Baqeer complete - Chapter 24
Baqeer complete Chapter 24: Baqeer complete Chapter 24. "Ameen dai distinguished, In Sha Allah kujerar nan tamu ce tunda muka samu manyan unguwa a hannun…
3,372 words
"Ameen dai distinguished, In Sha Allah kujerar nan tamu ce tunda muka samu manyan unguwa a hannun mu." Wani murmushin jin daɗi ya saki yana hango kanshi akan kurerar senator don ji yake yi kamar ma har yaci ya gama sai dai a jira lokacin zaɓe kawai.
*****
Tunda aka fitar dashi daga gidan maigadi ya mayar da gate ya rufe yake faman zazzaga masifa har mutane na tsayawa suna kallonshi sai dai babu wanda y tambayeshi dalilin faɗan shi domin kuwa kowa yasan hali Mallam Badaru mafaɗacin mutum ne, ba'a taɓo shi ba ma ya aka ƙare dashi bare an takaleshi. Sai da yaga dai an mayar dashi kamar mahaukacin shi kaɗai yake faɗan shi babu abokin tayi sannan fa ya kama hanyar gidan shi yana cigaba da zazzaga masifa, har ya isa gidanshi bai yi shiru ba sai da ya ganshi a tsakar gidanshi ko sallama bai yi ba tsabar bala'in dake cin zuciyarshi. Da yake Jamila tasan tsiyar data shuka mishi ko leƙowa tsakar gidan bata yi ba bare kuma Fatima da dama yanzu ba wani shiga sabgar shi take yi ba ganin shima ya tattara al'amarinta ya watsar don ko ranar girkinta idan bai ga dama ba ɗakin Abu yake shigewa ko kuma ya gaiyaceta nashi ɗakin, Jamila ce dai da aka san ba zata yarda a danne mata hakki ba basa yi mata wannan kama karyar amma yadda Abu ta sameshi a hannu sai abinda tace yanzu ake yi a gidan.
Abu na fitowa yace mata "Ina biredi na dana bayar aka shigo mini dashi ɗazu?"
"Biredi kuma? Gaskiya ba'a bani ba sai dai ko idan Jamila aka bawa. Amma waye ka bawa ya shigo dashi don ni dai ina ɗaki ban ji shigowar kowa ba".
Ai tuni ya ƙara harzuƙa jin wai Abu bata san an shigo da biredi ba. "To wa aka bawa biredin nawa bayan ke nace a kawowa?"
"Gaskiya Mallam ban sani ba don ni dai babu wanda ya kawo mini biredi". "Jamila. Jamila!" Ya hau ƙwala mata kira ita kuwa tana jin shi tayi luf kamar ba ita yake yiwa wannan kiran mafarautan ba, sai da taji ya nufo ɗakinta yana cigaba da ƙwala mata kira sannan ta fito tana cewa "Mallam lafiya, irin wannan kira haka kamar naci bashi ban biya ba". Hannu ya miƙa mata yace "bani nan". Yi tayi kamar bata san akan me yake magana ba tace "me zan baka?" Cikin tsawa yace "Kinga Jamila kada ki kawo mini rainin hankalin da kika saba, shiga ki ɗauko mini biredi na dana bayar a shigo mini dashi."
Tsuke fuska tayi itama tace "Kuma ɗan aiken ni yace maka ya kawowa biredin naka? Ko kuwa dai tijarar taka ta fama zaka sauke a kaina, to wallahi sam ba zata saɓuba tun wuri gara ka nemi inda aka kai maka biredinka amma ba wajena ba, yo in banda neman fitina ma irin taka da kayanka kake bani da zaka zo wurina neman abunka ko kuwa ni kaɗai ce a gidan da don ka rasa abunka zaka tsallake kowa ka taho wajena nema? Me yasa baka tambayi Fatima ba yanzu haka ma ita aka bawa tana ji kana tuhumar mu tayi shiru a ɗaki." Ai kamar kada ta ambaci sunan Umma sai ya mayar da akalar kiran nashi a kanta, ita kuwa baiwar Allah tana zaune akan sallaya tana lazumi tunda ta idar da sallar isha'i bata tashi ba, duk hayaniyar da suke yi tana jiyo su sai dai ko kaɗan bata ji zata saka musu baki ba shi yasa har sai da ya dangana da ɗakinta sannan ta ɗaga kai tana kallonshi. "A ina kika ajiye mini biredin don wulaƙanci kina ji ina nema ba zaki fito ki bani ba?" Yana yi yana bincike ɗakin yana neman inda ta ajiye mishi biredin. Bata tanka mishi ba har ya gama bincike ɗakin tsaf bai ga inda ta ajiye biredin ba don haka ya zuba mata ido yana jin wani sabon ɓacin rai na taso mishi yace "ba dai har kin cinye biredin ba?"
Sai sannan ta amsa mishi cikin tausasawa da "Wai wane biredi ne kake nema haka? Ni babu wanda ya bani biredin ka hasali ma tunda nayi alwalar sallar magriba ban ƙara fita tsakar gidan ba har yanzu sai dai ka tambayi su Abu ko Jamila." A harzuƙe yace "Basu na fara tambaya ba suka ce ba'a basu ba idan ba ke aka bawa ba to ina biredin yayi?" Ƙara tausasa muryarta tayi tace "Wallahi Mallam ba'a bani biredin ka ba, ni yaushe rabon da wani abu naka ma ya shigo hannuna" ta ƙare maganar idanunta na ciccikowa da ƙwalla. Fita yayi yana bala'i wallahi duk inda biredin shi yake sai an fito mishi dashi, ita dai Abu sai rantsuwa take yi akan ita ba'a bata wani biredi ba shi kuma yace ai ita yace almajirin ya kawowa to don me yanzu zata ce bata san maganar ba. Jamila dai na daga gefe tana dariya a zuciyarta tana cewa "Ai yau ko kafi ƙuda naci sai dai ka haƙura da biredin nan don bazan bayar ba, Allah ne ya ƙwato mana haƙƙinmu da kake dannewa, ke kuma makira algunguma ko banza dai nayi miki sanadin ɓacin rai fiye ma da yadda kika yi ta sakani a kwanakin nan" daga baya ma sai tayi shigewarta ɗaki tana rausaya jikinta irin na duniya tayi mata daɗi ɗinnan.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*
*BAQEER*🦼 *NA* *UMM ASGHAR* Da *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ƊAYA*
{31}
Badaru haka ya kwanta ranshi duk a jagule ji yake yi zuciyarshi nayi mishi zafi kwanan nan, har rasa irin masifar shi yake yi, to shi yanzu ba mutuncin kowa yake gani ba tunda burinshi ya lalace jin zafin kowa da haushin kowa yake, duk yanda Abu taso taja ra'ayinshi bata samu fuska ba, da yake sun san kwanan nan bala'i yake ji tun bayan abinda ya samu Baqeer yasa itama bata nace ba ta kwanta tana ƴan mitocinta wanda suka tsaya iya zuciyarta. Dole gobe a cikin jarinta ta bada a siyo mishi kwai da bread yanda zata ƙara kamashi kafin ya canza mata ita ma.
***** Zeey ce ta ajiye littafin dake hannunta tare da yin miƙa tana ɗan bubbuga bayanta, fuskar Inna a tamke tace "Sai kace wani abu kike yi, bayan tun safe in kika tashi ko gadonki ba iya gyarawa kike ba, yarinya sam an sangartata kamar ba mace ba." Zeey tayi gyaran murya tana kwanciya akan kujera tace "Inna wallahi ni ban san me yasa kika takura mini ba, ni kenan komai nayi ba daidai ba." Kallon kazar da take figewa tayi tace "Taso ki tayani to, tunda ke ko kunya ba kya ji irin taimakon nan ma baki iya ba, ke wai a haka ma zaki yi auren?" Kallon kazar tayi kamar tace bazata iya ba sai dai yafda Inna ke kallonta yasa ta sauka tana cewa "Dama ni mijin da zan aura ai komai yi mini zai sa ayi, nifa ko kitchen ba shiga zan yi ba idan nayi aure, iyakaci na bakin ƙofa nace a dafa kaza." Tsaki Inna taja tana mikewa tace "Shirmen banza kenan, ita Nabeela dana koya mata komai kina nufin talaka zata aura?" Da mamaki ta kalleta tace "Inna me ya kawo zancen Nabeela daga hira?" Kai Inna ta girgiza tace "Sam ni mamakin tarbiyar da aka baki nake, manya na magana kina magana, sannan Nabeela ma kike kiranta?" Baki Zeey ta turo don dama in dai tazo gidan Inna an dinga ɓata mata rai kenan shi yasa ko awa biyu cikakke bata iya yi a gidan, anya zata iya zama a gidan nan saboda son ganin Baqeer kawai? Muryar Nabeela ta jiyo ta miƙe ba tare da ta kalli kazar ba, Inna ta girgiza kai kawai ta dawo ta cigaba da figar kazarta. "Seee ji mana." Zeey ta faɗa tare da yi mata murmushi, baki Nabeela ta buɗe ta tsaya tana kallonta cike da mamaki, a tare suka sa dariya kafin tace "Saukar yaushe?" "Ke kai yawon yaushe?" Kai ta girgiza cike da jin daɗi tace "Ke dai wallahi neman maganarki yayi yawa In....." Da sauri Zeey ta rufe mata baki kafin tace "So kike dai a fasa mini jiki a kuma koreni." Dada tana figar kazarta tace "Banda dai jikina babu ƙarfi ai da tuni na aikata." Nabeela ce ta shigo ciki sosai tace "Meke faruwa?" Kafaɗa ta ɗaga tace "Zuwa nayi daukarki." Ai kamar Inna aka taɓa sai cewa tayi "Ɗaukan ta zuwa ina? Inda ba'a ganin girmanta?" Kallon Inna suka yi ta gefen ido sannan suka yi ɗakin Nabeela, gida ne madaidaici wanda aka ƙawatashi, ɗaki huɗu ne a gidan sai dai uku suka gyara ɗayan a ajiye kawai yake Inna na tara shirgi, akan gadon Nabeela ta kwanta ta sauke nannauyar ajiyar zuciya yanayinta a hankali ya canza. Nabeela ce ta zauna kusa da ita, tana kallonta cike da mamaki kafin tace "Meke damunki ne?" Zeey ta miƙe tare da janyo pillow ɗin dake kan gadon ta ɗora akan cinyarta tace "Aunty Nabs." Ta kira sunanta cike da sakalci. "Tunda kika dawo kema kin shareni ga Mummy sai baƙaƙen maganganu take yaba mini son ranta, ni kam ba shiri na tattara na bar muku gidan ku." Ta sake maida kanta kan katifa tana kallon ƙwan wutar ɗakin tace "Ni kaina ban san meke damuna ba, ga abu ina son faɗa amma daga nazo yin maganar sai na rasa abin cewa." Kai Nabeela ta girgiza tace "Wai da a duniya kina rasa abin cewa? Ni ai na ɗauka wannan sai dai mu." Tashi tayi ta zauna da sauri tace "Ya guy ɗin nan yanzu ya san kina sonshi kuwa?" Iska ta furzar tace "Ko kaɗan tsabar ma bai sani ba ni yake tambaya shawara akan ƴan matan shi." "Ba kanta kuma sai ki bashi?" "To ya zanyi?" Kai ta girgiza tace "Ba dani ba nifa sai dai mu hakura da abotar kawai kowa yasha zamanshi amma bazan maida kaina ƙawar ƙarfi da yaji ba, shi yasa nifa har yanzu ban fahimci ya kuke wannan son ba, shi yasa kuma nace bazan yi aure ba sai nima na samu wanda nake yiwa irin wannan son da ake faɗa." Dariya Nabeela tayi tace "Hmm ai ke ko in Allah ya tashi kamaki akan so ko? Harda hakkin mutanen da kika wulaƙanta zai haɗa miki, mu ganki a cikin ɗaki kina kuka shaɓe-shaɓe......" ai bata ƙarasa ba Zeey ta je kai mata duka, a guje ta fita ita ma tabi bayanta, bayan Inna ta ɓoye tana cewa "Wasa nake asibiti zamu kai ki a ƙara miki ruwa." Inna ce ta kalli Zeey dake neman jawo Nabeela tace "Wai ni kam Zainab baki san kunyar idon uwa ba ko?" Tsayawa tayi tana kallonta, ta cigaba "Shin Nabeela ba Auntynki bace kike neman dukanta? A gabana mahaifiyarta?" Takaici ne ya kama Zeey kawai ta koma ɗaki ta kwanta, shiru tayi tana tuno yadda ta bar Baqeer ɗazu, ko ya koma gida yanzu? Me yayi daya daɗe a tsaye ɗazu? Ji tayi zuciyarta ta kasa samun nutsuwa, nan da nan kuma taji hankalinta ya tashi, wayarta ta ɗauko ta dubo number Dada data amsa akan in mutumin ya iso zata kirata ta sanar da ita. Ringing uku ta ɗauka tace "Assallamu Alaikum wanene?" Zeey ce tayi murmushi tace "Hajiya Dada ba dai har kin kwanta ba? Naga dai ba'a daɗe da yin isha'i ba." Jin muryar Zainab yasa ta fara magana a rikice "Zainabu na shiga uku, tun ɗazu nasa a nemo Baqeeru amma har yanzu ba'a ganshi ba." A wani zabure ta mike tsaye tace "Kamar yaya ba'a ganshi ba?" "Wallahi tun fitar da yayi har yanzu bai dawo ba." Ai bata gama jin wani abu ba ta zari key a guje ta fito daga gida, Inna ce ta kalleta tace "Dama kece zaki iya zaman nan? Ke da ko faɗa ba kya so?" Ta kalli Innan sannan ta kalli Nabeela tace "Aunty Nabs zan je na dawo ki faɗawa Inna ta taimaka ta maida wuƙar." Tana kaiwa nan ta fita cikin hanzari. Da yake babu nisa tsakanin Ɗanladi nasidi zuwa Mariri inda Dada take yasa bata daɗe ba ta iso, maimakon tayi gidan inda ta ganshi ɗazu tayi sai dai babu shi babu alamar shi, hankali a tashe ta cigaba da nemanshi, tunanin zuwa wurin Dada tayi ganin tayi nisa cikin layin don har bata san inda ma take ba. Kamar a mafarki ta ganshi zaune gefen wasu yara kamar almajirai suna hira yana zaune yana kallonsu, can taga yana nuna musu abu kamar a takarda sai kuma suka sa ihu suna tafi. Wata nannauyiyar ajiyar zuciya ta saki tana jin zuciyarta na sauka a hankali, lallai ba kanta ƙalau ba, to wai ma Baqeer yaro ne da zata rikice haka? Amma ba laifinta bane tunda yanzu duniyar ce ta koma haka. Miƙa musu takardun yayi sannan ya fara ƙoƙarin burga kekenshi wani ta gani yazo da sauri cikin yaran yana turashi, bata san me suke cewa ba amma tabbas fuskar Baqeer ta canza da alama ya samu nutsuwa zaman da yayi dasu. Motar taja a hankali tana binsu a baya, waigawa yayi gefe nan suka haɗa ido da ita, da sauri ta ɗauke idanunta kallon yaron da yake turashi yayi ya mishi alama daya bari sannan suka yi magana sai taga ya juya. Fitowa tayi daga motar ganin bashi da niyyar cigaba da tafiya, daga ɗan gefenshi kaɗan ta tsaya, sanye take da kayan ɗazu. Shiru suka yi sai kallon gari da suke, a hankali tace "Me kake yi anan? Hankalin Dada ya tashi." Shiru yayi babu alamar amsa a tattare dashi, haka kawai taji duk takaicin kanta ya rufeta, tana mace mai aji me take yi haka ne wai? Ba tunani ba komai? Juyawa tayi sai dai bata yi taku ko ɗaya ba taji yace "Me iyayen yaran nan suke tunani da suka kawosu almajiranta?" Waigowa tayi ta kalleshi ba kallonta yake yi ba sai dai har yanzu idanunshi nakan gefe inda yaran suke, kallonsu tayi kafin tace "Neman ilimi, sannan da rage dawainiyar yaran da suke dashi." Kai kawai ya jinjina ga mamakinta bai ce komai ba ya fara tura kekenshi, so take ta tura mishi amma baza ta iya ba, so take yi ta bishi nan ma bazata iya ba, Baqeer kuwa tunanuka kala-kala ne suka zo mishi a fitar nan da yayi, anan ne kuma ya gane tabbas Allah na sonshi da rahama da bai ɗauke mishi hannayenshi ba, yaga abubuwa da aiyuka kala-kala, tsofaffi haka suke famar aikin ƙarfi don su tallafi iyalansu, zuwanshi wurin almajiran nan hankalinshi ya tashi ganinsu babu abinci babu wata suturar kirki, babu wani abun yi amma basu karaya ba, sai bi suke yi suna neman abun yi don a biyasu ko naira ashirin ne su samu suci abinci, nan ya tsaya wurinsu yana gani suna hirar yanda mutane ke cutarsu in suka yi musu aiki su hanasu hakkinsu wanda hakan ba ƙaramin tada mishi hankali yayi ba, sai dai ga mamakinshi duk da hakan basu karaya ba gobe ma komawa suke yi, kusan sama da rabinsu babu ma mai takalmi, almajirin ne taga ya sake tahowa da gudu ya bi inda Baqeer yake ya riƙe keken, yana turashi, barinta zai yi anan babu ko magana? To wa ya kawoki Zeey? Abinda zuciyarta tace mata kenan wanda ba shiri ta shiga mota, kiran Dada tayi da sauri ta ɗauka tace "Zainabu? Kinga nama sa an siyo minu kati na kirashi wai fita kawai yayi yanzu zai dawo." Tace "To Alhamdulillah, sai da safe." Nan ta kashe wayar ta kwantar da kanta a kujerar motar, ko Dada hankalinta bai tashi ba sanda ta kirata amma ita kalleta harta rugo kamar ance mata mahaifinta aka rasa. Babu shiri taja mota ta wuce, yana kallon sanda motarta ta wuce, da kallo yabi motar tabbas ƴar gidan masu kuɗi ce kuma yanzu ya tabbatar ta ɗauke shi ne a matsayin irin mutanen da suka saba taimakawa don haka dole ya miƙe ya bambanta kanshi daga ragwayen maza.
Tana komawa gidan Inna ɗaki ta wuce ta canza kaya tayi brushing ta kwanta, ko abincin ma bata jin ci sam ta kasa gane abinda ke yawo akanta sai dai yanayin Baqeer ya kasa fita a ranta, tabbas wani abu ya canza a tattare dashi amma bata san menene ba.
****** Bello ne ya kalli Babanshi yace "Baba maganar Asiya, kaga dai ance za'a sake kiranmu Abuja akan aikin da muka yi sannan tunda ni banci na ɗaya ba sun ce zamu je a bamu wasu ayyukan da zamu yi wanda za'a dinga tura musu suna siyarwa a ƙasar su ana dawo mana da kuɗin kafin lokacin tafiyarmu ƙaro karatun yayi, shi yasa nake ganin ba sana'ar data fi wannan a yanzu, don Allah aje gidansu Asiya ayi maganar aure." Wani mugun kallo Baban yayi mishi yace "Wai ni kam Bello kanka ɗaya dai ko? Ina ce kai da kanka ka sanar dani Baqeer shine saurayin Asiya kwanakin baya da na ganku a ƙofar gidan kace kai rakiya kayi?" Bayan kanshi ya shafa yace "Eh shine amma yanzu sun rabu ai." "Kai bana son shirme don Allah, kai da hankalinka yarinyar da ta rabu da saurayinta saboda ƙaddara ta afka mishi ita kake son aure? To ahir ɗinka ko ba don haka bama bazan bari ka auri budurwar abokinka ba, sannan Badaru kana gani yadda yake tijara tun bayan faruwar abun nan baza ka zo ka sake jaza min case dashi ba." Yana kaiwa nan ya fita ranshi a ɓace, Goggo mahaifiyarshi ce ta kalleshi tace "Bello don Allah kada kaci amanar Baqeer yaron nan ya taimakemu a rayuwa kada kayi abinda alhakinshi zai sa komai da kake taƙama dashi ya tafi." Ita ma tana kaiwa nan ta wuce, miƙewa yayi yace "Gobe wurin Baffa zan je ai dai kuna jin maganar shi dukanku idan ya sakaku baku isa kuce a'a ba."
****** Dada ce ta harari Baqeer tace "Haka kawai zaka tada mini hankali." "Dada nifa ba yaro bane, sannan kin san dai babu inda zanje kema, kawai abubuwa ne suka yi yawa a kaina na fita don na samu nutsuwa, kiyi haƙuri idan na tayar miki da hankali." "Wayar tawa ce babu kati babu yadda zanyi na kira ka bare naji kana ina, gashi babu kuɗi a hannuna a ƙarshe sai wurin Talatu na shiga na ari dari nasa aka siyo mini katin na kiraka." Kallon tausayi yayi mata tabbas ba zai cigaba da zama haka ba. Kallon almajirin yayi wanda bai ma san mai zai bashi ba na godiya, Dada ce ta ɗauko fruits ɗin nan lemon da ayaba ta bawa yaron tana yi mishi godiya, shima godiya yayi ya amsa ya juya ya fita.
***** Baba yau a fusace ya kwana washegari ma ko abinci bai ci ba ya ɗauki motarshi ya fita, jikin Abu ne duk yayi sanyi ta fito tsakar gida tana daka garin maganin mata tana yi ranta na ɓaci, Kamalu ne ya shigo yace "Hajiya ya bani makullin mota zan ɗan je yawo." "Kaima dai kasan Babanka ya fita da ita, baka ga bata ƙofar gida ba?" Bashir ne ya fito da alama makaranta zai je, Kamalu yace "Kai Bashir bani kuɗin hannunka." Kallon mamaki yayi mishi ya kalli ɗari biyu da Jamila ta bashi yace "Ai kam kayi hakuri amma bazan baka ba gaskiya babu dalilin da zai sa na baka kuɗin da zanyi amfani dasu na tafi makaranta." "Kai don gidanku ni kake yiwa magana a haka?" A ƙufule Bashir yace "Kayi haƙuri amma bazan bada ba."
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar