Baqeer complete - Chapter 15
Baqeer complete Chapter 15: Baqeer complete Chapter 15. Yana fita suka yi kaciɓis da makwabcin shi Mallam Nuhu, ɗauke kai yayi ya wuce kamar bai ganshi ba.…
2,885 words
Yana fita suka yi kaciɓis da makwabcin shi Mallam Nuhu, ɗauke kai yayi ya wuce kamar bai ganshi ba. Yana ƙoƙarin saka makulli ya buɗe motar yaji muryarshi daga bayan shi yana cewa "Mallam Badaru barka da asuba, an tashi lafiya?" Juyowa yayi irin kamar sai yanzu ya ganshi ya bashi hannu suka gaisa. "Kwana biyu bamu gaisa ba, ina taso na leƙo ma nayi maka jaje ashe tsautsayin da ya afkawa Baqeer kenan ban samu dama ba, wallahi Mallam Badaru sam bani da labari sai shekaranjiyan nan dana hange shi ana tura shi a keken guragu ake ce mini ai mota ce ta buge shi sanadin hakan har ya rasa ƙafafu gashi hannun nashi ma ya karye don haka ko gasar masu zane da zai je bai samu zuwa ba sai abokin shi ne ɗan wajen Alhaji Bala yaje a madadin shi. Allah ya kiyaye gaba ya mayar kaffara".
Tunda Mallam Nuhu ya fara magana Baba ya ƙara ɗaure fuskar nan tamau kamar bai taɓa dariya ba yana jifanshi da wani irin kallon wulaƙanci. Tsaki yaja yace "Ai sai ka kauce ka bani wuri tunda dai ka gama abinda ya kawo ka, in banda gulma da tsugudidi da can baka san Baqeer ɗin yayi hatsari ba sai yanzu zaka tareni da wasu zancen banza?" Ya buɗe motarshi ya shige ya jata a guje ya bar wurin yana baɗe Mallam Nuhu da ya bishi da kallon mamaki da ƙura, abun arziƙi ya taɓa zama na tsiya ne dama?
Har ya ƙarasa kasuwa zuciyarshi baƙi ƙirin yake jinta, ya rasa inda zai saka kanshi yaji daɗi, duk ya tuna wai Bello yaron da jajircewar Baqeer a kanshi ce tasa ya ƙware a harkar zane ne wanda ya tafi a madadin Baqeer har ma ya karɓo award sai yaji kamar ya kwanta a ƙasa yayi ta burgima ko ya samu yaji sauƙin raɗaɗin da yake ji a cikin zuciyar tashi, gashi mutane da gulma da kinibibi yayi wa yawa sai faman tararshi suke yi suna tambayar ba'asin yadda aka yi Baqeer bai tafi gasar ba sai dai abokin shi ne yaje a madadin shi, har rasa amsar bayarwa yake yi don ashe wai duk ɓoye-ɓoyenshi na kada asan halin da suke ciki da Baqeer ɗin mutane sun sani, har wani gugar zana ake yi mishi ana cewa yaron daya fifita fiye da sauran ƴaƴan shi gashi kuma inda rayuwa ta kaisu bai zama abinda yake kuri da cika bakin zai zama ba a harkar zane.
Yaran shagon shi kansu sun san yau zuciyarshi a wuya take, ɗan kuskure ƙalilan zasu yi sai dai ya rufe su da faɗa don haka suke takatsantsan dashi don sun daɗe da sanin halinshi dama shi yasa suke haƙuri da tijarar shi idan ya fara sai dai suyi ta bashi haƙuri. Yana zaune a cikin shagon shi inda yake sayar da kayayyakin sawar mata kama daga su atamfa, leshi, shadda, material da voiles yana kallon shige da ficen mutane masu shigowa yin sayyaya ɗaya daga cikin yaran shagon yazo ya russuna yace mishi yayi baƙo. Ɗan tsaki yaja irin na an takura shi ɗinnan ya cewa yaron ya cewa baƙon ya shigo daga ciki. Ƙara tsuke fuska yayi ganin mahaifin Bello Alhaji Bala ya shigo da fara'arshi. Hannu ya miƙa mishi haɗe da yi mishi sallama sai dai da ƙyar ya buɗe baki ya amsa sallamar ba tare daya bashi hannu sun gaisa ba. Sai ajiye hannunshi Alhaji Bala yayi ganin Mallam Badarun baya da niyyar mayar mishi. Bai fasa abinda ya kawo shi ba duk kuwa da yaga irin karɓar da yayi mishi. Da farko tambayarshi ya fara yi yanayin jikin Baqeer sai dai Mallam Badaru yayi kicin-kicin da fuska yaƙi amsa mishi don haka ya bar wannan maganar ganin kamar baya sonta ya fito da envelope daga aljihun shi ya miƙa mishi yana cewa "Dama zuwa nayi mu gaisa na kuma kawo maka ɗan wani abu daga abinda Bello ya samo a wajen gasar da yaje ganin komai ya zama Baqeer ne sila nace ai ba'a yi tuya a manta da albasa ba tunda ma banda Allah ya aikowa da Baqeer wannan tsautsayin kujerar ai tashi ce to kana naka ne Allah yana nashi ta Allah kuma ita ce daidai, dama can Allah ya nufa Bello ne mai zuwa wannan wurin shi yasa nace bari na kawo maka wannan kasa albarka, shi kuma Baqeer Allah ya bashi lafiya ya tashi kafaɗunshi ya bashi ikon cinye jarrabawar da yayi mishi." Da ace Alhaji Bala ya lura da yadda maganarshi ta fusata Mallam Badaru yana ƙara hawa kamar farashin mai a Najeriya da tuni yayi shiru sai dai da yake shi da zuciya ɗaya da kuma kyakkyawar manufa yazo wurin shi yasa bai lura da yadda yanayin shi ya canja ba har sai da ya daka mishi tsawa yace "Dallah Mallam yi mini shiru munafukin banza munafukin wofi, har ni zaka kawowa munafurci kazo da wani kuturun wulaƙanci kana ce mini haka Allah yayi ba Baqeer bane mai zuwa wajen gasa Bello ne? Ni dama na daɗe da sanin abotar Baqeer da ɗanka babu inda zata kai shi sai a ajin dana sani, shine bai sani ba har ya janyo Bello a jikinshi ya nuna mishi yadda ake zane ya baje mishi dukkanin wasu sirrikan samun nasararshi gashi nan yanzu yayi mishi halin ƴan adam ya munafurce shi ya tafi wajen gasar a madadin shi bayan yasan Baqeer baya da wani buri a rayuwa face zuwa wannan wuri, da Allah tattara gayyar tsiyarka ka fice mini daga shago idan ba haka ba nasa yara suyi maka dukan mutuwa wallahi."
Baki buɗe Alhaji Bala ke kallonshi yace "Dama abun arziƙi ya taɓa zama na tsiya? Daga zuwa nayi maka alheri ganin komai Bello ya zama ɗanka ne sanadi shine zaka bini da baƙaƙen maganganu kana nema ka zageni?"
A harzuƙe ya tashi tsaye shima yana nuna shi da ɗan yatsa yace "An zageka ɗin, nace maka an zageka ɗin, kai ɗin har wata tsiya ce da ba za'a zageka ba, munafukai masu saka alheri da sharri, duk alherin da Baqeer yayi wa Bello bai yi mishi baƙin ciki ba ya nuna mishi kan sana'ar shi amma ya rasa da abun da zai saka mishi sai wannan?" Haka dai suka yi ta cacar baki da ƙyar aka samu aka fitar da mahaifin Bello daga shagon don sosai ranshi ya ɓaci da tijarar da Mallam Badaru yayi mishi daga abun arziƙi. Har ya bar kasuwar zuciyarshi nayi mishi zafi, dama takaicin maƙwabcin shi daya tare shi da gulma wai yanayi mishi jaje sai kace ance mishi yana buƙatar jajenshi, a yanzu shi abu ɗaya ne zai wanke mishi zuciya yaga Baqeer ya dawo daidai ya koma harkokinshi kamar da.
***** Tunda ta kwanta sai faman juye-juye take yi akan makaɗeɗen gadonta da yaji shimfiɗa ta alfarma. Koda wasa ta kasa runtsawa data rufe idanunta shi kawai take gani yana yi mata gizo, ta kasa yardar wa ranta cewa wai wannan gurgun da take yawan gani ana tura shi a wheel chair Baqeer ne wanda ta sani tun suna yara, yayan ƙawarta Maryam mai yawan tsokanarta yana sakata kuka har ya janyo ta daina shiga gidansu saboda yawan tsokanarta da yake yi. Juye-juye kawai take yi tana saƙa da warwara maganar na cinta a rai ta kasa furtawa kowa ko don bata saba barin abu a ranta ba yasa wannan ɗin ta dameta ganin ta kasa faɗawa kowa yadda ganin Baqeer ɗin a keken guragu ya ɗaga hankalinta.
Yaye duvet ɗin data lulluɓe rabin jikinta tayi ta sauko daga kan gadon a nutse ta saka bedroom slippers ta fita zuwa ɗakin Nabila dake daura da nata. Cikin sanɗa ta tura ƙofar ɗakin ta zura kanta a hankali, switch ɗin fitila ta danna haske ya gauraye ɗakin. A naɗe akan gado taga Nabila tana bacci hankalinta kwance alamun babu abinda yake damunta, ƙarasawa tayi gaban gadon tasa hannu zata yaye duvet ɗin data rufe ilahirin jikinta dashi sai kuma ta fasa, yanzu idan ta tasheta tace me ya hanata bacci, ita dai tasan ko kusa ba zata iya fitowa tace mata ga abinda yake damunta har ya hana mata bacci ba don haka ta juya ta kashe mata fitilar ta bar ɗakin. Ɗakinta ta koma ta hau kan gado ta kwanta sai dai cikin ranta ta ƙudurce gobe zata koma gidansu ko don ta ƙara tabbatarwa da kanta cewa Baqeer ne dai data sani wannan gurgun.
Da ƙyar ta samu bacci ya ɗauketa koda ta tashi sai ta tashi da ciwon kai saboda rashin samun isashen bacci da bata yi ba. Haka ta fio idanunta a kumbure, Mummy na ganinta ta tashi ta tarota cikin tsantsar kulawa take cewa "Kinga yadda fuskarki ta kumbura kuwa Zeey? Ba dai wani abu ne ya sameki ba ko? Dan tun jiya na kasa gane kanki." Tana yi tana taɓa jikinta sai dai babu alamun zazzaɓi don haka ta ɗan kwantar da hankalinta sai dai Zeey ɗin nace mata headache ne take fama dashi ta ƙara rikicewa har sai da Nabila tayi magana tace "Haba Sis, headache ɗin ne zai ruɗar dake kamar baki san Zeey da raba dare tana kallo ba, yanzu haka kwana tayi tana kallo bata kwanta da wuri ba shi yasa kanta yake ciwo amma daga taci abinci ta sha magani zai warware."
Kallonta Mummyn tayi tace "Wai haka ne My Zeey?" Ɗaga mata kai kawai tayi don yau sam bata jin son yin magana, zama tayi akan kujerar dining table. Da kanta Mummy ta taso ta haɗa mata tea sannan ta ɗauki plate ta haɗa mata breakfast duk ta tura a gabanta tana cewa "daure kici kin ji baby sai ki sha magani kije ki kwanta ki huta". Da kai ta amsa mata sannan ta fara cakalar abincin kamar mai cin maɗaci, haka dai ta caccakala ta tashi ta koma ɗakinta bayan ta sha paracetamol tayi wanka sannan ta hau gado ta kwanta.
La'asar nayi ta tashi ta shirya cikin wata free English gown beige color sai ta yafa farin jersey veil a kanta, bata yi wata kwalliya ba sai perfume da ta fesa. Ɗakin Mummy ta shiga tace mata "Mummy don Allah zan ɗan fita yanzu zan dawo ba zan daɗe ba". Kallonta Mummy tayi tace "har kan naki ya daina ciwo da zaki fita? Wai shin ina ma kike yawan zuwa kwanannan da kullum sai kin ƙirƙiri fita bayan kin sani sarai Daddynki ba son yawan fitarki yake yi ba".
"Kiyi haƙuri Mummy wallahi ba zan daɗe ba yanzu zan dawo."
"Ni dai don Allah kada ki daɗe bana so Daddynku ya dawo bai sameki ba".
"Thank you Mum" tace haɗe da hugging ɗinta, fita tayi tana ɗokantuwa da son sake saka Baqeer a idanunta.
Zuciyarta sam ta kasa nutsuwa, wai Baqeer dai Baqeer?
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar ce* *Da* *Ayusher Muhd*
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*PAID BOOK*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA TARA*
*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O'O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?" *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯
08142800199 07068558096
{19} Tana shiga soron gidan ta ganshi daga bakin ƙofa ya ƙurawa ƙofar shigowa gidan ido sai dai idan ka lura sosai zaka gane hankalinshi ba'a wajen yake ba yayi nisa sosai wajen tafiya duniyar tunani. Tsayawa tayi tana kallonshi ta ƙara tabbatarwa da kanta lallai fa shine dai Baqeer ɗin data sani ba wani daban ba, kafin taja jiki ta shige cikin gidan tana jin wani irin tausayin shi yana ratsa ta. A tsakar gidan ta tsaya tana sallama, Umma da ɗakinta ke a kusa da ƙofar shigowa ta fito tana amsa sallamar. Ganinta a tsaye yasa ta washe baki tana cewa "Ah ah Zainab kece? Lale lale sannu da zuwa, shigo daga ciki." Bin bayanta tayi itama tana murmushin, kujera ta nuna mata ta zauna ita kuma ta koma bakin gado. Ɗan russunawa Zeey tayi ta gaisheta, da fara'arta ta amsa mata tace "Jiya kuma sai kika tafi ba tare da kin jirani ba, har waje na leƙa ban ganki ba."
Sai ta samu kanta da jin kunyar Umman kada tayi tunanin ko guduwa tayi saboda ganin halin da Baqeer ɗin yake ciki. Kanta a ƙasa tace "Kiyi haƙuri Umma wai fa zuwa nayi na gaisheki na kuma ƙarbi number wayar Maryam ranar mun haɗu har muka rabu kuma ban samu na ƙarba ba, sai dai ruɗewar da nayi da yadda naga Yaya Baqeer ya koma yasa na fice ba tare da ko sallama na tsaya yi miki ba." Ta ɗan ja numfashi kaɗan tana murza tafin hannunta a saman cinyarta, kafin ta cigaba "Umma ni kam meya faru dashi haka na ganshi a wani hali daban saɓanin yadda na sanshi ada?"Hawaye ne ya sulmiyo daga idanunta tasa gefen rigarta ta share. "Kin dai ga yadda Allah ya mayar da Baqeer, ƙaddara ce ta afko mishi wacce bawa bai isa ya kauce mata ba tunda haka Allah ya hukunta, wani ne ya kaɗeshi da mota sanadin hakan ya rasa ƙafafunshi likitocin sun ce sun tashi daga aiki baza su ƙara moruwa ba," ta ƙarashe maganar kukan da take riƙewa a cikin ranta na ƙwace mata, damuwar data yini a ciki ce ta taso mata lokaci guda har ta kasa riƙe kanta a gaban Zainab ɗin.
Duk sai Zainab taji babu daɗi ganin yadda Umman ke kuka kashirɓan gaba ɗaya tausayinta ya lulluɓeta, tashi tayi ta koma kusa da ita ta zauna ta kamo hannayenta ta riƙe cikin tausasa murya tace "kiyi haƙuri Umma, ƙaddararshi ce tazo a hakan kamar yadda kika ce kuma bawa bai isa ya kauce mata ba, Allah ya sauƙaƙa mishi ya bashi ikon cinye jarrabawar da yayi mishi".
Da ƙyar ta iya tsayar da kukan tana jin kunyar yadda ta tasa yarinya a gaba tana yi mata kuka sai dai kuma damuwar dake danƙare a cikin ranta ce ta taso mata lokaci guda tafi ƙarfinta, a halin da ake ciki yanzu bata san ya zata yi ta kai Baqeer asibiti ba gashi ita bata ajiye ba bata bawa wani ajiya ba bare ta samu abinda zata yi hidimar kula dashi, dama shine ya ɗauke mata dukkanin wasu buƙatunta to ga kuma ajin da rayuwa ta kai shi shima a yanzu neman mai taimaka mishi yake yi. Sun jima shiru babu wanda ya ƙara magana sai zuwa can Zainab tace "Umma zan tafi Mummy tace kada na daɗe". "To Zainab nagode kin ji, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci."
"Ameen Umma" tace tana nufar ƙofar ɗakin sai kuma Umma tace "Yau ma zaki tafi baki karɓi lambar Maryam ɗin ba?" Juyowa tayi tana dariya tace "Wallahi na sha'afa bayan kuma abinda ya fito dani kenan." Dariya itama Umman tayi ta ɗauko wayarta ta lalubo number Maryam sannan ta miƙa mata wayar ta kwafa. A daidai wannan lokacin Mallam Badaru daya kasa zaman kasuwa saboda ɓacin rai ya shigo yana ƙwalawa Umma kiran da duk wanda yaji yasan bana lafiya bane. A take jikinta ya hau ɓari ta fita daga ɗakin jiki na rawa har zanin jikinta yana kuncewa tsabar ruɗewar da tayi. Tana fita tsakar gidan taga ya janyo Baqeer ya dangwarar da keken nashi a tsakar gidan, komawa yayi ɗakin yana watsi da duk wani kaya da yasan na Baqeer ɗin ne. Sai daya gama fitowa dasu tas sannan ya fito, nunata ya hau yi da ɗan yatsa yana cewa "Wallahi na gaji, na gaji da zaman nakasashen ɗan nan naki a gidana, na gaji da zunɗena da nunani da mutane suke yi duk lokacin dana fita waje ana yi mini dariya saboda kawai naso ɗanki na fifita shi a cikin ƴaƴa gashi yanzu da abinda yazo ya saka mini, duk wani ƙoƙarina na ganin ci gabanshi a rayuwa ya tashi a banza, to bazan iya ba gashi nan ki fitar mini shi daga gidana don na tsani na buɗe ido na ganshi, yaje can yayi rayuwarshi inda bazan dinga ganinshi ba bare ya saka mini cutar hawan jini."