Baqeer complete - Chapter 10
Baqeer complete Chapter 10: Baqeer complete Chapter 10. Yadda Umma ke kallonta ne yasa gaba ɗaya jikin Hadiza yin sanyi cike da kulawa take bin Umma da…
3,262 words
Yadda Umma ke kallonta ne yasa gaba ɗaya jikin Hadiza yin sanyi cike da kulawa take bin Umma da kallo tace "Ba dai har lokacin tafiyar tasu Abuja yayi ba?" Umma zata yi magana suka jiyo salatin Bashir yana haɗawa da sunan Baqeer, cikin hanzari Umma ta miƙe ta fito ita ma Hadiza tabi bayanta, kafin su iso har Abu da Jamila sun fito, gaba dayansu ɗakin Baqeer suka nufa, a ƙasa suka ganshi ruwa duk ya malale a ƙasan, cikin sauri Umma ta ƙarasa kuda dashi tana cewa "Baqeer meya faru? Menene?" Kasa magana yayi sai hawaye kawai dake cigaba da taruwa a idanunshi, Bashir ta kalla tace "Me ya faru?" Yace "Ni ban sani ba na shigo zan ɗauki aron laptop ɗinshi na ganshi a ƙasa da alama ma ya daɗe da faduwa". Nan da nan Umma taji hankalinta ya tashi, Abu ta kalli Jamila kafin tace "To Fatima wannan fa ina ga sai dai ki sakashi kusa dake inba haka ba wani abun zai iya samunshi ba'a sani ba." Takaici ne ya kamata don tasan wulakancinsu ne ya tashi idan ba haka ba taya zasu ce ta mayar da Baqeer dakinta? Bata ko kulasu ba suka juya suna ƴan ƙananun maganganu, Bashir ne ya taimaka mata suka mayar dashi kan katifa sannan ya fita, Hadiza kam a ƙame take ƙam tana jin zuciyarta kamar zata fashe, me take gani haka? Meke faruwa? Gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta ta kasa gasgata mata abinda take gani, idanun Baqeer ne ya sauka kanta, sai a lokacin hawayenshi suka zubo ganin yadda take hawaye wani na bin wani, jan ƙafafunta ta shiga yi zuwa inda yake ta kama ƙafafuwan shi kawai tasa wani irin kuka, ganin haka yasa Umma ta miƙe ta bar musu ɗakin tana share ƙwalla, ta sani Baqeer kamar uba yake a wurin su ta daɗe tana tunanin yadda zasu ɗauki wannan abun, tafi minti goma tana kuka don har ƙarfinta na kukan ya fara raguwa kafin ta ɗago, kallonshi tayi kai kawai ya kauda tare da runtse ido, ta dawo inda yake tace "Yaya ba zai yiwu ba ka tashi kayi tafiya dan Allah! Na rokeka da Allah ka tashi kayi tafiya." Hannunta da tasa tana jan hannunshi ya kalla ya kai hannunshi na dama sai riketa yaji wani uban zafi ya maida hannun wanda hakan yasa ta kalleshi da sauri sai a lokacin ta kula da yanda aka naɗe hannun, a rikice ta sakeshi ta fashe da kuka tana cewa "Na shiga ukuna Yaya menene haka? Laifin me muka yi da Allah zai jarabce......" Hannu yayi saurin sawa ya rufe bakinta yana girgiza mata kai, hannu tasa ta goge hawayen idanunta tace "Meya faru Yaya? Yayan mu dan Allah ka tashi." Yawun bakinshi ya haɗiya don ko magana yanzu baya son yi, Baba da Asiya sun sake tabbatar mishi abinda yake tsoro. Bakinshi ya sake motsawa kafin yace "Mijinki fa? Babu dai wani abun ko?" Nan fa hawayenta suka ƙaru tace "Yaya wa ke tani kana cikin wannan halin? Yaya duk abinda nake ciki bai kai kwatan naka ba, na shiga uku." "Kin tabbatar ba wani abun?" Ji take yi kamar tayi ihu, wannan wani irin abu ne take fuskanta? Da gudu ta tashi ta bar ɗakin tana shiga ɓangaren Umma ta wuce ɗaki ta faɗa kan gado, shikenan su kuma sun zama marayu don dama Allah ne gatansu Baqeer gatansu, duk su biyun rayuwar auransu kowane na cike da kalubale amma babu wanda ya sani a gidan sai Baqeer saboda shi kaɗai ke saita musu komai ba tare da manya sun shiga cikin maganar ba, yanzu ya zasu yi? Kuka take sosai har ƙarar kukanta ya tashi yarinyarta Aydah dake kwance daga bacci. Umma ta shigo ta ɗauketa ta fita da ita don tasan dole Hadiza tayi kuka, samun Baqeer yasa su kwanciyar hankali wanda a koda yaushe take alfahari da yadda yake kula dasu.
******* Asiya ce kishingiɗe akan gado tana jin Inna da Habi nata aikin waina a waje amma tana kwance a ɗaki don ita sam bata son aiki ba kuma ta son girki especially da murhu, shi yasa tace gidanta inba gas cooker ba sai dai a siyo takeaway amma ba zata iya aikin hayaƙi ba. Waya take yi cike da fara'a, Habi ce ta shigo ɗakin sai gumi take yi na hayaki idanunta sunyi jaa ta shigo ɗaukan radion Inna ne data ara jiya da daddare, ganin Asiya tana waya yasa tace "Waye? Baqeer ne?" Asiya ta kauda kai alamun a'a sannan tace "Yanzu kana Abujan?" Daga jin haka yasa Habi ta matsa tasa kunnenta gefen wayar tana son jin abinda ke faruwa, Asiya tace "To shikenan Bello Allah ya bada sa'a sai ka dawo." Miƙewa Habi tayi tana wa Asiya kallon tuhuma harta kashe wayar, cike da mamaki tace "Bello kuma? Yaushe kuka fara waya akai-akai haka? Don jiya ma naji sanda ya kira yace miki kiyi mishi addu'a wai zai yi tafiya." Tsaki Asiya tayi tace "Koma yaushe muka fara menene damuwarki a ciki? Kawai kirana yayi yace in sakashi a addu'a akwai abinda yaje yi Abuja yana so Allah ya bashi nasara shikenan sai nace bazan yi ba?" "Ji wani munafurci, addu'ar iyayenshi bata isheshi ba sai ya haɗa da taki? Ko sanda Baqeer yake nemanki a waya kin ɗaga ne? Wallahi dai kunji asara daga ke har shi in ma wani abun kuke tunani, aikin banza kawai." Tana kaiwa nan ta juya ta ɗauki radio ɗin ta fita a fusace ranta a mugun ɓace, baki kawai Asiya ta taɓe don ita ƙarfin halin Habi har mamaki yake bata.
******* Da ƙyar Hadiza ta saki ranta, jin shirunta yasa Umma ta shiga ɗakin ta zauna kusa da ita ta sanar da ita duk abinda ke faruwa, ta kalleta a rikice tace "Yanzu suna nufin shikenan ya rasa ƙafafuwan shi?" Kai Umma ta ɗaga tace "Addu'a ce tamu amma haka suka ce." Ta goge hawayenta wanda idanunta har sun ƙanƙance saboda kuka tace "Umma ɗazu fa da alama ruwa yaje sha ya faɗo dan ga jug na ruwa nan a ƙasa, kina nufin haka zai dinga rayuwa?" "Wanda kuma Allah ya halicce shi a haka fa? Wanda kuma Allah ya jarabceshi da rashin ƙafa? Hannu da ido fa? Ko kuwa wanda Allah ya jarabceshi da ciwon da baisan inda yake ba fa? Ba haka suke cigaba da rayuwa ba?" Hadiza tayi ƙasa da kai don ita kam bata san me zata ce ba "To ya zamu yi? Mun isa jaa da hukuncin Ubangiji ne?" "Bamu isa ba sai dai ina ganin mu samu wani ya dinga kula dashi bazai iya zama shi kaɗai babu mai taimaka mishi ba." Hadiza tayi maganar cike da jin tausayin ɗan uwan nata. "To Hadiza in mun samu wani waye zai dinga biyanshi?" Umma tayi maganar tana kallonta, nan ta dago tana jin zuciyarta na zafi ace duk abinda yayansu yayi musu yanzu su lokacin rama mishi yayi amma babu hali? Ita mijinta ba mai babban karfi bane gashi kullum cikin rigima suke dashi saboda ba ita kaɗai bace a wurinshi gashi baya son haihuwa tunda suka yi aure bata dade da samun ƴan biyunta ba ya fara ito mata da halayenshi sai gashi kuma babu daɗewa ta ƙara samun cikin Aydah anan ne yace sai dai taje asibiti a zubar ita kuma tace sam, haka suka yi ta rigima data so yin yajin Baqeer ya daidaita su, sai autar Umma Maryam ita kuma mijinta dan kasuwa ne yana da kuɗi kuma yana kyautata mata bakin gwargwado sai dai matsalar uban miji wanda ya addabeta ya hana samun zaman lafiya da mijinta, gaba ɗaya zaman aurenta bata sati ɗaya ko biyu sai Baqeer yaje yayi sulhu akan saɓanin da uban mijin ke haddasawa a tsakanin su. Jin kalaman Umma yasa Hadiza tayi shiru, shikenan su babu yadda zasu yi? Miƙewa tayi ta koma wajen Baqeer ta gyara ƙasan ɗakin ta dawo ɗakin Umma ta ɗauki drawer ɗinta ta gefen gado ta kai ɗakin tasa kusa da inda katifarshi take tasa aka siyo ruwan pure water tasa a saman drawer ɗin, sannan tasa spoons da plate da wasu ruwan a cikin drawer ɗin, ta ɗauko papers da pencils tasa a na ƙasa nan ta fara kale-kale tana neman wasu abubuwan da zai buƙata, duk abinda Hadiza take yi idanun Baqeer na kanta, kallonta kawai yake yi don kwanan nan sam baya jin magana mutuwa kawai yake jira tazo ta ɗauke shi, ɗazu ma daya faɗi shi yasa ko ƙira bai yi ba azo a taimaka mishi, jira yake yana daga kwancen nan rai yayi halinshi, sai gashi nan garau sai ma wani tashin hankalin daya sake shiga. Wayarta ta ɗauko kawai ta cire sim ɗinta na mtn ta bar airtel a ciki ta ajiye kusa dashi tace "Yaya ga wayata sim ɗin bana amfani dashi data kawai nake siya idan na samu dama, Umma tace an sace maka waya dama kaine ka saya mini ita kaga yanzu sai ta dawo wurinka, ina zaka iya rayuwa babu waya babu aikin daka saba babu komai a ɗaki? Sannan anjima Salim zaizo sai mu turaka tsakar gida ka dinga samun iska kana shaƙa ba wai kullum kana ƙunshe a ɗaki ba." Wayarta ya miƙa mata kawai ya girgiza kai alamun a'a cikin dakewa ta girgiza kai tace "Don Allah Yayah ka rufa mana asiri kaine gatan mu, wannan rashin maganar Yaya baza mu iya ɗauka ba ka taimakemu ka dawo yanda kake kar baƙin ciki yayi maka illa don Allah!" Murmushi yayi na yaƙe, ta sake miƙa mishi wayar sannan ta fito, kallon wayar yayi yana ji kamar ya kira Asiya sai dai inaa bazai iya ba don shi yanada zuciya baya zama inda ba'a sonshi, balle yanzu da yake neman komawa ga Allah, hakan yasa ya ajiye mata wayar a gefe. Hadiza tana fitowa ta ɗauki wayar Umma ta kira Maryam tace Inda hali tazo gida in ta dawo daga ɗauko Areef daga makaranta. Ba tare da wata damuwa ba tace to zata biyo.
***** A hankali Zainab ke buɗe ido tana rufewa, kallon agoggo tayi ganin azahar har tayi yasa ta yin miƙa sannan ta mike, wayarta ta duba ganin missed calls tayi kusan guda goma, tsaki tayi sannan ta duba text ganin saƙo ne daga number ta duba, da alama yaron jiya ne dan bakaken maganganu yake faɗa mata akan ta zubar mishi da mutunci tasa yanzu ana yi mishi dariya. Baki ta taɓe sannan ta kira number, bugu ɗaya ya ɗauka tana jiyo alamun mutane daga gefe ana cewa "Yess karka barta." Nabeela ce ta shigo ɗakin ɗauke da kayan da aka aiketa ta siyowa Zeey na lotions ɗinta wai ta manta da nata acan, Zeey tana kallon Nabeela tace "Yes Jamal inaji!" "Najib!" "Oh Alhaji Najib!" "Ki bani haƙurin abinda kika yi mini sannan ki faɗawa friends ɗina wasa muke yi bawai da gaske muke ba." "Wai dama shine dalilin kiran? Okay! Friends hope kunji? Sannan please Jamal next time in zaka wurin budurwa dress properly, I mean dress like a real guy please." Tana kaiwa nan ta kashe wayar tare da blocking number ɗinshi. Nabeela ta girgiza kai tana ajiye kayan kan dressing mirror tace "Zeey please ki bar wulakanta mutane." "Wai gaskiya ce ban isa na faɗa ba? Ni ban wulakantashi ba abinda ke raina kawai na faɗa bana ji kuma laifi ne don nayi hakan" Shiru kawai Nabeela tayi don tasan ba'a cin Zeey a magana, miƙewa tayi tace "fita zan yi idan nayi sallah, bani car key ɗinki please bana so Dad yasan bana nan ba dadewa zan yi ba." Kamar zata musa sai kuma ta bata, da sauri ta shiga toilet bata dade ba ta fito ta shirya cikin English wears riga doguwa har gwiwa da wando, tayi sallah sannan ta miƙe tace "Ki zauna a ɗakin please kafin a nemeni in kika ga zata kwaɓe ki faɗawa Mum da wuri, bye." Bata ko jira taji amsarta ba ta fice. Saman kanta kawai Nabeela ta shafa. ita kam tasan watan maida ita baiwa yayi don Zeey maidata take kamar wata ƴar aikinta bayan ita kanwar mahaifiyarta ce kawai dai Zeey ɗin ta girmeta ne da wata shida. Zeey tana fara tafiya suka yi kiciɓis da wata mota, kallin juna suka yi cike da mamaki wanda hakan yasa kowa yaja gefe yayi parking, da sauri Zeey ta fito ta ƙara so jikin motar ɗayar, itama ta fito suka rungume juna cikin jin daɗi cike da mamaki tace "Wai ya aka yi kika ganeni? Ashe rai kanga rai?" Zeey tana dariya tace "Maryama Daso tawa, da gaske dai kece ni kuwa in ban ganeki ba a duniya ai duka za ayi mini, daga ina kike?" Tayi maganar tana kallon bayan motar ganin yaro a ciki yasa ta buɗe baki tace "What?" Maryam tasa dariya tace "Ehen ke fa?" "Inalillahi yaushe kika yi aure har dasu haihuwa?" Dariya tayi tace "Kinsan last mun haɗu dake sanda naje graduation na brother ɗina a Buk to lokacin ban ƙara 1year ba nayi aure." "Inalillahi I just can't believe it, how?" "How kamar ya? Ke fa? Kina nan kina neman maganar taki da kika saba?" Zee zata yi magana suka ji horn daga bayansu sai a lokacin suka kula da yanda Zeey tayi parking, dariya suka yi Zeey tace "I just hate naga mutane ba haƙuri, ya ɗan jira kaɗan mana." "Madam kin san uzurinshi ne? Halinki na nan dai ashe." "Hmm share kawai kin ji, Umma fa? Ina Umman mu?" "Tana nan bayan sam kin manta da ita tunda kuka tashi ko leƙota bakya yi." Fuska ta tsuke tana juyawa alamar zata tafi tace "Kin dai san dalili ai daga nan kuma ban san ya akayi ba zumunci ya watse." Dariya sosai Maryam tayi tace "Wai har yanzu baki manta ba? To kizo muje am sure Ya Baqeer na gida ku gaisa shi ya manta." Tsaki taja tace "Allah ya sauwake ni yaushe rabon dana ganshi ai ko a lahira kowa ya kama gabanshi, nifa banda yayanki ne da ɗan Umma wallahi da...." Sai kuma tayi shiru tana cewa "Zan aika a amsomin numberki wurin Umma tunda muna kan hanya." Kai Maryam ta gyada nan ta tuno abubuwan da suka faru shekarun baya wanda yasa ta murmushi da girgiza kai kafin ta shiga mota. Areef ne cikin gwaranci yace "Mamy itama ƙawar kice?" Ta ɗaga kai tana dariya tace "ƙawata ce sai dai ƙawancen da bai yi nisa ba." Ta ƙarasa tana tada mota cike da mamakin yadda aka yi Zainab ta ganeta da wuri haka wasu abubuwa na sake dawo mata waɗanda ta tabbatar nisantar junansu shine abinda ya kamata. Nan ta ƙarasa gidansu....
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
#Baqeer 🦼 #MBB #Asiya #Rayuwa da Kaddara #Nakasa #Hawayen rayuwa
Na Ummu Asgar Da Ayusher Muhd
*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*
*ƊANDANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA UKU*
https://www.tiktok.com/@maims_kiddies "Lallai Dr irin wannan kyau haka tamkar kunzo daga ƙasar UK? Gaskiya kayan jikin su Hanan sunyi matukar kyau, amma dai ba'a ƙasar nan kuka siya ba?" Cikin dariya Dr Aisha tace. "A ƙasar nan muka siya, sai dai kamar yadda kika ce ɗin haka ne, duk wannan kayan da kika gani a jikin yaran nan na ƙasar UK ne da *@Maims_kiddie* take sai da su a cikin Nigeria, muma a wajanta muka siya kuma ba tare da munje inda take ba, kayan na gani a Instagram account ɗin ta na *KIDS THRIFTY/OKRIKA STORE.* Kayane masu kyau da kwari daki bari kenan malam Khadija dan tun da na fara siyan kayan yara a wajanta shikenan na dena ganin kyawun na ko'ina. Kema/kuma zaku iya nemanta a Instagram link ɗin dake sama. Za kuma ku iya samunta a WhatsApp ta wannan link ɗin dake ƙasa. Ko lambar wayarta. https://Wa.me//08101378616
Maryam sai data kusa isa gida ta duba jakarta, takaici ne ya kamata ganin naira ɗari biyar ce kaɗai a ciki, ajiyar zuciya kawai tayi tare da yin parking sannan ta fito da Areef suka nufi cikin gidan, tun daga soro zaka jiyo hayaniyar Baba yana magana cikin faɗa, da yake tasan halin Baba sai bata yi wani mamaki ba, ta tabbatar Kamalu ne ko Bashir ko kuma Salihu wani a cikinsu ne ya taɓoshi tunda yara matan gidan daga wanda yayi aure sai wanda suke boarding school. Ta ƙara yin taku ɗaya taji Baba ya ambaci sunan Baqeer, cike da mamaki ta shiga cikin gidan, Hadiza ta hango jikin bango banda hawaye babu abinda take yi, Abu da Jamila suna tsaye daga jikin ƙofar ɗakunan su suna kallon abinda ke faruwa, Umma ce a gaban Baba wanda hakan ya tabbatar mata da Umma ake faɗan, mamaki ne ƙarara ya bayyana a fuskarta jin Baba yace "Kin san Allah Fatima ki fita idona, idan har kika bari na sake magana to tabbas zaki tsinci kayanki dana ɗanki a waje, ni zaku maida soko? Kuna nufin ni da gidana ban isa inyi hukunci ba? To ni nace Baqeer ya tattara ya koma ɗakin Kamalu ya zauna shi kuma Bashir da Salihu su dawo nan, hakan ba adalci bane?" Fatima ta share kwallarta tace "Bance ba adalci bane amma sai yanzu Malam? Ka manta sanda kasa aka gina ɗakin nan da kaina nace ka haɗa mazan nan bibiyu wuri ɗaya me kace min? Cewa fa kayi Baqeer ba zai haɗa ɗaki ɗaya da kowa ba, kai baka son a dinga ɗauke mishi hankali da shirme gwara yayi zamanshi shi kaɗai zai fi maida hankali akan zanen shi, ko ka manta tsakar gidan mu ka rage ka gina ɗakin saboda shi shi kaɗai? Kayi mishi ban ɗakin shi a ciki?" "To nace yanzu na janye? Ko ke kika bani kuɗin dana yi ginin? Tunda har yaron nan ya tozartani ya wulakantani kema ai kinsan dole ku kwashi kayanku a hannu ko?" Zata sake magana ya ɗaga mata hannu yace "Na dai faɗa miki, kima barni naji da yanda zanyi na maidawa Yallabai kuɗin shi da muka cinye, sannan ki barni da dana sanin yanda na sadaukar da rayuwata kan yaron da ba wata rana da zai yi mini." Cike da mamakin kalaman da Maryam keji take shigowa cikin gidan tace "Baba? Ya Baqeer ne fa?" Wani mugun kallo yayi mata ya maida kallonshi kan Umma da banda hawaye babu abinda take yi ya cigaba da cewa "Ki kuma sanar da yaranki wallahi duk wacce tayi gigin dawo mini gida da sunan yaji ko mutuwar aure sai dai ta shiga duniya ba dai ta zauna a gidana ba, sannan kafin naje na dawo ku tabbatar kun ɗauke shi daga ɗakin." Yana kaiwa nan ya juya ya fita yana balbala masifa, ranshi gaba ɗaya yau a ɓace yake tunda ya kunna radio yaji ana maganar gasar da za'ayi gobe a Abuja da yanda masu gasar suka hallara suna masaukinsu. Ji yake yi zuciyarshi kamar zata fito saboda ɓacin rai, shekara guda kenan da turawan suka shigo da maganar gasar kuma shekara guda kenan yana shirin gasar nan amma gashi da ranshi da lafiyarshi abu ya gagara.