Baqeer complete - Chapter 12
Baqeer complete Chapter 12: Baqeer complete Chapter 12. ***** A rikice Baba ya shigo cikin ɗakin lokacin Baqeer na zaune ya sa karatun Al-Qur'ani a waya…
3,123 words
***** A rikice Baba ya shigo cikin ɗakin lokacin Baqeer na zaune ya sa karatun Al-Qur'ani a waya kawai yana sauraro yana yi yana kallon Kamalu wanda har lokacin yake kwance yana bacci har Salim yazo ya taimaka mishi yayi wanka yaci abinci yayi sallah a zaune amma bai tashi ba, jin yadda Baba ya shigo a rikice ne yasa gabanshi ya shiga faɗuwa, ba dai wani wurin za'a ƙara kai shi ba ko? "Waye wannan kamar Bello?" Kalaman Baba daya juyo kenan a kunnuwanshi yana maganar yana miƙa mishi wayarshi, hannayenshi biyu ya miƙa duk da yasan bazai iya amsa da hannun daman ba. A guje Kamalu ya tashi ya afka banɗaki don yasan yanzu Baba zai ci mutuncinshi. Da mamaki yake kallon hoton dake jikin allon wayar "Ba Bello bane ko kuwa idona me ke yi mini gizo?" Kallon Baba yayi sannan ya sake kallon rubutun ƙasa da aka rubuta wanda yaci gasar zanen da akayi a yanzu haka a garin Abuja. Da sauri ya kalli Baba wanda ya ke kallanshi cike da takaici yace "Duba da kyau me aka rubuta a kasa?" "MBB?" Kallan Baba ya sake yi da sauri wanda ya fizge wayarshi yace "Ya maka kyau! Gashi dai abokinka ne yayi amfani da sunanka ya maye gurbinka kuma alamun da ya bayyana a fuskarka ya tabbatar mini baka sani ba, sanda nake hanaka nuna mishi sirrinka kaji magana ta? Allah ya kara yanzu gashinan ai duniya ta juya ma baya." Yawun bakinshi Baqeer ya haɗiya yana jin wani abu mai ɗaci na sake taso mishi "Yanzu ga ka nan a kwance shi kuma fa? Gashi can ya maye gurbinka, ka fake da wata karaya ka kasa taɓuka komai, sai kayi ta zama a nakashe baƙin cikin da ka sakani baka fara ganin komai ba, malalaci kawai." Yana kawi nan ya juya ya fita, hannu Baqeer yasa a sumar kanshi yana jin wani irin zafi na taso mishi, ya maida hannun saman ƙirjinshi dake yi mishi wani irin raɗaɗi, idan Bello ya faɗa mishi zai maye gurbinshi yasan ba zai hana ba tunda idan ma bai je ba wani dai za'a tura to amma me yasa ya ɓoye mishi cewa shi zai je gasar a madadin shi? Ba dai shima gudunshi yake yi ba saboda abinda ya faru? Ko kuwa abinda Baba ke yawan faɗa mishi ne ya tabbata akan ya daina yarda da abokai? Iska ya shiga furzarwa da sauri cikin ƙarfi sakamakon jin da yayi numfashinshi na neman ɗauke wa. Umma ce ta shigo da sauri don tunda taji kiran da Baba ke yi mishi tasan ba lafiya ba, karshe ma jinshi tayi a tsakar gida yana sababi akan ai dama shi yasan hakan zai faru, gashi nan kuma abinda yake tsoro ya afku, cikin sauri ta nufi ɗakin ganin halin da yake ciki yasa ta ɗauki littafi da sauri ta fara fifita mishi fuska wanda da ƙyar ya samu numfashinshi ya daidaita, kallonta yayi idanunshi sunyi jaaa yace "Umma na!" Ta goge kwallarta tace "Baqeer dole kasa dauriya a zuciyarka, abubuwan dake faruwa da kai yanzu ka fara ganin su in har baka ɗauki dangana ba baza ka taɓa samun salama ba." Kai ya ɗaga mata yace "In sha Allahu Umma, tun jiya na fara sawa kaina wannan tunani amma Umma kina ganin Bello ma munafurtata yayi?" Ajiyar zuciya tayi tace "In ma yayi kanshi ya yiwa, rayuwar nan nawa take? Ni ban damu da wani abu ba Baqeer ɗina nake so naga ya dawo daidai." Kallonta kawai yayi don bai san me zai ce ba.kuma, ta miƙe ta fita don bata son daɗewa a cikin ɗakin sanin Kamalu a ɗakin yake. Tana fita kuwa sai gashi ya fito daga wanka yana fito, kallonshi yayi ya kwashe da dariya yace "Shalele yaya? Abubuwan sun ƙi daidaituwa ne?" Baqeer bai tanka shi ba ya ɗan matso yace "Yarinyar jiya ka santa ne?" Da mamaki ya kalleshi yace "Kamar ya?" "Naga ta shigar maka faɗa ne har da yi mini shafar soyayya shine nake son tabbatarwa ko ƙanwar abokinka ce." Kai Baqeer ya kawar cike da takaici, Kamalu yaja tsaki yace "Kai sai faɗin ran tsiya kace baka sani ba ne bazaka iya faɗa ba? Wallahi na dai faɗa maka in har kana son kwanciyar hankali ka tabbatar ka bani girma stupid kawai nakasashe." Ya ƙarasa maganar yana zura kaya, sallar asuba da azahar ya haɗa sannan ya ɗauki wayarshi ya fita, dole ne ma ya shiga neman yarinyar nan lungu da saƙo don banda tunaninta babu abinda yake yi tunda ya haɗu da ita. Takaici ne ya kamashi daya fito yaga Bashir yana ƙoƙarin shiga motar Baba wato shi sam yaran gidan nan sun rainashi, shi kenan da hawa babur, cikin tsawa yace "Kai Bashir bani key ɗin nan ka hau babur." Da yake duk sun san halinshi yasa bai yi mishi musu ba haka ya miƙa mishi makullin motar ya amshi na babur ɗin, fuskarshi ya sake shafa inda Zeey ta mareshi dole ne yaje ya nemota ya tabbatar inta ganshi a mota shima zata kulashi.
***** Baqeer a cikin ɗaki yayi shiru, Hadiza da Maryam duk sun kirashi sunji yanayin jikinshi, Salim ya kira a waya wanda ringing biyu ya ɗauka yace "Baqeer akwai abinda kake so ne?" Wani abu ne ya ɗarsu a ranshi, Salim abokinshi ne tun na yarinta sai dai zuwan Bello unguwar da kuma yanayin karatunsu na Art yasa shaƙuwarsu tafi ƙarfi tun daga nan ya tattara Salim ya ajiye, in har ka ganshi da Salim to sai dai haɗuwar masallaci ko kuma a hanya su gaisa ya wuce. Jiki a sanyaye yace "A'a dama tambayarka zan yi kaji labarin Bello kuwa?" Ajiyar zuciya yayi da alama bai so yin maganar ba kafin yace "Kayi hakuri Baqeer kasan na faɗa maka Habi taji suna waya da Asiya akan tafiyarshi, ashe gasa yaje ɗazu Habi ta kirani take sanar dani abinda ke faruwa da link ɗin BBC inda suka ɗaura labaran, abinda ya bamu mamaki me yasa yayi amfani da initials ɗinka kamar yadda kake yi a matsayin sunanka? Sannan yaushe sunanshi ya zama Muhammad Bello?" Hannunshi dake riƙe da waya ya ɗan matse kaɗan zuciyarshi nayi mishi zafi, yace "Komai ta wurin Asiya ake ji kenan?" "To ni Habi bansan meya faru ba amma….." Sai kuma yayi shiru, Baqeer yace "Amma me?" "Babu komai kawai dai ban san meke damun Bello ba." "Wayar da Asiya take yi da Bello akwai alamar tambaya ne?" Tambayar da Baqeer ya daki Salim da ita kenan, haka kawai yaji ƙwaƙwalwarshi tana ayyana mishi abu, in har Asiya ta rabu dashi ta bar ɗaukan wayarshi taya zata cigaba da hulɗa da abokinshi wanda ta dalilinshi ta sanshi? Sannan ace duk wani abu daga wurinta ake fara ji? Salim yayi wata ƙaramar shaƙuwa yace "Ni dai wallahi ban sani ba kawai Habi ce dai bata son wayar da suke yi." Kashe wayar kawai Baqeer yayi don bai san me ma zaice ba, zuciyarshi na sake ayyano mishi abubuwa da dama.
******** Duk wani kayan ciye-ciye an jerashi a parlourn, Mummy ta shigo ta tabbatar Zeey tayi shigar daya dace, Nabeela na zaune akan gado tana murmushi don tasan Zeey in har ta leƙa wuein Najib to tabbas sai ta kwafsa, kallonta Zeey tayi tace "Aunty Beela ina fa kallon yadda kike kallona tun ɗazu." Dariya tayi tana kallon Mummy tace "Ni dai bance komai ba kawai dai ina jiyewa ne garin gyara a ƙara ruguza abu." "To ke kuma da baza kiyi fatan alkairi ba sai kiyi shiru." Mummy ta faɗa tana hararar Nabeela. Mai aiki ce tayi knocking ta sanar da su zuwan Najib sannan tace suna falo tare da Kabir.
Koya kuke ganin zata kasance da Baqeer akan Bello? Ga dai Kamalu an tafi neman Zeey, ga kuma Najib yazo ganin Zeey.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
#Baqeer #Shalele #Zeey #Kamalu # RayuwadaKaddara #Hawayena #UMMASGHAR #AYUSHERMUHD
https://www.arewabooks.com/chapter?id=656d9ccf22d5844413e4fa27
*BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*ƘARSHEN ƊANDANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA BIYAR*
MUMMY ce ta sake riƙe hannunta tace "Kin san ina bayanki a koda yaushe ko?" Cike da sanyin jiki ta kalli mahaifiyar tata kafin ta rungumeta tace "Mummy dole ne sai Daddy ya aurar dani ga wanda yake so?" "Sai haƙuri kin san shi ɗan siyasa ne shi yasa yake son aurar dake ga wanda yasan zai taimaka mishi a harkar siyasar shi." Ajiyar zuciya Zee ta sauƙe tace "Am sorry Mummy amma bazan taɓa auren wanda bana so ba." Daga haka ta zare jikinta ta bar cikin ɗakin, jiki a sanyaye Mummy ta kalli Nabeela tace "Nabeela please banda ke akan me bazaki dinga ƙarfafa mata gwiwa ba? Ya kuke so tayi ne? In har bazaku fahimceta ba?" Wani murmushin takaici Nabeela tayi tace "Yaya wannan abin da kuke wallahi ba so bane, nasan kinsha wahala kafin ki sameta amma wannan bai kai dalilin da zai sa ku sangartata ba, ku dinga barinta tana fitsarar data ga dama ba." Nan da nan fuskar Mummy ta canza tace "In ke kina kanwata kin faɗi haka na waje suce me?" Kai kawai ta kauda gefe zuciyarta na takaicin yadda idanunsu suka rufe saboda son yarinyar nan suka manta sam da abinda ya kamata suyi, hatta Daddy da ake ganin yana da zafi a kanta sam ita bata gani tunda zafinshi baya wani ɗaukan lokaci, tasan suna son Zeey amma a kalla….. "Ki wuce falon yanda in kinga zata faɗi ba daidai ba ki taimaka ki daidaita." Kalaman Mummy ne suka katse mata tunaninta, mayafinta kawai tasa ta fita daga ɗakin.
**** Ƙafa ɗaya kan ɗaya Najib ya ɗaura yana girgizawa shi a dole ta ƙona mishi rai yana jira ta bashi hakuri. Zeey ce ta shigo hannunta ɗauke da tray na drinks da fruits da aka yanka mishi, taga mai aiki zata kawo ta amsa tace zata miƙa da kanta. Mummy data fito daga ɗaki ganin haka yasa taji wani daɗi ta kalli Nabeela tace "Ɗan basu minti goma su biyu." Zeey da murmushi a fuskarta ta shiga sai dai tana sauke labulan ɗakin ta canza yanayin fuskarta, kallonshi tayi tace "J?" Wani kallo ya zabga mata tayi mishi alama da kai tare da nuna mishi tiren hannunta, sake watsa mata wani kallo yayi sai dai ya rasa me yasa yake sake kallonta, kyaunta yake ƙara gani sama da na jiya da alama kayan dake jikinta ne ya sake fito da kyaun nata don sanye take da lace an mata ɗinkin doguwar riga irin straight gown ɗin nan tayi kyau sosai a cik,i ba tayi kwalliya ba don mai kawai ta shafa sai ƴar powder data goga a fuskarta amma sosai tayi kyau kamar wata ƴar tsana. Yanda ta kalleshi ne yasa yaji kamar an sakashi dole sai gashi ya miƙe yazo inda take ya amshi tiren, ta nuna mishi table ɗin dake tsakiyar parlourn tace "Ajiye acan." Ajiyewar yayi sannan ya koma ya zauna ya ɗaure fuska tamau, bata ko bi ta kanshi ba ta ɗauki remote kawai yaga ta kunna tv tana kallo, sun fi kusan minti biyar ba wanda yake magana sai ita kawai da take kallon drama na Turkey a tv tana murmushi, Najib ya cika ya cika har bai san ɓacin ran dake damunshi ba don takaicinshi ma ko kallon inda yake bata kuma yi ba tunda ya zauna. A kufule yace "Zainab wai ba hakuri aka ce ki bani mu daidaita kan mu ba?" Waigowa tayi ta kalleshi tace "Ince me kenan?" "Kice kayi hakuri nayi kuskure amma bazan ƙara ba." Kai ta jinjina tace "Perfect gashi nan ka faɗa ai ko akwai sauran abinda kake son ji?" Wani huci yayi yace "Gashi nan na faɗa?" Ta ɗaga kai tace "Ka faɗa mana ko bayan haka da ƙari?" A wannan lokacin Najib ya gama kaiwa bango, ya miƙe a zuciye yana sakar mata wani mummunan kallo, kallonshi ta sake yi jin alamun ana kallonta tace "Oh! Ba dai har zaka wuce ba?" Kasa magana yayi kawai yana kallonta, ƴan mata nawa ne suke binshi yana wulakantasu? Ƴan mata nawa ne yake disgasu saboda yanda suke rububin shi? Kamar shi Najib Guy ace mace tana neman maidashi shashasha?" A fusace yayi hanyar ƙofa, Nabeela ce ta turo ƙofar jiki a sanyaye ta kalleshi, zata yi magana ya ɗaga mata hannu, Kabeer ne ya taho don dama yana ɗaki haka kawai jikinshi ke bashi rainin hankalin Zainab babu abinda baza tayi ba. Cikin sauri ya ƙarasa wurinshi yace "Najib menene?" Rasa abin faɗa yayi don a ganinshi ƙasƙanci ne ma ya faɗi abinda tayi mishi kamar ya zubarwa da kanshi aji ne, a fusace yace "Ka tambayi ƙanwarka sannan bazan sake dawowa ba taje can ta nemi wanda yayi mata." Nabeela tace "Kayi hakuri Najeeb ba wai har ranta tayi ba……" Bai jira amsa ba ya wuce, Kabeer ne ya bishi a baya da sauri, ita kuma Nabeela ta shiga ciki. Tana shiga ta ganta tana shan fruits ɗin da aka yankawa Najib tana kallo yanda kasan ba ma da ita ake abin ba, kasa magana tayi kawai ta juya tabar parlourn.
***** Baqeer ne duk hankalinshi yaƙi nutsuwa, baya son ya cika zargi amma dole ne yayi, wayar nan ya ɗauka ya kira Salim, ringing biyu ya ɗauka jiki a sanyaye yace "Salim don Allah gobe idan Bello ya dawo ka taimaka kazo ka kaini inje in ganshi in dai har shi bai zo ba, ina sin sanin amsoshin tambayoyin dake kaina." Yace "Shikenan nima anjima zan zo dama na gyara ka." Daga haka suka yi sallama ya maida kanshi kan katifa kawai yana addu'oin samun nutsuwa don zuciyarshi tuni take ƙissima mishi wasu abubuwan da bai dace ba. Kamalu ne ya shigo gidan ranshi a matuƙar ɓace, bokitin dake tsakiyar tsakar gidan yayi fatali dashi wanda hakan yasa Abu fitowa da sauri, don ta ƙule cikin ɗakin ne tana hada sirrin matsi na 'tif da taya' wai in dai mace tayi amfani dashi da yamma suka sadu da miji to fa shikenan sun zama gamgam, bata so Jamila ta gani balle ta fara mata surutan banza "Kamalu?" Ta faɗa tana yi mishi alama da yazo don dama nemanshi take yi, shiga yayi sai kumbura fuska yake cikin ƙunar rai yake cewa "Kinga Mama karki ɓatan lokaci don sauri nake yi ina so in ɗauki chager na wayata ne zan koma waje." Ƙofar ta mayar ta rufe bayan ta tabbatar babu wanda ya ganshi tace "Kamalu haka zaka zauna yanzu Bashir ya kwace fadar mahaifinku bayan Baqeer?" Cikin kakkausar murya ta irin fitinanun mazan nan yace "Wannan ya rage nasu ni abinda ya dameni daban, suje can da yawarsu." Iska ta furzar tace "Kai matsalarka kenan sam ba'a faɗa maka kaji, ko so kake wulakancin daka sha shekarun baya ya sake faruwa?" "Kinga Mama ba wulakanci ba suyi abinda ya fishi ma ni bai dameni ba, wannan ina zaune ya lalata ƙafa dan da ina da dama ma ni da kaina zan karya ƙafar da hannun to amma tunda wani ya rigani kinga na huta amma wannan mahaukacin ya rainani wallahi zaki jishi a maƙabarta." Yayi maganar a fusace tare da buɗe ƙofar ɗakin zai fita, ji yayi tace "Kamalu magana nake yi maka fa?" Kallonta yayi kawai ya fice tare da bugo ƙofar da ƙarfi, babu abinda ya tsana irin a dinga haɗa shi da mutane shi kenan daga a haɗa shi da wannan sai a haɗa shi da wancan to wallahi ba zai yiwu ba. Ɗakin shi ya nufa rai a ɓace. Baqeer yana zaune bayan Salim yazo ne da zai tafi yace ya sakashi akan kujerar dake gefen table ɗin zanen shi, pencil yayi ta ƙoƙarin riƙewa sai dai hannunshi na gocewa, sam ya kasa taɓuka komai, kanshi ya dafa yana tunani, shi ba wani abin ya sani ba balle yace zai gwada wani abin, zanen nan kawai ya iya da kuma shi ya dogara, yanzu ya zai yi da rayuwarshi? Ajiyar zuciya yayi gashi an ɗauke mishi waya bai samu ya kira mutanen da suka amshi aikinshi ba tare da sun biya ba, da wanda suka amshi aikinsu suka fara biya basu gama ba, ya zai yi? Banko kofar da Kamalu yayi ne yasa ya kalleshi, a fusace Kamalu ya shigo yace "Uban me kake kallo?" Baqeer ya kawar da kai dan baya son tanka mishi sam, hankaɗe table ɗin gaban Baqeer yayi yace "Wawa kawai in ma zaka farka daga shirmen mafarkin da kake to kayi ka farka don anyi gaba an wuceka, sannan daga yanzu na maka iyaka a cikin ɗakin nan kada ka kuskura ka wuce nan zagayen din nan ɓangarena ne." Ya ƙarasa maganar yana nuna mishi sashin da yake nufi, kallonshi kawai Baqeer yayi ya kauda kai wanda hakan ya sake tunzuro shi yace "Ni kake kawarwa da kai?" Bai tanka mishi ba sai ajiyar zuciya da yake don shi yanzu komai na rayuwar nan mamaki kawai suke bashi, yanzu yadda zai yi ya samu kudi ya sayi magungunan da aka rubuta mishi yake nema, don a gabanshi aka bawa Baba takardar magungunan daya kamata a saya mishi amma har yau babu abinda aka bashi sai paracetamol da Umma tasa aka sayo mishi sanda ya dinga fama da yawan ciwon kai. Takaici ne ya ƙara rufe Kamalu ya ɗauki charger wayarshi ya fito yana zazzaga masifa dama ranshi a matukar ɓace yake sakamakon tun safe yake yawon neman Zeey babu ita babu labarinta, duk wanda ya yiwa kwatancen yar masu kudi baƙa kyakkyawa sai dai a hankada shi wani gidan, akwai gidan da yaje ma kare ya biyoshi tun daga nan ranshi yake a ɓace gani yake ta leko ta koma Zee tayi mishi.
******* Ɗakinta ta kulle tana ji Kabir nata bubbugawa har sai da Mummy tayi mishi magana sannan ya ƙyaleta, gashi dama Dad baya nan yaje Gombe taron jam'iyarsu. Ko da Daddy yayi waya Mummy ce mishi tayi basu daidaita ba amma sun sulhunta tana saka ran inya sake zuwa su daidaita. Takaici ya kama Kabir yace "Mummy wai ba zaki bari na farfasawa yarinyar nan baki ba? Haka zamu zauna tana mayar da mutane kamar wasu yaranta?" Fuska sosai Mummy ta ɗaure wanda hakan yasashi tashi yabar parlourn.
****** Washegari…….