Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 20

Baqeer complete - Chapter 20

Baqeer complete Chapter 20: Baqeer complete Chapter 20. Ajiyar zuciya ta sauke tana share hawaye tace "Umma zaman gidan nan ya isheni, ana samun matsala da…

3,431 words

Ajiyar zuciya ta sauke tana share hawaye tace "Umma zaman gidan nan ya isheni, ana samun matsala da uwar miji ni uban miji ne matsalata, babu dama ya ƙyalla ido yaga muna zaman lafiya da Baban Aareef sai yasan yadda yayi ya wargaza zaman lafiyar nan, ko wani alheri Baban Aareef yayi niyyar yi mini sai ya hana yanzu motar da aka saya mini saboda kai Aareef makaranta da ɗaukoshi yasa ya karɓe saboda wai idan yasa ƙafa ya fita yawona nake ficewa nima bana zama ko Aareef ɗin ma bana zuwa na ɗauko saboda kawai rannan nazo na ɗauki Yaya Baqeer na kai shi wajen Dada kuma wallahi Umma daya dawo sai da nayi mishi bayanin abinda ya faru amma mutumin nan ya juyar da magana ya zuge ɗanshi ya karɓe makullin motar daga hannuna, da nace mishi to Aareef ɗin fa ya za'a yi da kai shi makaranta da ɗaukoshi sai cewa yayi wai ai makarantar bata da wani nisa sai na dinga zuwa a ƙafa ina kai shi ina ɗaukoshi don nace ni dai gaskiya ba zan iya ba sai dai ko ya ɗaukar mishi mai napep shine yace ai gidanmu ma dai yaga ba motar ce damu ba da har zai ce ga yadda za'a yi zan yi mishi gardama saboda na samu wuri."

Sauraren Maryam kawai Umma take yi tana girgiza kai, dama tana yawan ji Maryam ɗin na kuka da uban mijin nata sai dai bata taɓa zama ta bayyana mata halin da suke ciki ba sai dai taji suna maganar yawanci ita da Baqeer ita kuwa bata saka musu baki. Hannu tasa ta ɗauke ƙwallar da suka taru a cikin idonta tace "Kiyi haƙuri Maryam, kowanne aure da kike gani da irin ƙalubalen da ma'auaratan ke fuskanta ba kuma zai yiwu kowane lokaci ace akan mahaifinshi kuke samun saɓani ba, ai shi ubanshi ne kuma dolen shi ne yayi mishi biyayya. Saboda Allah ta yaya ubanshi zai ce ga yadda za'a yi ke kuma kice ba haka ba ya yarda, kenan sai ya ɗauki maganarki sama data ubanshi saboda kawai baya son ɓacin ranki, ai ba haka ake zaman duniya ba abinda haƙuri bai baka ba kuma rashin shi ba zai taɓa baka ba. Kici gaba da haƙuri don Allah duk abinda kika san yana janyo matsala a tsakaninku ki dinga ƙoƙarin kiyayewa, ni ranar dana san baki faɗa mishi zaki zo ba ai da ban bari kin ɗauki Baqeer kin kai shi har mariri ba da sai nasa a nemo motar haya na tafi na kai shi duk ba wani abun damuwa bane." Haka dai tayi ta mata nasiha tana tausar zuciyarta kafin suka yi sallama ta ajiye wayar tana jin ƙarin damuwa akan wacce take ciki. Gaba ɗaya ƴaƴanta babu wacce ke jin daɗin zaman gidan miji, dama Baqeer ne tsaye akan al'amuransu to shima ga yadda rayuwarshi ta koma dole yana buƙatar matallafi kafin suga yadda rayuwa zata yi dashi, watakila idan hannunshi ya warke ya koma kan harkokin zanen shi komai zai warware musu tunda ai dama rashin yin zanen ne ya saka su a cikin halin da suke ciki, rashin yin zanen ne yasa Mallam ya juya mishi baya ya fitar da hannunshi daga al'amuranshi, tasan daga ranar da ya warke ya komawa harkokinshi komai zai gyaru, daga wannan ranar Mallam zai janye korar da yayi mishi daga gidanshi don zai ga nakasar data sameshi bata hanashi cigaba da al'amuran rayuwarshi kamar da ba, sai dai kuma yaushe ne zasu ga zuwan wannan ranar? Dole ta tashi ta tsaya da ƙafafunta har zuwa lokacin da Baqeer zai samu lafiya ya koma kan harkokin nashi, kafin nan dole ne ta zama jaruma jajirtacciyar mace mai tsayawa ta nemi na kanta ba tare data jira sai wani yayi mata ba. Zata tashi ta kama sana'a komai runtsi komai wahala don ta tallafi rayuwarta data iyalinta.

***** Zainab na ƙoƙarin shiga gida ta hango samari tsaye a gate din gidansu, da mamaki ta karasa wurin, mai gadi ne ke ta mata alama da karta ƙaraso sarai ta gane sai dai bata bi ta kanshi ba ta nufo gadan-gadan zata shiga. Jikin motarta suka nufo hakan yasa ta gane Najib dake ɗaya daga cikinsu. Kai ta girgiza tare da furzar da iskar bakinta, wato dai yau mutane neman kaita bango suke yi da shirmensu na sunan soyayya? Knocking din glass ɗinta yayi, ta zuge tana yi mishi wani irin kallo na takaici, ya ɗan jingina da ƙofar motar yace "My Zeey mun zo wurin Kb ne zamu fita su kuma abokaina ganinki suke son yi." Kallansu tayi tace "Hi!" tana ɗaga ƴan yatsunta guda biyu. Matsowa suka yi suna murmushi, tana kallon Najib tace "Babu laifi ai, hope ka faɗa musu mun yi north-west?" Kallonshi suka yi tana ɗan murmushi tace "Kada ku damu ya samu wata ne, so ba wani issue bane, J bye sai munzo biki." Tana kaiwa nan ta shiga cikin gida zuciyarta na sake tafasa don sam ba wannan shirmen bane a gabanta, ita tunanin yadda zata taimaki Baqeer kawai take yi, ko yaci abincin? Fuskarta ta shafa tare da takaicin halin da ta shiga.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

#Baqeer #Zeey #Kamalu #Sanyin Zuciya #Rayuwata

*Na Umm Asghar* *Da* *Ayusher Muhd🏌🏻‍♀️ *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR*

{25}

Nabeela ce ta kalli Kabir wanda ke ta watso da kaya ƙasa a cikin ɗakin shi cike da kulawa tace "Ya Kabir me kale nema ne?" Kallonta yayi yace "Please ki fita, ko me nake nema ba ɗaki na bane?" Jikinta ne yayi sanyi ta fara neman barin ɗakin sai kuma yasa hannu ya riƙo rigarta yace "Sorry raina ne a ɓace ba wai wulaƙanci bane takardu na shigo dasu jiya kuma ban gansu ba." Ajiyar zuciya tayi cike da damuwa tace "Takardun menene? Akwai dai wanda Zainab ta kai ɗakinta jiya amma su na mota ne." Sakinta yayi ya fito daga ɗakin cikin sauri ya shiga ɗakin Zeey, akan dressing mirror ya gansu, ƙwafa yayi ya sake dubawa ganin komai yadda ya ajiye yasa ya ɗauka ya fito fuskarshi sam babu alamar walwala. Zeey ce ta shigo ranta duk a ɓace ama barta da damuwar Baqeer wannan mahaukacin da wannan yaron na neman ƙona mata rai, takardun ya nuna mata bayan ya tare ƙofar shiga yace "Uban wa yace ki ɗaukar mini takardun motar nan?" Kallon takardun tayi a wulaƙance sannan ta kalleshi tace "Kaga don Allah banda lokacin wasu takardun motarka, na shiga ɗakinka na gansu na ɗauka motar da aka ce za'a saya mini ne ka shigo da takardun, shine na ɗauka don na duba." "Kawai daga ganin abu a ɗakina sai ki ɗauka ko kin tambayeni ne?" Saman goshinta ta shafa tace "Please! Ya isa haka ba gashi ka ɗauka ba sai ka sakasu a abinci kaci……." Cikin ɗaga murya yace "Malama ni kike yiwa magana haka?" Mummy ce ta fito da sauri da alama ma sallah take yi don sanye take da hijab, kallonsu taiy tace "Zaku fara ko?" Zeey ce ta fara neman wucewa ciki don bata da lokacin Kabir balle shirmen da yake yi. Kallon Mumy yayi yace "Wallahi wata rana sai na fasawa yarinyar nan baki in dai ni zata dinga yiwa magana a haka." Zeey ko kulashi bata yi ba ta wuce cikin falo, tana jiyoshi ya fita wurin abokanshi tare da bugo ƙofar da ƙarfi. Kallon Nabeela tayi tace "Meya faru?" Nan ta sanar da ita abinda ya faru cike da ɓacin rai tace "To ke menene naki na sanar dashi? Sai ki zo ki faɗa mini gashi nan yanzu a dalilinki kin janyo musu sun samu matsala?" Zeey dake falo tana jiyosu ta dawo tace "Mummy menene laifinta a ciki? Gaskiya ta faɗa ni fa bani da lokacin Ya Kabir neman faɗa kawai yake ji, sannan idan ya dawo ki sanar dashi kada ya ƙara janyo ruɓaɓɓun abokanshi gidan nan su tare mutum suna yi mishi shirme inba haka ba wata rana sai na faɗa musu magana." Yadda Mummy take kallonta ne yasa ta shagwaɓewa ta shiga ɗaki cikin jin haushin kanta yanda takaici da damuwat halin da Baqeer ke ciki yasa duk hankalinta yaƙi kwanciya. Nabeela ta sake kalla fuskarta a ɗaure tamau tace "Kin dai san nace a'a ko? To wallahi bana son hauka in ba haka ba ki tattara ki koma gida." Wani abu ne ya tokare mata maƙoshinta sai dai bata iya cewa komai ba sai juyawa data yi idanuwanta na sake ciccikowa da ƙwalla ta bar wurin.

****** Kamalu daya biyo Zee a mota ashe yana ganin sanda Najib ya jingina da mota wanda hakan ya sake tunzuro shi, nan da nan kishi ya turnuƙeshi, Roshni ɗin tashi wani soko zai tare? Bayan shi ya gama shirya rayuwar love da ita? Ko kallon ƙauna data yi mishi ɗazu kaɗai ya tabbatar mishi ta gama amsar soyayyarshi. Tsayawa yayi a gefe har saida yaga sun shiga mota sannan shima yabi bayansu, a wani restaurant suka yi parking da motocinsu uku suna shiga ciki ya fito da ƙusoshi ya jera a ƙasan tayoyin yana yi yana waige-waige wai kada a ganshi, daya gama yayi wani murmushin jin daɗi ya shige motarshi yayi tafiyarshi ko banza dai ai ya rama. Haka ya dinga yawo a gari yana nunawa abokanshi motar babanshi wai shima yau gashi nan an bashi, wani wurin ma nuna musu yake yi kamar motarshi ce.

Su Kabir da Najib suna fitowa suka yi reverse suka bar wurin wanda shirmen ƙusoshin da Kamalu yasa bai yi musu komai ba.

**** Umma yau haka ta wuni sukuku saboda tunanin halin da Maryam take ciki a gidan mijinta, ita kaɗai ke da mata biyu dake zaune anan garin, ƴaƴan Abu mata da suka yi aure su biyu ba'a Kano suke ba, daga Hadiza har Maryam babu wacce tayi dace a gidan aurenta, wannan abu na bala'in ɗaga mata hankali, tana nan a kishingiɗe hankalinta duk ya tafi kan tunanin ƴaƴanta sam bata kula da shigowar Baba ɗakin ba kawai sai ji tayi ance "Kefa yanzu gaba ɗaya kin zama mara mutunci ko? Har kin isa na shigo gidan baki ko ɗago kai kin kalleni ba bare nasa rai da gaisuwa?" Da sauri ta miƙe zaune tace "Mallam sam ban ji shigowarka ba wallahi." Kallon ɗakin yayi ranshi na sake ɓaci yace "Au na ɗauka ai kin bi titi kema." Kallon mamaki tayi mishi don bata gama gane me inda kalamanshi suka nufa ba." Ya zabga mata wata muguwar harara yace "Bani." "Me zan baka?" "Kuɗin kujerun ko da ke a naki haukar bar miki kuɗina zan yi? Ko ba da kuɗina kika sayi kujerun ba?" Mamaki ya gama rufeta tace "Mallam kujerun nan fa Baqeer ne ya saya mini kuma kuɗin shi zan samu na tallafawa dasu." "Inyee? Fatima ni kike yiwa magana haka? Ni kike cewa Baqeer ne ya saya miki kujeru? To wallahi na saka ƙafar wando ɗaya dake a gidan nan, zanga in gurgun ɗan naki zai iya tallafa miki, ni zuciyata fari tas tunda ba shi kaɗai gareni ba sannan ina da lafiyayun ƴaƴa zan kuma nuna muku dukkanku a tafin hannuna kuke." Idanunta ne taji sun cicciko duk haƙurinta sai data ji ta kasa jurewa don haka tace "To Mallam tunda haka ka zaɓa mu bamu da ikon hanaka, sai dai shima ƙaddarace ta faɗo mishi ba yin kanshi bane." Ƙwafa yayi ya fice daga ɗakin ranshi a mugun ɓace, Jamila wacce dama take gadi a ƙofar ta sam bata so ya wuce bata tare shi ba tayi saurin fitowa tana lanƙwasa jiki da yanga tace "Mallam ashe ka dawo?" Wani kallo yayi mata yace "Ke kuma meye hakan kike yi kamar wata mai ciwon haƙarƙari?" Abu ce ta kwashe da dariya wacce fitowarta kenan tace "Kai Mallam yanga fa ake yi maka irin ta jan hankali." Tsaki yayi yace "Yanga ko hauka, ni bani wuri na wuce don Allah." Yayi maganar yana tureta ya wuce bangaren Abu, nan da nan zuciyar Jamila ta sake zafi ta dinga ji kamar zata yi hauka, kai tsaye ɗakin Fatima tayi wacce ke zaune tana tunanin yadda Mallam ya juya mata baya kamar ba ita ce ƴar lelenshin nan ba. Tana shiga tace "Fatima wai haka zamu zauna Abu ta mallake Mallam muna kallo ba zamu ɗauki wani mataki ba?" Ko kallonta bata yi ba tace "Ku mallaka ta dama ni dai don Allah kuje can ku karata." Jamila nan da nan takaici ya ƙara rufeta a fusace ta banko mata ƙofa ta fito, har ga Allah ita bazata taɓa yarda Abu ta ƙwace musu miji tana ji tana gani ba.

***** Dada tayi mamaki da Baqeer bai musa ba data kawo mishi abincin dare, kuma banɗaki da kanshi yake gungura kekenshi yake zuwa, hakan ya sake tabbatar mata zuwan yarinyar nan ne yayi tasiri sosai a tare dashi, to wacece ita? Dole ta tambayi Maryam alakarsu don bata san me tace mishi ba amma tabbas tun bayan tafiyarta ya canza, washegari haka kawai ya samu kanshi da tunanin ko zata zo sai dai babu ita ba labarinta, murmushin takaicin kanshi yayi, iyayenshi ma suka gujeshi bare yarinyar da har yanzu ko sunanta bai sani ba, yarinyar da kawai ganinta yayi amma wai har wani sashi na zuciyarshi ke kwaɗaita jin muryarta, wanda ya tabbatar ko a hanya ya ganta ba lallai ya iya ganeta ba, to wai wacece? Wannan tambayar ita ce ke sake ƙona mishi rai, wayarshi ya ɗauka abinda tunda ya fara ciwo bai taɓa yi ba, dubawa yayi yaga Maryam ta saka mishi kati kawai ya gwada siyan data na kwana ɗaya, facebook ya leƙa inda ya dinga ganin hotunan Bello na tayashi murna da ake yi da kyaututtukan da aka bashi, har ya canza sunanshi ma zuwa MBB, wani murmushin takaici yayi ya sake duba wani hoto inda yaga Bellon riƙe da hannun mace wanda ko ba'a faɗa ba yasan Asiya ce, nan yayi deleting account dinshi ya ajiye wayar kawai.

****** Zeey yau kwananta biyu kenan bata leƙa Baqeer ba sai dai yadda kasan mara lafiya haka take jinta, ko doguwar magana bata yi, Mumy har ɗaukan ta tayi suka je shopping amma sam taƙi dawowa daidai, suna hanyar komawa gida tace "Mummy don Allah ki barni naje gidan ƙawata akwai abinda zan amsa." Kamar zata hanata sai kuma ta fasa tace "Please Zainab in har da wani abun ki sanar dani na tsani ganinki haka." Rungumar Mummy tayi tace "Ni kaina ban san meke damuna ba Mummy shi yasa na kasa sanar dake." Kanta ta shafa don Daddynsu har ya gaji da tambayarta ko wani abun ke damun Zeey. "Muje gida sai ki hau motata ki je, tunda har yanzu bai baki motarki ba, kin dai san kulawa ce tasa hakan ko?" Kai ta girgiza tace "So yake yasan duk inda nake zuwa Mummy kema fa kin sani." Wani kallo tayi mata irin na son ta canza abinda ke ranta, Zeey kwantar da kanta tayi a saman kujera tace "Kema fa kin san haka ne." Haka suka isa gida sannan ta hau motar Mummy bayan tayi mata kashedi akan kada ta daɗe, ta tsaya ta sayi kayan marmari sannan ta isa ƙofar gidan su Dada, kanta ta maida bayan kujera tana mamakin yadda wai sam ta kasa cire Baqeer daga ranta, rayuwar da suka yi dashi a baya ta tuna hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya bayan ta tuno yadda mahaifinta sam ya hanata kallon gidansu Baqeer, ya zai ji idan yaji ita take bibiyarshi? Yaro ta samu ya shiga da ledojin cikin gida. Dada na zaune tana tsinke zogale yaron ya shigo ta tambayeshi inji waye yace "Watace a mota a waje." Da sauri ta miƙe tare da leƙowa nan ta hango Zeey tayi reverse tana neman wucewa, da sauri tace "Ƴar nan ina zaki?" Karaf a kunnenta hakan yasa tayi parking tana murmushi tace "Dada sai da kika fito?" Harara ta zabga mata tace "Ina nan ina ta addu'ar na ganki kuma zaki zo naga kin tafi baki shigo ba?" Fitowa tayi tazo kusa da ita tana dariya tace "Gani nayi ban sanar daku zanzo ba….." Ai bata ƙarasa ba taja hannunta ciki tace "Ni kullum in zaki zo daɗi zanji, wannan kayan duk na menene?" "Ke na kawowa kici kiyi ƙiba da lafiya." "Ni ko shi?" Ido Zeey ta zaro tace "Ke dai, rabani da wannan zancen Dada." Dariya suka yi tare da shiga ciki sosai. Baqeer na zaune a ɗakin shi bai rufe ƙofar duka ba, kallon ƙofar yayi jin kamar muryar data kasa barin cikin kunnenshi, muryar da kullum ke yi mishi yawo a zuciya. Zeey ce ta kalli ƙofar gabanta na wani irin faduwa haka kawai take jin faɗuwar gaban taƙi tafiya, idanunsu ne suka haɗu da juna nan ta ɗan lumshe ido sannan ta sake buɗewa, ta sake saukesu kanshi sannan suka wuce ciki ita da Dada. Zama tayi har yanzu bata daina ji gabanta na faduwa ba, ta sani tausayin Baqeer ne ke damunta amma faɗuwar gaban ta menene? Shakkar shi da kike yi tun da ko kin manta? Da wannan tunani ta gama tabbatar wa hakan ne. Baqeer na jiyosu daga ɗaki Dada na cewa "Wai da tafiya zaki yi da ban jawo ki ba?" Zeey tayi murmushi tace "To Dada mai zan shigo nayi? Wancan karon ma Maryam ce ta aiko ni." Ta ƙarasa maganar tana ɗan kallon ƙofar ta gefen ido. Haka kawai yaji kalamanta sun yi mishi zafi, to da yace tazo ne? Dada ce kawai yaji ta ƙwalla mishi kira tace "Baqeer ka fito mana ku gaisa." Ko amsawa ma bai yi ba don ji yayi kamar Dada ta gama tozartashi wato har ta gane abinda yake tunani shi yasa take magana da karfi haka? Miƙewa tayi tazo ta wangale ƙofar tana cewa "Kazo ku gaisa mana." Kai ya girgizawa Dada alamar baya son zuwa don baya son ma yin magana balle taji ta ɗauka son ganinta yake yi. Mikewa Zeey tayi tace "Dada kin dai san ba fitowa zai yi ba ko kin manta ya gama yanke alaƙa da duniya?" Nan da nan ran Baqeer ya kai bango, me take nufi? Zeey ta cigaba "Ai Dada kawai ki barshi yayi ta zamanshi a ɗaki tunda har yanzu bai fahimci abinda ya dace yayi ba." Dada dariya tasa a gaban Baqeer tace "To ka dai ji namiji da bai san me ya dace ba kuwa ai gani nake akwai matsala ko Muhammadu?" Fuskarshi ya tamke sosai don shi saboda tsabar baya son raini shi yasa ko wasan tsokana baya yi, Zeey da yake tasan halinshi tace "Dada ya gama azumin ne ko yasha ruwa?" Dada ta sake kwashewa da dariya wanda hakan ya sake ƙular da Baqeer matuƙa, ya gurguro kekenshi cikin ɓacin rai ya nufi ƙofa, tana jingine a jikin ƙofar tana murmushi, cak ya tsaya yana kallonta itama kallonshi tayi wanda ta sake sakar mishi murmushi tace "Dada bari na wuce kafin na ganni a waje." Tayi maganar idanuwanta a kanshi, a ina yasan fuskar nan? Tambayar da ta sake zuwa mishi kenan, baya son ta gane kallonta yake sosai hakan yasa ya ɗan kauda kai, zai rufe ƙofar Dada ta riƙe ƙofar tace "A'a ni kar a rufe dani a barni naje mu sha hira da ƙawata, tunda kai dai ka kulle kanka sai kasha zamanka lafiya." Wani murmushi tayi mishi wanda ya kasa gane wani iri ne tana kallonshi shima yana kallonta tace "Toh Dada in ma mutum zai farka ya nemi abin da zai debe mishi kewa ya farka in ba haka ba yana zaune mutanen da ya daɗe yana kula dasu zasu ƙarasa rayuwarsu cikin baƙin ciki." Tana kaiwa nan ta koma inda Dada ta saka musu tabarma ta zauna, Baqeer wani irin yanayi ya tsinci kanshi dashi wanda yaji yama kasa rufe ƙofar, Dada ce ta fito don tabbas tasan kalaman Zeey sun shigeshi dole ta roƙi Zeey ta dinga zuwa don ta tabbatar Baqeer na neman mai fada mishi gaskiya gwara ya san abun yi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull