Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 11

Baqeer complete - Chapter 11

Baqeer complete Chapter 11: Baqeer complete Chapter 11. Maryam kam da kyar ta iya jan kafafunta zuwa inda Umma take kame tace "Umma menene ke faruwa?"…

3,034 words

Maryam kam da kyar ta iya jan kafafunta zuwa inda Umma take kame tace "Umma menene ke faruwa?" Areef ta kalla tace yaje ciki gun Aydah, Hadiza ce ta taho inda take da sauri ta rungumeta kawai tana kuka sosai, haka kawai Maryam ta samu kanta da hawaye a haka ta jata zuwa ɗakin Baqeer, yana zaune akan katifa kanshi kawai ya jinginar a jikin bango duk abinda ke faruwa akan kunnenshi ne, a zaune kawai yake idanunshi yake buɗe wa kawai yana rufewa, Maryam ganin hanunshi a naɗe yasa tace "Na shiga Ya Hadiza meya samu Yaya a hannu?" Hadiza ta fito da ita suka koma ɗakin Umma sannan ta sanar da ita abinda ya faru, tasha kuka itama ta gode Allah sai dai babu yadda zasu yi ƙaddara ce Allah ya jarabcesu da ita, haka suka fito dukansu suka tattare kayan Baqeer suka shiga dashi ɗakin Kamalu, wanda dama tare yake dasu Bashir, ɗakin kaca-kaca kai kace ba mutane ke kwana a ciki ba, haka suka gyara ɗakin sannan suka saka mishi kayan zanenshi a gefe, sunyi sa'a Salim ya zo don dama yace yana dawowa daga aiki zai zo, nan aka maida Baqeer gefe a cikin ɗakin suka jera mishi komai nashi, duk abin nan da suke yi ba wanda yake iya magana banda kwalla kawai da suke sharewa gashi Baqeer kallo ɗaya zaka yi mishi kasan shi kaɗai yasan meke faruwa akanshi dan idanunshi duk sun shanye kawai kallon kowa yake yi babu alamun mamaki ko magana, sai da suka gama sannan Maryam ta zauna a gabanshi tace "Kome zai faru Yaya muna tare da kai, Allah kuma na tare da kai, don Allah kayi ta addu'a kada ka bari ƙwaƙwalwar ka ta gushe maka tare da kowa." Ido kawai ya lumshe mata ya buɗe alamun to, ya ɗauki wayar Hadiza ya miƙa mata, ta girgiza kai tace "Ka dinga saka karatun Alqur'ani kana saurara, ni zan bata ɗayar wayata tunda biyu gareni." Baya son magana shi yasa kawai ya maida kanshi kan pillow ya kwanta, karatu ta kunna mishi sannan ta fito daga ɗakin, Salim kuma ya zauna a wurinshi. "To ni wannan lamari, lokaci ɗaya yarima ya zama bawa? Ina aka taɓa wannan abu? Banda dai shi Malam bashi da hakuri?" Abu ta faɗa tana kallon Fatima dake gyara kayan shanyarta data zuge a labule saboda a wuce da kayan Baqeer. Jamila ce ta sauke ajiyar zuciya tace "To ai abin ne kin san in aka koroka daga sama yafi ciwo, kin san kuwa yanzu haka har Bashir yaje yayi registration? Yau fa da kanshi Baban nasu ya kai shi makaranta." "Yaron nan kin san ba zai faɗa mini ba don baya so nakasheshen mu ya shiga damuwa." "To nima ai Salihu ne ya kawo mini gulma, kin san Bashir ɗan albarka ne." Jamila ta ƙarasa tana zunɗen Fatima.

"To sai aka yi me? Ai Bashir da Salihu da Baqeer duk daya suke sannan ƙaddarar data sameshi bata wuce kan kowa ba, kuma menene ma sabon abu dan mahaifi ya kai ɗan shi makaranta? Banda dai……" "Maryam!" Umma ta faɗa cikin kakkausar murya wanda hakan ya sakata yin shiru don ita dama bakinta baya shiru, don Daso ma suke ce mata a gidan saboda tsiwarta, sam bata ɗaukan raini kuma bata jiran ta kwana, su kansu Abu da Jamila sun san halinta. Abu ta zabga mata harara tace "Sai tsabar rainin tsiya ko waye sa'anki anan ni ban sani ba, mu ba'a matsayin iyayenki muke ba? Ko kinji munce wani abu ne mai zafi da zaki faɗa mana magana?" Jamila ta cafe tana cewa "Yara sai raini da rashin tarbiyya, to mu kunji munce wani abu ne? Ba jimami muke akan abinda ya faru ba?" Maryam zata yi magana Umma tace "Maryam wuce ciki kizo ki koma gidanki." Jita yi kamar zata yi kuka don ɓacin rai, to amma ya zata yi? Haka dole ta wuce ɗaki tana shiga ta rungume Hadiza dake zaune akan kujera banda hawaye babu abinda suke yi, Umma tana gamawa ta shigo ta kallesu tace "Ku tashi ku koma gidajenku tun kafin ku sake samun saɓani da mahaifinku tunda mai kare mana gaba ɗaya kunga yadda Allah yayi mana dashi." Maryam ji take yi kamar zata yi hauka, babban baƙin cikinta duk kudin mijinta ace babu abinda zata iya yiwa ɗan uwanta? Ita yanzu account ɗinta ko dubu biyar babu tasan kuma tana yin magana uban mijinta zai fara zancen shima yana buƙatar ganin likita, kuma in tace a ɗauki mai kula dashi tasan kai tsaye ma zasu ce babu kuɗi, haka suka yi mishi sallama suka tafi don ko tanka musu bai yi ba yana kallonsu dai har suka bar ɗakin. Baqeer har Salim ya bar gidan bayan ya gama yi mishi duk wani abinda yasan zai bukata bai ce ko kalma ɗaya ba, sai da Salim yazo yi mishi sallama ne ya kalleshi yace "Salim nagode!" Cike da tausayi ya jinjina kai yace "Bello yazo?" Kai kawai ya girgiza alamun a'a, jiki a sanyaye Salim yace "Naji ance baya nan kenan da gaske ne abinda naji." Kallonshi yayi alamun tambaya nan Salim yace "Ban san ina yaje ba na dai ji Habi na maganar ne da muka yi waya." Kai ya ɗaga nan ya sake yi mishi sallama ya fita, Baqeer na nan a zaune yana kallon Kamalu ya shigo yana ƴan waƙe-waƙenshi, ko kallon inda Baqeer yake bai yi ba ya gama abinda yake yi ya ciro doya da kwai daya siyo da juice ya shanye sannan yayi miƙa a kan katifa, shiru ne ya ratsa ɗakin don Baqeer ya ɗauka ma Kamalu yayi bacci ne sai ji yayi yace "Yanzu ya kake ji? Gashi dai kai ne ɗan gata ga kuma halin daka tsinci kanka a ciki, ko banza ni ina da kafafuna, ko da ba'a barni nayi karatu saboda kai ba ina da lafiyata wanda kai yanzu baka da ita." Idon Baqeer na kanshi sai dai bai tanka mishi ba, zama Kamalu ya miƙe yayi yace "Ka cigaba da zama kamar kurma a ɗakin nan dan in har kana son zaman lafiya da ni to tabbas ka bini yadda nake so don wallahi haushinka da nake ji na shekara da shekaru wannan ciwon naka ba zai saka ya goge ba balle ya hanani tafka maka rashin mutunci."

"To ka fita dani daga ɗakin mana kowa ya huta? Zaka iya kaini waje ka yasar ai." Baqeer ya samu kanshi da faɗan haka. Da mamaki Kamalu ya kalleshi don ko sanda Baba yake ji dashi bai iya mayar mishi da magana sai dai kawai ya tafi ba tare da ya kulashi ba. "Ni kake faɗawa haka?" Baqeer bai tanka shi ba ya ɗan harɗe hannunsa a kirji kawai ya lumshe ido, shi da Kamalun ma zai fita dashi ƙila da hakan yafi mishi sauƙi don rayuwar ta isheshi. Kamalu dama da fitarshi ya ɗan sha ƙwayar da suka saba sha, nan da nan idanunshi suka yi jaa ya miƙe ya janyo keken Baqeer ya fara neman saka shi akai, yana tunanin Baqeer zai bashi hakuri yaga ko kulashi bai yi ba, Kamalu na haki haka ya saka shi a kan wheelchair hankalin Baqeer a kwance yake babu alamun dana sani ko bada hakuri. Da yake a soro suke kai tsaye ya fita dashi waje ya fara turashi a keke cikin ƙarfi yana cewa "Ka nemi yafiyar abubuwan daka aikata mana ni da ƙanne na." Sam Baqeer bai da ma niyyar yin magana, takaici ne ya rufe Kamalu kawai ya ajiye keken nashi daga can gefe tare da ja baya yana cewa "Kasan Allah yau zan nuna maka ni mahaukaci ne in dai baka bani haƙurin abubuwan da aka yita yi mini a gida saboda kai ba, Baqeer bai ko kalleshi ba sai addu'a kawai da yake yi a cikin ranshi. Wani irin birki da aka taka da ƙarfi ne yasa hankalinsu ya tashi, Baqeer abinda ya faru dashi ne ya dawo mishi nan da nan zufa ta shiga keto mishi ta wanke mishi jiki, shi kanshi Kamalu tsoro ne ya rufeshi don gabanshi sai dukan uku-uku yake yi. Zainab dake cikin mota tana ta sauri saboda wayar gaggawa da Nabeela tayi mata itace ta ɗago kanta daga sityarin motar cikin wani irin ɓacin rai ta fito, kan Kamalu tayi wanda yake kallonta hankali a mugun tashe, bai yi auni ba yaji ta zabga mishi wani irin mari. A fusace yana haki yake kallonta yace "Ke? Baki da hankali ne?" Cikin faɗa take kallonshi ita ma kafin ta kalli mutumin dake kan wheelchair, ba dai yaron jiya bane? Kauda tunanin tayi daga ranta sannan ta matsa inda yake ta janyeshi daga kan titi ta ajiyeshi a gefe cikin ɗan duhun farkon dare take kallonshi tace "Me yasa kai baka rabo da haɗuwa da mutanen banza? In kasan wanda kake tare dasu basu da hankali me yasa ba zaka zauna a gida ba? Ko kana tunanin kai ba mutum bane dan baka da ƙafa? Ko kuwa kana tunanin kai kaɗai ne ke cikin mummunar ƙaddara da har kake yarda ana juyaka duk yadda aka so? Rannan ba kai bane mai bin mace tana wulaƙanta ka? Sannan yau ka ɗauko wanda yake son yin ajalinka ma gaba ɗaya? To ka sani in har ka bari rayuwarka ta salwanta ko ka mutu ba lallai irin waɗannan mutanen suyi maka addu'a ba, in ma zaka buɗe ido ka buɗe akwai mutanen dake cikin wani hali sama da kai." Bata ko jira amsarshi ba ta fara ƙoƙarin shiga mota, a fusace Kamalu ya nufota yana shirin fizgota, waigowa tayi cikin tsananin ɓacin rai ta nunashi da yatsa tace "Don't you dare! Wallahi ni ba sa'arka bace sannan daga ganinka ma ba a hayyacinka kake ba, useless kawai." Ta shige mota tana jan wani tsaki. Kamalu ji yayi ya kasa motsi don motar kaɗai daya gani yasan ba sa'ar yinshi bace, haka yaja Baqeer sam babu wanda ya sake cewa uffan har suka koma gida. Duk yadda Baqeer yaso ya cire kalaman yarinyar daga cikin ranshi ya kasa, duk wani motsi da zai yi kalamanta ne suke sake taso mishi, tabbas gaskiya ce tsagwaronta ta faɗa mishi, bazai yiwu ya maida kanshi nakasashe ba don kawai Allah ya ɗauke wani sashi na jikinshi don ya jarabce shi, in har bazai warke ba to fa dole ne ya koyi rayuwa da ƙaddarar data same shi…..

Me kuke tunanin zai faru? Ga dai Zeey ta tafi gida ana mata kiran gaggawa, ga kuma Baqeer ya fara tunanin canza rayuwarshi, Bello fa? Kuna ganin zaiyi nasara?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

#Baqeer #Shalele #Zeey #MBB # RayuwadaKaddara #Hawayena #UMMASGHAR #AYUSHERMUHD

*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*ƊANDANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SHA HUƊU*

https://www.tiktok.com/@maims_kiddies "Lallai Dr irin wannan kyau haka tamkar kunzo daga ƙasar UK? Gaskiya kayan jikin su Hanan sunyi matukar kyau, amma dai ba'a ƙasar nan kuka siya ba?" Cikin dariya Dr Aisha tace. "A ƙasar nan muka siya, sai dai kamar yadda kika ce ɗin haka ne, duk wannan kayan da kika gani a jikin yaran nan na ƙasar UK ne da *@Maims_kiddie* take sai da su a cikin Nigeria, muma a wajanta muka siya kuma ba tare da munje inda take ba, kayan na gani a Instagram account ɗin ta na *KIDS THRIFTY/OKRIKA STORE.* Kayane masu kyau da kwari daki bari kenan malam Khadija dan tun da na fara siyan kayan yara a wajanta shikenan na dena ganin kyawun na ko'ina. Kema/kuma zaku iya nemanta a Instagram link ɗin dake sama. Za kuma ku iya samunta a WhatsApp ta wannan link ɗin dake ƙasa. Ko lambar wayarta. https://Wa.me//08101378616

{14}

Wani irin ihu Kamalu ya saki tare da durowa daga kan gadonshi wanda hakan yasa Baqeer kallan inda yake, cike da mamaki yake yi mishi kallon zararre. Kamalu ya sauke ajiyar zuciya tare da sa hannu gefen fuskarshi ya ƙara faɗawa kan gado a fili yace "Dole na nemoki Roshni ɗi ta ai bansan soyayyar lokaci ɗaya tana yiwuwa ba amma gaba ɗaya kin gigitani, nasan marin nan ke kanki yayi miki zafi." Yasa hannu ya finciko pillow ya ƙanƙame yana juyi, kai kawai Baqeer ya girgiza don shi abinda ke gabanshi yafi shirmen nan. Wayar da Hadiza ta bashi ya ɗauka ya saka number Asiya kawai yana kallo, wani abu ne yaji ya taso mishi hakan yasa ya mayar da wayar ya ajiye tare da runtse idanunshi, Bello yake jira yazo ya faɗa mishi abinda Asiya tayi mishi don har yanzu ƙwaƙwalwarshi ta kasa ɗaukar abinda ke faruwa. Yana kallan Kamalu na ta ƙara kankame pillow yana mannawa pillow kiss lalai yau ya tabbatar kanshi ba ɗaya ba, takaici ne ya rufeshi kawai ya juya kai gefe.

***** Tun daga bakin gate Zainab tana parking ta hango Nabeela, tana tsayawa da motar ta ƙaraso da sauri tace "Zeey ya muka yi dake?" Maimakon ta tanka mata key ɗin motar kawai ta bata tace "Whatever! Ni raina a ɓace yake please." Da kallo Nabeela ta bita harta shiga ciki bata iya bin bayanta ba, A ƙofar shiga taga Mummy, kusa da ita kawai taje ta rungumeta tace "Mummy ni kam me yasa mutane basu da kirki ne?" "Ki ajiye batun mutane kin san yau me kika nemi ja mana a gidan nan kuwa? Tunda Dad ɗinki ya dawo yake faɗa, me nace miki akan in zaki fita? Ba nace ki tabbatar kin sanar min ba?" "Oh yeah! Na tuna amma inda naje yana da muhimmanci ba wai yawon banza naje ba Mummy kin dai sanni." Ajiyar zuciya tayi tace "Shi yasa nace ki dinga sanar mini ɗin ai tunda kin san Babanki ba yarda zai yi ba." Zata yi magana taji an daka mata tsawa "Uban wa ya baki izinin fita ba tare da sanina ba? Sannan tun kafin ki dawo ba na sanar dake ba ke babu fita ke kadai ba? Ko kina tunanin wasa nake yi?" Idanunta ne suka yi raurau tace "Dad nasan nayi laifi amma......" "Amma me? Ke wato ba'a isa a faɗa miki magana kiji ba ko? Daga dawowarki ko jira baza kiyi ma mu gama murnar zuwanki ba zaki dawo da halin naki ko?" Hawayenta ta share don tasan inta tambaya ma ko zata mutu ba barinta zai yi taje ba shi yasa ta sulale ta fita ta ɗauka zata dawo da wuri kafin ya dawo amma babban uzuri ya hanata, cike da faɗa yace "Wuce ciki kuma wallahi kika sake gigin fita ba da izinina ba kin san sauran don shirmen da kika yi a baya a unguwar nan da maganar da kika janyo mini a yanzu bazan sake ɗaukanshi ba." Idanunta ne suka ciko da kwalla tayi ɗakinta da gudu kawai ta faɗa kan gado, Mummy ce tabi bayanta tana shiga itama ta shiga ɗakin, kusa da ita ta zauna tasa hannu kawai tana shafa bayanta alamar lallashi, cike da takaicin abinda ya faru ta ɗago tana hawaye tace "Mummy nasan nayi laifi amma aƙalla a tambayi ina naje ko? Sannan asan dalilin daya sa na fita, ban san me yasa Daddy yake yi mini haka ba…." Hannu tasa a saman bakinta tace "Dalilin kenan, Zeey bakinki ba zai yi shiru ba? In mahaifinki na magana ba zaki yi shiru kice ayi hakuri ba? Kin bari ɗabi'ar turawa ta shiga kanki kin manta da wacce muka baki?" Kallan Mu8my tayi tana share hawayenta tace "Mummy kema kin san ba haka bane tun kafin na tafi karatu muke samun saɓani da Dad sam baya yi mini uzuri." Ajiyar zuciya tayi tace "Taurin kanki ne baya so, in har kika saukar dashi zaku zauna lafiya, sannan bakinki, ki taimaka ki daina faɗar duk abinda ya fito daga cikinshi." Kallon Mummy kawai take yi tama kasa magana sai hawaye kawai da take zubarwa, share mata tayi tace "Yanzu in kinaso ku shirya gobe Najib zai zo don sunyi magana da mahaifinshi ki tabbatar kin bashi hakuri kun daidaita, Zee dan Allah kar ki ƙara jawo mana matsala." Tana kaiwa nan ta miƙe ta fita ta bar Zeey a zaune kawai tana hawaye.

***** Abu ce ta shige cikin ɗakin ta yau kwanan Jamila ne tasan kuma yanzun nan zata lalaɓo ta fara ce mata ta bata kayan mata ita kuma yanzu babu abinda zata iya bata tunda dai kambun Fatima ya rushe dole ne ta ƙwace Malam ya dawo gareta. Daga waje take jiyo kiran da Jamila ke mata cikin magana irinta raɗa "Abu! Taimaka ki miƙo mini saƙon da Hajiyar Sokoto ta aiko miki." Kwafa tayi tasa hannu ta ɗauko gutsiran tuwon alkama da sukai, tasa a ƴar farar leda ta shiga murza tuwon sai da ya fashe sannan ta ɗauko zuma ta zuba a ciki ta sake murzawa kafin ta ƙulle ledar, fitowa tayi tana dariya tace "Ke ina can ina nemo miki maƙal-maƙal kina nan kina nemana." Washe baki Jamila tayi ta amshi ledar tace "Kai Abu Allah dai ya bar mini ke ya raya mana Kamalu mu sha biki." "Ameen gashi nan kisa da audiga kin dai sani abu shar kayan mu ba wasa." "Heee! Ai har wani tsuma nake dole mu dawo da Malam hanunmu." Tana faɗa tana fita waje cike da jin daɗin abinda ke faruwa "To kar dai muji ihun Malam yana sambatu." Jamila sheke da dariya jin kalaman Abu tace "Ke dai wlh baki ji kisa audiga a kunnenki." Ta ƙarasa maganar tana fita. Abu ta ja tsaki da harara tace "Banda rainin wayau ɗakin Baqeer kin ƙwace kin bawa ƴaƴan ki kin haɗa Kamalu na da shi yanzu kuma mijin kike son ƙwacewa, wannan kuma kin yi kaɗan wallahi." Ta juya tana cigaba da masifa a ranta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull