Baqeer complete - Chapter 8
Baqeer complete Chapter 8: Baqeer complete Chapter 8. ****** Zainab ce tai wata irin miƙa sannan ta cire abinda ke rufe da idanta na sleeping mask, tunda…
3,283 words
****** Zainab ce tai wata irin miƙa sannan ta cire abinda ke rufe da idanta na sleeping mask, tunda ta shiga jirgi take bacci sai dataji an tsaya ta farka, kallan waje tai sannan ta ɗan saki murmushi, ta ɗauko madubi tana kallan fuskarta wacce ta dan gyara da zaman ɗan kwallinta. Macece baka sai dai ba mai duhu can sosai ba, kana ganinta zakaga tsayinta irin tsaka-tsakin nan ne, batada jiki sai dai tana da shape ɗinta, sanye take da english wears na riga doguwa maroon colour har gwiwa sai wando datasa na jeans ta ɗau ra dankwali shima maroon, sai yanzu ta ɗauko wani karamin mayafin baki ta sa a saman kanta, wayarta ta zaro a gefen jakarta ta kunna, fitowa tai janye da suitcase ɗinta fara, airpod ne a kunnenta tana waya, cike da sakalci tace "Mum na iso Allah duk na gaji." Tai maganar tana tsayawa jikin wani shop dake gun inda tasai juice na gwangwani, ƙoƙarin buɗe wa take ga kuma wayarta dake riƙe, ga jakar hannunta da kuma wanda take jaa. Mum ce tace "Kinga wanda muka turo ɗin? Mundai tura miki hotonsa tun jiya." Da mamaki sai ta hangoshi yana nufo inda take, alama tamai da hannu akan ya ƙara so da sauri, aifa guy ɗin ya kara hanzari yana tafiyar niggas irinta samarin dake ji da kansu, kayan da yake sanye dashi da trainers ɗinshi kaɗai zaisa kasan ɗan masu kuɗi ne dan kuma riga t Tommy Hilfiger ne ga takamin Adidas. Tace "Mum gashi ma ya iso." Cike da jin daɗi tace "Please Zeety wannan karan karki wulakantashi yaran babban mutum ne Babanshi yana ganin mutumcin Dad ɗinki." Zeey ce ta katse ta jin tana cewa "Please ja jakar, inata jiranka kana tafiya kamar bakai breakfast ba." Da mamaki guy ɗin yake kallanta sai dai ya amsa baisan ya nuna gazawarshi, juice ɗin ta miƙa mai tace "Ɗan Buɗe min hannuna." Baki ya ɗan buɗe cike da mamaki ya amsa ya buɗe ta amsa daga hannunshi tana sipping tace "Yauwa Mum kikace me?" Acan kuwa Mum ta runtse ido tace "Zeey please ya isa haka." Sai tace "Okay sai mun iso." Kallanshi tai wanda da alama kunya yake a ganshi yana binta a baya, dan ta kula sai saurin matsowa daf da ita yake dan su jera, kallanshi tai tace "Yauwa yama sunanka? Jamil? Jamal?" Takaici ya sake kamashi yace "No ni sunana Najib." Ta jinjina kai tace "Ohh! Yaushe Dad ya daukeka aiki? Hope dai personal driver ɗina ne kai dan inada abubuwan yi." Cak ya tsaya yace "What? Driver? Na miki kama da driver?" Waigowa tai tace "Then?" A kufule yace "Ba'a turo miki hoto na bane?" "Ooops! Anturomin, wai kaine dama?" Hanci ya fara hurawa ta fara kunshe dariya tace "Sorry! Sorry! Amma kamar filter kasa a hoton ko? I'm not trying to be rude amma you look different." Jakarta ya tura mata daga inda yake yace "Mene?" Wuyanta ta ɗan shafa tace "Kamin kama da driver ne da Dad ya min magana akan zai ɗaukar min kafin na dawo." Nabeela wacce ke makale a gefe tana kallansu ta ɗan daki goshinta kaɗan tana girgiza kai tare da furzar da iska, dariya ta fara tana ƙara sowa ta dafata tana matsa kafaɗarta cikin magana kasa ƙasa tace "Ya isa yi shiru kafin ki ƙarasa lalata komai." Zeey da ƙarfi tace "Ouch! Me nai? Jamal ranka ya ɓaci?" "Najib nace miki sunana." Yai maganar cikin ɗaga murya, nan kawai ya juya ya fara tafiya da sauri Nabeela ta bishi tace "Dan Allah kayi hakuri bata ganeka bane, bawai wulakanci tama ba." Ai bai kulata ba yai gaba yana huci kamar shi? Kamar shi babban yaro a maidashi wani gaja? Waigowa tai ta zabgawa Zeey harara wacce ta ɗan ɗaga kafaɗa alamar oho. Haka suka fito Zeey tana dariya ita ko a jikinta, a hanya Nabeela tace "Zeey wai haryanzu bazaki daina wulakanta samari ba? Sai yaushe ne zaki bar abin nan?" "Sai sanda zuciyata ta aminta da abinda nake so, Aunty Nabs please mu bar maganar, to ya gida? Ina Nan?" Ajiyar zuciya Nabeela tai tace "Da kin ɗauken a matsayin Auntyn da kinji magana ta ai." Dariya tai tana danna waya tace "Ke fa dariya kike bani, nafa girmeki da 8month." "Ko dai kin girmeni dai ni kanwar Mumyn ki ce." Dariya sukai a tare haka suka cigaba da tafiya suna hirarakinsu sam Zeey bata tauna magana take faɗa kuma kanta tsaye sai dai kai maganar ta ɓata ma rai amma ita ko a jikinta. Zeey ta kalli Nabeela bayan sun shigo unguwarsu tace "Please kaini shago a layin nan na sai abu." Da mamaki tace "Meyasa baki faɗa da wuri ba? Da munje store." "No bana san can, simple abu zan siya." Tace "to" **** Baqeer sun samu sun fito shi da Salim kamar yanda suka tsara sukacewa Umma wai iska zaisha a waje, sunyi sa'a Baba bai dawo ba. Asiya kuwa ta fito ita da Habi wacce tace zasuje shagon Sidi su siyowa innarsu abu wai tsoron fita take ita kaɗai suna tafe Asiya na masifa akan ta sakata ta fito ba tare da ta yi niyya ba, suna isa turus tai ganin Baqeer daga lungun shagon, kallan Habi tai wacce tai saurin fara tafiya. Neman juwaya tai Baqeer da sauri yace "Asiya please!" Dawowa tai ganin inba tayi da gaske ba bazai kyaleta ba. Daga kusa dashi ta tsaya ta ɗan kauda kai yace "My luv nasan halin dana shiga ne ya jefaki cikin wani hali sai dai mu sani haka Allah ya kaddara mana ba yanda....." Katseshi tai da sauri tace "Ya kaddara ma dai! Baqeer kalleni hanna yena da kafafuna garau suke, ko ina zan iya zuwa da kaina kuma ko me nake so zan iya zama indai nasa kaina, mena cema akan ka nemi wani aikin ka ajiye shirmen zanen nan? Cemin kai zane ma sana'a ce, to yanzu ga hannunka ya samu matsala taya zaka cigaba? Ga kuma kafarka wacce har abada a keke zaka kare kaga kuwa kaine ke dauke da kaddara ba ni ba." Mamakin kalamanta ne suka hanashi cewa komai da kyar yace "Me kike nufi?" Tace "Abinda kake tunani kaga please ka daina ƙirana kaje kaji da yanda zaka amshi kaddararka bani ba, aurenka zanyi ko jinyarka?" Tana kaiwa nan ta fara tafiya, cikin sauri ya fara tura keken nashi da hannun hagu dan Salim ya ɗan basu guri yana tsaye a shago yana jiransu. Da sauri ya tsaya ganin mutum a gabanshi, Zeey bata san sanda ta fara kunshe dariya ba tana girgiza kai, ashe ta fito a shago taga abinda ke faruwa ita kuma da san abin dariya kawai ta tsaya tana kallansu. Baya tai ta kaucemai tana sake kunshe dariyarta, Baqeer ne ya sauke idanunshi da sukai jaa a kanta, da sauri ta ware hannu tace "Oops sorry!" Ta fara tafiya tana magana ƙasa-ƙasa "Maza sai ka rasa irin kwakwalwarsu, clearly kasan ba sanka ake ba ta kuma nuna ma tunda kai gurgu ne batayi, amma inaa kan nan ba komai.." Karaf a kunnen Baqeer a fusace yace "Me kikace?" Yai maganar cikin daka mata ɗan tsawa. Ƙofar mota ta buɗe tace "Sorry no time."
Ayusher Ce 🏌🏻♀️ Da Ummu Asgar Baqeer #Shalele #Asiya # RayuwadaKaddara #Hawayena
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 - Uku 1200 - Biyu 1000 - Ɗaya 500 -
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
Promo zai kare zuwa wani satin, garzaya kisai naki🙌🏻💃🏻
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
BAQEER🦼 NA UMM ASGHAR DA AYUSHER MUHD
DADANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA
Kallon inda Asiya ta fara tafiya kawai yake yi baki a sake, jikinshi na wata irin rawa da tsuma ta tsananin tashin hankalin daya tsinci kanshi a ciki yanzun nan, shi maganar yarinyar can ma bata ɗaga mishi hankali ba irin maganar da Asiya tayi. Cikin rawar murya yace "Me kike nufi kenan Asiya? Saboda Allah ya aiko mini da ƙaddara kike nema ki gujeni? Ina alƙawarin da muka yiwa juna na duk rintsi duk wuya muna tare babu abinda zai iya rabamu, shine yanzu zaki janye maganar saboda kinga Allah ya mayar dani haka?" Yai maganar wani siririn hawaye mai ɗumi ya biyo gefen idonshi ya silalo kan kumatun shi, yana jin wani irin ciwo mai zafi na damƙa a cikin ƙirjinshi har ma fiye da yadda yaji lokacin da aka sanar mishi da ƙaddarar data same shi, dan tunda yake rayuwa bai taɓa tunanin akwai abinda zai sashi rabuwa da Asiya ba, komai na rayuwar shi da ita yake ginawa, dame akeso yaji?
Cak ta tsaya sannan ta waigo tare da sake takowa inda yake, wani wulaƙantaccen kallo ta watsa mishi tayi tsaki "Kai nan a tunaninka zan iya cigaba da yin soyayya da kai, a hakan? Kalle ka fa ka kalleni kai ma kasan ajina yafi gaban na zama matar gurgu, never wallahi har abada" Ta ƙarasa maganar tare da tofar da yawu kamar taga wani abun ƙyama. Juyawa tayi ta fara tafiya sai kuma ta juyo ta kalleshi irin kallon tsaf ɗinnan kafin tace "Ina fata zaka cireni daga cikin ranka ka manta ka taɓa sanin wata mace mai suna Asiya, ka ɗauka duk soyayyar da muka yi a cikin mafarki ta gudana ba gaske bane don ni tuni na cireka daga cikin zuciyata daga lokacin da nasan ka zama nakasashe gurgu nasa a raina ban taɓa saninka ba don haka nake haɗa ka da Allah kada ka ƙara nemana ko a waya ko kace zaka zo gidanmu don idan kazo ma bazan fito ba." Daga haka ta juya tayi tafiyarta ta barshi yana ƙwala ƙiran sunanta yana cewa "Please Asiya kada kiyi mini haka, kada ki juya mini baya don kinga larura da ta sameni, idan kika barni a cikin wannan halin dana tsinci rayuwata ban san inda zan waiwaya ba naji daɗi kuma."
Ko waiwayowa bata yi ba har ta ƙurewa ganinshi kuwa, haka ya sunkuyar da kai yana zubar da hawaye mai ciwo yana jin wai yau shi Baqeer, Asiya take faɗawa waɗannan maganganun saboda taga yadda Allah yayi dashi, har Salim ya dawo kanshi yana ƙasa ya kasa ɗagowa, sai da ya dafa kafaɗarshi sannan yasan ya dawo don dama matsawa yayi ya basu wuri. Salim gani yayi fuskar Baqeer tayi jawur gashi tayi caɓa-caɓa da hawaye.
"Lafiya kuwa Baqeer? Wani abu Asiyan tace maka naga duk ka firgice ka fita daga hayyacinka?"
Girgiza kai kawai yayi don bai ji zai iya buɗe baki yayi magana a daidai wannan lokacin ba, maganganun da Asiya ta yaɓa mishi sosai suka dakeshi duka bana wasa ba don ko kusa bai taɓa tsammanin tana daga cikin butaulallun mutane ba masu saurin manta alheri, bai ɗauka a cikin ɗan taƙaitaccen lokaci Asiya zata juyawa soyayyarshi baya ba sai kuma gashi ta ƙaryata tunaninahi ta nuna mishi rashin amana irin na mutanen wannan lokacin.
*****
A kwance Habi ta shigo ta tarar da ita akan katifarsu tana danne-danne a cikin waya. Kallon tsaf tayi mata taga babu abinda ya dameta da abunda tayi sai ma wani ɗan murmushi da take saki idanunta manne da allon wayar. Ninke hijabin ɗin data fita dashi tayi ta ajiye akan jakar kayanta kafin ta zauna daga bakin katifar wajen ƙafafun Asiya zuciyarta duk babu daɗi. "Ke kuwa Asiya me yasa zaki yi haka saboda Allah, ko ba kya son Baqeer bai kamata kiyi mishi irin wannan cin fuskar ba babu tausayin halin daya samu kanshi a ciki a haka ya taso don ya ganki yana ganin ko da ya rasa komai a rayuwa kasancewarshi tare dake zai sauƙaƙa mishi abubuwa ashe ke ɗin mayaudariya ce mai saka alkhairi da sharri, me manta girman soyayya da sanin darajar masoyi."
A harzuƙe ta tashi zaune tayi wurgi da wayar can gefe ta hau nuna Habi da yatsa tana cewa "Kinga Habi ki kiyaye ni ki fita daga idona na rufe, akan gurgun kike cewa na manta alkhairi, gurgun? To idan na aureshi bara zai yi ya ciyar dani ko kuwa ni zan turashi a keken guragun mu tafi yawon barar, wallahi nafi karfin auren nakasashe Allah ya tsareni da auren wahala, to me na sama yaci bare ya bawa na ƙasa? Idan ban rabu dashi tun yanzu ba sai yaushe? Ko kin fiso nayi ta bashi false hope ina yaudararshi alhalin ba aurenshi zan yi ba? To ni ba haka nake ba tun farko da nasan gurguncewa zai yi ma bazan fara kula shi ba bare har ki samu bakin faɗa mini baƙar magana, aikin banza kawai bayan ko kece babu yadda za ayi ki yarda ki aureshi shine ni zaki cikani da baƙin munafurci da iyayi har da wani wai abinda nayi ban kyauta ba, mtsew" Ta ɗauki wayarta ta koma ta kwanta tana cigaba da chatting ɗin da take yi kafin shigowar Habi tayi mata ruining mood ɗin ta.
Murmushin takaici Habi tayi tace "Gaskiya ce ba kya so ni kuma bazan daina faɗa miki ba idan kin so ki ɗauka kiyi aiki da ita idan kin so kiyi watsi da ita kamar yadda kike yi da duk wata gaskiya da zan faɗa miki, kada dai ki manta ramin ƙarya ƙurarre ne kuma ƙarya fure take yi bata ƴaƴa kuma duk wanda ya hau motar kwaɗayi zata sauke shi a tashar dana sani, ni sai yanzu ma na fahimci tun asali dama ba son Baqeer ɗin kike yi ba hidimar da yake yi miki kike kwaɗayi yanzu daya rasa duk wata dama tashi shine kike nema ki guje shi."
"An guje shi ɗin, idan kin ji haushi ke ki aureshi mana, ha'an kin fa isheni Habi wallahi ki fita idona in rufe, tom," tayi wata irin ƙwafa alamun dai ranta ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, daga baya ma tashi tayi ta fice ta bar mata ɗakin.
Bin bayanta Habi tayi da kallo tana jin takaicin halin ƴar uwarta tana jiye mata aikin dana sani don tasan komai daren daɗewa sai tayi dana sanin yaudarar da ta yiwa Baqeer ta gujeshi kawai don Allah ya jarabce shi da larura. Asiya ta gyara kwanciyarta dan dole ta yakice komai a ranta, duk da a can kasan ranta tana tausayinsa sannan tasan bata kyautamai ba, sai dak hakan shine daidai dan tabbas a yanda tasan Baqeer na santa in har tamai lagwa-lagwa to fa bazai taɓa rabuwa da ita ba, ita kuma a yanzu tasan wutsiyar rakumi tayi nesa da ƙasa shiyasa bama tasan abinda zai ja rabuwarsu ta ɗau lokaci gwara yaji zafin kalamanta ya kyaleta.
*****
Suna tafe shiru babu mai iya cewa ɗan uwanshi komai, shi dai Salim tausayin Baqeer ne fal a ranshi don lokacin da yaga budurwar nan tana magana ya taho ya ɗauka wani abin ne, ganin sun ja mota sun tafi yasa yai kamar zai koma cikin shagon, sai yaji kalaman Baqeer wanda ya sashi tsayawa gefe hakan yasa yaji duk abinda Asiya take cewa, sosai ya cika da tsoron Allah yana mamakin halin mutanen yau. A yadda yasan soyayyar Baqeer da Asiya bai taɓa zaton zata guje shi cikin lokaci ƙanƙani ba don kawai Allah ya jarabce shi da wata larurar da bashi ya ɗorawa kanshi ba. Suna tafe yana tura Baqeer a keken guragun shi sai dai ya kasa ce mishi komai don yana jin yadda yake sauke ajiyar zuciya akai-akai, fatanshi Allah yasa kada ya ɗauki damuwar Asiya ya ɗora a ranshi alhalin dama ba wai ya warware daga damuwar ƙaddarar da ta sameshi bane.
Har suka ƙarasa gidansu Baqeer babu mai magana, dama dai tunda abun nan ya faru Baqeer bai cika yawan magana ba idan ba ya zame mishi dole ba, Salim ɗin ne mai yawan maganar ko ba zai amsa ba yasan yana jin shi to shima yau damuwar abinda Asiya ta yiwa abokin nashi ta hanashi sukuni. A ƙofar gida suka tarar da Baba dake ta faman kaiwa yana kawowa tunda ya dawo gida ya tambayi ina Baqeer Umma tace mishi baya nan sun fita da Salim sai dai bai faɗa mata inda zasu je ba hankalin shi ya tashi, sam baya so mutanen unguwa su san halin da Baqeer ɗin ya samu kanshi a ciki don a ganinshi kamar zai zama abin zunɗe da dariya ganin yadda ya ɗaukake shi a cikin dukkanin ƴaƴan shi ya fifitashi ya fifita uwarshi akan baiwar zanen da kowa yake ganin ɓata lokacin shi yake yi akai don basu ɗauke shi wani sana'ar kirki ba kamar yadda shi ya ɗauka, har nasiha an sha zuwa har gida ayi mishi akan bai kamata yake fifita Baqeer ɗin da ƴan uwan shi ba sai yace ai dole ya fifita Baqeer don kuwa shi ɗin ɗa ɗaya ne tamkar da ɗa goma, shine zai share mishi hawaye ya cika mishi daɗaɗɗen burinshi na rayuwa suma idan suna so ya gatantasu kamar Baqeer suje su koyi yadda ake zane zasu ga yadda zai ji dasu ya ɗaukaka su a cikin ƴaƴa. A duk sanda ya faɗi haka kallan mara tunani mutane ke mai, zane fa? Ya rasa abinda zaiyi alfahari dashi sai zane? Dan mu kasarmu sam bamu ɗau ki zane da sunan sana'a ko abin alfahari da mutum zaiyi dashi ba.
Wani wulaƙantaccen kallo ya watsawa Salim daya durƙusa yana gaishe shi, bai amsa ba sai masifa daya balbaleshi da ita akan don me yazo ya fita da Baqeer yawo, wato gurgunta shin da yayi bai isa ba shine yake zuwa har gida yana fita dashi salan wani abun ya ƙara samun shi. Shi dai haƙuri kawai yake bashi don idan da sabo yaci ace ya saba da halin Baban abokin nashi, shi Baqeer ɗin ne yake bashi tausayi shi yasa baya kula duk wani baƙin hali na Baban yake zuwa yana taimakawa Baqeer ɗin da wasu abubuwan amma in banda haka ai da tuni yayi zuciya ya fita daga rayuwar ɗan shi tunda dai dashi ne baya son ganin shi.
Shi ya tura wheelchair ɗin zuwa cikin gida yana ƙwalawa Umma ƙira tun daga soro. Tuni su Abu da Jamila suka fito daga ɗakunansu tun ma kafin Umman ta fito don son jin gulma sun san tunda ya shigo da hayaniyar nan tabbas tijara zai yi mata. A nutse ta fito daga ɗakin duk kuwa da yadda gabanta yake faɗuwa tunda taji mahaukacin kiran da yake ƙwala mata. Daga bakin ƙofar ɗakinta ta tsaya tace "Gani Mallam, barka da shigowa."
Da wani irin kallon takaici ya bita kafin yace "Kina cikin gidan nan don shashanci zaki dinga bari wancan lalataccen yaron yana zuwa yana ficewa dashi yawo salon mutanen unguwa su ganshi a keken guragu suyi min dariya, owo zane ne ba zai iya ba idan anyi magana kuce bai warke ba har yanzu hannunshi nayi mishi ciwo amma ya iya ficewa yawo har sai an nemeshi kafin ya dawo gida, ni dama nasan baƙin ciki kike yi mini shi yasa kika ƙi yarda ya koma aikinshi na zane, to ai ba ni kaɗai na rasa ba harda ke uwarshi tunda kafin yayi mini maganin naira goma ai yayi miki na ɗari, kuma na faɗa miki kada ki ƙara bari wancan yaron ya shigo mini cikin gida ya fita dashi yawo, tunda dai ba zai yi zane ba sai yayi ta zama a cikin gida amma na yanke hulɗa a tsakanin shi da shi."