Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 22

Baqeer complete - Chapter 22

Baqeer complete Chapter 22: Baqeer complete Chapter 22. ***** Zeey ce zaune a ɗaki ta shige cikin bargo tana kallon korean drama 'Killing Vote' mind dinta…

3,296 words

***** Zeey ce zaune a ɗaki ta shige cikin bargo tana kallon korean drama 'Killing Vote' mind dinta gaba ɗaya yana kan tv ɗin dake manne a bangon ɗakinta, wayarta ce tayi ƙara da takaici ta janyota, number ce hakan yasa ta kara a kunnenta ba tare da tayi magana ba, Baqeer shima kasa magana yayi sai sautin numfashinsu ne daya sauka a tare, Zeey cike da mamaki ta kalli wayar tata ta sake karawa a kunnenta haka kawai taƙi yin magana don rainin wayon ya isa a kira ka a waya a ƙi magana kuma. Baqeer kuwa ji yayi ya kasa cewa komai, to yace me? Mun gode karki sake? Ko kuwa karki sake zuwa? Bayan yasan in tace ta daina ba daɗi zai ji ba. Takaicin kanshi da rashin sanin abinda zai ce duk ya isheshi. Zeey ranta ya ƙara ɓaci don ta tabbatar wannan kuma rainin wayau ne, a speaker tasa wayar kawai ta ajiye a gefe ta cigaba da kallonta, Baqeer ganin kuɗin shi na tafiya ba tare da yasan me zai ce ba yasa ya kai hannu zai kashe wayar, mamaki ne ma ya kamashi da ya fara jiyo sautin kallo a cikin wayar, nan ya kashe tare da ajiye wayar akan katifarshi, haushin kanshi ya ƙara kamashi, haka zai zauna komai bai iya ba kamar wani yaron da aka haifa yanzu? Ƙofa ya buɗe Dada na ganinshi ta ɗauke kai ta cigaba da tsinke zogalen da take yi, kusa da murhu ya nufa ya sunkuyo taga yana neman haɗa wuta, duk yanda taso ta ƙunshe dariyarta kasawa tayi haka tana gani ya haɗa wuta yasa tukunya da ruwa, Dada abin sai ƙara bata dariya yake da yanda fuskarshi take a ɗinke babu alamun fara'a, yana gamawa ya koma ɗaki. A hankali ta girgiza kai lallai Baqeer babu shakka zuwan yarinyar nan da shawarar da take bashi yasa ya fara canzawa, murmushi ta saki ko ƴar gidan wacece? Tabbas zata tambayi Maryam in tazo. Zeey kuwa ganin an kashe wayar tayi tsaki tace "Ni dai kwanan nan ban san da wasu irin mutane nake haduwa ba." Ta sake maida hankali kan kallon aka sake kiran ta, kanta ta cusa cikin bargo ta ɗan yaye bargon tana bubbuga ƙafafunta, cike da takaici ta janyo wayar gwara ta dauka in kudinsu ya ƙare sun daina damunta, tana ɗauka tasa a speaker ta ajiyeshi a gefenta "Don Allah a maidani kunne bana son a ajiyeni a gefe." Kalaman da suka fito kenan daga cikin wayar wanda ya sata bin wayar da kallo, ganin number Junaid ya sata sakin murmushi sosai wanda har haƙoranta suka fito "To ya?" "Haka dai zaka cigaba da saka mini ido kamar mai CCTV ko?" Shima murmushin yayi yace "To ni dai ɗari bisa ɗari ina da yaƙinin babu wanda yasan ki sama dani." "Shiyasa ka turo a ganni?" Dariya yasa yanzu kam tace "Kar ka wani wayance nasan kaine." Ya ɗan yi juyi a kan gado yace "Wato dai kin gama sanina kema?" Kafaɗa ta ɗaga kamar a gabanshi take tace "Ai ƴar ƙure ne abun?" "Na sakar miki ƙotar don nasan tabbas aka fara tsab za'a ƙure ni." Hira suka cigaba dayi sosai wanda kana ganinsu kasan sun saba da juna sosai, can tace "Ya aikin ba zaka dawo nan ka cigaba ba?" Ajiyar zuciya yayi yace "Dole na dawo tunda an ce na aureki." Kai ta girgiza tace "Kasan dai bazan aureka ba, na sha faɗa maka abota ne kawai a tsakanin mu." "Nima na sha faɗa miki abota tana komawa soyayya, kuma a kaina zaki amince." Shiru ta yi jin wani abu yazo ranta, da sauri ta gyara zama tace "Junaid please serious magana when will you be back? Akwai wani brothern ƙawata da ya samu matsala a kafafunsa, an dai ce paraplegia ne so nasan ku da yake aikin ku ne kun san ko akwai wani abu da mutum zai yi." Cike da kulawa yace "Subhanallah, garin yaya?" Tace "Am not sure exactly nasan dai accident yayi." Ya ɗan yi ajiyar zuciya yace "Lallai he needs us, kinga karatun da aikin da nake kenan na physiotherapist so ina saka ran nan da 4days zan dawo don abinda ma na kira na sanar dake kenan, idan na dawo zan fara aiki a asibitin Dad ɗina in yaso sai ki ma friend ɗin taki magana su kawoshi mu gani, ko bai warke ba at least zai iya controlling ɗin jikinshi." Wani irin daɗi ne ya kamata wanda yasa shi cewa "Yana da aure ne?" Tace "A'a menene?" Shiru ya ɗan yi sai dai yasan Zee ba yanda za ayi taso gurgu yarinyar da manyan maza kyawawa masu kuɗi ma bata kulasu ba. Da wannan suka cigaba da hira kafin suyi sallama, wani nishaɗi ne kawai yake sake rufeta don Junaid har shaidar yabo an bashi saboda ƙwazonshi tana saka ran zai taimaki Baqeer sosai, ji take ba zata ba gobe saboda akwai inda zasu da Mummy amma jibi zata je ta sanar mishi.

****** Hadiza ce kawai ke share hawayenta ganin ta rasa me zata dafa a cikin gidan, gidan babu komai balle ta lallaɓa ta dafa wani abun, gashi ko naira biyar bata da shi balle ta sa a siyo mata kuka, yarinyarta tasa a baya ta fito daga ɗaki, kishiyarta dake wanke tsakar gida ta kalla don ko abinci basa hadawa saboda ita tana ɗan aikinta na gwamnati tana samun ƴan kuɗaɗen ta. Gida ta nufa tana tafe tana hawayen tunanin Baqeer don tabbas wannan abu ita yafi shafa. A ƙafa taje tafiyar sama da minti ashirin, da Salim suka haɗu shima zai je gidan Umma, nan suka gaisa suka ƙarasa gidan sun ƴar hira, ta bayansu kawai suka ga an tallewa Salim ƙeya sai ji kake tass. Da sauri suka juya a tare, Kamalu ne anci riga da wandon gayu yana girgiza ƙafa, Bashir na gefenshi don ya kira shi zai aikeshi ne ya hango Salim ya taho da sauri shima yabi bayanshi. Da mamaki Salim yake kallonshi yace "Kamalu menene hakan?" Daƙuwa yayi mishi yace "Gidanku ne, uban me kazo yi gidan mu? Ko zuwa kayi kaja faɗa dani don na ƙwace Roshni ta dawo inda ya kamata?" Wani kallon mamaki yayi mishi yace "Yanzun ma zancen Roshnin ne?" A ƙufule Kamalu yace "Kasan Allah inma ni kake nema da fitina daidai nake da kai, muje filin casu kaga hauka." Tsaki Salim yayi yana neman shiga ciki Kamalu ya finciko shi yace "Wai ni ka yiwa tsaki? Kai dan gidanku ni sa'anka ne?" Salim na neman ƙwace jikinshi amma Kamalu sai hayagaga yake yi yana zage-zage wanda yasa Hadiza saurin shiga ciki don ya kira azo ayi mishi magana.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS*

{28}

Bashir ne ya rirriƙe Kamal daga ƙoƙarin kaiwa Salim duka da yake yi shi dai Salim yayi tsaye kawai yana kallon shi da haukar da yake yi don baya saka Kamal a sawun mutane masu hankali. Umma ce ta fito daga cikin gidan tana cewa "Kamal lafiya kuwa?" Don ko da Hadiza ta shiga gida ta faɗawa Abu ko zata fito tayi mishi magana gashi can a ƙofar gida yana cakumar Salim da faɗa cewa tayi babu inda zata, ai haka nan Kamalu ba zai nemi rigima dashi ba sai idan shi ya fara tsokanarshi don haka a ƙyaleshi yaci ubanshi yadda gobe ko kallon banza bai isa yayi mishi ba tunda yasan idan yayi ma ba ƙyaleshi zai yi ba, sai Umma ce ta saka hijabinta ta fito jin da Salim ake faɗan tasan kuma wurinta yazo tunda dai Baqeer baya gidan yanzu bare tace ko wajenshi yazo.

Wani banzan kallo yayi wa Umma yace "Malama ki rabu dani na koyawa wannan tsageran yaron hankali, kai har ka isa kayi mini tsaki a ƙofar gidanmu don ubanka?" Ya nuna Salim da yatsa yana ƙoƙarin kai mishi mari sai dai Bashir ya rirriƙe shi ya hanashi kaiwa ga Salim ɗin. "Umma ina yini" Salim ya durƙusa yana gaisheta kamar ba da shi Kamalu ke faɗan ba. "Lafiya lau Salim, me ya haɗa ka da Kamalu ne?"

Murmushi ya saki yace "Wallahi Umma babu abinda nayi mishi kawai ina tafiya naji ya talle min ƙeya yana cewa zai koya mini hankali." Ita kanta Umma sai da tayi dariya jin wai ya talle mishi ƙeya kamar wasu ƙananan yara. Kallon Kamalu tayi tace "Kayi haƙuri kome yayi maka kaji Kamalu zan yi mishi faɗa In Sha Allahu ba zai ƙara tsokanarka ba". Ƙwace jikinshi yayi daga riƙon da Bashir yayi mishi ya saki wani dogon fito kafin ya kalli Salim da har lokacin yake durƙushe yace "zamu haɗu ne don kada ka ɗauka ka sha, sai ka raina kanka wallahi duk ranar daka sake ka shigo hannuna" ya wucesu anan yana tafiyar ƙwambo irinta nigogi. Gaba ɗaya suka bi bayanshi da kallo har sai da ya karya kwana sannan umma tace "Salim mu shiga daga ciki ko?" Har ya miƙe zai bi bayanta zuwa cikin gidan sai kuma ya tuna da Baba da tijarar da yayi mishi akan Baqeer to ina ga ace ya ganshi a cikin gidanshi ai duk abinda yayi mishi shi ya saya da kuɗin shi don haka yaja ya tsaya yace "a'a Umma ba sai na shiga ba, dama Baqeer ne yace nazo na duba mishi ke". Sai taji ƙwalla ta cika idanunta, Allah sarki Baqeer wato har a halin da yake ciki ma ita ce damuwarshi, yasan rashin shi a kusa da ita ba ƙaramin taɓa zuciyarta yake yi ba to amma ya zasu yi bayan suyi haƙuri su rungumi ƙaddarar data raba tsakaninsu tunda Baba yayi rantsuwar ya bar zama mishi a gida kenan ita ma kuma baza taso ya ƙara dawowa cikin gidan da zama ba gara ya koma gefe yayi rayuwarshi har Allah ya dubesu ya kawo musu ɗauki a cikin halin da suka tsinci kansu a ciki.

Tayi murmushi "Baqeer kenan, abinda kullum sai ya kirani a waya mu daɗe muna hira shine kuma ya taso ka daga kan ayyukan ka don kazo ka duba mishi ni kawai, bai gamsu da cewar da nake yi ina lafiya ba kenan". "A'a Umma ba haka bane, kin san bai taɓa daɗewa irin haka bai ganki bane shi yasa duk yabi ya damu amma ba don bai yarda dake bane".

"To ai shikenan tunda kareshi kake yi sai ka faɗa mishi lafiya ƙalau muke nima ina nan tafe naje na ganshi ai In Sha Allahu". Hannu yasa a aljihu ya fito da kuɗi naira dubu biyu ya miƙa mata "Umma gashi wannan babu yawa dai". Kallonshi tayi ta kalli kuɗin da yake miƙo mata tana girgiza kai tace "a'a Salim bazan karɓa ba, gaisheni da kazo yi ma ya wadatar, nagode ƙwarai Allah yayi muku albarka".

Ƙara miƙa mata kuɗin yayi yace "na ɗauka ni da Baqeer ɗaya muke a wajenki, kenan ɗa zai yiwa mahaifiyarshi alheri ta maida". Hannu tasa ta karɓi kuɗin tana yi mishi godiya haɗe da jera mishi addu'o'i. Sosai yaji daɗin hakan kuwa shi yasa kuma yake son Umman Baqeer ɗin saboda yadda ta ɗauke su duka ƴaƴanta bata taɓa bambantasu ba a komai, yadda take zaunar dashi tayi mishi nasiha haka suma take yi musu bare shi da yayi maraicin iyaye tun yana ƙaramin shi. Tana shiga gidan ta miƙawa Hadiza kuɗin hannunta ba tare data ƙirga taga ko nawa bane. "Na miye wannan ɗin Umma?" Ta tambayeta. "Salim ne ya bani sai kije ki riƙe a hannunki don nasan ba lallai ne da akwai wani abu a hannunki ba". Kuka kawai ta fashe dashi cikin ranta tana ƙara jin ƙaunar mahaifiyar tasu mai yawan kyautayi da tausayawa a garesu. Sai da tayi kukanta ya isheta sannan ta share hawayenta tace "nagode ƙwarai Umma, Allah ya ƙara girma yaja mana da rayuwarki, wallahi kamar kin san fitowar nan da nayi rashin abincin da zamu ci ne dalili, yau na tashi ko ƙwaya bani da ita ga yara sun kusa tasowa daga makaranta dama kuma ba wani abu na basu ba da safe koko ne na saya musu da ɗan canjin da ya rage mini suka sha suka tafi makarantar. Yanzu shikenan a haka zamu yi ta zama cikin wahalar rayuwa Umma? Dama Yaya Baqeer ne yake taimaka mini yanzu shima ga yadda Allah yayi dashi shi kuwa Babansu Aydah ko zamu mutu da yunwa ba damuwa yayi ba".

Da tausayi Umma ke kallonta tunda ta fara kukan, ita dama tunda ta ganta yanzu da ranar nan tasan ba zuwan daɗi tayi ba, miji ne ta gamu da wani irin mugun mutum da bai san ya sauke haƙƙoƙin su dake kanshi ba. Idan ma da ace yana basu abinci sauran haƙƙoƙin su ne baya saukewa da sauƙi to shi ko abincin ma ba basu yake yi ba ba don ba zai iya basu ba sai don bai ɗauki hakan a matsayin wani abu mai muhimmanci daya zame mishi dole ba. Haƙuri Umma tayi ta bata akan irin zaman da take yi a gidanta, tashi tayi ta ɗaga katifa ta ƙirgo wasu kuɗin ta dawo ta miƙa mata tace "Kuɗin kujeruna ne dana sayar dama nace zan shawarceku muga abinda ya kamata muyi dasu don zama a haka bai ganmu ba daga ni har ku don har gara ma Maryam bata nemi komai ta rasa ba a gidanta tunda mijinta na bakin ƙoƙarin shi a kanta, wacce sana'a kike ganin ya kamata muyi tunda dai kin san Allah ne gatanmu Baqeer ne gatanmu shi kuwa a yanzu sai dai ma a tallafa mishi tunda ga yadda rayuwa tayi dashi, dole ne ki dage ki nemi na kanki don ba zai yiwu ki cigaba da zama a haka ba abincin da zaki bawa ƴaƴanki yana gagararki."

Karɓar kuɗin tayi tana jujjuyasu tace "To ni Umma wacce sana'a zan yi bayan kin san mutumin nan idonshi idon kuɗi sai yasan yadda yayi ya rabani dasu, dama ace zan samu aiki nema ko na cleaner ne sai nayi amma a yanzu ina fara sana'a zai kafa mini ƙahon zuƙa sai yaga yadda yayi ya rabani da ita hankalinshi zai kwanta.

"Ai kuwa dole ki tashi ki nemi na kanki ki kuma san yadda zaki yi ki tattala abunki ki bar bari yana sanin samunki tunda wanda yaji ya gani ya ɗauke miki larurorin gidanki yanzu baya dashi, ita kishiyarki da yake ta iya tattala kayanta ai kinga bata cikin wahalar dake kike ciki. Dole ne ki nemi wani abu ki dinga yi da zaki taimaki kanki ba kullum ba kina jira ayi miki ba."

"To Umma, In Sha Allah zan duba naga me ake buƙata a wajen namu sai na fara, dama Yaya Baqeer ne yace zai saya mini injin markaɗe idan yaje Abuja wajen gasar nan ya dawo to ashe ma baya da rabon zuwa wajen gasar tunda ga ƙaddarar data afko mishi," ta ƙarashe maganar tana share hawaye.

Itama Umma hawayen ta share sai kuma tace "Nawa ne injin markaɗen? Idan wannan kuɗin zai saya ai gara a saya ki fara sana'ar akan dai kiyi ta zama a haka babu abun yi abincin da zaku ci yana gagararku idan yaso abinda ya ragu daga cikin kuɗin sai na sayi wani injin taliyar na auni fulawa na dawo da yin aikin taliyar dama kwana biyun nan sai shigowa ake yi nema sai dai nace babu." Murmushi ta saki jin Umma zata saya mata injin markaɗen tace "Wallahi Umma ban san nawa bane sai dai na bincika naji duk yadda ake ciki zan kira na faɗa miki."

Tace "to shikenan kiyi hakan, Allah ya taimake mu ya dafa mana". "Ameen Umma, bari na tashi na koma kada yaran nan su dawo su tarar bana nan gashi ban bar musu komai da zasu ci ba."

*****

Kayanta ta haɗa cikin akwati kamar mai yin wata idan ta tafi ta janyo trolley ɗin ta nufi ɗakin Mummy, bata tarar da ita a ciki ba sai ta fita parlour nan ma bata ganta ba sai data shiga kitchen sannan ta ganta suna haɗa abinci ita da masu aikinta. Kallonta Mummy tayi ta kalli ƙatuwar akwatin da take ja tace "Ina zaki haka da akwati baby kamar mai gudun hijira?" Turo baki tayi gaba irin na shagwaɓaɓɓun yara abinda ya riga ya zame mata jiki har ma bata sanin lokacin da take yi tace "Nima gidan Inna zani tunda kin korar mini small Aunt gashi nan taƙi dawowa ko ɗaukar wayata ma bata yi nasan kuma duk laifinki ne ya shafeni." cikin ranta kuwa cewa take yi gara ta tafi gidan Inna yadda zata samu tana zuwa duba Baqeer akai-akai don tasan Inna ba hanata fita zata yi ba bare tabi ba'asin inda zata je.

Baki Mummy ta taɓe tace "Da dai wata ce bake ba, ke ɗin ce kike iya zuwa wani wurin ki kwana?"

Dire-dire ta hau yi tana cewa "Allah Mummy idan na tafi sai kin je kin yi bikona kafin na dawo, gara ma na matsa na baku wuri kinga ai sai ina nan Kabir zai samu wacce zai takurwa." Har ta juya zata fita sai Mummy ta tsayar da ita tace "Da dai kin haƙura da tafiyar nan har Daddynku ya dawo ki faɗa mishi kin dai san halin shi bai cika son yawan zuwa wani wuri a kwana ba."

Dawowa tayi ta rungume Mummyn tace "Please mana Mummy idan ya dawo sai ki faɗa mishi, kin dai san yadda zaki lallaɓa shi kada yayi faɗa amma wallahi idan ni na tambayeshi ba bari na zai yi ba kina dai ji ranar nan daga cewa ina so naje Ɗambatta ya rufe ido yana zazzaga faɗa kamar cewa nayi idan naje bazan dawo ba." Zeey ita ce weakness ɗin Mummy bata iya yi mata musu duk abinda tace tana so shi take yi mata don haka ta kasa hanata tafiya gidan Innar kamar yadda ta buƙata duk kuwa da tasan idan Daddy ya dawo ya tarar bata nan sai yayi faɗa. "Shikenan Zeey ki gaishe da Innar amma fa idan yace bai yarda da zamanki acan ba dole ki dawo don kin sanni ni dai bana son tashin hankali".

"Thank you my Mummy, ba ma zai ce ba In Sha Allah, na tafi sai na dawo" taja akwatinta ta fice daga kitchen ɗin tana jin wani tsantsar farin ciki yana ratsa ta, ko babu komai ta samu hanyar zuwa taga Baqeer ba tare da ta yiwa Mummy ƙarya ba.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA TARA*

{29}

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull