Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 9

Baqeer complete - Chapter 9

Baqeer complete Chapter 9: Baqeer complete Chapter 9. Murmushi tayi mai ciwo ganin yadda maigidan nata ya ware murya yana yi musu tijara a tsakar gida…

2,818 words

Murmushi tayi mai ciwo ganin yadda maigidan nata ya ware murya yana yi musu tijara a tsakar gida kamar ba shine wannan uban dake ji da Baqeer yana lallaɓashi ba amma yanzu saboda ƙaddara ta sameshi shine na farko wajen juya mishi baya babu tausayi bare tausayawa halin da yake ciki shi dai damuwarshi kawai burinshi ne da ba zai cika ba. Sai da ta gyara tsayuwarta sannan tace "Amma Mallam idan ka hana Salim shigowa wajen Baqeer waye zai tallafa mishi wajen yin buƙatun da dole yana buƙatar mataimaki, kasan dai ni mace ce akwai larurar da dole sai namiji ɗan uwanshi ne zai taimaka mishi da ita kuma shi Salim ɗin da baka son ganinsu tare shi kaɗai ne yake tallafa mishi a irin waɗannan lokutan kaga kuwa ko don wannan ai baka rabasu ba tunda dai mu muke amfana dashi ba shi yake ƙaruwa damu ba."

Tsaki yayi cikin ranshi yana ganin kuma fa haka ne dole Baqeer ɗin yana buƙatar mataimaki gara ya bar Salim ɗin yaci gaba da kula dashi tunda dai yaji ya gani shi yasa kanshi ba wani ya saka shi ba don haka yace mata "Shikenan yana iya zuwa ko don kula dashi ɗin amma sai a kula da fita dashi waje don bana so."

Sai a sannan Baqeer ya ɗago kai ya kalli mahaifinshi yana tunanin dama haka yake ko kuwa wannan ƙaddarar data sameshi ce ta mayar dashi hakan, a tunaninshi ko kowa ya juya mishi baya banda mahaifin shi mi ji dashi mai tsanani so da ƙaunar farin cikin shi, sai dai kash mutanen duniya ba'a ci musu alwashi don baka sanin asalin kalarsu sai idan wata ƙaddara ta afka maka sannan suke bayyanar maka da asalin ɓoyayyiyar fuskarsu.

***** #Baqeer🦼 #RayuwadaKaddara #Hawayena #Samudarashi #UmmuAsgar #Ayushermuhd

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

Umm Asghar Ce Da Ayusher Muhd

*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*ƊANƊANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA ƊAYA*

Da taimakon Umma Baqeer ya koma ɗakinshi. Abincin shi ta fita ta ɗauko sai dai ko kusa ya ƙi yarda ya sanya ko loma ɗaya a bakinshi don halin da ya tsinci kanshi a ciki yafi gaban ya iya sakawa cikin shi wani abu, haka tayi ta lallaɓa shi da ban haƙuri da nasiha akan ya daure yaci ko kaɗan ne amma ya kasa, haka nan ta haƙura ta ƙyaleshi ganin duk yadda tayi dashi ya ƙi karɓar abincin da take kaiwa bakinshi, sai da ta tabbatar baya buƙatar komai kafin tayi mishi sallama ta fita daga ɗakin taja mishi ƙofar ta rufe. Tana fita hawayen da yake ta riƙewa suka samu sararin zubowa, idanu ya kai kan ƙafafun shi da ko kaɗan baya jin alamun su a jikinshi, shi kenan shi yanzu haka zai yi ta zama ya nakasa ya zama musaki ba zai iya ƙara amfanawa kanshi komai ba sai dai ayi mishi. Sai ƙoƙarin ɗaga ƙafafuwan yake yi amma ya kasa, yayi-yayi ya motsa su ko yaya ne abu yaci tura. Hannunshi mai lafiyan yasa yayi ta dukan ƙafafun ko zai ji wani feeling nan ma babu abinda yake ji.

Wani irin ihu yasa yana cewa "Nooo..." haɗe da dukan ƙafafun da yake jin su tamkar ba a jikin shi suke ba da ƙarfi. Duk mutanen gidan babu wanda bai ji ihun da yake yi ba don haka duk suka firfito daga ɗakunansu suna kallon ƙofar ɗakin Baqeer ɗin sai dai babu wanda ya iya ƙarasawa ya duba halin da yake ciki. Kamalu ne yaja tsaki yace "Wannan hala bayan gurguncewar harda matsalar ƙwaƙwalwa ya samu ba'a sani ba, shine aka kawo mana mahaukaci cikin gida aka ajiye" babu wanda yayi magana sai ma kallonshi da suka yi suna gasgata hasashen da yayi a cikin ransu.

Umma ce ta fito daga ɗakinta sanye da hijabi don duk abinda ake yi tana jin su hankalinta kuma yana wajen ɗanta sai dai ba zai yiwu ta katse sallar da take yi ta fito ba. Suna ganin ta Kamalu ya saki wani ɗan iskan fito cikin magana irinta ƙauraye yace "Yauwa da Allah in kin shiga sai ki faɗawa mahaukcin ɗanki bashi kaɗai bane a gidan ya ɗan sassauta murya haka nan ko don muna so mu kwanta muyi barci, ah to." Ko kallonshi bata tsaya tayi ba ta faɗa ɗakin Baqeer a gaggauce tana cewa "Baqeer lafiya kake kuwa? Ko wani wajen ne yake yi maka ciwo?" Ta ƙarasa kan katifar ta zauna sannan ta rungumo kanshi a jikinta tana shafawa kamar mai lallashin ƙaramin yaro. Jin shi a jikin Ummanshi yasa ya fashe da kuka mai tsanani, kuka irin wanda tunda ƙaddarar rasa ƙafafunshi ta afko mishi bai samu yayi kamar shi ba. Kuka yake yi yana shesheƙa abun tausayi kamar ba saurayin nan ɗan kwalisa mai ji da kyau da iya ado ba, matashi mai tsayuwa da ƙafafun shi ya nemi na kanshi abun alfaharin kowanne iyaye.

Ita kanta Umma kukan take yi don tasan yanzu ne Baqeer zai san mecece rayuwa, yanzu ne zai san asalin masoyanshi na gaskiya da masu yi mishi soyayyar bogi don ba kowa ne zai karɓi ƙaddararshi a yadda tazo musu ba, tasan da yawan mutane yanzu gudunshi zasu yi shi yasa take ƙara tausaya mishi tasan ɗaukar dangana ba abu ne mai sauƙi ba a wajen shi yanzu. Sosai yayi kuka mai yawa kafin ya tsagaita da kukan ya ɗago kai ya kalleta suka haɗa ido sai yaga ashe itama hawayen take yi, hannu yasa ya goge mata hawayen yace "Shikenan ni yanzu bani da wani amfani Umma kowa guduna yake yi saboda na zama gurgu, har Baba da ya kasance mahaifina ba zai tausaya mini ba da ƙaddarar data sameni? Yanzu tsakani na dashi sai kyara da hantara kamar ba shine wannan Baban mai yawan nuna mini soyayya da tattalin farin cikina, ashe mutanen duniya sai kana da wani amfani da zaka yi musu suke sonka daga inda ka rasa duk wata dama taka sai kowa ya juya maka baya," sai ya ƙara fashewa da kuka don wani irin ciwo yake ji a cikin zuciyarshi, ji yake yi da zai iya babu abinda zai hanashi fincikota ya jefar ko ya huta da azabar raɗaɗin da take yi mishi.

Kanshi ta dafa cikin sigar lallashi tace "Kayi haƙuri Baqeer kowa da kake gani da yadda ƙaddara take zuwa mishi ba kuma ka taɓa sanin asalin masu ƙaunarka sai idan wata ƙaddara ta same ka, mahaifinka ba gudunka yake yi ba ya dai kasa karɓar ƙaddarar data same ka yayi haƙuri ya gane cewa komai daya faru nufin Allah ne, babu wani daya isa ya tsara maka rayuwa face abinda Allah ya hukunta zai sameka don haka nake jan hankalinka daka cire damuwar komai daga ranka ka sanya dangana a cikin ranka, nakasa ba kasawa bace jarrabawar rayuwa ce." Haka nan dai tayi ta mishi nasiha har ta samu ya daina kukan ya koma sauke ajiyar zuciya kawai cikin hukuncin Allah kuma sai bacci mai nauyi ya ɗauke shi, ganin da tayi ya samu bacci sai ta gyara mishi kwanciyar shi ta mayar mishi da kanshi akan pillow ta janyo abun rufar shi ta rufe shi, sai da ta tofe shi da addu'a sannan ta tashi ta kashe mishi fitila ta fita.

Tana fitowa suka haɗa ido da Baba dake tsaye a ƙofar ɗakinshi ya kalmashe hannu a ƙirji yana watsa mata wani irin wulaƙantaccen kallo, ashe duk abinda ke faruwa yana ji bai dai yi niyyar fitowa bane sai da yaga lokaci yaja Fatima dake da girkin ranar bata je ɗakin shi ba sannan ya fito. "Saboda nakasashe musakin ɗanki kika bar ni ina jira har yanzu?" Ya watso mata tambayar cikin faɗa tamkar ya mance dare ne yanzun komai ƙanƙantar sauti ɗauka yake yi. A sanyaye ta ƙaraso daf dashi sannan tace a taƙaice "kayi haƙuri" don bata son jan magana mai tsawo a tsakaninsu, tasan halinshi sarai ba haƙuri ne dashi ba don ya kwana yana yi mata tijara ba damunshi yayi ba ita kuwa yanzu bata da lokacin biye mishi suyi tashin hankali damuwar halin da ɗanta yake ciki ne a gabanta. Har ta wuce shi ta shige ɗakin nashi ta karkaɗe gado ta hau ta kwanta bai shigo ba, sai zuwa can kuma har bacci ya fara ɗaukarta taji motsin shigowar shi ɗakin.

***** A guje Mummy ta rungume Zeey cikin tsananin murna itama ta ƙanƙame ta, Nabeela dake gefe tana kallonsu ta girgiza kai tace "Aunty na ɗauka kunnenta zaki ja? Kinga abinda ta yiwa guy ɗin nan kuwa?" Hararar Nabeela tayi tace "To kanwa uwar haɗi, har wani abu ma nayi mishi?" Mummy zata yi magana suka ji ana kwallawa Zeey kira cikin magana mai sauti, Kabir ne shiyasa basu wani ɗagawa kansu hankali ba har ya ƙaraso, kallonta yayi cike da masifa yace "Kina nufin abokina kika yiwa kallon driver? Kika wulakantashi a gaban mutane? Kalli..." Yayi maganar yana nuna mata wayarshi inda da alama wasu ne suka ɗauki video ɗin abinda ya faru suka watsa a social media. "Calm down bro, meye kake exaggerating ɗin abun haka wai? Chill out!" Takaici ne ya sake rufeshi yace "Kinsan Allah zan zabga miki mari, ina miki faɗa kina cemin wani chill out?" "To chill in shikenan?" Kallon Mummy yayi yana ji kamar ya shaƙota ya zabga mata mari, Mummy ta ɗan murmusa tace "Ya haƙuri Kabir am sure ba da saninta tayi ba, kayi haƙuri kaji? Kema bashi haƙuri." Huci Zeey ta saki kafin tace "S" Kabir ji yai kamar yayi hauka don takaici, a fusace ya bar parlourn yasan shi kenan yanzu zaman gidan zai fara bashi haushi don sam yarinyar nan ta gama rainashi. Harararta Mummy tayi tace "Me kika yii haka?" Tace "Ban fa sani ba, na ɗauka driver ne." Daga waje suka jiyo shigowar motar Dad cike da jin daɗin dawowar Zeey.

A ɓangaren Bello kuwa tunda ya samu aka kirashi zuwa wajen deputy gwamna gashi har an mayar da sunanshi a madadin na Baqeer a matsayin wanda zai wakilci Jihar Kano a wajen gasar da za'a yi yake murna. Shi dai kam yasan kakarshi ta yanke saƙa, ya taki sa'a irin wacce bai taɓa zaton zai samu ba a rayuwa, wannan accident ɗin na Baqeer ai shi aka yiwa don a komai Baqeer ɗin na gabanshi gashi yanzu cikin ruwan sanyi ya samu abinda ya daɗe yana mafarkin samu. Fifikon da Baqeer yayi mishi na matuƙar baƙanta mishi zuciya ganin dai harkar zanen duk ita suke yi hasali ma ita ce ta fara haɗa su abota sai dai kafin a ambace shi a waje sai an fara kiran Baqeer kafin a ambace shi sau ɗaya an ambaci Baqeer sau babu adadi, duk wani alheri daya tunkarosu to wajen Baqeer yake fara zuwa kafin su, a komai sai dai ya samu sauran Baqeer, abinda yake baƙanta zuciyarshi don a ganinshi Baqeer bai fi shi da komai ba sai tsantsar sa'a da tsayayyen uban dake tayashi wajen faɗi tashin ganin ya cimma burinshi.

Shirye-shiryen tafiyarshi Abuja kawai yake yi inda anan ne za'a yi gasar da za'a zaɓi waɗanda suka yi nasara a ɗauki nauyin faɗaɗa karatunsu a harkar zane a ƙasashen ƙetare. Yana ta shirin shi ba tare da ya bari wani daga cikin abokansu yasan shi zai tafi a madadin Baqeer ba don baya ma so kowa ya sani har sai yaje yayi abinda ya kaishi ya dawo inda yake fatan nasara ta zama tashi, a lokacin ne zai nunawa duk masu cewa Baqeer yafi shi da masu cewa baya iya yin zane sai da taimakon Baqeer ko shi waye, a lokacin zasu yi dana sanin wulaƙanci da cin fuskar da suka yi tayi mishi suna nuna mishi iyakarshi suna ganin shi ba kowa bane.

***** Har aka kwana biyu Baqeer na ƙunshe a ɗaki baya fitowa ko tsakar gida bare ya fita waje dama kuma yana da banɗakin shi a cikin ɗaki don haka ya ƙara takure kanshi da zaman ɗakin don sosai yasa maganar Baba a ranshi ta kada ya ƙara ganinshi a waje don kada mutane su ganshi ayi mishi dariya. Inda Allah ya taimaka ma kullum Salim ke zuwa safe, rana da dare yana taimaka mishi wajen turashi zuwa banɗaki ya taimaka mishi yayi wanka da duk wasu ƴan buƙatocin shi dai amma haka Salim zai zo ya ƙari maganarshi Baqeer ba zai ɗaga kai ya kalleshi ba bare ya tanka mishi sai dai ko kusa hakan bai taɓa damunshi ba sosai yake yi mishi uzuri tunda yasan da can ba haka yake ba yanayi ne kawai ya mayar dashi hakan.

Yau Umma na wankin kayanta dana Baqeer da suka yi datti, wankin da a baya ta manta yadda ake yi don kayanta na yin datti Baqeer zai haɗa ya fita dasu sai dai ya kawo mata a wanke a goge iyakaci ta shirya a cikin wardrobe amma gashi yau kuɗin sabulun da zata yi wankin ma da ƙyar ta samu Baba ya bata bayan ya gama sauke mata kwandon tijara akan shi fa ba zai iya da tsirfarta ba idan ma zata nemi abun yi gara ta nema don bai ɗaukewa sauran matan shi sabulun wanki dana wanka ba ba zai fara a kanta ba.

"Umma yau da kanki kike wankin da tsakar ranar nan? Ina Yaya Baqeer ɗin bai samu ya fita dasu ba?"

Jin maganar yasa ta ɗaga kai tace "Hadiza? Yau kece da safen nan?" Shigowa tayi tana sallama Hadiza, ƴarta ta biyu ce wacce ke bin Baqeer, tana shigowa tana cewa "Umman mu abin ne ya bani dariya kece da wanki?" "Da kaina nake yi Hadiza, ku shiga daga ciki yanzu zan ƙarasa na shigo nima."

Bata shiga cikin ba sai ma saka hannunta da tayi a bokitin wankin tana cewa "Kawo na ƙarasa miki Umma ki zauna ki huta kema."

"To kuma daga zuwanki ko zama baki yi kin huta ba sai ki kama wanki?"

"Idan ban yi miki ba Umma wa zan yiwa, don Allah ki bari na ƙarasa, gashi naga ma ƙarashe ne wankin naki." Haka nan ta sakar mata kayan ta ɗauki jakarta da ƙaramar ƴarta data yaye suka shige ɗaki, sauran abincinta na safe ta ɗaukowa yarinyar ta zauna tana bata a baki kamar tasan da zuwansu dama. Ai kuwa yarinyar ta ware ciki tana cin abinci sai kace kuncen yunwa, tas ta cinye abincin duk kuwa da yana da ɗan yawa, ita kanta Umman tayi mamakin yadda yarinyar ta cinye abincin tas ga alama daɗaɗɗiyar yunwa ce a jikinta, ganin ta fara gyangyaɗi yasa ta miƙe ta ɗebo ruwa ta bata ta sha sannan tasa zani ta goyata, kafin wani lokaci har bacci ya ɗauketa. A daidai wannan lokacin Hadiza ta shigo, ganin ƴarta a baya yasa tace "Wannan ƙatuwar yarinyar kika goya Umma salon ta saka miki ciwon baya?"

Harararta tayi tace "Ina abun girma a wannan ƴar yarinyar da bata haura shekara biyu ba banda dai lalaci da yayi muku yawa ba kwa son goyo." Zama tayi akan doguwar kujera ƙwaya ɗaya dake ɗakin Umman wacce Baqeer ne yasa aka yi mata ita tana dariya. "Umma ina yini? "Lafiya lau Alhamdulillah, duk ƙalau kuke? Ya yaran?"

"Lafiya ƙalau Alhamdulillah, kwana biyu bamu gaisa ba gashi ni wayar tawa akwai da babu sunanta ina ta roƙon ya bar ni nazo ya hana sai yau Allah ya nufa ya barni nazo a hakan ma wai kada na kai yamma, Allah yasa dai Yaya Baqeer na nan don ina son ganinshi." Kallo ɗaya zaka mata kasan cikin damuwa take, gaban Umma ne ya ɗan faɗi, Allah dai yasa ba wani abin bane mai girma itama tazo dashi?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

#Baqeer #Shalele # RayuwadaKaddara #Hawayena #UMMASGHAR #AYUSHERMUHD

Umm Asghar Ce Da Ayusher Muhd

*BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*DADANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA BIYU*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull