Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 18

Baqeer complete - Chapter 18

Baqeer complete Chapter 18: Baqeer complete Chapter 18. *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

3,355 words

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar ce* *Da* *Ayusher Muhd*

*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*PAID BOOK*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA ƊAYA*

{22}

"Ta wani abokina ne da muke mutunci sosai na aro tunda kasan ba zai yiwu mu ɗauki motar haya a wannan marrar da ake ciki ba ga nisan wuri ga tsadar mai". Jinjina mishi kai kawai yayi ya juyar da fuskarshi yana kallon waje. Har suka ƙarasa gidan Dada babu wanda ya ƙara magana don tun Salim na takalarshi da zance har ya haƙura yayi shiru ganin ba kulashi zai yi ba. Da taimakon wasu almajirai da suke yawan zama a ƙofar gidan Dada Salim ya samu suka fitar da Baqeer daga cikin mota suka ɗaurashi akan keken. Godiya yayi musu sannan ya turashi suka shiga cikin gidan. Sai da yayi wa Dada bayanin duka magungunan da aka rubuto mishi ta tabbatar mishi zata kula da bashi akan lokaci sannan ya sallame su ya tafi.

Yana shiga unguwarsu yayi kiran Zeey a waya yace mata ya dawo ya za'a yi ya kawo mata motar, sai cewa tayi yayi parking ɗan nesa kaɗan da gidansu zata fito ta karɓa. Hakan kuwa aka yi don bai wani daɗe da tsayawa ba sai gata ta fito, yana ganin fitowarta ya buɗe motar ya fito shima yana murmushi. Miƙa mata mukullin motar yayi yana ta godiya don sosai ta taimaka musu da basu aron motar da tayi in banda hakan da sai dai ya ɗauki drop ɗin taxi ya kuma san kuɗi ne za'a kashe ba ƴan kaɗan ba. Karɓa tayi tace mishi "haba dai ai babu komai yiwa kai ne, ni nasan irin taimakon da zaku yi mini ne a gaba, fatanmu dai Allah yasa an dace da abinda kuka je yi asibitin".

"Ah Alhamdulillah don an kunce ɗaurin ma kuma likitan yace gyaran yayi kyau sosai sai fatan Allah ya ƙara mishi lafiya".

"Masha Allah, ni bari na wuce sai mun ƙara haɗuwa kenan".

Yace mata "to Zainab nagode ƙwarai Allah ya bar zumunci".

"Ameen Ya Rabbi" kawai tace ta shige motarta taja ta ƙarasa da ita gidansu, sai da tayi horn maigadi ya taso ya buɗe mata gate har ta shige ciki sannan Salim ya juya zai bar wurin. Yana juyowa suka kusa yin karo da Kamalu da tun ɗazu yake dakon dawowar Salim ɗin don haka akan idonshi Salim yazo ya wuce da motar Roshni ɗin tashi, har tsayuwarshi da duk maganganun da suka yi shi da Roshni ɗin akan idonshi suka yi sai dai baya jin me suke cewa, shi satar babur ɗin da aka yi mishi ma bata dameshi ba kamar tsayuwar Roshni da wancan tsageran yaron da yake jin kanshi kamar yafi kowa saboda kawai yana abota da wancan gurgun. Ƙwafa yayi cikin ranshi yana jaddada dole ma yaci uban yaron nan Salim don yaga alamun yana so ya kawo mishi raini tunda har yake zuwa wurin Roshni masoyiyar zuciyarshi.

Kallonshi Salim yayi yace "Mallam lafiya zaka tare mini hanya?". Wani irin kallo yayi mishi irin na sama da ƙasa ɗinnan kafin cikin fusata yana nuna shi da ɗan yatsa yace "zuwa nayi naja maka kunne ba naga kanka yana rawa ba ka fita daga hanyar Roshni ɗita ita ɗin ba sa'ar yinka bace idan kuma kaƙi ji wallahi kaji na rantse jikinka ne zai gaya maka". Wata irin dariya ce ma ta zowa Salim ganin yadda ya dage yana zuba masifa har kamar ya kai mishi duka, kasa riƙe dariyar yayi sai da yayi abarshi sannan ya tsagaita ya kalli Kamalun da irin kallon da yake yi mishi yace "wacece kuma hakan? Kai kaga nayi maka kama da wanda zai tsaya yana kula irin tarkacen ƴammatan da kake kulawa marasa nutsuwa da kamun kai? Da Allah Mallam kauce mini daga hanya ni na wuce don ina da abun yi ba irinka bane zauna gari banza marasa aikin yi sai dai yawo daga wannan inuwar zuwa waccan kuna jiran ƴan Allah ya baku mu samu".

Ai kuwa ba ƙaramin kunna Kamalu yayi ba don haka yasa hannu ya janyo rigarshi yace "don ubanka kai har ka isa ma ka buɗe baki ka zagi Roshni bayan ta gama yi maka rana har tana ɗaukar motarta ta baka aro shine kake kiranta mara kamun kai? Kai har ka isa ma kace zaka faɗi wata maganar banza akan Roshni ɗita na ƙyaleka" don ganin nan fa da yayi wa Salim a cikin motar Roshni gashi kuma wai har ta bashi aro ya tuƙa ba ƙaramin zafi yayi mishi a rai ba don gani ma yake yi kawai shima Salim ɗin son Roshni yake yi shi yasa ma har ta ɗauki motarta ta bashi ita ta dawo a napep. Sai lokacin Salim yasan akan wacce yake magana don haka ya ƙara kwashewa da dariya, cikin dariyar yace "au wai dama Zainab ce Roshni ɗin da kake magana akai, lallai kuwa na yarda abar da kasha tayi maka karo har tana faɗa maka ƙarya tunda gashi ka hau kai ka zauna". Kaucewa yayi ya wuce ya bar Kamalu a wurin yana nanata suna ZAINAB, ashe sunan Roshni ɗin shi kenan Zainab suna mai daɗi sai kuma aka yi dace irin sunan Innarshi gareta wato Abu. Ji yayi kamar ya ƙarasa ƙofar gidan yasa ayi mishi sallama da ita tunda dai yau Allah ya taimake shi yasan sunanta sai kuma ya kalli kayan jikinshi yaji ina ai basu dace da zuwa zance wajen Roshni ba don haka ya juya ya koma gida da nufin canjo kaya sannan ya dawo wurin Zainab ɗin.

*****

Tunda dai ta samu tabbaci daga Salim cewa ya kaiwa Baqeer kuɗaɗen har ma sun je asibiti an kunce ɗaurin sai taji hankalinta ya kwanta, godiya tayi ta mishi tana saka mishi albarka don tasan ba don shi ba da bata san yadda za'a yi saƙonta ya iske Baqeer ɗin ba bare da aka ƙara samun tazara mai yawa a tsakaninsu. Tashi tayi ta koma ɗakinta tana ƙarewa ɗakin kallo ko ta samu wani abu mai muhimmanci da zata ɗaga ta sayar ko ta samu taja jari don zama haka bai ganta ba ita da take da ɗa mai larura ga Hadiza da take da wani irin mugun miji da yake ƙyashin abincin da zai basu suci ma bare sauran buƙatu na rayuwa, dama Baqeer ɗin ne mai taimaka mata to shima yanzu ga yadda Allah yayi dashi. Kallon tsaf ta ƙarewa ɗakin ta rasa abu guda ɗaya mai daraja da zata ɗaga ta sayar idan dai kuma ba kujerunta zata saka a kasuwa ba, zama tayi akan doguwar kujerar tana shafata tare da tuna lokacin da Baqeer yayi mata su sababbi fil a leda haka aka shigo dasu ɗakinta aka jera, a waccan ranar taga tashin hankali don muraran su Jamila suka kasa ɓoye hassada da baƙin cikinsu don a cewarsu ma Mallam ne yayi mata aka fake da wai Baqeer ne yayi duk don a raina musu hankali, to ina ma yaga kuɗin da zai iya yin waɗannan kujerun masu daraja banda dai ana so a raina musu wayo, a cewar Abu kenan data kasa ɓoye hassadarta a wannan ranar saboda ita tafi Jamila wayo ba komai take fitowa ta nuna ba sai dai tayi ta mata ingiza mai kantu ruwa ana ganin laifinta.

Zuciyarta babu daɗi saboda duk ta kalli kujerun ta tuna Bqeer ne ya saya mata ba ƙaramin daɗi take ji ba gashi yanzu halin rayuwa yasa dole zata ciresu ta sayar tayi jari ko ta samu abinda zata rufawa kanta da iyalinta asiri. Wayarta ta ɗauko ta kira makwabciyarsu da suke hulɗar arziƙi sosai da ita tace mata ko zata taimaka ta samo mata masu sayen kujerunta, ba tare da bin ba'asi ba tace ai ko itama sai ta saya don kujerunta nata babu abinda suka yi. Haka dai suka ajiye akan zata shigo ta ƙara ganinsu sai suyi ciniki.

***** Tana shigowa cikin gidan ɗakinta kawai ta wuce ta kwanta, sai ma tayi sa'a bata haɗu da kowa ba don bata so Mummy tayi mata magana akan tafiya da tayi ta bar Nabila a kantin da suka je da sai keke napep ta hau ta dawo gida don bata san wani uzurin zata bayar ba kuma duk kuwa da tasan Mummy bata cika yawan matsanta mata ba to amma fa bata so tana yawan ɓata mata rai. Tana shiga ta sakawa ƙofar ɗakinta makulli ta rufe don bata so kowa yazo ya dameta, tana jin lokacin da Nabila tazo tana buga ƙofar ɗakin amma tayi shiru ta rabu da ita kamar bata jinta, a haka har bacci ya ɗauke ta inda bata farka ba sai ana wajen ƙarfe biyu da rabi, tana tashi bathroom ta faɗa tayi alwala tazo ta tada sallah, sai data idar sannan ta tashi ta buɗe ƙofar ɗakin nata ta fita. Akan dining table ta tarar dasu Mummy suna cin abinci. Mummy na ganinta tace "baby har kin tashi?"

A shagwaɓe ta ƙaraso wajen tana ɗagawa Mummyn kai ba tare data buɗe baki ta amsa ba. Kujera kusa da Mummyn taja ta zauna, da kanta Mummyn tayi serving ɗinta su dai Kabir da Nabila suna kallonsu sai ma taɓe baki da Kabir yayi yace "wallahi Mummy ke kike daɗa shagwaɓa yarinyar nan shi yasa take tsula iskancinta son ranta don tasan babu abinda za'a yi mata".

Harararshi Mummy tayi haɗe da cewa "to ina ruwanka? Ko kuwa dai sa ido". Gwalo Zeey tayi mishi tana dariya ƙasa-ƙasa. Ƙwafa Kabir yayi yace "wallahi idan na damƙeki sai kin gane ke ƙaramar mara kunya ce, na lahira sai yafi ki jin daɗi".

"Mummy kin ganshi ko" tayi maganar kamar zata saki kuka.

"Mummy kin ganshi ko" shima ya kwaikwayeta da irin muryarta. Anan suka hau cacar baki kamar wasu ƙananun yara, dama kuma sabon su ne don babu yadda za'a yi su zauna a waje ɗaya basu takali junansu sun yi faɗa ba. Sai da Mummy ta tsawatar musu sannan suka bari sai dai suna ta hararar junansu ƙasa-ƙasa ba tare da sun bari Mummyn ta gani ba. Sai da suka gama cin abincin har ma ta tashi zata bar wurin Mummy ta kira sunanta tare da bata umarnin ta koma ta zauna magana zasu yi. Zama tayi gabanta yana faɗuwa don tasan akan abinda ta aikatawa Nabila ne Mummy zata yi maganar.

Ai kuwa dai tana zama Mummyn ta fara magana cikin tausasawa kamar mai gudun ɓacin ran Zeey ɗin tace "wai ni kuwa Zeey meke damun ki ne kwana biyun nan duk kin canja idan kuma an tambayeki sai kice babu komai?"

Shiru Zeey tayi ba tare data amsa mata ba. Kallonta Mummyn ke yi tana jiran jin amsa daga bakinta sai dai har wucewar wasu mintuna Zeey bata ce komai ba don haka Mummy tace "baki da lafiya ne?" Girgiza kai tayi alamar a'a. "To meke damunki?" Mummyn ta ƙara tambayarta nan ma tayi shiru. "Shikenan to tunda ba zaki amsa ba amma ina kike yawan zuwa da kullum sai kin fita bayan kin san Daddynku ba cika son yawan fitarki yayi ba, kuma ina kika je yau da kika bar Nabila a inda kuka je kika tafi da motar sannan kuma kika dawo a napep kamar yadda maigadi yace sai daga baya kika fita kika amso motar kika shigo da ita? Wama kika bawa aron motar ke kika hayo napep Zeey ba kya gudun wani abu ya faru dake a hanya?"

Kawai sai ta sakawa Mummy kuka abinda ya dakatar da Mummy daga jerin tambayoyin da take yi mata kenan. Tuni hankalin Mummy ya tashi ta koma lallashinta, su Kabir da Nabila dai takaici kamar ya kashe su, su dama sun sani Mummy ba zata iya yiwa Zeey faɗa ba don a wurinta komai Zeey tayi daidai ne sai tace ai yarinta ce tasa wata rana ko ance tayi ba zata yi ba. Tashi suka yi suka bar musu wurin, sai da Zeey tayi kukanta ya isheta Mummy nata aikin lallashi sannan ta iya cewa "kiyi haƙuri Mummy wallahi ni kaina na rasa meke damuna, abun haushi abun takaici kuma na kasa cire abun daga raina".

Ajiyar zuciya Mummy tayi tace "ke kuwa wane irin abu ne wannan daya dameki haka kuma baza ki iya buɗe baki ki faɗa ba ko kya ji daɗi, fatana dai ba akan saurayi bane don kin san fa akwai wanda Daddynku yake son haɗaki dashi, don Allah kada kije kiyi abinda zaki janyo mana ɓacin rai daga ni har ke".

Sai da gabanta ya faɗi da jin wai za'a haɗata da wani duk kuwa data tsinci zancen a parlourn Daddyn ranar da yayi baƙi amma bata wani ɗauke shi da muhimmanci ba. "Ba akan saurayi bane Mummy, ke dai ki tayani da addu'a Allah ya yaye mini damuwar dake raina" kawai ta iya cewa Mummyn ta tashi ta koma ɗakinta, binta Mummy tayi da kallo tana tunanin to me yake damun yarinyar nan ne wai? Gaba ɗaya ta canja kamar ba Zeey ɗinnan ba ƴar hayaniya don in dai tana wuri baka taɓa jin shi tsit.

*****

Sai da ya nufi gidansu da zumuɗin son ya shirya ya koma wajen Roshni ɗin shi sannan ya tuna ashe fa an samu wani ɗan shegiyar ya ɗauke mishi babur ɗin shi, kamar shi kuwa ai yawa ne ya tafi zance wajen Roshni a ƙafa don haka ya fasa shiga ɗakin shi yayi shirin tafiya wajen Roshni ɗin sai ya shiga cikin gida wajen Abu yasan dai ba zai rasa na sayen wani babur ɗin ba a wajenta don a yadda take da zafin neman nan ko mota yace ta saya mishi yasan tsaf zata saya.

Tana zaune a tsakar ɗakinta tana ɗura tsumi a jarkoki saboda masu zuwa saye. Zama yayi daga bakin gadonta yana cika yana batsewa. Kallonshi tayi ta mayar da kofin da take ɗibar tsumin cikin robar tsumin ta ajiye. "Kai kuma lafiyarka ka shigo sai faman kumburi kake yi? Ko kuwa dai wani abu aka yi maka a wajen ka shigo ka huce a kaina?"

Sai da yaci serious irin maganar da zai yi mai matuƙar muhimmanci ce kafin yace mata "babur ɗina fa aka sace".

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta hau cewa tana tafa hannaye, "kai kuwa garin yaya aka yi haka?"

Kasa faɗa mata yadda aka yi yayi sai ce mata yayi wai ya ajiye shi ya shiga shago sayen abu kafin ya fito har anyi gaba dashi. "Yanzu dai Inna ɗan wani abu zaki bani naje na sayi wani don wallahi yadda na saba da babur ɗinnan bazan iya komawa yawo a ƙafa ba".

Dariya ta saki haɗe da shewa tace "to kai in banda abinka baga motar Mallam nan ba don me kaima baza ka riƙa karɓa kana tuƙawa ba".

"Hmm Inna kenan, Baban ne zai yarda ya bani motarshi?"

Da sauri tace "yo me zai hana bayan a yanzu gida ya dawo hannunmu, dama ai saboda wancan gurgun yasa yaƙi kowa amma yanzu da idanunshi suka buɗe ya gane ashe shayi ruwa ne ai dole ya dawo wajenmu mu ɗin dai daya watsar, kada ka samu wata damuwa duk lokacin da kake da buƙatar motar ka faɗa mini kawai ni nasan yadda zan bi dashi na karɓar maka makullin daga haka wata rana ma har sai kaga ya bar maka motar gaba ɗaya in yaso shi ya sayi wata",

Suka saka shewa harda tafawa kamar wasu abokai, Kamalu dai daɗi fal ranshi don yana ganin kamar Roshni taso shi an gama ne in dai har yayi dace da samun motar nan....

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA UKU*

{23}

Zeey tana jin isowar mahaifinsu ta fito daga ɗaki suna gaisawa bata jira wani abu ba tace "Daddy don Allah gobe ina son zuwa Ɗambatta." Ai kafin ta ƙarasa maganarta ya tsuke fuska tamau kai kace saƙon mutuwa aka kawo mishi, fuskar nan babu alamar wargi yace "Kina sake yi mini maganar Ɗambatta wallahi ranki in yayi dubu sai ya ɓaci." Sosai itama ta canza yanayin fuskarta tace "Daddy wai haka ake rayuwa?" "Haka ake rayuwa? Ni kike yiwa magana haka?" Yayi maganar cikin ɗaga murya da tsawa, da sauri Mummy ta ajiye abinda take yi a kitchen ta taho wurinsu tace "Senate ya isa haka nan don Allah, ke kuma wuce ɗaki." A fusace yace "Bata isa ta tashi ba sai ta faɗa mini dalilin da yasa ba'a isa ayi mata magana ba sai ta mayar da martani, akwai sa'anta anan ne ko kuwa don mun kashe kuɗi mun kaita waje karatu shine take neman juye mana abubuwan banzan data koyo a can?" Kasa tayi da kanta ranta na sake ɓaci, daga maganar Ɗambatta sai ya hau faɗa? Menene laifinta anan saboda Allah? Mummy ce ta dafashi tace "Senate please ya isa haka kasan yarinya ce ba komai take ganewa ba." "Yarinya ce amma ta iya zabgawa Najib rashin mutunci ko? To wallahi wannan karon in har kika kori Junaid ki shirya auren duk wanda naga dama don kuwa baza ki janyo mini magana ba." Murmushi tayi ta kalleshi tace "Daddy in dai maganar Ɗambatta ne na daina amma please kai ma ka bar maganar Junaid, yaron nan fa sa'a nane kuma hatta ƴan matan da yayi da na sani." "Wannan damuwarki ce ko cewa aka yi don kin san ƴan matanshi shi kenan bazaki iya aurenshi ba?" Fahimta da tayi ran Daddy ya gama ɓaci yasa ta ɗan dafa kanta kawai sai gani suka yi tayi baya ta kwanta, a rikice Mummy ta taso Daddy ma haka duk ya rikice don Zeey ce sanyin idaniyarahi dauriya kawai yake yi yana yi mata faɗa don ya lura rashin tsawatar mata na nema yasa ta kangare, ɗagota Mummy tayi tana kiran sunanta cikin ƙarfi, a hankali ta fara buɗe idanunta tana lumshesu tace "Mummy ki bawa Daddy haƙuri…."ta sake maida idanunta ta rufe, hankali a tashe ya ƙaraso suka hau ƙoƙarin maidata kan kujera, Mummy ta kwallawa Kabir da Nabeela kira. A kusan tare suka shigo falon, Kabir daga gefe yaja ya tsaya ranshi na sake ɓaci yace "Wallahi in baki tashi ba zaneki zan yi da belt ɗin jikina." Shareshi tayi tana ji Mummy nayi mishi faɗa ai kuwa Kabir ya nufota yana ɗan ware belt ɗin shi, ido ta buɗe kaɗan ganin yadda ya nufota yasa tayi saurin miƙewa ta ɓoye a bayan Daddy wanda mamaki duk yasa sun kasa magana, hararar Kabir tayi tace "Bro wallahi ka canza rayuwa." Ta kalli Daddy tace "Sorry Dad just joking." Tana kaiwa nan ta ruga tayi ciki tana dariya. Takaici ne yasa su dariya wanda Kabir yace "Daddy ka gani ko? Shi yasa nace ka barni da ita na gyara mata zama.

Zainab kuwa kwanciya tayi akan gado har yanzu dariya take yi, can ta tsaya da dariyar tunowa da halin da Baqeer yake ciki da tayi. Ko ya yake yanzu?

***** Washegari…….

Umma tana kallon Baba yadda ko kallon ɓangarenta bai yi ba yake ƙoƙarin fita daga gidan, gaisuwar ma da take yi mishi bai amsa ba, cike da dauriya tace "Mallam nace nasa kujeru na a kasuwa saboda magungunan Baqeer tun jiya nake so na sanar da kai."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull