Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 14

Baqeer complete - Chapter 14

Baqeer complete Chapter 14: Baqeer complete Chapter 14. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

3,324 words

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

#Baqeer #Shalele #Zeey # RayuwadaKaddara #Hawayena #UMMASGHAR #AYUSHERMUHD

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*PAID BOOK*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI*

*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O'O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?" *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

08142800199 07068558096

{17} Taku biyu tayi baya, tsabar rudanin data shiga yasa ta fice daga cikin gidan a gaggauce ba tare data tsaya jiran fitowar Umma ba, jikinta gaba ɗaya rawa yake yi ta rasa takamaimai abu ɗaya da zata kama. Haka nan dai taja jikinta da yayi wani irin sanyi ta ƙarasa wajen data ajiye motarta ta buɗe ta shiga ciki ta zauna, ta daɗe zaune a cikin motar da ƙyar ta iya saka makulli ta tashi motar ta bar wurin, har ta ƙarasa gida zuciyarta nata kai kawo akan abinda ta gani yanzun nan, kasa fita tayi daga cikin motar sai ma kifa kanta da tayi a jikin stearing wheel tana tunanin to me ya faru dashi haka? Ita dai tasan lafiyayyen mutum ne mai ji da ƙarfi to garin yaya ya zama gurgun da sai an turashi akan wheel chair? Kai Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, abun duniya ya dameta duk ƙoƙarin da take yi na kawar da tunanin shi daga ranta ganin tun da can babu wani shiri a tsakaninsu bare damuwar halin da yake ciki ta dameta ta kasa sai ma ƙara kutse da tunaninshi yake yi cikin zuciyarta.

Tsaki tayi cikin ranta tana cewa "to wai ni miye ma damuwata ne da daga ganin mutum zan bi na rasa sukuni?" Tunanin hakan yasa ta ficewa daga cikin motar ta shiga gida sai dai duk da hakan ta kasa yakice ganin da ta yiwa Baqeer akan keken guragu a zaune daga ranta. Da murna Mummy ta tareta ganin yau ɗaya dai Zeey taji maganarta ta dawo gida da wuri don tun fitarta take zullumin kada Daddy ya dawo bai tarar da ita ba bayan ya hanata fita ko ina, tasan da ba ƙaramin ɓacin rai hakan zai janyo mata ba sai kuma ta taimaketa ta dawo kafin Daddyn. Akan doguwar kujera ta zube ta kwanta ba tare da ko takalman ƙafarta ta cire ba, kallon tsaf Mummy tayi mata ta lura kamar da akwai abinda ke damunta sai dai ba tayi magana ba sai ma tayin abinci da tayi mata ganin har ta fita bata yi lunch ba.

Ga mamakinta ko musu Zainab bata yi mata ba ta tashi ta nufi wajen da suke cin abincin taja kujera ta zauna, Mummyn ce tayi serving ɗinta don dama ita ta sabar mata da komai take so sai anyi mata gashi yanzu har girmanta bata iya tsinanawa kanta komai. Juya cokali kawai take yi a cikin abincin ta kasa kai ko loma ɗaya bakinta, haka nan sai ganin abinda ya faru tsakaninshi da buduwarshi take yi da kuma lokacin da wannan marar kan gadon ya ajiye shi akan titi. Wane irin canji ne ya samu rayuwarshi haka a ɗan taƙaitaccen lokacin data ɗauka bata sanya shi a ido ba? Tunanikan sun kasa barin zuciyarta har ma ta kasa cin abincin duk kuwa da tarin yunwar da take ji tun ma kafin ta fita ta bar gidan, tashi kawai tayi ta bar abincin ba tare da ko ɗanɗanawa tayi ba.

Kallonta Mummy tayi ta kalli plate ɗin da yake cike taf da abinci yadda ta zuba haka Zeey ta bar mata shi. "Meke damunki ne Zeey? Tun dawowarki na lura kamar akwai abinda ke damunki, ba dai wani mummuna abu aka yi miki a inda kika je ba ko?" Kallon Mummyn tayi ta girgiza kai alamun babu komai sai kuma tace "Babu komai Mummy kawai dai na gaji ne."

"Allah ya kyauta," kawai Mummy tace ba don ta yarda da amsar da Zeey ɗin ta bata ba sai don bata fiye son matsanta mata ba amma a yadda take da surutu da rawar kai tasan tabbas akwai abinda take ɓoye mata don haka nan Zeey bata iya shiru in dai har tana wuri to sai ta addabi kowa da karaɗinta. Juyawa tayi zata bar wurin ta koma ɗakinta Daddy ya shigo, yana ganinta kuwa ya fara faɗa ko sannu da zuwan da take yi mishi bai amsa ba.

"Wato Zainab har abada ke ba za'a faɗa miki magana ki ji ba ko, shine don ki nuna ban isa dake ba kika sake wulaƙanta yaron nan Najib bayan cewa da nayi ki bashi haƙuri?" Faɗa kawai yake yi irin wanda bai taɓa sakata a gaba yayi mata ba sai dai ko kusa hankalinta baya wajenshi bare ta tanka mishi irin yadda a mafi yawan lokuta take yi idan yana yi mata faɗa tana ƙoƙarin defending kanta, a yau zuciyarta tayi nisan kiwo ba saurarenshi take yi ba, tunaninta na wajen Baqeer da alhinin abinda ya sameshi, to wai ma shin yaushe ne yaji ciwon da ya nakastashi haka?

Mummy ce tace "Zainab" da ɗan ƙarfi lura da tayi sam hankalinta baya wajen, sai cewa tayi "Eh naji" kawai alhalin bata ma san maganar da ake yi ba. A halinta na rashin barin abinda ke cikinta sai ta samu kanta da kasa furtawa kowa damuwar halin da taga Baqeer ɗin, tana mamakin wai dama wannan gurgun da take yawan gani a mabanbanta lokuta Baqeer ne.

*****

Mamaki ne ya kama Umma data fito bata ga Zainab ba, leƙawa tayi ƙofar gida ko zata ganta sai dai ko alamunta bata gani ba, haka ta juyo tana cewa "Kenan tafiya tayi?" Komawa tayi ta kama aikin taliyar da maƙwabtansu suka kawo mata, tana yi tana share ƙwallar tausayin Baqeer. Wai kenan haka zasu cigaba da rayuwa baya da mataimaki? Salim ɗin da suka dogara a kanshi Mallam yayi sanadin da yayi fushi ya daina zuwa alhalin shi ba tausaya mishi zai yi ba bare ya tallafe shi. Dole ta tashi tsaye ta kama sana'a ta yadda zata samu ta ɗaukar wa Baqeer mataimaki ko almajiri ne da zai ke taimaka mishi tana biyanshi. Ta gama aikin taliyar ta shanya akan igiyar data ɗaura a kusa da ɗakinta, tattare wajen da tayi aikin ta hau yi tana kawar da kayayyakin data ɓata.

Abu dake zaune a ƙofar ɗakinta tana zuzzuba garin dakan da take sayarwa a ƙananun robobi ta kalleta ta taɓe baki kafin ta saki shewa tace "Ahayye nanaye, duniya rawar ƴan mata na gaba ya koma baya, yau ga uwar shalele, mowa a cikin ƴaƴa na sana'ar hannu, ai na ɗauka neman kuɗi sai mu irin ku sun girmi sana'a sai dai ƴaƴan ku su fita su nemo su kawo muku kuna daga kwance, ashe dai duk abun bogi ne," ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya har da kama hanci ta saki guɗa. Har Jamila dake aikin abincin rana na tayata tace "Yo ba dole ta tashi ta nema ba tunda mai kawowar ya zama gurgu, zaman gida kuma ya aureshi? Kin manta sanda ɗan kanzagi ya ɗauke injin taliyarta ya ajiye wai ta huta?" Dariya suka sheke dashi duka su biyun wannan abu na basu dariya. Ran nan na Abu fari ƙal da farin ciki don a yanzu ji take yi tamkar tafi kowa, ƙiris ya rage gida ya dawo hannunta tunda ma gashi ta fara samun Mallam a hannu. A wulaƙance ta kalli Umma da ko ɗaga kai bata yi ta kallesu ba duk kuwa da yadda zuciyarta ke tafarfasa da wannan cin kashin da suke yi mata tace "Dama sakin wannan aikin taliyar kika yi kika tura shi bakin titi kuka yi bara sai kiga kun samo kuɗi fiye ma da abinda yake samu a harkar zanen don yanzu almajirai ai sune da kuɗi tunda su kullum cikin karɓa suke basu san su bayar ba." Sai wannan lokacin Umma ta kalleta har zata yi magana sai kuma ta fasa ta shige ɗakinta ta barsu anan suna cigaba da sakin baƙaƙen maganganu duk dai akan fifikon da Baba ya dinga nunawa Baqeer akan ƴaƴan su. Zama tayi a bakin gado tana kukan tausayin kansu daga ita har Baqeer ɗin ganin yadda aka mayar da larurarshi abun gori har ana cewa ta turashi su fita bara kamar shi ya ɗorawa kan shi.

Yana daga ɗakinsu yana jiyo duk abinda ke faruwa a cikin gidan da duk gore-goren da suke yiwa Umman. Wani irin ƙunci da baƙin ciki yake ji a cikin ranshi, yadda kowa ya juya mishi baya nayi mishi ciwo. Kallon ƙafafun shi yayi da ko kaɗan baya jin alamun su a jikin shi, ya kalli hannunshi dake naɗe a cikin bandage yace "Shikenan yanzu ni a haka zan yi ta zama ba zan morawa kaina komai ba?" Ƙoƙarin motsa ƙafafun yayi tayi yaga ko zai iya tashi ya kasa, haka nan ya haƙura ya buɗe drawer dake ajiye a gefen katifarshi ya ciro takarda da pencil ya hau ƙoƙarin yin zane sai dai hannunshi baya da ƙwarin da zai iya riƙe pencil dole ya haƙura yayi watsi da kayan a tsakar ɗakin yana sakin huci kamar wanda yayi tseren gudu. Gabaki ɗaya rayuwar bata yi mishi daɗi ji yake yi ina ma ya mutu ya huta, duk ya juya ya kalli ƙafafun shi naɗe a waje ɗaya basa iya ko motsi ya ɗaga hannunshi ya ganshi a naɗe a cikin bandage sai yaji to shi miye amfaninshi ma tunda ba zai iya amfanar kanshi da komai ba. Ƙarfin imani ne kawai ke hanashi ɗaukar mummunar shawarar da zuciyarshi take kitsa mishi don wasu lokutan sai yaji kamar ya datse rayuwarshi ya huta gaba ɗaya da waɗannan matsaltsalun da suka dabaibaye rayuwarshi.

***** Kamalu kuwa yana fita ya burga babur ɗin shi yabi kwatance tiryan-tiryan kamar yadda aka yi mishi sai gashi a ƙofar gidan su Zeey. Kallon ƙatuwar katangar gidan yayi yana jin wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarshi, yau dai gashi a ƙofar gidansu Roshni ɗin shi fatanshi dai tayi na'am dashi ta amshi tayin soyayyar shi, kallon rigarshi yayi yana ƙara kakkaɗeta yana tabbatar da shigarshi tayi ko gaban gwamna zai iya zuwa a haka. Sauka yayi ya ajiye babur ɗin a gefe ya ƙarasa gaban gate ɗin gidan yasa hannu ya ƙwanƙwasa. Daga ciki mai gadi ya taso ya buɗe ƙaramar ƙofar gate ɗin ya leƙo da kanshi waje.

"Sannu dai" Kamalu yace yana ɗaga mishi hannu. "Yauwa sannu" maigadin yace bayan ya fito waje ya janyo ƙofar ya rufe yana ƙarewa Kamalun kallo. "Lafiya dai ko? Wa kake nema?" Wani kallo Kamalu ya jefa mishi irin na kada ka raina mini wayo kafin cikin maganarshi irinta gagararrun ƴaƴa yace "ka gane ba wato akwai Roshini ɗita wata ƴar black beauty nan haka tana jan wata jar Honda Accord ance nan ne gidansu, da Allah ita zaka yiwa magana kace mata Kamel ne yake sallama" yana yi yana gyara zaman rigarshi irin a dole shi ga gayu ɗinnan. Wani irin kallon banza maigadin ya watsa mishi yace "Kai kama kalli kanka a madubi kuwa kafin ka fito? Anan gidan ne kake da wata Rashida take ko wa? Don Allah ɓace mini da gani tun kafin kayi mini sanadin aikina, in banda sakarci ma irin naka ta yaya kamar kai guntun ƙwaya da wiwi zaka ce kazo wajen wata ƴa a cikin gidan nan, ni wallahi da farko na ɗauka wajen Alhaji kazo irin ƴan bangar siyasar nan ne ashe wai kai wajen Rashida kazo, to babu Rashida a gidan nan sai ka ƙara gaba ko zaka yi dace da samunta a wani wurin."Ya juya zai bar wurin Kamalu ya damƙo wuyanshi yana cewa "Kai kasan koni waye da har kake faɗa mini maganar banza? Kai matsiyaci ma maigadi har ka isa ka hanani ganin Roshni? Tun Roshnin bata fito ba har kana da bakin kore mata NI, to wallahi baka isa ba, ko ka shiga ciki ka kira mini ita ko nayi maka rotse a wajen nan." Ya hankaɗa shi jikin gate ɗin yana sakin huci. Shi kuwa maigadi yana jin an sake shi ya shaƙi iska ya kwasa a guje yayi cikin gidan ya datse ƙofar gate yana mayar da numfashin wahala don ba ƙaramar shaƙa yayi mishi ba. Leƙa gate ɗin Kamalu yayi ta tsakankani, motoci ya gani yace "Ai Roshni ina auranki wancan zan amsa don babu shakka ita ta dace dani." Ya sheƙe da dariya yana tuno wata ragwargwajajiyar motar Baba wanda ake faɗa akanta a gidansu, kafin yaja tsaki yace "Ni yanzu nafi karfin shiga Golf ɗin ku sai kuje can ku karata." Ya ɗan daka tsalle tare da sake kallon mai gadin yana ji kamar ya zabga mishi mari. Horn suka ji daga cikin gidan da sauri Mai Gadi ya nufi wurin shi kuma Kamalu ya maƙale a lungu yana leƙe, ganin an fito da ɗaya daga cikin motocin nan yasa yabi wanda ke cikin motar da kallo, namiji ne da bai fi sa'anshi ba, huci ya furzar yana jin ina ma shine a cikin motar nan? Ko da yake an kusa ai.

An kusa me Kamalu?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

#Baqeer #MBB #Zeey #Hawayen zuci #Kaddara #Kamalu KB #AYUSHERMUHD #UMMASGHAR

*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*PAID BOOK*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS*

*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O'O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?" *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

08142800199 07068558096

{18} Tun jiya da dare take dakon shigowar mai gidan nasu sai dai har lokacin barci yayi ta shiga ɗaki ta kwanta bata ji ɗuriyarshi ba, hakan yasa yau tun sassafe ta fito tsakar gidan ta zauna sanin halinshi ba wai ya kula da bin ɗakunan matanshi ya duba lafiyarsu idan gari ya waye ba, haka nan idan bada wani ƙwaƙƙwaran dalili ba baya taɓa shiga ɗakunan baccinsu sai dai su haɗu a tsakar gida idan kuma kece da girki ki iskeshi a ɗakinshi, ko wacce irin magana gareki sai dai ki faɗeta a tsakar gidan gaban kowa don bai yarda da bin bayanki don kuyi sirri ba, ita ce ma take da wannan alfarmar ada lokacin da ɗanta yake da mamora ba yanzu ba da ya gama yi mishi amfani yayi watsin ruwan tsarki da al'amarin da duk ya shafe su. Tana nan zaune Jamila ta fito ta hau kici-kicin ɗora abun karyawa.

"Ina kwana" tace mata ganin bata lura da zamanta a wajen ba. Waiwayowa tayi ta kalleta sai kuma ta taɓe baki tace "ke kuma lafiyarki kika fitowa mutane tsakar gida da duku-dukun safiya, ko kuwa dai wani sabon salon munafurcin ne kika ɓullo dashi". Bata tanka mata ba jin bata amsa gaisuwar da tayi mata ba sai ma wasu ƙananun magangnu data bita dasu. Jamila na aikinta tana sakin maganganu ita dai tana jan carbinta don tun zamanta dama abinda take yi kenan shi yasa ma zaman wajen bai gundureta ba. Har Jamila ta gama ɗumamen tuwo ta dama koko ta zubawa kowa nashi, sai sannan ta tashi ta ɗauke nata dana Baqeer ta kai ɗaki ta ajiye ta dawo ta cigaba da zama a ƙofar ɗakinta tana dakon fitowar Mallam ɗin.

Bai fito ba sai can da rana ta take ya fito da shirin shi na fita kasuwa. "Ina kwana Mallam" ta gaishe shi a ladabce cikin muryarta mai sanyi. Juyowa yayi ya kalleta ya watsa mata wani banzan kallo kafin ya juya yana miƙawa Jamila kuɗin cefanen su na ranar, ganin ya nufi hanyar fita yasa ta ɗan ɗaga murya tace "Mallam magana ce dani don Allah". A fusace ya juyo yace "sai aka yi yaya idan kina da magana? Ko kuwa saboda maganarki sai na fasa fita kasuwa, banda kinibibi da kutinguila sai da kika ga na gama shiri zan fita sannan zaki tsayar dani salon ki sakani makara, ko kuwa yau nake cikin gidan da baki samu lokacin magana ba sai da na fito zan fita".

"Kayi haƙuri" tace kanta a ƙasa. "Tun jiya nake tsumayen dawowarka har bacci ya ɗaukeni baka dawo ba, dama maganar komawar Baqeer asibiti ne da aka ce bayan sati shida a koma don a kunce ɗaurin da aka yi mishi zan yi maka ganin yau har an ƙara kwana uku akan sati shidan da aka bamu ban ji kace komai ba". A fusace cikin masifa da tijara irin tashi ya hau nunata da yatsa yana cewa "kinga Fatima ki kiyayeni, na lura raini kike neman kawo mini a cikin gidan nan, au bayan kin gama zuge ɗan naki yayi fatali da dukkan sadaukarwata a kanshi yaƙi yin abinda na sakashi shine yanzu zaki kwaso jiki ki tareni da batun mayar dashi asibiti? Don bance ku biyani kuɗaɗen da yasa nayi asara a kanshi ba shi yasa kike tunanin zan mayar miki dashi asibiti a kunce ɗauri, to ya dauwama a haka mana ina ruwana tunda dai babu wani amfani da zai yi mini na ƙare kashe kuɗina a kanshi a banza ba tare dana amfana da gina shin da nayi tayi ba sai ma nakasa da yayi yana nema ya ɗora mini wahala, to ba zan yi ba idan kinga zaki kai shi asibiti ban hanaki ba amma sisina ba zai ƙara yin ciwon kai a kanshi ba, sai ku gode abincina ma da yake ci a kullum ba tare da yayi wata wahalar nemowa ba, mtsew" ya saki wani dogon tsaki ya juya ya fice daga gidan yana huci kamar kububuwa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull