Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 23

Baqeer complete - Chapter 23

Baqeer complete Chapter 23: Baqeer complete Chapter 23. Zeey ɗaya daga cikin motar Mummy ta shiga wacce da ita take amfani saboda Daddy bai bata mota ba…

3,346 words

Zeey ɗaya daga cikin motar Mummy ta shiga wacce da ita take amfani saboda Daddy bai bata mota ba har yanzu, fuskarta ta daka da tafin hannunta ta tuno yanda ta dinga zuba atamfofinta cikin akwati dazu da tana haɗa kaya, yanzun ma sanye take da brown doguwar riga har ƙasa take sai wata tattara da aka yi a daidai ƙugunta da black colour, ta naɗa mayafi black a saman kanta, ba mai kwalliya bace amma fuskarta bata rabuwa da kwalli da kuma lipstick, ƙamshin turaren nan nata wanda ya gama bin jikinta wanda sau da dama ko bata sa ba baya barin jikinta na Dior Miss Dior, goshinta ta sake bugawa lallai kanta ba ƙalau ba, yau wai ita ce da karya don ta tafi gidan Inna saboda Baqeer? But why? Tambayar data zo kanta ta furzar da iskar bakinta tace "Whatever ni dai nasan abu ɗaya tausayinshi nake ina kuma so naga ya dawo yanda yake da." And? Tambayar da zuciyarta tayi mata kenan tace "Hmm and ya nunawa Babanshi kuskurenshi na wofintar da rayuwarshi da yayi." And? Zuciyarta ta sake tambayarta, ta ɗan kwantar da kanta jikin kujerar motar kafin tace "And? Shikenan?" Idanunta ta lumshe tana tuno wasu abubuwa da suka faru tsakaninsu a shekarun baya, yaƙe tayi kafin tayi wani murmushi sama-sama, nan ta ja motar ta bar gidan, zuciyarta na kwaɗaita mata dawowar Junaid don tasan tabbas Baqeer zai samu taimakon da yake buƙata. Mai makon tayi gidan Inna kamar yadda ta tsara gidan Dada ta fara yi duk da taso tsayawa ta siyan musu wani abu tasan bata isa ba, tunda tasan waye Baqeer tun kafin ma ya hanata zuwa gara ta shiga hankalinta.

***** Baqeer yau ya tashi duk zuciyarshi babu daɗi sakamakon mafarke-mafarken da yayi daren jiya na auren Asiya da Bello wai gasu nan a gabanshi yana bata abinci a baki, suna yi mishi dariya, ko kunu da ƙosan da Dada ta kawo mishi bai iya ci ba sai kunun daya kurɓa kaɗan wanda ɗacinshi ma yaji. Duniyar gaba ɗaya ta canza mishi babu wani abu da yake burgeshi a cikinta, kamar a mafarki yaji Dada na mata lale da zuwa, kekenshi ya tura da sauri zuwa saitin ƙofar ya jingina da ƙofar kamar yadda ya saba in yana son jin muryarta. Dariya ta6i tace "Dada faɗa mini gaskiya dama jirana kike yi ko?" Tace "Kamar kin sani wallahi har addu'a nake yu Allah ya kawo mini ke ki yiwa yaron can faɗa ko abincin safe bai ci ba ɗan kunun da ya sha ina ji bai fi cokali biyu ba." Baki ta buɗe tace "Dada rufa mini asiri ina na isa?" Hannunta ta kama suka shiga ciki, Baqeer na jin almun tahowarsu ya burga kekenshi da sauri zuwa wajen window garin sauri har hannunshi ya buge da jikin bango ya ƙarasa yana ɗan murza hannun a jikin cinyarshi. Dada tana ƙwanƙwasawa kafin ma yayi magana har ta buɗe ƙofar, Zee daga bakin kofar ta tsaya tare da juya baya da sauri don ita kam bata san me zata ce ba "Tunda baka jin magana ta nace bari tazo tayi maka faɗa." Kallon Dada yayi fuskarshi a tamke sosai yace "Dada me kike faɗa haka don Allah? Salon a samu damar rainani." "Raini na nawa kuma? Tunda gaka nan kullum a ɗaki kamar munafukin miji." Saman goshinshi ya shafa don lamarin Dada ya wuce misali, Zeey kuwa dariya ta bata ta juyo tana kallonshi tana ƙunshe dariyarta, Dada ta bar wurin tana cewa "To sai ka nuna mana ba hakan bane ai." Zeey ce ta kalleshi fuskarshi sam babu annuri a ciki, tana nan tsaye ta jingina da ƙofar dakin, gyaran murya yayi yace "In ba wani abu ki maida mini ƙofar ki rufe." "Ni?" Ta tambaya tana waigawa bayanta ko zata ga wani, takaici ne ya sake rufeshi don banda rainin wayau ba ita kaɗai bace a wurin? Baya tayi tace "Kofarka ce." Bai tanka mata ba ya burgo keken shi zuwa ƙofar ranshi duk a ɓace don ya kula ta raina mishi wayau, sai da yazo daf da ƙofar tasa ƙafa ta jikin ƙofar ta ƙasa ta tare wanda ya hanashi rufewa inya ja kuma yasan bugewa zata yi. Kallonta yayi sai yaga itama kallonshi take yi tace "Dada tayi maka faɗa ba kace komai ba." Kallon mamaki yayi mata mai cike da ayat tambaya, tayi mishi alamu da abinci da hannunta, shima alama yayi mata da ido na meye nata a ciki? Yawun bakinta ta hadiya tace "Ƴar aikenta." Kallon kafarta yayi ta sake gyara ƙafar tace "Muje waje ka bata hakuri." Da mamaki ya kalleta yaushe yarinya kamarta sa'ar Maryam bama Hadiza ba ta fara bashi umarni? Ta ɗaga mishi kai, duk yanda take shakkarshi da yanzu gani take yi dole ne ta canza. Baqeer mamakinta ne ya rufeshi kawai ya juya yana neman komawa ciki, hannu tasa ta rike hannun wheelchair ɗin, cike da mamaki Baqeer ya waigo ya kalleta, idanunshi ta kalla shima ya kalleta wanda tunda suke haduwa basu taba tsayawa kusa da juna haka ba sai yanzu, ji tayi gabanta na wani irin faduwa, tana shakkar Baqeer sosai shi kuma kallonta yake tabbas yasan kamaninta a wani wuri, amma a ina? Zeey ce ta daure tare da haɗiyar yawun bakinta tace "Dada ce keso ka fito abu take so ta nuna maka." "Da shine baki faɗi gaskiya ba kika fara wani zancen?" Hannunta ta zare jikin wheelchair ɗin don yanda take ganinta daf dashi yasa ƙafafunta sun ɗan sage, baya taja wanda hakan yasa ta fitowa daga ɗakin, Baqeer ne ya tura keken ya fito shi kanshi mamakin kanshi yake yi. Sakin baki Dada tayi tana kallonshi har ya fito waje yaja ya tsaya a gefe yana wani kakkauda kai. "A'a Baqeeru? Da na ɗauka abu kake so ba dai fitowa kayi shan iska ba?" Kallon Zeey yahi da sauri wacce tayi saurin yin gyaran murya tace "Dada kin manta abinda zaki nuna mishi?" "Ni? Me zan nuna mishi ni kuwa?" Baqeer ya kalli Zeey sosai, lallai yarinyar nan, kekenshi ya fara neman turawa ya koma tana kallon Dada tace "Dada maganar fa da muka yi akan halin mutum, in ya zauna wa yake so ya kula da mahaifiyarshi?" Jaa Baqeer yayi ya tsaya ba tare da ya juyo ba, wani abu ne ya samu Ummanshi? Zeey tana wurin Dada tace "Dada kina dai ganin mutum shine gatan su Umma, kina kuma ganin yanda Baba ke abubuwanshi don haka mu dai shawarace namu mutum ya samu abun da zai yi don ya taimaki kanshi, akwai abubuwan yi kala-kala da ba sai da kafa ake yinsu ba, wanda basa gani ma suke sana'a bare." Idanun Baqeer ne suka kaɗa suka yi jaa ya waigo yana kallonta, Dada kuwa cike da jin daɗin kalamanta tace "Hmm gashi ni kuma dai ba daɗewa zan yi a duniya ba, duk da ba wanda yasan gawar fari Baqeer dole ka ajiye wannan kuncinin ka san abun yi, in kuma ba so kake Fatima ta tattaro ta dawo nan ta kashe aurenta saboda kai ba." Kallon Dada yayi wani abu na sake taso mishi, maimakon yayi ciki kawai saii ya fita waje yana tura keken, Dada har zata bi bayanshi Zeey ta riƙeta tare da yi mata murmushi tace "Mu barshi Dada dole ya dawo Baqeer ɗinshi nada sannan akwai wani da zai zo ya dubashi ko mu kai shi asibiti sai dai nasan ba yarda zai yi ba in yaji daga nine." "Yayi miki faɗan kayan marmarin da kika kawo ne?" Dada ta tambayeta tana kallonta. Kai ta girgiza alamar a'a, "Hmm to shekaran jiya ko abu ɗaya bai sha ba saboda faɗa." Raurau tayi da ido tace "An kusa hanani zuwa wurinki da alama." "Shareshi wannan ne bai isa ba, in zaku je wurin mutumin sai ku tafi da Salim, in ma zuwan ne ya zama dashi ina ganin zai fi fahimta." Kai ta ɗaga cike da gamsuwa.

Baqeer kuwa keken shi ya burga gaba da gidan Dada kaɗan inda ya tsaya yana kallon mutane kowa nata hada-hadar kasuwanci, kowa dai harkar neman kudin shi yake yi.

******** Abu ce ta kalli yaron da aka aiko tace "Kai bana son iskanci wallahi wannan robar ko ba'a faɗa ba an ɗiba ruwa aka ƙaramin a cikin tsumin nan don haka ka koma kace bazan amsa ba." "Don Allah ki amsa ki bata kuɗinta tace bata so." Tsaki tayi tace "Wallahi ko kabar gidan nan ko nasa Kamalu yayi maka dukan tsiya." Juyawa yaron yai a tsorace don kuwa sun san waye Kamalu, tsaf yanzun nan sai yaji mishi ciwo. Jamila ce ta fito tana ƴan harare-hararenta, Abu ko kallonta bata yi ba, zama tayi akan kujera sai kuwa ta fara kakarin amai, ji kake buiu, ta sake yi buuui. Dariya Abu ta kwashe dashi tace "Hala kinci ƙuda ne ko tsutsa shi yasa kike ƙoƙarin yin amai?" "Kin manta maciji naci ba tsutsa ba." Abu ta sake fashewa da dariya tace "A'a to wai dai ba cewa zaki yi ɓatan watan kika yi ba ko?" Jamila tayi ƙwafa ta koma ciki ranta na sake ɓaci. Umma na daga ɗakinta tana jiyosu, kai kawai ta girgiza…

***** Baqeer ya ɗan jima kafin ya dawo, sai dai kafin ya dawo Zeey ta tafi don yana tsaye tazo ta wuce bai kula ba, sai ita data ganshi, ta dade a gefenshi daga baya sai da taga yana shirin tafiya sannan ita ma ta tada mota tayi gaba, zuciyarta duk ba daɗi. Gidan Inna ta wuce kai tsaye. Inna na ɗaki tana ƙirga kuɗi tana jin Zeey ta ɗaga katifa ta sakasu sannan ta kuna radio tana ji kamar ba a gidan ake sallamar ba. Zee ce ta shigo tace "Hajiya Inna tawa dama nasan kina ciki magana ce bakyajin yimin." Fuskar nan tata a ɗaure babu alamun fara'a tace "Tunda ke bakinki bazaiyi shiru ba sai kin faɗa ai ba laifi." Zama tai tace "Hmm Allah dai ya kawo randa zaki saki rai dani." Wani kallo ta mata tace "Yau kuma me ya kawoki? Bayan ba san zuwa kike ba?" "Aunty Nabila fa? Batanan?" "Ba'a sani ba, wai mai aikin ku ce Nabilan da baza'a barta tazauna a gidansu ba? Bayan in taje gidan naku banda aiki ba abinda kuke sata?" Kai ta girgiza tace "Kedai Inna neman faɗa kike amma yaushe aka sakata aiki a gidan?" A fusace Inna tace "Ke ai ba'a isa ai magana ba sai kin bada amsa san ranki, wannan halin naki yasa sam bana sake miki an bi an sangartaki ace komai ya fito daga bakinki sai kin faɗa? Sannan Nabilan karya akai ko gadan da kika kwana na zakice ba ita ke gyarawa ba?" Mikewa Zeey tai tace "Bari na shiga ɗaki na huta in kin huce mayi maganar." Tana kainan ta fita nan fa Inna tahau faɗa Zeey kam ko a jikinta ɗaki ma ta shiga ta baje a kan gado tana tunanin abinda ya faru tsakaninsu da Baqeer.

****** Bayan magriba ne Daddy ya halarci babban falon bakinshi inda ya gayyato dattijan unguwar, anyi abinci kala-kala yadda kowa zai ci ya ƙoshi, sosai yaji dadi da aka ce Zeey bata nan shi yasa ko faɗa bai yi ba a ƙalla babu abinda zai bashi matsala. Zama suka yi duk wuri ɗaya ana ci ana hira kowa na yaba miah da bashi tabbacin zai bashi gudunmawa ɗari bisa ɗari. Badaru ne ya sauka gaban mai bread zai sayi na karin safe. Mai bread ya kalleshi yace "Malam Badaru har kun gama taron ne?" Da mamaki yace "Taron me kuma? Don ni dai daga kasuwa ma nake." Taro dai da za ayi a gidan Alhaji Suleiman Karaye ko da yake kai ai kowa yasan ba kwa shiri to na tabbatar shi ya hanaka zuwa." Nan da nan Baba ya gimtse fuska tamm, ranshi ya ɓaci sosai yace "Yanzun taro ake yi a unguwar babu ni?" Yana kaiwa nan ya amshi bread ɗin shi ya nufi gida, a waje ya bawa almajiri ya miƙa mishi ciki sannan ya wuce gidan Suleiman Karaye, dole ne yaci zarafinshi don ba zai yarda da wannan iskancin ba, ai ko ba zaije ba sai a faɗa mishi yace baya son zuwa yafi yaji a titi.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Muhd Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN*

{30}

Almajirin da Baba ya bawa saƙo ne ya shiga cikin gidan yana sallama, Jamila ce kaɗai a tsakar gidan tana alwala, Abu da Umman Baqeer duk sun shige ɗakunansu suna sallar isha'i. Miƙa mata ledar yayi yace "Wai gashi aka ce na shigo dashi ciki". Karɓa tayi ta latsa ledar sai taji biredi ne, ajiyewa tayi a gefe tace mishi "To jeka angode." Sai da ta gama alwalar sannan ta ɗauke ledar ta shige da ita ɗakinta ta buɗe durowa ta ajiye tana cewa "Wannan biredin dai ya shigo kenan wallahi sai dai ka sayi wani baƙin munafuki, da haka zaka ɗauka ka kai mata ku cinye ba tare da mun san anyi ba." Hijabi ta ɗauka ta kabbara sallah ranta fal farin ciki don wallahi babu mai karɓar biredin nan a hannunta yau, suma sun samu na karyawa da safe ita da yaranta.

Shi kuwa Mallam Badaru ya nufi gidan Alhaji Suleiman Ƙaraye yana ta zage-zage a hanya kamar wani sabon kamu. Tun daga gate maigadi ya tsayar dashi ya hana shi shiga nan ma ya rufe shi da masifa yana cewa "Da zaka hanani shiga ni ba dattijon unguwa bane? Ko kuwa ce maka aka yi kada ka barni na shiga wurin taron da ake yi? owoo wato kun san abinda kuka taka baku da gaskiya shi yasa kuke ƙoƙarin hanani shiga?" Mamaki ya rufe mai gadi ganin ba zai iya da jidalin Mallam Badaru ba yasa ya buɗe mishi ƙofa tunda yasan ana taron da yace mishi yazo a cikin gidan. Wucewa yayi ciki yana ayyana tabbas sai yayi wa Suleiman Ƙaraye rashin mutunci irin wanda bai taɓa zato ba, don cin fuska da rashin mutunci har ya shirya taron manyan unguwa a kasa sanar mishi saboda munafurci, haka ma fa kwanaki da yazo ya saka mishi kuɗi a aljihu irin ga ɗan maula yazo, sannan shi fa har yanzu ba wai ya yarda da cewar da yayi ba ɗanshi bane ya nakasta mishi yaronshi ba kawai dai yayi shiru ne ganin baya da tartibiyar shaidar da zai gabatar.

Yana shiga parlourn da ake taron sai ya tarar da mutanen unguwar wanda yawancin su abokan hulɗar shi ne ana ta raha ana cin abinci babu wanda ya kula da shigowar shi wurin. A take yaji ranshi yayi wani irin ɓaci cikin fusata yace "Ehh yau na tabbatar da mutum mugun icce ne shine don munafurci za'a shirya taron manyan unguwa a kasa shaida mini saboda an mayar dani saniyar ware, ko kuwa kun cireni daga cikin dattijan unguwa?" Ya kalli makwabcin shi Mallam Nuhu dake ta yagar naman kaza yace "Au don munafurci har da kai ake cin dunduniyata, Mallam Hamza? Alhaji Kabiru? Ashe dukkan ku munafukai nake tare dasu ban sani ba, ai dai kun san ƴar tsamar dake tsakanina da wancan mutumin" yace yana nuna Suleiman Ƙaraye dake zaune akan doguwar kujera yana kallon duk abinda yake yi fuskarshi ƙunshe da murmushi kamar ba taro Mallam Badaru yazo ya ɓata mishi ba, ya cigaba "Amma shine don munafurci har da ku a halartar taron daya shirya? Eh wato gani ni ba kowan-kowa ba shi yasa aka shirya taro aka kasa sanar dani, ko?"

Kowa dai yayi tsit sun zubawa Mallam Badaru ido yana ta zuba tijara sai mahaifin Bello ne ya taso yace "Haba Mallam Badaru ya kamata fa idan an girma a riƙa sanin an girma, ta yaya abinda ya faru tun da ƙuruciya zaka yita riƙe dashi har yanzu?" A take ya taso mishi da masifa kamar zai kai mishi duka yana cewa "Dalla gafara can yi mini shiru baƙin munafuki da wani munafukin gantalallen ɗanka maci amana. Waye kai da har zaka taso ka tareni kana faɗa mini maganar banza, in banda ma Baqeer daya janyo mini masifa da bala'i ya haɗa sabga da ɗanka kai ka isa ka kalli inda nake shine har zaka zo kana yi mini zancen banza, dalla matsa ka bani wuri, ko sanda aka yi abun ka sani ne? Sai shishigi kamar an aikeka." Sai a lokacin Suleiman Ƙaraye ya taso cikin lumana saboda ya kare mutuncin shi dana kujerar da yake nema yace "Haba Mallam Badaru ya kamata mu manta duk wani abu daya faru lokacin ƙuruciya a yafi juna haka nan, bai kamata ace har girman nan namu da muka fara ajiye jikoki ana jin kanmu akan ɗan abinda bai taka kara ya karya ba."

Ai kuwa dai ranshi yayi mummunan ɓaci don yana ganin rainin wayo kawai Suleiman ɗin ke neman kawo mishi irin wanda ya saba yi mishi tun da can don haka yayi ta bala'i yana masifa har yana cewa in dai yana raye Suleiman Ƙaraye bai isa hawa kujerar senator ɗin da yake hari ba don sai ya tabbatar ya nunawa mutane asalin waye Suleiman Ƙaraye da ɓoyayyiyar manufarshi akan su. Da ƙyar dai aka samu aka fitar dashi daga cikin gidan yana ta zage-zage yana masifa, bayan fitarshi sai suka hau zancen ba'a san meke damun shi ba da sam baya so a zauna lafiya. Wani yace "Ai kun san tunda iftila'in nan ya faɗawa ɗan shi ya koma kamar wani zararre, watakila dan ganin burin da yaci akan ɗan ba zai cika ba ƙwaƙwalwar shi ta taɓu."

Anan Alhaji Suleiman Ƙaraye ke jin abinda ya faru da Baqeer ɗin, sai yayi ta mamaki yana jinjina lallai kam dole Badaru ya ƙara gigicewa tunda ɗan da yake ji dashi ya zama nakasashe. Haka dai taro ya tashi kowa ya tafi da abinda Mallam Badaru yayi a bakin shi sun kuma tabbatarwa da Alhaji Suleiman Ƙaraye da zasu taimaka mishi wajen yaɗa kyakkyawar manufarshi a wajen sauran mutanen unguwa don irin shi dama suke buƙata da tsayawa takarar siyasa waɗanda suka san su suka san buƙatunsu da zasu yi musu aiki tuƙuru wajen magance musu matsalolin su ba waɗanda ba'a ganinsu ba sai lokacin campaign yayi. Haka suka yi sallama yana jin daɗin yadda taron ya kasance don yana hangowa kanshi nasara a zaɓen da za'a gabatar duk da ma Badaru yaso ya watsa mishi taro amma da yake kowa yasan halin shi sai abun bai zama wata babbar matsala ba. Yana shiga gida yake faɗawa Mummy yadda taron ya kasance har ma da ƴar hatsaniyar da Mallam Badaru yaso tayarwa anan nema yake faɗa mata abinda ya samu Baqeer. A take ta nuna bata san zancen ba duk kuwa da ita ta taimakawa Kabir wajen ɓoye laifin shi a wajen mahaifin nashi, tasan tabbas in har ya sani tofa akwai matsala sai cewa tayi "Garin yaya kuwa?" Yace "Wallahi ban sani ba sai dai ban sani ba ko hatsarin da yazo yace yaron yayi kwanaki ne sanadi wanda har yace Kabir ne ya buge ɗan nashi."

Sai ta taɓe baki tace "To waya sani ne kam, shi da ba'a rabashi da neman rigima, ai tun lokacin na faɗa maka sharri ne kawai yake so ya ƙullawa Kabir don ya samu abinda zai riƙe yace kayi mishi kaga in yayi haka ai ya zubar maka da mutuncin da yasan mutane na ganinka dashi."

"Haka ne kuma fa, to Allah ya kyauta mishi ya ganar dashi hassada dai ba abu bace me kyau."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull