Baqeer complete - Chapter 16
Baqeer complete Chapter 16: Baqeer complete Chapter 16. Zainab da tun fara faɗan Mallam Badaru ta kasa zaune ta kasa tsaye mamakin jin tijarar da yake yiwa…
3,314 words
Zainab da tun fara faɗan Mallam Badaru ta kasa zaune ta kasa tsaye mamakin jin tijarar da yake yiwa Umma da Baqeer a tsakar gida cikin mutane kawai take yi kamar ba shine wannan mai ji da Baqeer ɗin ba da baya iya ɓoye soyayyar da yake yi mishi a gaban kowa ma nuna mishi so yake yana alfahari dashi, wai shine yanzu don wani iftila'in rayuwa ya saukar mishi yake neman ya juya mishi baya, ji take yi kamar ta fito ta faffaɗa mishi baƙaƙen maganganu ko ranta yayi sanyi ita dai tasan ko me zai sameta a rayuwa Daddynta ba zai taɓa barinta ba amma shi wannan sai gashi shine ma kan gaba wajen nunawa ɗan nashi ƙiyayya. Kasa haƙurin jure jin waɗannan maganganun tayi ta fito ta fice fuu a fusace ta bar gidan, da kallo ya bita yana tunanin ita kuma wannan wacece, idanunta kan Baqeer suka sauka wanda daidai nan shima ya ɗago ya kalleta, yanayin kallo tayi mishi wanda ya sakashi sake kallonta sai da ta ƙurewa ganinshi sannan kalaman Baba suka dawo dashi daga kallon wurin, me idanunta ke son ce mishi? Meya kawota gidansu yau ma? Baba yaji ya cigaba da zazzagawa Umma tijara tana tsaye tana zubar da hawaye, shi kuwa Baqeer baƙin cikin yadda Baban yake nuna mishi ne ya cika fal cikin zuciyarshi sai wani irin kallo da yake bin Baban dashi yana tunanin wai dama can haka yake ko kuwa yanzu ne dai ya canja halinshi ganin babu wani amfani da zai iya yi mishi. Ajiyar zuciya yayi wanda Baban yace "Kai Baqeer ina fada kana sauke mini ajiyar zuciya?" Kai ya kauda kafin ya samu kanshi da cewa "In ka gaji dani ka sallamani mana, wannan wace irin rayuwa ce?" Baki buɗe Baba ya kalleshi a fusace yayi kanshi yana neman ya dakeshi cike da hargagi yake cewa "Ni kakewa magana haka?" Umma ce tayi saurin shan gabanshi tace "Mallam na rokeka da Allah ka bari, wannan wace irin rayuwa ce? Dame ake so yaron nan yaji?" Kallon Baqeer yayi yanda ko kallonshi baya yi, nan ya sake fusata yace "Ni Baqeer zai yiwa haka? Duk yadda na kula dashi a rayuwa? Sannan ina faɗa ki dinga cemin wace irin rayuwa ce wannan to wallahi yattara kayanshi ya bar min gidana, kuje can kusan abun yi." Abu ce tace "Mallam ayi haka? Ba dai almajiranta kake so su fara janshi ba ko? Gurgu ina zai je in ya rasa wurin zama?" Jamila ce tayi saurin cafewa tace "To ai yanzu barar ma sana'a ce kawai dai yaron Mallam ya girmi sana'ar barar ne." Ai kamar sun sake ingizoshi sai cewa yayi "Yaje yayi abinda yafi bara ma ya dameni ne? Na dai faɗa muku wallahi kafin nan zuwa magriba kusan inda kuka kai shi, har ni zai faɗawa magana? Duk ya gama tallata kanshi a titi wato azo aga Baqeer babu ƙafa ko? To kai ma ka ɗana kaji ya zaka yi rayuwa in ba gida." Yana kaiwa nan ya juya cikin ƙunar rai yayi waje. Umma ce ta kalli Baqeer wanda take tunanin zata ga yana hawaye da mamaki ganinshi tayi garau, kallonta yayi sannan ya ɗan murmusa gefen leɓenshi kaɗan yasa hannu yana tura keken zuwa ɗakin shi. Jikin window yaje ya zubawa waje ido abubuwa da yawa na sake yawo a cikin ranshi, rayuwa kenan, ada ko a mafarki aka ce Babanshi zai yi mishi haka ba zai yarda ba, mutumin da ko dukanshi aka yi a islamiyya da kanshi yake zuwa yaci ma malaman mutunci, wai yau shine ke faɗar ya bar mishi gida. A hankali ya runtse idanunshi idanuwan yarinyar ne suka sake giftawa ta idanunshi, wai wacece dake neman shigowa rayuwarshi ƙarfi da yaji? Wayarshi ce tayi kara a hankali yasa hannu ya ɗauka sai yaga Salim ne, hakan yasa bai ɗauka ba, ba wai don yayi fushi ba sai dai ba zai bari Baba ya dinga cin zarafin shi ba daga taimako, ya sani abinda Baba yayi mishi tabbas ya taɓa ranshi sosai tunda yasan yadda yake ji in wani yayi mishi gori, kuma shi yanzu dake gaf da tafiya lahira baya ji zai bar Salim ya shiga wani halin saboda shi, saƙo Salim yayi mishi 'Baqeer ya jikin? Kayi hakuri tun daga ranar nan ban sake zuwa wurinka ba.' Kamar kada ya mayar mishi saƙon sai kuma dai ya rubuta mishi 'Salim ina godiya har abada bazan manta da hallacinka gareni ba, haƙiƙa kai aboki na gari ne.' Yana kaiwa nan ya tura tare da kashe wayar gaba ɗaya. Sake maida idanunshi yayi ya rufe yana son sanin wani irin kallo yarinyar nan tayi mishi, na tausayi ne ko na jin ƙai? Me take son cewa wanda idanunta suka nuna mishi? Kanshi kawai ya kwantar yana sake yawo da abun a ranshi.
**** Abu ce tace "Tab din jam! Fatima yanzu ya zaku yi? Ba dai da gaske barar zaku fara ba?" "In ma barar zamu fara ina dai ba Kamalu bane ɗan jagora?" Umma ta faɗa tana komawa ciki ranta a matukar ɓace, Jamila ce ta sheke da dariya tace "Abu kema dai da neman magana kike." Wani mugun kallo Abu ta watsa mata ta koma ciki, Jamila ta taɓe baki ta koma nata ɗakin ita ma, haɗin da Abu ta bata rannan ta ɗauko tabbas wannan haɗin ba abin arziki aka bata ba dan gashi sai cusawa take yi bata ga wani canji daga Mallam ba iya kace ma kwanciyar da ƙyar take samu suke gamawa. Ƙwafa tayi tace "Muguwa wato ni zaki cuta ko? To nima zaki ga wulakanci, ai ina da mutane a Sokoto, mu saka ƙafar wando ni dake.
Umma kuwa tana shiga ɗaki ta ɗauki waya ta kira Maryam da Hadiza ta sanar dasu suzo gida akwai gagarumar matsala.
***** Da ƙarfi ta daki steering wheel na motar tana sauke wani huci tare da furzar da iskar dake bakinta, ji take yu zuciyarta na wani irin azalzala, da ƙyar ta kai kanta gida tana shiga ta maida ƙofar motar cikin ƙarfi ta nufi ciki da sauri, Mummy na kitchen ana ta shiryawa Daddy abinci don yau akwai baƙin daya gayyata zasu zo. Zeey na shiga ta ƙarasa wurinta da gudu ta rungumeta. Bayanta ta shiga shafawa tana cewa "Ya isa haka nan, ni kam meke damunki ne gaba ɗaya kin canza? Kin san maganarki nawa kuwa daga jiya zuwa yau?" Zeey ta ɗago ga mamakin Mummy hawaye ta gani a fuskarta, hankalinta ne yayi mugun tashi ta kamata suka yi ɗaki a bakin gado ta zaunar da ita ta kwantar da kanta saman cinyarta tana shafa saman kanta tana cewa "Zainab menene? Menene yake damar mini ke haka?" Kallon Mummy tayi ta share hawayenta tace "Mummy nima ban san meke damuna ba, takaici ne kawai yake damuna na rasa yadda zanyi nayi magana." "Kamar ya kenan?" Yawun bakinta ta haɗiya tace "Mummy ashe iyaye ba zasu iya yarda da ƙaddara ba in Allah ya jarabci ɗan su? Ashe iyaye zasu iya manta soyayyar da suke yiwa ɗa saboda ya samu wani giɓi a rayuwar shi? Mummy ta yaya hakan zata kasance?" Murmushi ta ɗan yi kaɗan tace "Ba lallai sun manta da soyayyar bane watakila dai abinda ya samu ɗan nasu ne ke damunsu sosai wanda yasa suke huce takaici a baibai." Kai ta girgiza tace "A'a wannan ba haka bane." Ta sake shafar kanta tace "Kin san Allah yayi mu daban-daban dole wasu halayensu zai banbanta, amma ke menene naki na damuwa? Ko wanda aka yiwa hakan kin sanshi ne?" Kallon Mummy tayi da sauri, Mummyn tace "Namiji ne?" A zabure Zeey ta miƙe tace "A'a mace ce sannan ba wai saninta nayi ba Mummy a hanya na gani shine abun ya dameni." Kai ta jinjina cike da gamsuwa don tasan Zeey da tausayi, shi yasa abin bai wani bata mamaki ba.
****** Maryam da Hadiza sun sha kuka jin abinda ke faruwa, jiki a sanyaye Maryam tace "Ni matsalata uban miji, da zai bari da sai na kaishi BQ na gidana ya zauna, amma kun san halinshi dai yana gani na tafi dashi gidan sai hakan ya zama abun magana har ma ya nemi haɗa fitina a tsakanina da Baban Aareef." Umma ta girgiza kai tace "Kema kin san ba bari zai yi ba don haka kar ma ki fara." Hadiza tace "wurin Dada ne kawai ya rage mana amma ta tsufa Umma ita kanta tana buƙatar mai kula da ita." Maryam tace "Ya zamu yi? Haka nan zamu kaishi sai mu nemi mai aiki ko a layin ne ta dinga zuwa tana gyara gidan da safe." Shiru suka yi don tabbas sunsan basu da wata mafita data wuce wannan. Cikin takaici Maryam tace "Gwara ma ya bar gidan don zamanshi anan ba abinda zai jawo mishi sai depression, ace gidan iyayenka sam baka da kwanciyar hankali?" Hadiza ta girgiza kai tace "Wallahi abin nan na cimin rai dole mu tashi mu nemi kuɗi mu taimakawa Ya Baqeer wahalar da yayi damu shekara da shekaru muma mu nuna mishi yana da ƴan uwa masu ƙaunarshi." Umma ta share kwalla tabbas itama tana ganin gwara ya bar gidan don ko kalmar bara dasu Abu ke ambata inta tuna ranta ɓaci yake yi. Haka su Maryam suka kwashe kayanshi aka saka a motarta, nan suka jawo kekenshi, wani babban almajiri ya taimaka aka sakashi a mota ko sallama basu yiwa su Abu ba suka yi gaba. Abu na ciki ta fito da sauri jin ƴar hayaniya kaɗan, Jamila ma ta fito da sauri suka kalli Umma dake tattare kaya a tsakar gida suka kalli juna, Abu tace "Na ɗauka ma baƙi aka yi?" Umma ko tankasu bata yi ba ta cigaba da aikinta, tunanin saida injin taliyarta ne ya faɗo mata akan ta sayar ta aikawa Dada da kuɗin su fara amfani dashi kafin ta samu abun yi.
Baqeer kuwa har suka isa gidan baice komai ba don shi kanshi bai son zama a gidan su kuma yanzu ya tattara rayuwar ya ajiyeta, me zai yi a cikin duniyar nan? Baba ya juya mishi baya, zanenshi ya tafi, Asiya daya gina rayuwa da ita ta juya mishi baya, Bello amininshi, sannan Salim dake rage mishi radadi an rabasu to me yayi saura?
😪 Wannan lamari
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* "DA* *AYUSHER MUHD*
*PAID BOOK*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN*
*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O'O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?" *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯
08142800199 07068558096
{20} Dada a garin Mariri take wanda ɗan gefe ne kaɗan da cikin garin Kano, tana zaune a waje tana tsince ragowar shinkafar da take dashi zata ɗan dafa, mace ce mai yawan kyauta wacce duk sanda kaje gidanta zaka taddata bata rabuwa da yan matan dake shigowa suna tayata aiki tana basu dan wani abin, hakan yasa kayan abincinta basa daɗewa, sai dai bata kuma rasa kayan abinci, yayyen Umma maza suna ƙoƙarin haɗa mata kayan abinci bakin gwargwado yadda zai isheta, tunda ta fahimci matan su ba so suke su zauna da ita ba shi yasa tace su barta a gidanta, to da yake suma duk maza ne Umma ce kawai mace sai suka ɗauka kayan abincin kawai da suke bata ya isheta, gashi dama dukkansu babu wanda yayi aure a Kano. Kamar daga sama ta jiyo muryar Hadiza hakan yasa ta miƙe a hankali tana cewa "Yau kuma Dijangala ce a gidan namu?" A tsaye ta ganta da gudu Hadiza ta taho ta rungumeta, bayanta ta shiga shafawa tace "Meya faru? Ko mijin naki ne har yanzu abun bai daidaita ba?" Ta girgiza kai tana share kwalla tace "Dada ya zamu yi?" Da mamaki take kallonta tace "Name kenan?" Ta ƙarasa maganar tana leƙa waje kaɗan, a cikin mota ta hango Baqeer a zaune yana kallon ƙofar gidan, tace "Da Baqeer kuke tafe?" Kafin Hadiza ta samu damar ba ta amsa taga Maryam na buɗe keken guragu, da mamaki take kallonta sai dai haka kawai taji jikinta yayi sanyi, don Baqeer ba zai taɓa ganinta a tsaye ba tare da ya fito da sauri ya gaisheta ba, balle yadda ya kalleta kallo ne na wanda kamar baya cikin ma hayyacinshi, kallo ne na wanda damuwa da takaicin rayuwa suka ma yawa. Maryam tasa keken daf da gefen inda zai fito tare da buɗe ƙofa, bai ko tanka ba Hadiza da Maryam suka taimaka mishi ya hau kan keken, da sauri Dada tayi baya tana girgiza kai, wannan wace ƙaddara ce ta samesu haka? Kasa motsi tayi har suka ƙaraso dashi cikin gidan, Dada da sauri ta rungume Baqeer ta sa wani kukan tausayi wanda hakan ya ƙara saka Baqeer cikin wani kunci shi kenan kai daga an ganka sai kowa ya hau kuka? Wannan wace irin rayuwa yake ciki? Hannu yasa ya toshe kunnenshi kawai ya fara sakin wani irin kara wanda yasa hankalinsu duka ya tashi, da sauri Dada ta sake riƙeshi tace "Baqeer menene haka? Meya sameka wai?" Jikinshi ne kawai yake rawa yana sake toshe kunnuwanshi, ganin haka yasa tace akai shi ɗaki, suna hawaye haka Maryam ta tura keken zuwa ɗakin suka fito cike da tausayi, a nan tsakar gida suka zauna a tabarma suka sanar da Dada duk abinda ke faruwa, hankalinta yayi mugun tashi sai dai takaicin Badaru yafi komai damunta, sam dama kowa yasan rashin mutunci da wulakancinshi amma bata taɓa tunanin zai yiwa Baqeer haka ba. Tace su barshi anan ita batada matsalar mai gyara mata gida don yaran layin har rububin zuwa gyara mata gida suke yi. Maryam ta buɗe jakarta ta ciro dubu biyun da mai gidanta ya bata tayi cefane ta miƙawa Dada tace "gashi ku sayi wasu abubuwan kafin muga yadda hali zai yi." Nan ta amsa suka fito bayan sun mata sallama don tace kada su leƙa ɗakin Baqeer don da alama hankalinshi tashi yake yi in yaga an damu da halin da yake ciki.
***** Maryam a gidan Hadiza ta ajiyeta sannan ta wuce ta makarantarsu Aareef ta ɗaukeshu, ta san tayi lattin zuwa ɗaukarshi shi yasa take ta sauri, tana isa makarantar aka sanar da ita ai mahaifinshi ya ɗaukeshi, ajiyar zuciya tayi sannan ta fito daga ciki ta shiga mota ta koma gida fuskarta sam babu walwala don tasan tabbas yau akwai ɓacin rai, tana shiga ta hango surukinta a zaune a harabar gidan yana karanta jarida, parking tayi sannan ta ƙaraso ta gaisheshi da gida tana cewa "Baffa shan iska kake yi ne?" Kallonta yayi yace "Kin dawo?" Ta miƙe tana cewa "Abban Areef fa? Naga banga motarshi ba." "To ke da mijinki ni ina zan san inda yake?" Yayi maganar tare da cigaba da karatunshi, miƙewa tayi ta koma ciki, a kitchen ta tsaya ta sauke ajiyar zuciya tana tunanin yadda zata yi girki ba nama tunda dai kuɗin ta ɗauka ta bawa Dada, da sauri ta fara dafa shinkafa da wake, ta yanka kayan miyan da take dashi ta ɗauko kifin gwangwani na mackerels tasa tana yi tana addu'ar Allah yasa kada yayi maganar nama. Daga waje ta jiyo ƙarar buɗe gate ta gyara da sauri tare da ɗan jingina da kofar kitchen tana murmushi, Areef ne ya shigo da gudu ya rungumeta yace "Ummy yau ina kika je baki zo da wuri kin ɗaukeni ba?" Ta shafi kanshi tace "Ka manta Uncle ba lafiya? Naje na dubashi ne, a ina kuka tsaya naga baku dawo da wuri ba?" Kafin yayi magana mahaifinshi ya shigo tana murmushi tace "Gwaskana sannu da dawowa." Babu alamun zai tanka ta a fuskarshi kawai ɗaki ya wuce, bin bayanshi tayi tana tsokanarshi "Yau ka tashi da wuri nayi mamaki da akace ka ɗauki Areef daga school." "Don me na saya miki mota?" Kalmar da taji ya faɗa kenan, jikinta ne yayi sanyi tace "Kai Areef makaranta da ɗauko shi." "To akan me baza ayi abinda aka siya domin ta ba? Yanzu da Baffa bai kirani ya sanar dani kin fita ba da bazan taɓa tunanin ɗauko yarona daga makaranta ba, tunda dai ke wayarki bata shiga, sam ni na kasa gane wannan halin naki." Zata yi magana taga ya shige toilet, kitchen ta dawo idanunta na neman cikowa da ƙwalla, babu shakka tasan tayi laifi da bata sanar dashi ba amma ya zata yi? Yanayin data shiga ne ya hanata ga wayarta ba charge.
******
Tunda su Daddy suka shigo da abokansa tana ɗaki a kwance, tanaji su Nabeela nata zaryar kai kayan abinci da tarar baki, kamar daga sama taji muryar Kabir yana kwalla mata ƙira daga bakin ƙofar ɗakin, taba daga kwance tace "Menene?" "Dalla malama ki taso Dady yace kizo ku gaisa da bakin." Baki ta turo sannan ta zura abaya a saman vest da short ɗin dake jikinta, Mumy ce ta ganta ta saki murmushi tace "Saki ranki mana auta." Kabir ne ya cukume fuska yace "Karma ta saki ran ni ba sai na farfasawa mutum baki ba." "Bro please chill kai meyasa kake abu kamar gangster?" Ai kamar ta taboshi ya fusata yace "What? Wallahi yau sai na karya yarinyar nan." Kai ta girgiza irin na takaicin halayensa ɗin nan, wannan abu ya tunzurashi sosai sai dai ba yanda zaiyi ya wuce ciki rai a ɓace. Zeey shiga tai ta tsuguna ta gaishesu, bata wani kallesu ba dan ba kasafai take san kallan mutanen da bata sani ba. Kamar daga sama taji wani yace "Ai wannan haɗin yayi daidai kaga ita dama bata saba da nan ba shima haka sai su saba tare." Dady yai dariya yace "Sosai! Na tabbatar hallayarsu zata zo ɗaya in har ya dawo." Wani ne yace "Wani satin ne ai insha Allahu." Itadai kanta na ƙasa ta kuma tabbatar abinda take zargi shi suke yi, Dady ne ya sake cewa "Wai Zainab baki ganeshi ba? Mahaifin Junaid ne fa." Taɗan saki fuska kaɗan tana sake gaisheshi ya amsa yana cewa "Kuna waya kuwa?" Kai ta girgiza tace "Mun kwana biyu wlh tunda na zama busy shima haka muka daina." "Masha Allah." Mikewa tai dan zaman ya isheta, kalaman mahaifin Baqeer duk sun hanata sukuni, burinta kawai taji yanda ake ciki dashi, ba yanda zatai ta fita yanzu dole sai dai gobe, haka ko falo bata fito ba takaicin halin data shiga duk ya isheta, wai akan me ta damu da Baqeer? Kamar ta manta wani Baqeer ɗin ne? Wanda ko hanya ta taho ya taho ta gwammace ta koma? Duvets ɗin data luluɓa dashi taja ta rufe kanta tana ɗan bubuga ƙafa cikin takaici.