Baqeer complete - Chapter 19
Baqeer complete Chapter 19: Baqeer complete Chapter 19. Cak ya tsaya sannan ya waigo ya zabga mata wani kallo yace "Ya aka yi baki haɗa dake kanki ba?"…
3,195 words
Cak ya tsaya sannan ya waigo ya zabga mata wani kallo yace "Ya aka yi baki haɗa dake kanki ba?" Yayi maganar tare da ƙarasawa waje, ajiyar zuciya tayi sai kuwa ji tayi Abu na guda, fitowa tayi tana taku ɗaɗai ta wani turo ɗaurin ɗankwali gaba tana tauna chewing gum, Jamila ce ta fito sa sauri tace "Abu lafiya?" Girgiza jiki ta ɗanyi tana wani yauƙi tace "Wallahi Mallam ne da wasan shiririta jiya goyani yayi a ɗaki shine yanzu nayi mishi maganar ya arawa Kamalu mota ya bani key babu ko musu." Jamila nan da nan ta ɗaure fuska tamau tace "Bayan Bashir ne zai shiga da motar makaranta yau kuma jiya ya faɗa mishi sai ya bawa Kamalu?" Ta ɗan murmusa tace "To kinga ai bashi da laifi abinka da wanda so yake ɗawainiya dashi, mantawa yake yi da wasu abubuwan balle abu in ya shafi wanda suke zaune kara zube….." ai kafin ta karasa magana Jamila ta cakumota rai a mugun ɓace, Abu tayi murmushi tace "To kin dai san hannunki in ya kai jikina za'a iya sallamarki." Jamila ta hankadata baya a fusace ta koma ɗaki, Fatima dake wanke-wanke ko kallonsu bata yi ba bare susa ran zasu ji ta tanka musu. Abu ta sake yin dariya tace "To borori asha aikin gida da kyau.
***** Yau Zainab ta gama sawa ranta dole taje taga Baqeer ta kuma sa a ranta wannan shine zuwa na karshe da zata yii, shima zuwan zata yi ne don kawai taga ya jikin nashi yake bayan jiya ya dawo daga ganin likita. Da wannan tunanin ta yiwa Mummy k6arya akan zata je amso saƙo a wurin wata ƙawarta. Kamar zata hanata sai kuma ta barta don bata son damuwar nan da take gani a fuskarta. Ɗaki ta koma ta janyo riga da wando zata saka sai kuma ta maidasu runa wurin wanda zata je, kallon atamfa tayi tana tuno wasu kalamanshi na can baya shekaru masu ɗan yawa, daga ya ganta da kayan turawa zai ce ko kyau babu, tsaki tayi a fili tace "Damuwar ka ai dama ba don kai zan saka ba." Mai makon tasa kayan turawan sai kuma tasa atamfa, doguwar riga ce tayi mata kyau sosai, kasancewar ba sawa take yi ba sai ta fito daban kamar ba ita ba. Bata ɗaura ɗan kwali ba don bata ma iya ba kawai mayafi tasa a sama ta fito, da mamaki Mummy ke kallonta sai dai ganin wajen ƙawarta tace zata yasa tayi shiru, Nabeela bata nan don tun safe taje gidansu inda mahaifiyar su take. Sai data hau kan titi sannan ta fara tunanin wanda zata kira ta tambayi address ɗin don dama ita ba wurinshi zata je ba kawai dai jikinshi zata je gani daga nan kuma tasan ba zata ƙara ganinshi ba. Har zata kira Maryam ta tambayeta kwatancen gidan sai ta fasa ta kira Salim, bayan sun gaisa ne tace "Salim dama naga wani kwalin magani ne a mota nake son na baka to kuma na fita nima nace ko kawai zaka faɗa mini gidan Dada sai na ajiye mata na wuce?" Mamaki ne ya kamashi don ya tabbatar ya fita da duk magungunan sai dai zai iya yiwuwa bai kula da lokacin da wani ya faɗi ba. Nan yayi mata kwatance ta kashe sannan ta shafi fuskarta, me yasa ta koyi ƙarya saboda Baqeer ne? Iska ta furzar sannan ta cigaba da tuƙi, bata sha wahala sosai ba don tana shiga layin ta tambaya aka nuna mata. Tafi minti biyar a waje tana kokwanton shiga kafin ta daure ta fito, har ta kai ƙofa ta girgiza kai lallai ajinta zubewa yake nema yayi, ta ya ma zata shiga gidan tace me ya kawota? Neman juyawa tayi sai taɗan ji sautin maganar Dada da ɗan ƙarfi tana kiran Baqeer, da alama ƙofa take bugawa, sam ta manta ta fasa shiga gidan sai kawai ta tura ta shiga hankali a tashe, Dada ce ta kalleta da mamaki don bata ganeta ba. Zee sai a lokacin tasan ta kwafsa, to meya kawota ma ne? Murmushin yaƙe tayi ta gaisheta, nan ta amsa tare da cewa "Wacece?" Yawun bakinta ta hadiya tace "ƙawar Maryam ce magani suka manta a mota nazo kawo mishi." Nan da nan ta saki fuska tace "Ayya Masha Allah! Mun gode kuwa." Zeey ta ciro paracetamol a jaka ta miƙa mata, Dada ta amsa sannan tace "Na rasa yadda zan yi da yaron nan tunda ya shiga ɗaki tun jiya har yanzu bai ko leƙo ba, ga baici abinci ba balle ya samu yasha maganinshi." Dada ce ta sake buga ƙofa tace "Baqeer wai din Allah wace rayuwa ce wannan?" Zeey ce ta kalleta tace "Dada bari na wuce." Tayi saurin riƙeta tace "Ai kam dai ba kyazo ki tafi ba ko ruwa ban baki ba, zo ki zauna mu gaisa kici abinci." Baqeer da ƙamshin turaren da yaji jiya a motar nan ne ya shigo ɗakinshi yasa ya tura keken shi da hannunshi zuwa bakin ƙofa, jingina bayan keken yayi da ƙofar don son sanin wacece? Muryarta kaɗai da yaji ya gane ta. Akan me take bibiyar rayuwarshi ne wai? Shiru yayi yana tunanin turaren nan da yaji jiya ba dai jiya har motar abokin Salim ta shiga ba? "Dada Allah babu komai, amma ya zaki yi in bai buɗe ƙofar ba?" Kalamanta ne suka doki kunnuwanshi, "Ni kaina ban sani ba wallahi sam na kasa gane me ke damunshi, ƙaddarar nan Allah ya riga ya aiko mana ita dole ne mu amsheta." Tunowa tayi da yadda taga mahaifinshi na magana jiya ta tabbatar waɗannan abubuwan sune suke damunshi, murmushin da ya tsaya iya leɓe tayi kafin tace "Sai mutum ya halaka kanshi saboda ƙaddarar da Allah ya ɗaura mishi? Dada ashe mu baza mu godewa Allah ba mu san iskar kaɗai da muke shaƙa a duniya kyauta bace daga Allah zuwa garemu?" Kallon ƙofar yayi saboda kalamanta da yaji, Dada ce tace "Abin ne duk na rasa kanshi wallahi ni kaina jiya ban yi bacci ba." Tayi maganar cike da jimami, fitowa tayi Zeey ta kalli ƙofar, alamun motsi taji daf da ƙofar wanda Baqeer ke neman barin bakin ƙofar. "Haka zaka cigaba da rayuwa?" Abinda ta faɗa kenan wanda ya sakashi tsayawa da tura keken, "Baka duba mutanen da ke tare da kai waɗanda suka damu da kai? Sai wasu ƙalilan da basu damu da kai ba?" Yawun bakinshi ya haɗiya tare da kallon ƙofar, "In har kana son ƴan uwanka to ka cire rashin ƙafar ka a matsayin nakasa ka maidata challenges na rayuwa da Allah ya ƙaddara maka, baka san me Allah ya shiryawa rayuwarka ba da ya jarabceka da hakan. Please ka sha magani ka kuma ci abinci." Tana kaiwa nan ta fito waje, Baqeer ji yayi wani abu ya tokare mishi zuciya, wacece wannan? Wani abu yake ji wanda shi kanshi bai san menene ba. Zeey a waje taga Dada da alama so take yi ta kawo mata abu, kallon yadda take juye abincin daga robobin biyu tana ƙoƙarin maidasu ɗaya take, shinkafa da wake ne, da alama ma babu yaji don gwangwanin take ta ɗan bugawa a ƙasa tana tashin wanda ya danƙare daga ƙasa, idanun Zeey ne ya nemi cicikowa, da sauri ta maidasu tace "Dada ni nama tuna ana nemana bari nayi sauri naje zan samu lokaci nazo naci abincinki." Tana kaiwa nan ta fito da sauri ta faɗa motarta, janta tayi ta bar wurin tausayin Dada sai damunta yake yi, bata yi auni ba sai gata a gaban babban shagon unguwar, ajiyar zuciya tayi ta duba account dinta wanda take da kudi sama da naira duba ɗari takwas, amma gashi can abincin dubu ɗaya yana neman gagararsu. Ya zata yi ta taimaka ba tare da an san ita bace? Salim ne ya faɗo mata ai zata iya siya ta bashi ya kai a matsayin aikenshi aka yi ko? Haka ta cigaba da tafiya tana nazarin abinda ya kamata.
***** Kamalu yana fitowa daga ɗakin Abu kawai ya daka tsalle tare da dukan bokitin robar dake tsakar gidan da kafarshi, ji yake wai yau shine zai tuka motar Baba da Baqeer, kallon kayanshi yayi babu laifi gwanjo ne amma masu kyau, comb yasa ya taje kanshi sannan ya fesa turare ya shiga mota ya ƙure kiɗa cikin ƙwambo ya fara tuki, unguwar su Zeey ya nufa, yana shiga layin yaje gidan mai gadi ya ce bata nan yana yi mishi kallon mara hankali, cike da takaici ya juyo yana tunanin ba dai wurin Salim taje ba? Kwafa yayi don wallahi yana tausayawa Salim duk ranar daya damƙeshi, kamar a mafarki ya hango motarta, ai cikin hanzari ya jaa motar yasha gabanta, wanda saura kaɗan ta buge shi, burki ta taka da sauri tana maida ajiyar zuciya, Allah ya taimaketa kan layi ne ba titi ba, da mamaki ta ɗago ta kalli motar, Kamalu ne ya sakar mata wani murmushi tare da ɗaga mata gira, bata ganeshi ba hakan yasa ta tsaya tana kallonshi har ya fito daga motar da yake yazo inda take, glass din da take ciki ya ɗan buga yana mata alama data fito tare da kashe mata ido. Mamaki ya sake rufeta ta sauke glasses ɗin motar tace "Yaro ya haka?" "Yaro?" Ya maimaita kalmar tare da nuna kanshi, tace "Eh, saboda halin yarinta kake yi, menene hakan?" Yawun bakinshi ya hadiya yace "Roshni plz magana nake so muyi ina ta zuwa gidanku ba'a barina na ganki." Kallon mamaki kawai take yi mishi tace "Roshni?" Dariya yayi yana haɗe leɓenshi yace "oh Zainab mantawa nayi." Takaici ne ya isheta kawai ta zuge glass tana neman yin reverse da sauri ya tsaya bayan motar tare da tare hanyar da zata yi reverse ɗin, mamakinta ne ya sake ƙaruwa hakan yasa ta fito don sam bata da hakuri yanzun ma damuwar Baqeer ne yasa take kokarin haƙuri da shirmen yaron. Murmushi yayi ganin ta fito ya dawo yana tafiyar nigga ya tsaya kusa da ita yace "Roshni nine fa Sadaath ɗinki kin manta love at first sight." Ya kanne mata ido yana shafa kuncinshi.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
#Baqeer #Zeey #Kamalu #Sanyin Zuciya #Rayuwat
*Na Umm Asghar* *Da* *Ayusher Muhd*🏌🏻♀️
*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA HUƊU*
{24}
Wani irin wulaƙantaccen kallo tayi mishi tare da sakin tsaki, ita duk sai taji ranta ya ƙara ɓaci ma ajinta ya zube ƙasa warwas idan har wannan mahaukacin zai iya tararta ya buɗe baki yace yana sonta ba tare daya duba ɗumbin tazarar dake tsakaninsu ba. Cikin fusata tace "Dallah mallam bana son hauka, tun wuri gara ka kauce ka bani wuri na wuce ko kuwa kaga nayi maka da mai taɓin ƙwaƙwalwa irinka da zaka zo ka tareni a titi kana yi mini soki burutsun zance mara kai bare ƙafafu?" Shi kuwa duk hargagin da take yi bai ma san tana yi ba sai ma kallonta yake yi cikin shauƙi yana jin wata iriyar soyayyarta na ƙara ratsa dukkanin wasu sassa na jikinshi. Yau dai gashi ga Roshni a tsaye, sakarar zuciyarshi ma sai take ayyano mishi ai kallon soyayya take jifanshi dashi don haka yake ta washe mata haƙora shi a dole murmushi yake yi. Ganin ɓata lokacin ta kawai take ƙara yi da tsayuwa a wajen wannan mahaukacin yasa ta koma cikin motarta ta tasheta da nufin idan har bai matsa ba tabi ta kanshi kawai ta wuce sai dai duk abinda zai faru ya faru amma ba zata tsaya tana cigaba da jin zantukan bakin mara hankalin nan ba.
Sai da yaga ta nufo kanshi gadan-gadan kamar zata bugeshi sannan ya matsa yana cewa "A'a Roshni ya zaki tafi kuma bayan muna hirarmu ta soyayya gwanin daɗi?" Bin bayan motarta yayi da kallo yana jin tamkar ta tafi da wani ɓangare na zuciyarshi, sai da ya daina ganinta sannan ya nufi motar Baba da Abu tasan ƙulunboton da tayi har ya bashi aro ya buɗe ya shiga yana jin kanshi on top don yau yayi dacen haɗuwa da Roshni don ma basu samu sun zanta sosai kamar yadda shi yaso ba amma dai babu damuwa zuwa anjima zai je gidansu ya sameta yadda zai ƙara kafa kanshi sosai.
*****
Bayan wucewar Zainab ne Dada ta ƙara ɗauko abincin Baqeer data mayar kitchen ta ajiye ganin yaƙi buɗe ƙofa ya karɓa ta nufi ɗakin da yake. Ƙwanƙwasa ƙofar tayi tace "Yanzu saboda Allah Baqeeru ba zaka buɗe ƙofar nan ka fito ba? Ga abincinka nan tunda zafinshi nake bin kan ka kazo kaci gashi yanzu har ya huce, ayi rayuwa a haka ace bawa yayi ta zama da yunwa, shikenan don Allah ya jarabceka da wata ƙaddara sai ka shige ɗaki ka ƙuntata rayuwarka maimakon ka gode mishi bisa tarin ni'imomin da yayi maka sai kuma kake nema ka butulce mishi saboda ya jarabci rayuwarka don ya gwada imaninka, wannan wacce irin rayuwa ce da bawa ba zai karɓi ƙaddara a duk yadda tazo mishi ba?" Ga mamakinta sai gani tayi Baqeer yazo ya buɗe ƙofar ɗakin ya miƙo hannu ya karɓi kwanon abincin nashi da tuni ya huce. Miƙa mishi tayi ta juya tana cigaba da ƴan mitocinta akan rufe kanshi a ɗaki da yake yi.
Shi kuwa maganganun yarinyar nan ne suka tsaye mishi a rai yake ta faman juyasu a cikin ranshi inda take cewa "Haka zaka cigaba da rayuwa baka duba mutanen dake rayuwa tare da kai suka damu da damuwarka? Sai maganar wasu ƙalilan da basu san ciwon ka ba basu damu da kai ba zaka ɗauka ka saka a rai?" Shi yasa yaji ba zai iya ƙyale Dada tana maganganunta ba shine kuma yasa shi buɗe ƙofar ba tare daya shirya wa hakan ba. Gara kekenshi yayi ya koma cikin ɗakin ya tasa abincin a gaba yana kallo, tun asali shi ba mai son cin kowanne irin abinci bane shi yasa ma Umma ke yi mishi girkin shi daban don baya iya cin girkin su Abu saboda daga ita har Jamila basa iya tsayawa su gyara girkinsu saboda maigidan ba wani kuɗin cefanen kirki yake bayarwa ba su kuwa kowacce na ƙyashin ta cire daga aljihunta ta ƙara yadda za'a yi wadataccen abinci mai kyau, dama Umma ce bata ƙyashin gyara girkinta bare kuma da Baqeer ɗin yake tsaye akan al'amuranta bata nemi komai ta rasa ba shi yasa yaran gidan har ɗokin zagayowar ranar girkinta suke yi don sun san zasu ci abinci mai daɗi ba kamar na iyayensu ba.
Haka nan ya daure ya tuttura abincin gashi aka yi rashin sa'a wake da shinkafa ba cimar da yake so bane sai dai kuma a yanzu dole yayi haƙuri da duk abinda ya samu tunda dai bai kawo ya ajiye ba bare yayi zaɓen abinci. Ko rabi bai ci ba ya mayar da murfin ya rufe ya samu wuri ya ajiye kwanon, ƙishirwa yake ji sai dai duk ɗakinshi babu ruwa shi kuma yana jin ƙyuiyar ya buɗe baki yayi magana bare ya cewa Dada ta kawo mishi ruwan. Kallon tsakar gidan yayi ya hango randar ruwan Dada mai ɗan karen sanyi daga can hanyar fita daga gidan sai dai baya jin zai iya kai kanshi tsakar gidan bare ya ɗebi ruwa ya sha. Rufe idanunshi kawai yayi ya buɗe yana ƙara kallon wajen da randar take yana ƙara ganin nisan wurin daga nan inda yake zaune, kamar Dada tasan ruwan yake da buƙata sai gani yayi ta nufi wajen randar ta ɗebo ruwan ta kawo mishi. Karɓa yayi ya kafa kai ya sha bai ajiye ba sai da ya shanye ruwan nan tas dama ya daɗe yana son shan ruwan ya buɗe baki yayi magana ne yake ganin asara. Hannu yasa ya gara keken wajen katifar da yake kwanciya sannan yasa hannayenshi duka biyun ya daddafa ya sauka daga kan keken ya koma kan katifar ya kwanta yana murza hannunshi na dama inda ya samu karaya, duk da likita yace hannun ya warke zai iya yin komai dashi kamar da har yanzu yana jin ciwo a wurin bare daya kasance har aikin da ƙafarshi zata yi yanzu hannayen ne ke yi.
*****
Tana ji tana gani haka ta cire kujerunta ta sayar, sauƙinta ma ƙawarta data saya ta sayesu da daraja. Tunani ta zauna tana yi to yanzu wacce sana'a ya kamata ta kama don fa ba zai yiwu ta saka kuɗi a gaba su cinye ba alhalin basu da mataimaki sai Allah, duk da ƴan uwanta na cikin wadata tasan zai yi wuya su tallafe ta don dukkansu daga su sai iyalin su sai ko Dada da suke yiwa aiken kayan abinci lokaci zuwa lokaci, tun can asalinta ma Allah bai yita mai kwaɗayin abun hannun wasu ba shi yasa bata taɓa nufar ƴan uwan nata da nufin su taimaka mata ba sai kuma tayi dace da samun ɗa ɗaya tamkar goma daya ɗauke mata dukkanin wasu larurorinta yake yi mata hidima bakin gwargwado daga ita har ƴan uwanshi basu nemi komai sun rasa ba sai fa yanzu da Allah ya jarrabce shi da larura duk da ma dai akwai kuɗaɗen shi a wurin Mallam don duk abinda ya samu shi yake karɓa yana juyawa don yace ba zai yiwu abar kuɗaɗen haka ba a juyasu ba, a yanzu kuwa tasan bata isa ta tambaye shi batun waɗannan kuɗaɗen ba don tasan dai ba bayarwa zai yi ba sai dai ma ranta da zai ɓaci a banza.
Wayarta ta ɗauka da nufin kiran Hadiza suyi shawarar yadda za'a yi da kuɗin da irin sana'ar daya kamata ta fara sai kuma ta tuna ashe fa babu waya a hannun Hadizar tunda tata ce ta barwa Baqeer ba kuma lallai ne ta samu ta sayi wata ba tunda tasan halin matsin da take ciki gashi sanda Maryam taso bata daga komawa gida tasan mijin ne ya hana. Maryam ta kira a maimakon Hadizar sai taji muryarta tayi sanyi ƙasa-ƙasa kamar wacce ke cikin damuwa. Hankalinta ne taji ya tashi ta hau jerowa Maryam ɗin tambayoyin ko lafiya suke? Jin muryar mahaifiyarta kawai sai tasa kuka, yi take yi babu ƙaƙƙautawa Umma na jinta bata katseta ba sai dai yanayinta gaba ɗaya ya canja ta tsinci kanta cikin damuwar itama. Sai da tayi kukanta ya isheta sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya. "Ki cigaba da haƙuri Maryam komai mai wucewa ne watarana sai kiga kamar ba'a yi ba sai dai a labari, kin ji?" tayi mata maganar cikin tausasawa ba tare data buƙaci jin abinda yasa ta kukan ba tunda dai tsakanin harshe da haƙori ma ana saɓawa tasan ba zai wuce tsakaninta da maigidanta bane.