Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 13

Baqeer complete - Chapter 13

Baqeer complete Chapter 13: Baqeer complete Chapter 13. Daf da magriba Bello ya sauka a Kano ta jirgin sama wanda murna da yake ciki ba zata misaltu ba,…

3,402 words

Daf da magriba Bello ya sauka a Kano ta jirgin sama wanda murna da yake ciki ba zata misaltu ba, mahaifinshi da kanshi yazo ɗaukan shi a airport. Yallabai ya sake yi musu godiya da sanar dasu akan za'a kirasu wanda suka ci na ɗaya zuwa na uku a sake karramasu kafin a tallafa musu akan karatunsu zuwa kasashen ƙetare. Nan suka shiga motar mahaifin Bello, basu fita daga airport ba yace "Bello meke faruwa? Baka sanar dani akan tafiyar nan ba? Sannan a iya sanina ba Baqeer bane mai zuwan?" Ajiyar zuciya yayi yace "Baba nima ba'a son raina hakan ya faru ba, Baqeer yayi hatsari wanda ƙafarshi da hannunshi suka samu matsala, shine ya tursasani akan sai naje a madadin shi nima banyi niyyar zuwa ba ganin kamar hakan bai dace ba sai dai ya matsa don haka na tafi kawai." Jin kalaman Bello yasa hankalinshi ya ɗan kwanta, da sauri Bello yace "Shi yasa na kasa sanar daku don ni kaina kunya nake ji gani nake yi kamar ban kyauta ba." Cike da jin daɗi yace "Masha Allah wannan abotar taku tana sanyaya zuciyata Allah ya ƙara kareku, da hankalina ya tashi amma yanzu na fahimci MBB ma da kayi amfani dashi hala saboda asan shine kai?" Bello yayi murmushi yace "Sosai Baba shine dalilina, don Allah ko zaka bari in sauka don ina son na fara nuna mishi sakamakon abinda ya mayar dani." Baba ya ƙarasa gida sannan yaba Bello key ɗin motar yace "Amma karka dade Goggonka na jiranka." Cike da jin dadi ya ja mota ya bar wurin. Salim ne zaune shi da Baqeee sun kira Bello a waya har sun gaji bai ɗauka ba, Salim ya kira Baban Bello inda ya sanar dashi ai yana nan hanyar tahowa wurinsu. Mamaki ne ya kama Baqeer ya kalli Salim tare da ƙara kiran Bello sai dai yanzu ji suka yi ma wayar wai a kashe. Habi ce ta kira Salim wanda ya ɗauka don sanar da ita tayi hakuri zai kira ta daga baya. Sai dai me? Yana ɗagawa ta sanar dashi wai Bello yana ƙofar gidan su. Kallon Baqeer yayi wanda bai san me ake cewa ba sai dai yanayinshi kaɗai zaka kalla kasan akwai zargin da yake yi, Salim na kashewa ya kalleshi, jinjina kai Baqeer yayi yace "Salim zaka iya kaini gidan su Asiya?" Dafa hannunshi Salim yayi yace "Baqeer ka share kawai." "Please! Ganinsu ne kaɗai zai tabbatar da abinda nake tunani kuma shine zai ɗauke kokonton da nake yi akan su." Shiru yayi sai dai shi kanshi zuciyarshi ta kasa nutsuwa, Umma na murjin taliyar hausa da take yi in ta samu masu auna, so take ta samu kuɗi ta taimakawa Baqeer ya samu mai taimaka mishi da safe don bazai yiwu su cigaba da takurawa Salim ba. Da mamaki ta kallesu tace "Sai ina?" Salim ne yace "Zamu ɗan fita shan iska ne tunda duhu ya ɗan kawo kai." Kamar ta musa sai dai tace "Sai kun dawo." Haka suka yi ɗan tafiya kaɗan kafin su isa kwanar su Asiya duk cikinsu babu wanda ya iya tanka wa wani. Tun daga nesa Baqeer yake kallon motar mahaifin Bello don kuwa rabin hawa motar sune suke yi, Salim ne yace "Baqeer don Allah mu juya." "Please Salim!" Yayi magana cikin wata karyayyiyar murya, suna tafe yana tuno rayuwar da suka yi da Asiya mai tsafta, harta gama boarding school shi ke mata shopping a ɓoye don iyayenta ba wani abun kirki suke iya saya mata ba to shi ke saya mata abubuwa da yawa, da yadda take tsananin ƙaunarshi, a rana in bai kirata sau biyar ba ta dinga tambayarshi ko lafiya? Balle rayuwarsu da Bello wanda ke cike da farin ciki, yawanci zancen da yake zuwa ma dashi yake zuwa. Cak ya tsaya daga gefen gidan dake gaba da nasu kaɗan gidan mai kyau ne sosai dan fitilun gidan ne suka haske inda Asiya da Bello ke tsaye, daidai lokacin Bello ya matso tare da ciro award ɗinshi ya miƙa mata, wani irin murmushi ta saki ta ɗan jingina da gaban motar cikin farin ciki take yi mishi wani kallo, kafin daga bisani ya ɗauko waya ya fara ɗaukan ta hotuna tana tsaye rike da award din kai daga ka gansu kasan love ake sha. Baqeer kanshi ne yaji yayi mishi wani irin nauyi, shekara kusan guda kenan yana ayyana wannan ranar yana cikawa Bello baki akan duk ranar da ya amshi award ita zata fara gani ya sakata a gaba yayi mata hoto, ashe ba shi bane hakan zai faru dashi Bello ne? Idanunshi ne suka canza launi sosai da sosai yana jin zuciyarshi nayi mishi wani irin zafi, ya zai yi da rayuwarshi? Ina zai saka kanshi yaji daɗi? Asiya ya hango ta miƙawa Bello award ɗin ga mamakinshi hannunta ya riƙe ita kuma tana murmushin ta dake sanyaya mishi rai a baya wanda yake gani shi kaɗai take yiwa……

Tsaye take a jikin balcony na gidansu wanda daga gefe take hango mutanen biyu wanda ta gansu kwanaki ta kuma ga na keken shekaran jiya, hannayenta a harɗe a kirjinta duk abinda ke faruwa akan idanunta, yanda taga yana kallon gaba kaɗan da inda yake ne yasa ta kalli wurin, dan hasken fitilun gidan su ya haska layin, idanunta ne ya sauka akan yarinyar da ta wulakanta gurgun kwanaki, kana kallonta kasan soyayya suke yi da wanda ke tsaye kusa da ita, wani murmushin takaici tayi tare da girgiza kai, ta rasa me yasa maza sam wasu basubsan me ya dace dasu ba, kalaman wanda ke kusa da gurgun ne ya katse ta yana cewa "Please ka furzar da iskar dake bakinka, ka taimaka kayi magana." Nan da nan takaici ya sake rufeta ta rasa me yasa ita bata ganin abu ta ƙyale, wayarta kawai ta ɗauka ta fito daga gidan, kusa dasu kaɗan ta tsaya tana yi kamar mai yin waya tana cewa "Some people are just helpless, sai su dinga zuwa inda ba'a nemansu, in kasan ba'ayi da kai you just need to move on, amma wasu kamar basu da zuciya, sannan gani suke kamar in Allah ya jarabcesu rayuwarsu ta riga ta tsaya kenan."

Waigawa Baqeer yayi don kalamanta kaf cikin kunnuwanshi kuma tabbas muryar nan dai ita ce wacce tayi mishi magana sau biyu. Kafin yayi ƙoƙarin yin magana tayi gaba…..

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

#Baqeer #Shalele #Asiya #Zeey # RayuwadaKaddara #Hawayena #UMMASGHAR #AYUSHERMUHD *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*PAID BOOK*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA SHIDA*

*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O'O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?" *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

08142800199 07068558096

{16} Kallon Salim yayi bayan ya ɗauke kanshi daga kallon inda yarinyar ta suce, muryarshi cikin sanyi yace "Salim taimaka mu koma gida." Babu musu Salim ya fara turashi, bai sake iya waiwayen su Bello ba don wani irin zafi da ƙuna yake ji a zuciyarshi, tabbas Asiya da Bello sun yi mishi abinda bai taɓa tunanin wani mahaluki zai yi mishi ba, yana gani ana cin amana amma bai taɓa kawowa zai zo kanshi ba. A ƙofar gida suka tsaya ganin ƴar ƙofar shiga gidan a kulle, da mamaki suka kalli juna don ba'a kulle gidan sai ƙarfe sha ɗaya na dare, ya zaro wayar dake aljihun gaban rigarshi yaga tara da rabi, nan yasa hannu ya ɗan buga kofar gidan, basu jima ba aka zo aka buɗe, hankali a tashe suke kallon Baba dake tsaye a ƙofar, bai yi wani auni ba kawai ya tsinke Salim da wani irin mari, a razane Baqeer yace "Baba?" Ai bai tsaya saurarenshi ba yace "Kasan Allah in har na sake yi maka magana ka take umarnina gidana hana ka shiga zan yi, kai a duniyar Allah ba'a koya maka bin maganar manya bane? Nasan ka taso ba mahaifi ina yi maka uzuri tunda mahaifiyarka da tayi aure ajiyeka tayi gun iyayenta wanda dama kowa yasan tsofafi ba tarbiyar da zasu iya badawa, amma naga alama uzurin da nake baka sam baya shiga cikin kunnenka, to wallahi ka fita idona na rufe kaji na faɗa maka." Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Salim ya kalli Baqeer da kunyar duniya ta rufe shi yace "Baqeer kayi hakuri amma ba zaka sake ganin na tako ƙafata gidan ku ba." Daga haka yayi gaba yana share kwalla, an daɗe ana ci mishi mutunci amma bai taɓa jin zafi ba kamar wanda mahaifin Baqeer yayi mishi duba da yadda yake tunani iya ƙoƙarin yana yiwa ɗan shi, to menene laifinshi? Banda yana tausayin Baqeer dama da tuni sun raba abota. Juyawa Baba yayi ya barshi a zaune akan kujera a ƙofar gida, Umma na ta safa da marwa a tsakar gida, Jamila na daga gefe tana kallonta, ita kuwa Abu yau banda shirin tarbar mai gida babu abinda take yi. Baba yana shiga kai tsaye ɗakin Abu ya wuce ba tare da ya tanka musu ba. Da sauri Fatima ta zura hijab ta leƙa waje, yana zaune yadda kasan ba mai rai ba ko motsi baya yi, tunani kawai yake yi ina ne zai je ya zauna yayi rayuwarshi bayan nan gidan? Ina yake dashi da zai tattara ya tafi ya zauna shi kaɗai? Ganin Umma ne yasa zuciyarshi ta ƙara karaya kawai ya damtse hannu yana jin wani abu na sake tokare mishi zuciya. Haka ta turashi cikin ɗakin, Kamalu na zaune yana kallon ball a wayarshi, ta kalleshi cikin sanyin murya tace "Kamalu din Allah taimaka mishi ya kwanta." Wani kallo ya watsa mata yace "Ya kwana a kujerar in dai ni ne zan taimaka mishi." Wani kallo Baqeer yayi mishi zuciyarshi na takaicin yadda yake yiwa mahaifiyarshi magana sam babh respect, sai dai me zai ce? Bayan a dalilinshi ne ake faɗa mata magana? Kallonshi tayi tace "Kana gani zaka iya in na taimaka maka?" Zuciyarshi ce ke sake rauni tausayinta na ƙara kamashi a hankali ya ɗaga kai, haka ya dinga ƙoƙarin akan kar ya sakar mata nauyinshi gaba ɗaya wanda dalilin hakan yasa sai kifawa yayi, nan ya shiga jan jikin shi iya karfinsa, ganin yadda yake yi yasa bata ƙara takurawa akan sai ta taimaka mishi ba. Haka ya kwanta kawai yayi shiru don yasan bacci kam yau ko barawo ne ba zai ɗauke shi ba.

****** Iska Zeey ta furzar iya karfinta cikin tsananin ɓacin rai ta fara fifita da hannunta tana dafa ? ɗin apple dake table ɗin ɗakin "Wai Zeey baza ki faɗa mini menene ya ɓata miki rai ba? Nasan dai ba shakkar gobe Daddy zai dawo kike yi ba? Balle nace kina tsoron abinda Najib zai je yace ne ya dawo kanki." Zama tayi a bakin gado tace "Aunty N please ki duba mun wannan abun, wani ne……" Sai kuma tayi shiru ta fasa maganar, to ita tace me? Wani wa? Baya kawai tayi da kanta kan katifa cikin ɓacin rai don tasan bakin Nabeela baya shiru in har tayi magana to yanzu zata ji maganar wurin Kabir azo ana tambayarta menene nata na shiga abinda bai dameta ba, wa zata faɗawa ko zata huce? Tsaki tayi da takaicin rashin amsar number Maryam da tayi dole gobe ta duba gidansu taje ta gaida Umma ta amso tun kafin Daddy ya dawo ya hanata fita. Da wannan tunanin ta kwanta sai dai har tayi bacci takaicin saurayin ya isheta, ita a rayuwarta ta tsani taga ana wulakanta mutum yana mannewa a wuri.

****** A kafadar Mummy tasa kanta tace "Mummy please kinga ba dadewa zan yi ba." "Kuje ke da Nabeela ai tafiyar biyu dai tafi ko?" "Please Mummy ni kaɗai nake son zuwa sannan ko 30minutes bazan yi ba zan dawo, i promise." Zeey tayi maganar tana kallonta don tasan in har taji ina zata je tofa ko zata mutu ne ba barinta za ayi ta fita ba. Cikin kokonto Mummy tace "Baby don Allah karki dade yau Daddynki zai dawo in har ya dawo ba kya nan bansan me zance mishi ba." Kiss ta manna mata a kunci tace "Max 1hr." Tana kawai nan ta fito da sauri hannunta riƙe da key na motar Nabeela don Daddy ya hanata fita, balle in aka san inda zata je ko mutuwa zata yi babu mai barinta taje, sam itama ba son zuwa gidan take yi ba number Maryam kawai take son ta amso ta kuma gaishe da Umma daga nan kuma In Sha Allahu bazata sake komawa. Da sauri ta fito ta faɗa mota sannan ta fita daga gidan, ta ina zata fara duba gidan? Don rabonta da gidan har ta manta, gaban yaron dake sayar da rake akan titi ta tsaya tace "Don Allah kasan gidan su Maryam?" Da mamaki yace "Maryam wacce?" Tace "Kanwar Hadiza?" Nan ma yace "Bangane ba." Ƙasan leɓenta ta ciza sunan dai da bata son ambata a dole ta kula sai tayi. "Maryam ɗin Baqeer." Nan fa yaro yace "Oh na gane." Ya shiga yi mata kwatance da hannu, tayi godiya tare da bashi 1k sannan ta ja mota ta tafi shi kam sai godiya yake zubawa. A nesa da gefen gidan ta tsaya tana tunanin ta yadda zata taka kafafunta zuwa cikin gidan, gidan da sam tasa a ranta ba zata ƙara zuwanshi ba, sai dai darajar Umma da Maryam fa? Abinda yazo mata kenan wanda yasa ta shafar fuskarta, ta tabbatar Baqeer ba zai ganeta ba, kuma ƙila harta shiga ta fito ma bai san tana nan ba.

***** Kamalu ne ya diro daga kan gadonshi cike da jin daɗin wayar da aka yi mishi cigiyar Zeey daya bada aka ce an gano gidansu, ba zai iya jira ya watsa ruwa ba hakan yasa ya shiga fesa body spray sai daya kusa ƙarar da shi ya cillar anan tsakar ɗakin sannan ya zura wando da riga yana yi yana taka rawa, kallon Baqeer yayi dake zaune yana karatun Qur'ani yace "In an kawo abincina a ajiye mini zance zani." Ko kallonshi Baqeer bai yi ba balle yasa ran zai amsa mishi, a kufule ya naushi iska da ƙafa saitin inda Baqeer yake yace "Gurgu kawai." Fitowa yayi bai kula da motar dake gefen gidan ba ya hau babur ɗinshi yayi gaba.

***** Abu a tsakar gida sai girki take tana zabga nishadi din tabbas jiya Malam ya tsunduma a tarkonta jinta take yi kamar wata yarinya ƴar shekara ashirin da biyar, yo dama ina zata yarda ace wai don ta girma shikenan baza ta ɗana sakalci ba? Jiya ta tabbatar da kalmar da ake cewa maza basa girma. Jamila sai kallonta take yi tana binta da harara don yau sai 12 na rana Malam ya fito daga ɗakin Abu wanda kuma baya yi musu hakan ko a lokacin da Fatima take ƴar gaban goshinshi, ta tabbatar wani makircin ta sake yi ta barta a gefe. Fatima ce ta fito daga ɗaki ganin Salim har rana babu shi babu labarinshi, ta tabbatar Baqeer na neman taimako don da asuba da ƙyar ta lallaɓa su Bashir suka taimaka mishi yaje banɗaki, Abu ta kalla tace "Abu dan Allah ko zaki yiwa Kamalu magana ya taimakawa……" "Aye yare aye nayi yara ye iya aye yare munga idon wasu yara ye iye, wasu gasu can ba ƙafa yara ye iye, sai bi suke a taimaka yara ye iya to in kunsan da haka? Yara ye iye meya sa baku yi biyayya ba tun farko?" Waƙar da Abu take yi ne yasa Fatima kasa ƙarasa maganar da take yi, Jamila ta sheƙe da dariya suka tafa tace "Kai Abu yaushe kika zama mara kirki haka?" Fatima ta share ƙwallarta ta zura hijab ta leƙo waje, Zeey dake tsaye bakin mota tana saƙar shiga da warwarewa akan ta koma gida ta hangota, kallo ɗaya tayi mata ta tuna Umman nan ce dai mai ƙaunarta, murmushi ta saki tana jin sanyi a ranta, da sauri ta fara takowa wurin daidai nan wani yaron almajiri yazo wucewa Umma tana cewa "Dan Allah bawan Allah ka taimaka ka dubo mini Salim a gidan can. Ko kuma in akwai almajirin daya fika girma ka kirashi kace zamu biya ya taimaka mana." Yaron na juyawa idanunta ya kai kan Zeey, sam bata ganeta ba hakan yasa ta nemi juyawa da sauri Zeey tace "Umman mu?" Da mamaki ta kalleta, nan idanuwanta suka fara mata alamun kallon sani, Zeey ce ta rungumeta tace "Nice Zainab fa? Zainabun ki." Da mamaki ta ɗan zareta tace "Zainab? Kece?" Kai ta ɗaga tare da sake rungume Umma, cike da jin dadi suka shiga cikin gidan, Jamila ce ta watsawa Zeey kallo ganin shigar dake jikinta tace "Ha'a ba dai ita ce wacce Baqeer ke zancen zai aura ba? Ta shigo mana ganɗarɗar haka?" Umma tace "Ba ita bace wannan…." Hannun Umma ta riƙe da sauri tare da girgiza mata kai alamar a'a, Umma tasan dalili hakan yasa tace "ƙawar Maryam ce." "Oh na ɗauka ai budurwarshi kika ɗauko don ta taimaka mishi." Kalaman ta sun konawa Umma rai sai dai bata da damar amsawa. Abu dake zuba maganin mata a jarkoki tace "Wai ma kin dubashi ko? Kin san zai iya gangarawa ba tare da an sani ba tunda ba kafafun guduwa." Gaban Umma ne ya faɗi wanda yasa tayi hanyar ɗakin da sauri tana tafe tana addu'a. Bin bayanta Zeey tayi don da alama ba lafiya ba, bata tsaya maida ƙofar ba ta tura ɗakin da sauri zuciyarta cike da tsoro. Baqeer ta samu a zaune ya rufe idanunsa gam hannunshi na hagu ya cukwikuye takardar zane da ita, ƙasan ɗakin duk pencils ne a zube an watsar. Da sauri Umma ta ƙarasa ta riƙo shi tace "Baqeer menene? Meya faru?" Zeey jin Umma ta ambaci sunan Baqeer yasa ta nemi juyawa da sauri, idanuwanta ne suka hango mata keken guragun dake gefen katifar shi, gabanta ne yayi wani irin faduwa nan da nan jikinta ya fara rawa, kalaman Umma ne suka sake rikitata "Baqeer kayi hakuri ban san ina Salim yake ba, na aika dai yanzu a kira shi zai zo ya taimaka maka, wannan bala'in da muka shiga Allah ya fitar damu Baqeer rashin ƙafar nan taka na daga mini hankali, sai yaushe zanga ka dawo Baqeer mai yawan fara'a? Zee bata san sanda tayi karo da bango ba, Baqeer? Umma ce ta waigo ta kalleta tace "Zainab kin tsorata ko? Ƙaddara ce ta afka mishi." Zeey tana kallonshi tana girgiza kai, Baqeer? Baqeer data sani wanda kwarjininshi yasa take tsananin shakkarshi? Wanda kusan kullum sai ya sakata kuka ba tare da ya damu ba? Wanda akan baƙar maganar da yake yi mata har zazzabi take yi? Wanda a dalilinshi abotarta da Maryam ta yanke? Ina Baqeer ɗin data sani da har zai bari mace ta wulaƙantashi? A nemi illatashi a titi? Meke faruwa? Ƙwaƙwalwar ta sam ta kasa gasgata abinda ke faruwa cikin wata murya tace "Umma meya faru haka?" Muryarta daya ji ne yasa shi buɗe idanunshi da suke rufe gam a hankali ya saukesu a kanta, wacece wannan dake bibiyarshi? Yanzu kuma har gida? Ya aka yi ma tasan Ummanshi?

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull