Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 17

Baqeer complete - Chapter 17

Baqeer complete Chapter 17: Baqeer complete Chapter 17. ******* Baba tun daga waje yana packing Bashir ya taho da sauri ya sanar dashi Baqeer baya gidan,…

3,370 words

******* Baba tun daga waje yana packing Bashir ya taho da sauri ya sanar dashi Baqeer baya gidan, kai tsaye ɗakin su Baqeer ɗin ya nufa ya buɗe ƙofar ya shiga, ganin baya nan yasa ya kara shiga ciki yana bin ɗakin da kallo, babu komai na Baqeer agun sai kayan zanenshi, wanda hakan ya sake tunzuroshi ya jijiga kai tare da yin ƙwafa, ya fito ya nufi ciki, mai makon ya shiga ɗakin Fatima sai ya nufi ɗakin Abu duk da kuwa kwanan na Fatima ne, tana jinshi sanda ya shiga ta kauda kai dan ita yanzu ba wannan bane a gabanta, tunanin yanda zata samo kuɗi ta aikawa Baqeer takeyi, dan yana bukatar komawa asibiti, ta sani Baqeer nada kuɗi sai dai kaf kuɗin shi a hannun mahaifinshi suke, wanda yake ajiyewar kuma duk ya musu hidima dashi ita da kanenshi, idanunta ne suka sauka akan injin taliyar nan ba ɓata lokaci ta ƙira wata kawarta mai saida kayayyaki ta sanar da ita zata saida injin taliyarta amma tana san kuɗi hannu, dubu biyar tace zata siya haka Umma tace to tunda tasan ba yanda zatai. Jamila kam an shaka an shaka lalai Abu banu munafuka irinta, maganin data bata ta ɗauko rai a ɓace ta sa a bin hanzu zargi ma take kila ma asiri ta bata na rabata da Mallan ita kuma ta dinga cusawa.

***** A bangaren Baqeer kuwa, tunda ya shiga ɗaki yake jin komai na duniya ya sake fita a kanshi, Dada ta shigo tai ta magana bai iya ko furta kalma ɗaya ba, daga baya ma ta fara tunanin kamar baima san me take cewa bane, haka ta ajiye abinci ta fito, tagumi kawai tai tana mamakin yanda rayuwa ta juyawa Baqeer baya, yaran da ganinshi kaɗai ke sata farin ciki yau shine haka? Tun yana saurayi ya mata alkawari shi zai kaita Hajj ashe haka Allah ya shiryawa rayuwarsa? Tana gani ya turo keken ya nufi bandakinsu dake waje, yanzu kam bai nemi taimakon kuwa ba haka ya dage ya matsa jikin toilet seat yai fitsari yai tsarki sannan yai alwala ya sake tura keken ya koma ɗakin, baisan kallanta dan ya tabbatar zuciyarta a karye take saboda shi, sallah yai daga zaune bayan ya gama ya fara rokar Allah yai gaggawar datse rayuwarshi ko ya samu sassaucin raɗaɗɗin da yake damunsa, bai ko kalli abincin ba balle yaci sai ruwa kawai dayasha. Yana zaune yana juyo Dada da yara a waje suna ƴar hira wanda ya tabbatar shigowa sukai, yau wayar ma airplane ya sakata kawai ya kunna karatun Qur'ani.

***** Wajen azahar aka aikowa Fatima da kuɗi ita kuma ta bada injin taliyar a boye dan kar asan meke faruwa. Sunyi waya da Dada ta sanar da ita halin da Baqeer yake ciki, Umma abin duniya ya sake taruwa ya mata yawa tana juyo Abu na shewa wai yau da gaza zatai girki, Jamila ce ta fito tana mata kallan sama da ƙasa tace "To kiyi da agwagwa ma mana meya damemu." Abu ta dan wurga mata wani kallo tace "Ke kawata kar muyi haka dake ai ke cinya ma zakici." Takaici ya kama Jamila tace "Hala a ɗakin da kuka shige ciki ranar kwanan Fatima baku tuna da hakkin wata kuke ci ba?" "Ke bansan iskanci har yaushe kika fara maganar hakki? Kedai na kula da bala'i yau kika tashi ni zuciyata tas take yau shiyasa bana san husuma da kowa." Tsaki Jamila tai ta wuce ciki ranta a matukar ɓace, Abu ta taɓe baki tace "Wannan kuma damuwarki ne."

Fatima kai kawai ta girgiza dan ita duk wannan abun ba shine a gabanta ba, addu'a kawai take Allah ya kawo wanda zata aikawa da kudin nan.

******** Zeey ce tsaye jikin shagon da Nabeela ke siyayya, takaici tsayuwar duk ya isheta ta kalleta tace "Kinga na kula baki shirya gama siyayyar nan ba, in kin gama ki kira driver ya maida ke gida zan ɗan je wani guri na dawo." Mamaki ne fal ya rufe Nabeela tace "Ina zaki?" Card ɗinta na atm ta mika mata tace "Gashi sai na dawo." Bata jira amsarta ba ta juya da sauri ta shiga mota tai gaba, gidansu Baqeer tai parking shiru tai a cikin motar tana tunanin inta shiga tace me ya kawota? Dabara ce ta faɗo mata akan zataje tace ai number jiya batai saving ba ashe, har zata fito sai kuma ta sake komawa ta zauna tana maida ajiyar zuciya kafin ta sake daurewa ta fito, da sauri ta shiga dan bataso Baqeer dake soron gidan ya hangota. Abu na ta fige kaza sanda ta shigo ko kallo bata isheta ba balle tai mata magana. "Nikam ke wacece wai? Dan jiya ma naga fitarki daga gidan nan." Zeey kamar batasan da ita takewa magana ba tai sallama ƙofar ɗakin Umma, wata hamdallah Umma tai ganin Zainab, bayan sun gaisa ta amshi number Maryam ne Umma ta mika mata kudin tare da rokon taba Salim ya taimaka yakai Baqeer asibiti. Da mamaki tace "Baya gidan ne?" Jin Umma na cewa dama ta rasa wanda zaije inda Baqeer yake. "Yana gidan Dada a Mariri." Cike da mamaki take kallan Umma sai dai bazata iya tambayarta komai ba, nan Umma ta bata number Salim kamar tace Umma tabar 5000 ɗin zata bada amma tasan halinta tabbas ta faɗa yanzu za'a juyo faɗan ta, a cikin mota ta zauna tai shiru tana kallan kuɗin ko dai ta kara musu ne ba tare da sun sani ba? Amma in Umma taji kuma tace ba ita bace ba fa? Shafar fuskarta tai kafin ta ƙira Salim a waya ta sanar dashi sako ne Umma ta bada zata bashi. Nan yace gashinan zuwa, taɗan gangara cikin layin tai parking sannan ya fito. Kamalu dake ta sauri a babur ɗinsa zasuje kallan kwallio ɗakin wani abokinsu, kamar a mafarki yaga Roshni ɗinsa ta fito ta tsaya kusa da Salim, baiyi auni ba yaji yabar kan titi saura kadan ya kifo daga kan mashin ɗin, da sauri ya tsaya yana waiwayensu, ganin murmushi yai a fuskar Roshni nan fa kishi ya turnuko shi lallai Salim dama ya tsaneshi ya aka yi ma yasan Roshni ɗin shi?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*PAID BOOK*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA ƊAYA*

{21}

Cike da sauri Kamalu ya fara ƙoƙarin tsallaka titi ganin Salim na neman shiga motar, ganin da gaske babur ɗin babu dama yayi kwana dashi yasa ya jingineshi a titi ya tsallaka da gudu yana neman zuwa inda suke. Zeey ce ta kalli Salim bayan ta mika mishi 10k wanda ta ƙara 5k akai tare da fatan kada Allah yasa Umma ta gane, ta kalleshi tace "Gidan Maryam ɗin kusa ne?" Ya sauke wayar da suka gama da ita akan kai Baqeer asibiti, sannan yace "Eh ba nisa sosai zan hau mashin naje na amshi motar na kai shi sai na maida mata motar gida." Kai ta jinjina kafin tace "Muje nayi dropping ɗinka tunda in ka tafi da motorcycle ɗin ma dole ka ajiye." Daɗi ne ya kamashi don dama ba wani man kirki gareshi a ciki ba hakan yasa ya shiga gaban mota ita ma ta shiga, ta kunna mota suka fara tafiya. Kamalu sai haki yake yi wurin gudu sai dai kafin yazo yana gani suka yi gaba, iska ya nausa cikin matuƙar ƙunar rai yace "Wallahi Salim sai na fasa maka baki sai kasan motar Roshni ɗi ta ka shiga shegen yaro da shishigin tsiya." Juyawa yayi yana tafe yana zage-zage da masifa, turus yayi a gefen titi ya fara waige-waige yana neman inda ya ajiye babur ɗin shi, mamaki ne duk ya gama rufeshi ya rikice a wurin yana waige-waige sai dai babu babur babu alamarshi, hankali a tashe ya nufi wani mai saida yalo yace "Yayana don Allah kaga babur ɗina?" Yaron ya kalleshi yace "Yaushe na zama yayanka? Sannan wani babur kake magana?" Kamalu zufa ce ta fara keto mishi yace "A daidai nan na ajiye don Allah yi tunani kaga wani ya ɗauke?" "Wa zai ɗauke maka babur in har key ɗin na hannunka?" Nan ya laluba aljihunshi ashe ko key bai cire ba? Yaron ya kalleshi yace "To Allah ya kiyaye." Gaba ɗaya Kamalu kanshi ne ya ɗauki zafi ya fara bin hanya yana neman babur sai dai babu shi babu alamarshi. Haka nan ya haƙura ya nufi gida kamar wanda aka yiwa dukan tsiya.

****** Maryam ce ta kalli mai gidan nata dake zaune a ɗaki tana yi mishi tausa cike da sanyin murya tace "D don Allah kaji? Ba dadewa zai yi ba yana kai shi zai dawo." Kallonta yayi takaicin yadda take fifita ƴan uwanta sama dashi na damunshi don jiya ko bata faɗa ba yasan kuɗin cefanen daya bata su taje ta kashewa, sai dai ya zai yi? Yana sonta iya so shi yasa yake haƙuri da waɗannan abubuwan nata. Zare ƙafar shi yayi yace "To shi kenan ni bari na fita." Sumbatarshi tayi a saman leɓe tare da tsotsan kasan leɓen nashi kaɗan tace "Love you." Murmushi ya sakar mata sannan ya fito, ta rakashi har mota sannan ta dawo ɗaki, kayan da bai saka ba wanda ta ciro mishi ta mayar cikin drawer. Waya suka sake yi da Salim akan yana waje zai turo mai gadi ya amsar mishi key ɗin motar. Tace to tare da fitowa falo dan ɗauka me zata gani? Babu key ɗin motar a wurin, cike da mamaki ta hau dubawa sai dai babu shi babu alamarshi, ganin haka yasa ta kira mai gidan nata din tana tunanin faɗan da suka yi jiya watakila yasa ya manta ya ajiye a wani wurin. Bayan ya ɗauka take sanar dashi bata ga key ɗin motar ba, buɗar bakinshi sai ce mata yayi Baffanshi ya amsa zai je wani wuri daga nan zai taho da Areef. Gaba ɗaya mamaki ne ya rufeta tace "D me kake cewa? Na ɗauka mun yi magana da kai akan zan bawa Salim ya kai Ya Baqeer asibiti?" "Ohh haka ne fa ki cewa Salim ya nemi adaidaita sai ki bashi 1k duk da nasan ba zai wuce 500 ba kinga ai babu laifi, kin dai san ba zai yiwu Baffa ya hau adaidaita ba bayan ga mota a gida, sannan don motarshi na wurin gyara bazan ce mishi kada ya fita da motar dana sayawa jikanshi ba." Kasa magana tayi saboda tsananin mamakin kalamanshi, duk da ba yau suka saba guma mata takaici ba amma na yau yayi mata zafi fiye da ƙima, yanzu duk soyayyar da suka sha daren jiya har ya manta ya koma gidan jiya? Kasa magana tayi sam bata ma san shi ya kashe wayarshi ba sai ringing taji a kunnenta, kallon wayar tayi Salim ne ta ɗauka cikin dakushashiyar murya taji yace "Nayi mishi magana zai zo ya amsa nima yanzu na iso, ƙawarki ce ma ta ajiyeni." Hawaye taji sun gangaro mata, ta sharesu tana cewa "Wacece?" "Zainab dai Zeeyn Baqeer, nayi mamakin ganinta wallahi data cemin Zeey ce nayi ta mamaki har muka iso mamaki bai bar kaina ba." Murmushin yaƙe tayi tace "Don Allah taimaka ka bata." Shi kanshi yadda ta amsa yasan da wani abun sai dai bai tambaya ba ya miƙawa Zainab, ta kara wayar tana cewa "Umma ce ta bani saƙo wurin Salim ashe ma wurinki zaizo, ban yi plan da shigowa gidanki ba shi yasa bazan leƙo ba." Maimakon taji ta bata amsar maganar data yi sai ji tayi tace "Zeey don Allah ki taimaka ki bada motarki akai Baqeer asibiti na rasa ya zan yi....." ta ƙarasa maganar cikin rawar murya "Okay, amma kin tabbatar babu wani abu?" Ta sauke ajiyar zuciya tace "Nagode sosai babu komai wannan ma da kika yi mana kin biya mana, Allah ya saka miki da alkhairi." Kashe wayar Zeey tayi don daga yanayin maganar Maryam tasan babu lafiya gashi bata so taga mutum cikin damuwar da ba zata iya tallafa mishi ba. Da murmushi ta kalli Salim ta miƙa mishi key ɗin motar tace "Kaje da tawa ashe ta manta akwai abinda zata yi kuma uzurin na dole ne." Ya amsa tare da godiya, kallonta yayi yace "In ajiyeki kafin na wuce?" Tunowa data yi in har tsautsayi yasa aka ganta akwai tashin hankali hakan yasa tace "No kawai kaje inka gama ka kirani na fito nazo inda kake na amsa." Da mamakin kalamanta yake kallonta to taya zata koma gida? Ƴar gayu kamar ta? Sai dai yasan a yanayin yanda Zeey take magana da isa bai isa ya sake tambayarta ba, bata ko tanka shi ba ta fito yana kallonta ta tari adaidaita kai daga gani kasan bata san ya ake tarar su bama, ta sanar dashi inda zataje yace 700 ga mamakinshi yaga ta shiga bayan shi jan magana yayi ya tsuga mata kuɗi, zaune take a ciki tana kallon yadda ake gwajab-gwajab da ita a hanya gaba ɗaya mamakin kanta ya isheta wai anya itace dai Zainab? Zainab Sulaiman Karaye? Anya kuwa a cikin hankalinta take abubuwa? Tun ɗazu take kallon kiran da Nabeela keyi mata amma taƙi ɗauka, kanta kawai ta shafa tana mamakin yadda ta manta abubuwan da suka faru a baya tsakaninta dashi sannan har ta ke manta kanta wurin ganin ta taimaka mishi. Gefen titi ta kalla daidai nan mai adaidaita ya sake jijiga tace "Ai ba don shi nake yi ba don su Umma nake yi." Ta ƙarasa maganar tana sauke ajiyar zuciya. A gefen gidansu ta sauka ta bashi 1k tana neman wucewa, daga nesa ta hango yarinyar nan tsaye da saurayin rannan da alama kyauta ma ya kawo mata don ga abu nan a hannunta sai smiling take yi, shi kuma yana jingine a jikin mota, wani kallo tayi musu na takaici kawai ta shiga gida, shi kam mai adaidaita daɗi ne ya kamashi don ya kula bama tasan nawa ta bashi ba saboda hankalinta baya wurin, cikin sauri yaja adaidaitarshi yayi gaba don ma kada ta dawo tace ya biyata, mamaki ne ya rufe mai gadi daya buɗe mata ƙofa ta shiga, kai tsaye ɗakinta tayi ta faɗa kan gado tayi ruf da ciki tana ƙullawa da kwancewa.

***** Bello dake tsaye kusa da Asiya wata irin gigitaciyar soyayya ce take taso mishi, ji yake yi kamar yafi kowa dace a duniyar nan, ya mata alama data shiga cikin mota ta buɗe gift din, shiga tayi shima ya shiga ya zauna ta buɗe jakar sannan ta dauko box din dake ciki, kwalin jaka ne set ɗinshi da takalmi, wani sanyayyen murmushi ta sakar mishi tace "Bae ka bar sakaltani da yawa fa, kullum ne sai an kawo mun gift?" Hannunta ya riko yace "My love kin dai san kin fi ƙarfin komai a wurina, nayi miki alkawari zan jiyar dake soyayyar da ko sunan Baqeer baza ki tuna ba nan gaba." Murmushi ta sakar mishi tace "Yanzun ma kana yi" "Tukunna ki jira na samu fita ƙaro karatun don ƙafata ƙafar ki gwara muyi aure na tafi dake." Wani sanyi ne ya ratsata tabbas Bello zai cika mata burinta, har yanzu ba wai tana sonshi bane amma future ɗinta ta tabbatar a wadace take in har ta aureshi.

******* A bangaren Baqeer kuwa Dada ta sakashi ya fito falo yana zaune yana kallonta tana ta ƙoƙarin bashi labarin tasowar Umma duk don taga ya saki jikinshi sai dai kawai kallon gefe yake yi babu alamar hankalinshi na inda take, jiki a sanyaye take kallonshi ita kam Baqeer ɗin daa take son gani, sallamar Salim suka jiyo, ta amsa ba tare da tasan wanene ba, sai daya shigo ta ganshi, cike da fara'a ta amsa tace "Salim yau kai ne a gidan?" Ya shiga yana dariya yace "Tunda kin gujeni kuma me zaki ce mun?" "To kai in banda abinka in na aureka ai sai dai a binne ni da kai don tabbas baka isa ka rabu dani ba sannan ko aure baka isa kayi ba ko na mutu." Dariya sosai yasa yace "Wai abun haka ne dama? To ai ana auren ɓoye." "Ahaf kai na mutu'a ma kagani." Sun dade suna tsokanar juna sai dai Baqeer ko kallon inda suke bai yi ba, jiki a sanyaye Salim ya mika mishi hannu yace "Baqeer don Allah kayi hakuri kaji?" Bai kalleshi ba har yanzu idanunshi na gefe, yana murmushi yasa hannu a aljihu ya ciro kudi yace "Umma ce ta bada zamu je muga likita yanzu." Da kallo yabi kuɗin nan da nan yaji kanshi na wani irin sarawa, ina Umma ta samo kuɗi haka? Kanshi kawai ya shiga girgizawa yana neman tunano inda ta samu wannan kuɗin, ya tabbatar injin taliyarta ta sayar kila ma har da kayayakin ta. Hannu yasa kawai ya hau dukan ƙafarshi da hannun hagu yana wani irin numfashi, A zabure Salim ya taso yana ƙoƙarin janyeshi sai dai Baqeer cikin sauri ya tura kekenshi ya fara tafiya, binshi Salim ya nemi yi Dada ta girgiza mishi kai, har Baqeer yayi ciki ya banko ƙofar da karfi kai kace ɓallata yake son yi. Suna daga waje suna jiyo yadda yake ihu da alama kafar yake ci gaba da duka, dukkansu basu san sanda hawaye ya gangaro musu ba, Salim yana hawaye yace "Dada ya zamu yi da Baqeer?" Ido kawai ta runtse tace "Addu'a babu yanda zamu yi dashi sannan wannan halin da yake ciki shine zai maidashi jajirtacce, dole yasan rayuwarshi ta daa da kuma ta yanzu ba ɗaya bace, sannan dole ya miƙe ya nemarwa kanshi mafita ni da kai da ita Fatiman duk babu abinda zamu iya yi mishi in har shi bai shirya canzawa ba." Ya daɗe a cikin wannan yanayin kafin ya samu nustuwa, me za ayi da rayuwarshi? Ya tabbatar iyayenshi da zai faɗi ya mutu yanzu hankalinsu sai yafi kwanciya. Jin shiru yasa Dada ta buɗe ƙofar tace "Kazo kuje asibiti lokaci na ƙurewa, magana ce bai son yi sai dai yaja ya turje, ta kalleshi tace "Kasan dai ni kakar kace ko? To in har na isa da kai ka wuce ku tafi." Kallonta yayi yana son sanar da ita kuɗin injin taliyar Umma ne fa sai dai ba zai iya ba ji yake yi baya son ko furta kalma ɗaya har ajalinshi yazo. Haka Salim ya jashi suka shiga mota, wani kamshi ne yaji wanda yasa yaji zuciyarshi ta samu wata nutsuwa da shi kanshi bai san daga ina ta fito ba, idanunshi ya maida ya kulle yana ɗan maida numfashi sama-sama, har suka isa asibitin bai yi magana ba, suka shiga ciki Doctor ya musu magana akan tun last week ya kamata suzo amma basu zo ba, nan Salim ya bada hakuri aka kwance naɗin karayar da aka yi mishi ya sake duba Baqeer sannan ya rubuta musu magunguna, dubu takwas Salim ya siyo magungunan, suka koma mota, har yanzu kamshin motar ɗazu yana nan, ya sake kwantar da kai jiki a sanyaye ya cewa Salim "Salim don Allah ka ji da kasuwancinka kada ka damu dani wannan yawon da kake zai iya dakushe maka kasuwarka." "Baqeer mu dai fatan mu ka cire wannan damuwar dake ranka kana dai ji Dr yana cewa depression ne yake damunka don Allah ka....." Kanshi ya kawar gefe wanda hakan yasa Salim yin shiru, sun dade babu wanda yayi magana sai can yace "Motar waye wannan?" Kallonshi Salim yayi, anya yace mishi ta Zainab ce? Bayan kaf unguwarsu shekarun baya sun san cases ɗin daya shiga tsakanin mutanen biyu? Wanda a dalilinshi su Zeey suka tashi daga unguwar?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull