawa Bashir yayi ɗakin Jamila yana bata haƙuri kafin ya fito ya tafi makarantar ranshi duk babu daɗi.

*****

Yau ta tashi cikin farin ciki ganin tun jiya suke daɗi da maigidan nata. Sandwiches tayi musu sai ta dafa milk tea ta zuba a flask, a gefe ga farfesun kayan cikin rago da ta dafa tun jiya da dare yau kawai ɗumamawa tayi. Kwalliya tayi cikin wata riga da tabi jikinta ta lafe duk wasu curves na jikinta suka bayyana, rigar iya kacinta gwiwarta sannan siririn hannu gareta guda ɗaya ɗaya hannun babu komai don haka ko bra bata saka ba. Tunda ta fito yake binta da kallo domin kuwa shigar da tayi ta tafi dashi ba kaɗan ba, a ƙarshe ma kasa haƙuri yayi ya janyota ya zaunar da ita akan cinyarshi yana sunsunar sassanyan ƙamshin turaruka da tayi amfani dasu. Haka suka ci abincin a cikin nishaɗi yana saka mata a baki itama tana bashi, ɗagowar nan da zata yi kawai taga Baffa(surukinta) tsaye a kansu. Wata irin zabura tayi sai kuma ta koma ta cukuikuye a jikin Baban Aareef kamar mai ƙoƙarin komawa cikin shi. Shi kanshi sai da yaji babu daɗi da yadda Baffan yayi musu tsaye aka yana bin su da wani irin kallo. Murya a cunkushe yace "Baffa barka da asuba," har wannan lokacin Maryam na naɗe a jikinshi baƙin cikin duniya ya lulluɓeta saboda ganin da uban mijin nata yayi mata da shigar da ko nata uban bai kyautu ya ganta da ita ba.

A ɗage ya amsa mishi "Barka kadai, kana nan mace ta sanya ka a gaba tana zuba maka karuwanci kai kuma sai faman yage baki kake yi kamar wani sakarai ina ta kiranka a waya kaƙi ɗagawa?" Murya a shaƙe yace "kayi haƙuri Baffa, amma don Allah ka fita daga waje sai na fito na sameka" ranshi idan yayi dubu ya ɓaci don ko shi yau abinda Baffan yayi ya ɓata mishi rai. Sai da ya watsa mata wani mugun kallo da bata ma san yana yi ba don ta ɓoye fuskarta akan ƙirjin mijinta bama ta son ta ɗago bare taci karo da fuskarshi sannan ya fita. Sai da ya tabbatar Baffan ya fita sannan ya ɗagata daga jikinshi yace "Ina zuwa please, bari naje naji me Baffa yake so."

Ko kulashi bata yi ba don haushi ganin kamar ma bai damu da yanayin da Baffan yazo ya samesu ba. Yana fita ta fashe da wani irin kukan baƙin ciki tana jin takaicin yadda uban mijinta baya kunyar faɗo musu ɗaki ko tunanin yanayin da zai iya riskarsu a ciki baya yi gashi kuma Baban Aareef baya kallon hakan a matsayin wani abun damuwa idan tayi magana ma har saɓani suke samu akan hakan. Har ya dawo ciki bata daina kukan ba, duk sai taji farin cikin da take ciki ya gushe takaici da baƙin ciki duk sun mamaye mata zuciya. Tsayawa yayi yana kallonta ganin tana kuka sai kuma ya taɓe baki yace "Shi kuma kukan da kike yi na menene? Ko kuwa dai jin daɗi?" Ko ɗaga kai bata yi ta kalleshi ba ta cigaba da kukanta shima sai yayi kamar bai fahimci dalilin kukanta ba yace "to ni zan fita nasan dai babu wata matsala tunda komai da za'a buƙata akwai, idan lokacin tashin Aareef yayi sai kije ki ɗauko shi" ya miƙa mata kuɗin napep.

Kasa karɓar kuɗin daya miƙa mata tayi ta kuma kasa haƙuri sai da tace mishi "Saboda Allah haka zamu cigaba da rayuwa duk lokacin da Baffa yaso kawai sai dai mu ganshi tsaye akan mu ya shigo mana wuri babu tunanin a wane irin hali zai iya riskarmu kuma kai baza ka iya yi mishi magana ya daina ba, wannan wace irin rayuwa ce ace ni da gidana amma bani da wani sakewa a cikinshi, shikenan ni ban isa nayi wa mijina kwalliya ba saboda fargabar kada a shigo a tarar dani da shigar da bata dace ba. Gaskiya ni dai ya kamata a sake tsari ko dai ya daina shigo mini ciki ko kuma ka canja mini wurin zama amma ba zai yiwu ya dinga shigo mini ɗaki koyaushe ta raya mishi ba."

Wata uwar harara ya watsa mata yace "Duk waɗannan maganganun a Baffan kike yi? Mahaifin nawa? Shine kike iya buɗe baki kina faɗar duk maganar da tazo bakinki a kanshi, to da zaki ce ya daina shigo miki gida nan ɗin gidanki ne? Nace gidanki ne da zaki ce ba zai shigo ba, ina ce dai gidan ɗanshi ne ai ko kuma yadda yake da iko dani haka yake da iko da duk wani abu dana mallaka don haka ke baki isa ki kafa mishi doka ba a cikin gidan nan, idan kina ganin zamanki dashi akwai matsala zaki iya fita ki bar mishi gidan tunda zaman bai zame miki dole ba shi kuwa baya da wani wurin zuwan idan ba nan gidan ba." Ya watsar da kuɗin a tsakiyar parlourn yayi ficewarshi ya barta anan babu wani tausasawa bare lallashi sai kace ba ita aka yiwa laifi ba. Sai da taji kanta ya fara ciwo saboda kukan da tayi ba kaɗan bane sannan ta bawa kanta haƙuri ta goge fuskarta ta tashi ta tattare kuɗin daya watsar mata a ƙasa ta adana sannan taje ta sakawa ƙofarta makulli duk dai da baya shigo mata wuri sai idan Baban Aareef na nan amma bata so ta sakankance tunda shi bai san ya kamata ba. Tattare kwanukan abincin da ta ɓata lokacin ta wajen shiryawa tayi ta mayar kitchen don gaba ɗaya sai taji abincin ma ya fita daga ranta halin ɓacin ran da ta samu kanta a ciki ya cika mata ciki. Haka nan ta yini sukuku zuciyarta duk babu daɗi komai take yi dauriya kawai take yi har lokacin ɗauko Aareef daga makaranta yayi ta fita ta ɗauko shi. A harabar gidan sai data tsaya ta ƙarewa motarta kallo wacce Baffan ne yasa aka karɓe daga hannunta kawai don ta fita tayi hidimar ɗan uwanta da ita gata nan yanzu an ajiye ta kawai tana busar iska ita kuma duk wani uzurinta sai dai ta fita ta hau napep duk da ma ba wani fita take yi ba kai Aareef makaranta da ɗauko shi ne kawai sai kuma uzurin zuwa gidansu idan ya kamata da take fita a motar taje ta dawo amma shine sai da yasa aka ƙwace kawai don dai ya nuna mata iyakarta bayan shi nashi ƴaƴan kowacce na warwasawa a gidan aurenta sai ita da yazo ya sakawa ido.

*****

Haka nan ta tashi yau sukuku da ita zuciyarta fal tunanin Baqeer da duk mafarkanta na yau shine a ciki, ta rasa me yasa ta damu dashi har haka alhalin tun asali ma ba wai suna wani shiri bane bare tace ko yarintarsu take tunowa yasa yanayin da yake ciki a yanzu ya tsaye mata a rai. Ta dai fi bayarwa tausayin halin daya samu kanshi a ciki ne yasa take yawan tunawa dashi ta damu da dukkanin wasu al'amuranshi da har idan bata je taga halin da yake ciki ba bata samun nutsuwa. Tunda ta tashi tana kwance akan gadon bata tashi tayi komai ba sai dai ta juya nan ta juya can sai Nabila ce kawai take kaiwa tana kawowa tana ƙoƙarin tsaftace gidan. Ɗakin Inna ta shigo ta watsa mata harara tace "To sannu ƴar mai da ba'a koya mata komai ba sai sakalci da lalacin tsiya, kina nufin haka zaki yi ta kwanciya ba zaki tashi ki kamawa Nabila komai ba ita kaɗai zaki bari da aiki kina naɗe akan gado sai idan ta gama abinci kice zaki buɗe ciki kici. Ke dai wallahi baki ji daɗin halinki ba kuma ni dai idan kin san ba za'a amfana da zamanki ba gara tun wuri ki tattara ki koma gidanku inda ba'a sakaki ba'a hanaki amma ba zai yiwu kizo sai dai ki naɗe akan gado ba kice ba zaki yi aiki ba ah to."

Tashi zaune tayi tace "Haba don Allah Inna daga tashi na bacci kawai zaki rufeni da faɗan ki na fama da baya ƙarewa tun ban gama wartsakewa ba, shi yasa wallahi ban cika son zuwa wurinki ba don nasan takura mini kawai zaki yi da yawan faɗa kamar irin kina jin haushi na ɗinnan."

"Ungo naki nan ƴar ƙaniya mai bakin tsanya, wacce baka kasheta a zance" tayi mata daƙuwa da duka hannayenta bibbiyu. "Shikenan ke ba za'a yi miki faɗa ki saurara ba sai kin mayar da amsa saboda a gidanku ba'a yi miki tarbiyyar sanin darajar manya ba, to ni gidannan ba'a yi mini iya shega in ƙyale, idan kinga ba zaki iya zama ba ƙofa a buɗe take ki tattara ya naki ya naki ki bar mini gidana dama ai bani na gaiyaceki ba". Tagumi kawai Zeey tayi ta zubawa Inna ido tana ta faman zazzaga mata masifa sai dai sam yanayin da take samun kanta a ciki a ƴan kwanakin nan yasa bata ji zata iya tanka mata ba don haka har tayi ta gama bata ƙara ce mata komai ba, sai bayan data fita tayi mata gwalo tana cewa "Jarababbiyar tsohuwa kawai, haka kurum daga tashi na zata zo ta cika mini kunne da masifa kamar ance mata ina da energy ɗin ɗaukar jidalinta yanzu da sassafen nan".

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

#Baqeer🦼 #Zeey #RayuwadaKaddara #Hawayena #Samudarashi #UmmuAsgar #Ayushermuhd

*BAQEER*🦼 *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA UKU*

{33}

Yau Junaid ya sauka a garin Kano ya wuce gida inda ya huta yayi bacci, tashi yayi ya watsa ruwa sannan yasa riga t-shirt da wandon jeans ya fesa turare sannan ya fito, a falo yaga Mamy ta jera mishi abinci, murmushi yayi sannan ya zauna yana cewa "Mamy inyi maza-maza dai in kawo miki suruka kema ki huta." Dariya tayi tace "Ah to ka dai ce kana dawowa zaka kawo mana Zainab." Wayarshi ya kalla dake ƙara ya dagota tare da kallon Mamy yace "Gata ma ƴar halak." Ya ƙarasa maganar yana saka wayar a kunnenshi. "J ya? Ka iso?" "Duk hankalinki dai da alama yana kaina, hope anyi mini shirye-shirye ne shi yasa kike jirana." Dariya tayi kaɗan tace "Kada ka damu in muka je kaga mara lafiyan daga nan zan kai ka yawo." Wani sanyi yaji a ranshi da alama ita ma ta fara cireshi daga bangaren aboki yace "Shikenan ki bani zuwa bayan la'asar In Sha Allahu." "Shikenan zan zo sai mu wuce." "Wai zuwan ma ɗauka na za ayi? Ki bari zan zo na ɗaukeki." Ajiyar zuciya tayi tace "Kai da kasha hanya? Kai dai ka shirya zan zo." Da yake yasan dagiyar Zeey yasa yace to kawai, Nabeela dake tsaye tana gyara drawer ce ta kalleta tace "Waye kuma J?" Zeey ta kwanta akan gado tana ɗan wasa da kafarta tace "Junaid." Da mamaki tace "Junaid dai naki?" "Nawa ko nasu? Shi dai ya dawo yau." Kallonta Nabeela tayi cike da zargi da sauri Zeey tace "Kada ma ki fara babh abinda ke tsakaninmu." Dariya ta saki tace "Wannan karan kin bani mamaki kece yau kwananki biyu a gidan nan?" "Ni kaina mamaki nake bawa kaina, don ma yanzu mitar Inna ba wani bani haushi yake ba." "Dama can bai kamata ya baki ba tunda kin san halinta." Ajiyar zuciya tayi tace "Matsalar bana iya yi mata shiru ne." "Dama ina zaki mini shiru kina kwance kowa yana aiki banda ke?" Suka jiyo muryar Inna data shigo ɗauke da kayan gugar da aka kawo, ta miƙawa Nabeela tana kallon Zeey dake kwance akan gado tana magana tana cin soyayyiyar cashew, ko a jikinta ma. Fita tayi hakan yasa Zeey ta miƙe tace "Bari nayi wanka fita zamu yi da Junaid." Kai kawai Nabeela ta ɗaga ita kuma ta shiga toilet, ƙwalawa Nabeela kira tayi wai ta miƙo mata towel ta manta bata ɗauka ba, ɗauka tayi ta miƙa mata sannan ta cigaba da aikin, tana mamakin Zeey sam halinta na ko in kula abinda ke gabanta kawai shi take yi amma ragowar ba damuwarta bane, gadon ta gyara sannan ta ɗauko tsintsiya ta share ɗakin ta fito falo inda ta samu Inna zaune tana sauraren radio, kallonta tayi tace "Inna me za'a dafa?" Innan ta kalleta tace "Me kike gani? Ni ko menene ma bani da matsala." "Ko muyi shinkafa da wake?" Kai ta ɗaga alamar 'eh' kafin tace "Allah yayi miki albarka ya kawo miki mijin da zaki aura wanda zaki ji daɗin shi." "Ameen Inna," ta faɗa cikin jin daɗi. Inna tana zaune tana binta da ido har ta shiga kitchen, ajiyar zuciya tayi don tana tsananin tausayin Nabeela. Zeey kam kaya ta saka ta fara jawowa tana tunanin wanda zata saka, atamfa ta ciro doguwar riga irin buba ɗinnan, tasa ta ɗaura ɗankwali irin na Zarah Buhari, nan fa ta fito cass tasa turare, kallon kayan data cire tayi kamar baza ta kwashe ba sai kuma ta ɗauke tace "Kafin yanzu a hauni da masifa." Jaka ta ɗauko ta ɗauki wayarta, falo ta zauna gefen Inna tace "Inna wai ni kam radio ɗinnan kunna shi kawai kike yi amma dai ba saurara kike ba ko?" "To ko ma dai menene ai kunnena ne ko?" Baki ta taɓe, wayarta ce tayi ƙara ta ɗauka da sauri ta fashe da shagwaɓa tace "Mummy Allah Inna ta takura mini." "Kin gani ko? Ki tattaro ki dawo don ni har yanzu mamakin zaman nan naki nake yi." Tana kallon Inna dake harararta tace "Wasa nake yi wannan karon Inna lallaɓani take yi? Ko Inna?" "Ahaf ita tasan bazan lallaɓaki ba ai, tunda su sun gama sangartaki." Dariya tayi tace "Mummy gaba ɗaya Inna fa bata gajiya da mita." Mummy ta sauke ajiyar zuciya tace "Daddynki ma ya ƙosa ki dawo gidan babu daɗi da ba kya nan." Tana murmushi tace "In Sha Allahu Mummy, kema kin san ina missing ɗinki, love you Mummy." Nan suka yi sallama Inna tayi tsaki tace "In ma roba ne can ku kuka sani." Zeey tasa dariya sosai tace "Love you ake cewa." "Can muku nace kuce samira ko tangaran ma bai dameni ba." Miƙewa tayi tana cigaba da dariya don Nabeela dake kitchen ma dariya take yi musu, Zeey ta fito ta shiga mota ta fita har lokacin ta kasa daina dariya. Inna ce ta bita da harara, Nabeela ce ta leƙo Inna tana kallonta tace "Ki tabbatar in zata koma kun koma tare, gwara kije can ki huta ni in Basira ta zo tayi mini abinci na ya isheni, sannan ki rage wannan saurin fushin naki." Kai ta ɗaga sannan ta koma kitchen ta cigaba da girkin.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull