Baqeer complete - Chapter 21
Baqeer complete Chapter 21: Baqeer complete Chapter 21. *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
3,176 words
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
#Baqeer #Zeey #Kamalu #Sanyin Zuciya #Rayuwata
*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*🏌🏻♀️
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA*
{26}
Maida ƙofar Baqeer yayi kawai ya juya kekenshi tare da jinginar dashi a jikin ƙofar, kunnenshi sosai ya kasa a waje yana son sanin me suke tattaunawa. Dada ce tasa dariya tace "Ahh yau naga babban, haka kawai an turkeni can a lungun ɗaki ana neman rufeni da raina." Zeey ce ta buɗe baki cike da mamakin kalamanta tace "Dada ni dai ba ni bace kin san wanene." Harararta tayi tace "Amma ai kina kallo ana neman rufeni baki taro ni ba." Dariya Zeey tayi don tana son zolaya takaicinta ɗaya gidansu komai da gaske ake ɗaukan shi tace "Ke dai Allah Dada har da neman magana, ni ina bakin ƙofa ina ni ina shiga ciki kinkimo ki?" "To ai da baki kinkimoni ba na kinkimo kaina, ke ni ba wannan ba wai kin tabbatar babu komai tsakaninki da Baqeeru?" Ido ta zaro da sauri tace "Babu komai kamar ya?" "A'a to naga ne kuna wasan kallon-kallo nan don kar a ganni a tsofe a ɗauka ban san komai ba." Mikewa Zeey tayi da sauri tace "Kinga Dada ki rabani da wannan zancen, ni kinga ma wucewa ta." Riƙo hannunta tayi tana miƙewa suka fito waje tana sake godiyar fruits data kawo musu Zeey ce tace "Dada kar kice wa Ya Baqeer nice na kawo in ba so kike yayi faɗa ba." Dariya tayi tace "Don Allah ni dai in da hali ki cigaba da zuwa lokaci zuwa lokaci Baqeer na buƙatar wanda zai dinga faɗa mishi gaskiya, kuma na kula ke kaɗai ke iya faɗa mishi gaskiyar kai tsaye." Kallon Dada tayi jiki a sanyaye kafin ta ɗaga kai kawai alamar to, haka ta shiga mota idanuwanta na sake hango mata kallon da Baqeer yayi mata, ta tabbatar yaji zafin kalaman data faɗa mishi kawai don baya da niyyar kulata ne yayi shiru, amma tasan da yasan itace Zainab ɗin daya sani ta faɗa mishi magana haka babu shakka da tuni yaci mutuncinta. Har ta isa unguwarsu zuciyarta na saƙawa da kwancewa, akan layinsu da zata shiga motar Bello ita kuma tazo fita, kallo ɗaya tayi mishi ta ganeshi ga Asiya nan zaune a gefen mota sai hira suke ana wani rirriƙe hannu cike da so da ƙauna, nan da nan takaici ya turnuƙeta, babu shakka mutanen nan basu da kunya don ranar da suka je gidan Maryam da Salim yake bata labarin wai Bello abokin Baqeer ne, ranar tayi mamaki har ta gaji ace wai abokinka shine zai ci amanarka irin haka, da saninta ta ɗan bugi gefen motarsu kaɗan wanda hakan yasa Asiya da Bello suka yi ɗan gaba kaɗan sannan suka yi baya, da sauri ya ɗago tare da riƙo gefen fuskarta yace "Sweetheart are you okay?" Kukan shagwaɓa tasa tana nuna wuyanta wai ta buge da kujera, a fusace Bello ya fito ya nufi motar Zeey, wacce ke jiran fitowarshi dama, sun glasses tasa kafin ya ƙaraso ta ɗauki waya ta fara daddannawa. Knocking glass ɗin motar yayi saitin inda take, Zeey ta zare glasses ɗin fuskarta kaɗan wanda ya bashi damar haɗa ido da ita sannan taja motarta tayi gaba ta barshi tsaye cike da mamaki, ganin gidan data nufa yasa ya kasa ƙarasawa don duk sun san gidan Suleiman Karaye ne wanda kaf unguwar babu wanda ya kai shi kuɗi bare yafi shi, bai san meye haɗinta da gidan ba amma yasan tunda yaga ta shiga to akwai dangantaka mai ƙarfi a tsakaninta dasu, Asiya har tutiya take yi akan layinsu ɗaya. Dawowa mota yayi yana saka hannu a aljihu, ta kalleshi cikin sakalci tace "My heart me tace? Don na hango mace ce." Ya zauna yana dariya yace "Ta bada hakuri ashe bata kula bane." Turo baki tayi tace "Ni ya kamata kace ta bawa hakuri ai don ni ta buge, amma ƴar wacece na ganta a katuwar mota haka?" Don kada ta rainashi yayi saurin cewa "Da alama wucewa tazo yi." Motar ya tada yana ɗan murmushi, ita ma murmushin tayi don restaurant zai kaisu cin abinci tace Habi tazo suje wai bata zuwa gayyar mayaudara.
***** Gida ta shiga tana ɗan kaɗa key ɗin hannunta ko banza ta ɗan huce takaici don da ta fito sunyi magana lallai da sai taci zarafinshi. Ɗakin Nabeela ta shiga taga ba ta nan, fitowa tayi ta nufi bangaren Mummy, nan ma bata nan, hakan yasa ta nufi kitchen, ma'aikatan gidan ne ke girki tana kallon banbar cikinsu tace "Iyani ina Mummy?" Murmushi tayi tace "Tana nan a ciki don bata leƙo mu ba." Cike da mamaki ta sake komawa ciki tana mamakin inda take, don gidan tsit babu alamun mutum, ɗakinta ta nufa ga mamakinta Mummy ce kwance akan gadonta da alama bacci take yi, kai ta girgiza tare da sakin murmushi, tana mamakin yadda Mummy ke ji da ita, shi yasa a koda yaushe take tabbatar da ita ɗin ƴar gata ce, don sau da dama Mummy nace mata haihuwarta ce ta ceci rayuwarta wanda zuwa yanzu ta tabbatar da hakan, alwala tayi sannan tayi sallah haka nan take jin nutsuwa na sake ratsa zuciyarta, tazo kusa da Mummy ta kwanta itama nan bacci ya ɗauketa don kwanakin nan sam bata samun bacci mai daɗi. Cikin barcinta ne ta fara mafarkin Baqeer wai ga mahaifinshi nan yana neman turashi daga saman dutse, zabura tayi ta miƙe zaune tana addu'a, nan da nan Mummy ta tashi ta rungumeta tace "Menene?" Kai Zeey ta girgiza tana mamakin abinda ke damunta, anya kanta ƙalau kuwa? Anya baza taje ganin likita ba kuwa? Don wannan abinda take yi tabbas ba na masu cikakkiyar hankali bane.
***** A hankali Baqeer ke buɗe ido yana rufewa yanzu kam ya tabbatar kalaman yarinyar nan yake son ji, ya tabbatar ba ƙaramin tasiri kalamanta ke yi a zuciyarshi ba, hakan yasa ya gurgura kekenshi ya zubawa kaɗan daga cikin takardunshi da Umma ta bada aka kawo mishi ido, ajiyar zuciya yayi tare da rike pencil a hanunshi yana kallon takardar sai dai ya kasa ɗora pencil ɗin akai bare har ya gwada yin zanen, to shi yanzu ya zai yi? In ma yayi zanen waye zai siya? Ina zai nemo mutanen da zasu gani su siya? Bayan wayarshi dake ɗauke da duk wasu muhimman abubuwa nashi an sace? Sannan Baba dake tallafa mishi akan harkokin shi shima yayi watsi dashi? Wannan dalilin ne yasa ya ajiye takardun sannan ya maida idanuwanshi ya rufe kafin ya buɗe, yanzu haka zaka cigaba da rayuwa? In Allah yaja kwanakinka fa? Haka zaka zauna komai sai an miƙo maka ba zaka tashi da ƙafafunka ka nema ba? Wata nannauyiyar ajiyar zuciya ya sauke haɗe da ƙara ɗaukar pencil ɗin don ya gwada yin zanen sai dai kuma ina ya kasa don ƙwaƙwalwar shi ce yaji ta zama blank kamar bai taɓa sanin yadda ake riƙe pencil ba, hannunshi kuma ya hau rawa yaji tamkar an ɗauki wani abu mai nauyi an ɗora akan hannun har ma ya kasa riƙe pencil ɗin ya sake shi ya faɗi a ƙasa. Wani irin ihu ya saki yana ƙara haɗe da riƙe kan shi da hannu bibbiyu. A sukwane Dada ta faɗo ɗakin tana cewa "kai Baqeeru lafiyarka ƙalau kuwa?" Ja tayi ta tsaya tana kallon ikon Allah ganin yadda yayi watsi da takardun zanen nashi duk yabi pensiran ya kakkarya.
"Yau ni nake ganin abinda ya girmi kakata Saude, su kuma takardun da kayi watsi dasu laifin me suka yi maka? Anya kuwa Baqeeru shikenan haka zaka cigaba da rayuwa ba zaka sanyawa ranka haƙuri da dangana ba ka karɓi ƙaddararka da haƙuri da ikhlasi? Kai kenan kullum cikin ƙunci da baƙin rai ka ƙuntata rayuwarka ka ƙuntata rayuwar makusantan ka yau gashi har takardun ma baka ƙyalesu ba. Haba wannan wacce irin rayuwa ce, shikenan shi bawa Allah ba zai jarabce shi ba sai yace don me? Har ina murna ka fara samuwa kwana biyu shine kake nema ka koma ruwa, idan ka kassara rayuwarka a tunaninka ubanka yana da asara ne, uwarka da ƴan uwanka su zaka yiwa don kuwa ubanka yana da wasu ƴaƴan a yanzu ma ai ka gani yadda yayi watsi da kai ya koreka daga gidanshi bayan a lokacin da kake da lafiya yafi kowa cin moriyarka, to tun wuri ma idan zaka yiwa kanka faɗa ka ɗauki rayuwa a yadda tazo maka kasan cewa rayuwarka kai kaɗai zata amfana gara kayi."
Sunkuyawa tayi ta tattare kayan daya watsar ta killace su a gefe tana cigaba da yiwa Baqeer faɗa, shi dai yayi bakam kamar bai san tana yi ba sai dai duk abinda take cewa yana saurarenta yana kuma gaskata duk abinda ta faɗa sai dai ya kasa daina jin ciwon yadda rayuwa tayi dashi, ya kasa yardar wa ranshi cewa shine rayuwa ta mayar dashi haka, yau shi Baqeer da yake ji da lafiya da ƙuruciya ne a kanannaɗe a keken guragu ya zama musaki, gurgu wanda ba zai ƙara amfanuwa da ƙafafunshi ba. Ko yayi ƙoƙarin cire abun daga ranshi sai wani dalilin yasa shi tunowa sai yaji gaba ɗaya rayuwar ta fita daga ranshi, ƙuncin zuciyar da yake fama dashi ya daɗu, sai yaji baya son ganin kowa kaɗaici kawai yake buƙata. Hannu yasa ya ɗauke hawayen daya gangaro daga idanunshi ya biyo kuncin shi, shikenan shi yanzu haka zai cigaba da rayuwa baya da wata mamora, zanen daya ɗauki dukkanin burikanshi na rayuwa ya ɗora akai na neman ya gagareshi yi. Gangarawa yayi ya rufe ƙofar ɗakin sannan ya koma kan katifarshi ya kwanta yana jin ina ma Allah zai ɗauki rayuwarshi da yaji daɗi ya rabu da dukkanin wasu ƙalubalen rayuwa da abinda ke cikinta.
***** Zama Zeey tayi tana kallon Mummy dake haɗa wasu kaya a ɗakinta, miƙewa tayi ta sake nufar ɗakin Nabila, kwana biyu yanayin data samu kanta a ciki yasa ko zama basa yi suyi hira, ita komai ma daina yi mata daɗi yayi shi yasa ta gwammaci ta killace kanta wuri ɗaya inda ba za'a dameta da hayaniya ba. Shiga tayi tana ƙwala kiran small Aunt sai dai ta iske ɗakin wayam Nabila bata ciki yanzun ma, hankalinta ne ya kai yanda ɗakin ya ɗan ragu, gashi babu wasu daga cikin kayayyakinta a ɗakin kamar ma dai tayi tafiya ne. Fita tayi ta koma ɗakin Mummy tana tambayarta inda Nabilan taje. Taɓe baki tayi tace "Share ta fushi tayi akan nayi mata faɗa shine ta haɗa kayanta ta koma gida, kin dai santa ai bata so ana faɗa mata gaskiya ni kuwa tana zaune a gidana ba zan kawo ido na zuba mata sai abinda take so zata yi ba."
A shagwaɓe tace "Kai Mummy don Allah, wai me Aunty Nabila take yi miki ne da kullum sai kin yi mata faɗa, duk ƙoƙarinta nata burge ki ba kya gani? Yanzu har wani laifi ma take yi da za'a dinga yi mata faɗa?"
"Au haka ma zaki ce bayan duk abinda nake yi saboda ke nake yi, har wani ƙoƙari take yi ta burgeni daga neman suna kawai, tana dai yi don ta burge waɗanda take son burgewa amma bani ba."
"Ni dai Mummy don Allah ki daina abinda kike yi mata wallahi bana jin daɗi kamar ba ƴar uwarki ba, kefa kike yi mana faɗa akan rashin jituwarmu da Kabir amma gashi ke kuma kina yiwa ƙanwarki hakan." Kallon Zeey tayi baki buɗe tama kasa ce mata komai, da bata san halin Zeey ba da ta mata faɗar rashin kunya. Tashi tayi ta fita daga ɗakin tana cewa "Ni gashi sam bana jin daɗin zaman gidan nan idan bata nan gashi yanzu kinsa tayi fushi tayi tafiyarta gidan Inna, dole ne ma naje nayi bikonta gaskiya ko kuma na bita can mu zauna tare amma bazan zauna wancan Kabir ɗin nayi mini jaye-jayen tarkacen abokanshi ba." Tayi maganar a shagwaɓe tana fita daga ɗakin
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI*
{27}
Zeey na shiga ɗaki ta kira wayar Nabeela sai dai harta katse bata ɗauka ba, takaici ya kamata ta cilla wayar gefe, mamakin kanta take yiwai har da jan faɗa akan faɗan da bai shafeta ba, so take ta samu yiwa wani magana amma bata san wa ba. Ƙofar ɗakinta aka buɗe hakan yasa ta kalli wurin don tasan Mummy ce. Shigowa tayi tana kallon ɗakin kamar ba yanzu da suka tashi tace ta ɗan gyara ba amma yafda ta tafi haka ta dawo ta sake samun ɗakin babu alamun gyaran, sai ma ƙara ɗan batashi data yi,
Mummy ce ta kalleshi wanda gaba ɗaya hankalinshi baya maganar da take, cike da mamaki tace "Senate ni kam lafiya dai ko? Tunda ka shigo hankalinka ba a jikinka yake ba." Ƙaramar iska ya furzar daga bakinshi yace "Yau zamu yi taron manyan unguwar nan, zan ji ƙorafe-ƙorafensu na kuma taimaka musu tare da yardar su kuma zasu taimakeni har kar siyasa ta." Ajiyar zuciya tayi tace "Ah Alhamdulillah, ba dama abinda muka zo zama anan din kenan ba?" Kai ya jinjina yace "Haka ne amma ba kya tunanin mutumin can zai iya ruguza mana shirin mu?" Ajiyar zuciya tayi don ta gane Badaru yake magana tace "Da wannan kuma, amma shi don neman masifa shikenan taron ma ba zai bari ayi lafiya ba? In ba zai zo ba kawai ya zauna a gidanshi mana." "Taya zan hanashi zuwa bayan kina ganin yana daga cikin dattijan unguwa." Kai ta girgiza tana riƙe hannunshi tare da cewa "Mantawa kayi wanene Badaru? Ai bana ji zai zo in har yasan taron naka ne, ko ka manta ko ganinka yayi a hanya canzata yake yi? Bayan kuma dama an riga anyi muku tsakani dashi." Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke yace "Har kinsa naji hankalina ya kwanta, sam yanzu bana son abinda ya faru tsakaninmu shekarun baya ya sake faruwa." Tana murmushi tana cewa "Ba zai faru ba in Sha Allah! Muna hawa kujerar zamu bar Kano mu koma Abuja daga nan kuma ka fara plans ɗin ka da cikar burinka na zama govenor." Rungumeta yayi tabbas shi kam har mamaki yake yi yadda manyan mutane ke yawan complain akan matansu don shi dai kam sai hamdalla, kanshi ta shafa tace "Allah ya kare mini kai Senate." Nan yace Ameen yana miƙewa daga kan gadon.
****** Baqeer ne ya turo kekenshi zuwa falo inda Dada take, wanka yake son yi amma bai san ta yadda zai yi yace mata yana son ruwan ɗumi ba, sam tausayi take bashi, sau da dama in zai yi wanka kafin ya nema ma zata ce ta kai mishi ruwan banɗaki amma yau zuwan baƙuwar nan yasa ta sha'afa, dariyarta ya jiyo ta bayanshi tana cewa "Ka huce ka gama fushin da takardar?" Fuskarshi sam babu fara'a ya ɗan kawar da kai kaɗan, plate ɗin hannunta ta miƙa mishi wanda ke ɗauke da yankakkun kayan marmarin da Zeey ta kawo. Bai amsa ba sai dai yanayin kallonshi da ya canza jiki a sanyaye yace "Dada daga ina kika samu fruits?" Murmushi tayi tace "Aiko mana aka yi." Cike da kokwanton kalamanta yake kallonta ko me ya tuna sai kuma fuskarshi ta canza sosai yace "Ba dai yarinyar ɗazu bace ta kawo?" Dada tayi saurin waskewa tana cewa "Ruwan wanka kake so hala? Don dama ɗazu nake tunanin ɗora maka." "Itace ko?" Ya ƙara jifanta da tambayar. Kallonshi tayi tace "Wai Baqeer ni kam fitinar me kake ji da ita ne? Nace aiko mun aka yi ba shikenan ba?" Ajiye plate ɗin yayi ya gara kekenshi zuwa ɗaki, rufewa yayi yana jin zuciyarshi na wani irin zafi, me kenan take yi haka? Yaji ta bada motar da bai san tata bace ko ta aro ce amma banda ta dinga kawo abu cikin gida, ba zai lamunci wannan ba tunda ba saninta suka yi ba. Waya ya ɗauka ya kira Salim, ringing uku ya ɗauka yace "Baqeer inzo ne?" Kai ya girgiza tare da yin shiru to wai ma taya zai ce a bashi number ta? Bayan ko sunanta bai san yadda zai yi ya tambaya ba? Sumar kanshi ya shafa yace "No babu komai kawai dai tambayarka zan yi ya kasuwa?" Cike da jin dadi Salim yace "Alhamdulillahi gashi nan muna fama." "Don Allah ko zaka leka Umma kaga ya take? Mun yi waya amma hankalina ya kasa kwanciya." Ba tare da wani dogon nazari ba yace yana tashi zai biya, shiru suka yi ya ɗan yi gyaran murya kaɗan yace "Ranar da muka je asibiti da motar wa ka kaini ne ni kam? Ina taso na tambayeka." Salim yayi shiru yana nazarin abinda zai ce, Baqeer ne yayi saurin cewa "Kar kayi mini ƙarya Salim please, motar ƙawar Maryam ce ko?" Yawun bakinshi ya haɗiya yace "Eh! Am really sorry da ban sanar da kai ba, Maryam ce tace nayi using ɗinta tata bata ga key din ba." Kai ya jinjina kenan har hancinshi yasan ƙamshin ta? Nan da nan yaji hankalinshi ya tashi, lallai Baqeer "Don Allah number fa? Kana da shi? Ina son nayi mata godiya." Cikin jin daɗi Salim yace "Yanzu kuwa zan turo maka." Nan suka yi sallama ya kashe wayar.
Muryar Dada ya jiyo tana buga kofa tana yan mita "Ni kam hala dai halinka gaba ɗaya aka canza? Yanzu ko itan ce ta kawo sai kace ba zaka sha ba? Kyautatawa ce ai ba roko ba, maimakon ka amsa kayi godiya sai ka hau fushi kaƙi amsa?" Hannu biyu yasa ya shafi fuskarshi ba wai bai gode bane haka kawai yake ji wani sashin na zuciyarshi na tunanin rayuwar yanzu, mahaifinshi ma ya banzatar dashi taya wata da bashi da haɗi da ita zata dinga kula dashi kamar yadda take yi? Dole zai yi mata magana akan abinda tayi.