Baqeer complete - Chapter 7
Baqeer complete Chapter 7: Baqeer complete Chapter 7. An ɗauki lokacin tana yi mishi nasiha akan falalar haƙuri da karɓar ƙaddara a duk yadda ta zowa bawa…
2,763 words
An ɗauki lokacin tana yi mishi nasiha akan falalar haƙuri da karɓar ƙaddara a duk yadda ta zowa bawa har ya samu ƴar nutsuwa ya daina kukan da yake yi. "Umma Baba fa, ya zan yi dashi bayan ya kasa gane a yanzu babu abinda zan iya yi da hannuna, gani yake yi kamar da gangan naƙi yin abinda ya sakani?" Yayi maganar idanunshi akan hannunshi na dama yana jujjuyasu a hankali, yana ayyana ko sai yaushe zai fara amfani dashi wajen yin zane kamar da. "Shima haƙurin zaka yi dashi har ya fahimci ba yin kanka bane ƙaddararka ce tazo a hakan ya sauko, kasan yadda ya ɗora dukkanin wani buri nashi a kanka lokaci guda hakan tazo ta faru dole abun ya dakeshi to amma ya zamu yi bayan muyi haƙuri mu fawwalawa Allah dukkanin al'amuranmu In Sha Allah yana sane damu ba kuma zai ƙyale mu a haka ba zai kawo mana mafita ta inda bamu yi tsammani ba, kayi haƙuri kaji ka cire komai daga cikin zuciyarka sai kaga Allah ya dafa maka."
Miƙewa tayi zata fita sai kuma ta dakata tace "Ko akwai abinda kake so nayi maka kafin na fita, ba dai wani daɗewa zan yi ba wanki kawai zan je in ƙarasa yanzu zan dawo, dazu na fara na ajiye." Girgiza kanshi yayi yace "Babu wani abu Umma har kin gama ki dawo ina nan ai ba wani wuri zan iya zuwa ba." Sai taji tausayinshi ya ƙara kamata, wai yau Baqeer ɗinta ne ya dawo haka, Ya 'Allah ka sauƙaƙa mishi ka bashi ikon ɗaukar wannan ƙaddarar daka sukar mishi' ta samu kanta dayi mishi addu'ar a cikin zuciyarta. '"Ko dai zaka kwanta kafin na dawo don naga kamar ba wani jin daɗin zama akan kujerar kake ji ba?"
"A'a Umma barni a zaune kawai don na gaji da kwanciyar nan ciwon jiki take sakani." "To ai shikenan, bari naje nayi maza na gama na dawo, don Allah ka cire komai daga cikin ranka kaji? Kada ka zauna kana tunane-tunanen da baza su ƙare ka da komai ba sai yawan damuwa." "To" kawai yace mata cikin ranshi yana cewa tunani kam ai ya zama dole a wurinshi a yanzu tunda baya da wani abun yi da zai ɗauke mishi hankali daga halin daya samu kanshi a ciki.
*****
Baba kuwa yana fita ɗakinshi ya shige ya fara shirin fita kasuwar da duk kwanakin nan bai samu yaje ba don ma Allah yasa yana da yara masu kular mishi da harkokin kasuwancin nashi ai da ba ƙaramar asara ya tafka a cikin kwanakin nan da yayi ta sintiri a asibiti bai je ba gashi alamu sun nuna ba lallai ne ya samu abinda yayi sadaukarwar domin shi ba tunda Baqeer nema yake yi ya watsa mishi ƙasa a ido abinda bai taka kara ya karya ba na neman gagararshi, yayi fatali da dukkan wani ƙoƙarin shi da jajircewarshi wajen ganin sun cimma nasara ya cika burinshi. Har ya gama shiri ya bar gidan zuciyarshi bata daina tafasa ba hakan yasa ko sallam bai yiwa matan gidan ba yasa kai yayi ficewarshi. Koda yaje haka yayi tayi wa yaran nashi masifa, abu ƙalilan zasu yi mishi sai ya rufe su da faɗa, gaba ɗaya ya rasa nutsuwarshi tunanin ta yadda zai takura Baqeer yayi zane kawai yake yi, har tunani yayi to ko wani zai nema da ya iya zanen su tafi wajen gasar tare yayi zanen a madadin Baqeer idan yaso shi sai ya biyashi, tunane-tunane dai iri-iri babu wanda bai yi ba na neman mafita amma kasa samun matsaya guda ɗaya da zai kama. Dole ne ma Baqeer ya dage ya ƙarfafi zuciyarshi ya cigaba da zanen idan ba haka ba kuwa sai dai shi da uwarshi su biyashi duk abinda ya kashe akan harkar zanen Baqeer ɗin.
Yana cikin waɗannan tunanin ne aka kirashi a waya, sai da gabanshi ya faɗi daya duba yaga Yallaɓai ne ke kiranshi. Ido kawai ya zuba yana kallon screen ɗin wayar tana ta ƙara ya kasa amsawa saboda dai bai san kuma me zai faɗawa Yallaɓai ɗin ba, sai da ta kusa katsewa sannan ya amsa wayar cikin sallama. Ko gaisawa Yallaɓai bai bari sun yi ba yace "Haba Mallam Badaru, ta yaya zan yi ta nemanku a waya kuna raina mini hankali bayan kasan tafiyar nan ta matso, idan Baqeer ɗin ba zai iya ba tun wuri ba sai ka faɗa mini ba a nemi wani sai kayi ta yi mini yawo da hankali".
A ladabce kamar yana gabanshi don har ɗan russunawa yake yi yace "Kayi haƙuri Yallaɓai wallahi wata ƴar matsala aka samu shi yasa kaji har yanzu ban nemeka ba, amma ya za'a yi mu raina maka hankali".
"Yanzu ina Baqeer ɗin? Ina fata dai ya gama shiryawa don kasan gobe ne zamu je wajen deputy gwamna a game da batun tafiyar." ya katse shi ba tare da ya bari ya gama jin me zai ce ba. Shiru Mallam Badaru yayi yana juya ta inda zai fara faɗa mishi abinda ya samu Baqeer ɗin. A ɗan tsawace yace "Wai wani abu ya faru ne Mallam Badaru da kake ɓoye mini?"
"Wallahi Yallaɓai tsautsayi ne ya afku da Baqeer, yau sati guda kenan da mota ta kaɗeshi ya karye a ƙafa da hannu, zancen nan da nake yi maka ma dai ya zama gurgu don ance ƙafafun nashi sun tashi daga aiki," yayi maganar yana jin baƙin cikin halin da Baqeer ya sakasu a ciki, daya zauna a gida bai fita shegen yawonshi na tsiya ba ai duk da haka bata faru ba gashi nan yanzu suna nema suga samu suga rashi.
Cikin wani irin fushi Yallaɓai yace "What? Karaya? Kana nufin karaya dai? Kuma shine kayi shiru da bakinka kaƙi faɗa mini na nemi wani, wai me yasa mutane sam baku san ku rama alkhairi da alkhairi bane, ka barni anan sake da baki zamu je wajen taron nan da ɗanka ashe shi ya zama useless ni ban sani ba, sai kayi gaggawar dawo da kuɗin tallafin da kuka karɓa daga hannun gwamnati don kasan dai ba bar muku za'a yi ba tunda ba zuwa zai yi ba."
Shi dai haƙuri kawai yake bayarwa kamar ya ari baki, haka Yallaɓai ya kashe wayarshi yana ta masifa yana mamakin halin mutanen wannan zamanin da basu san komai ba sai son kansu da yayi musu yawa. Wayar Bello ya ƙira, Bello yana ganin Yallaɓai ne ya amsa da hanzari don yasan ba zai wuce yaji abinda ya samu Baqeer ba shine yake kiranshi. Cike da ladabi ya amsa yana gaisheshi, sai bayan sun gama gaisawa sannan Yallaɓai yace "Ni zaku maida karamin mutum? Ashe abinda ya samu abokinka kenan shine kuke ta ɓoye-ɓoye kuka kasa faɗa mini na nemi wani gashi gobe zamu je wajen deputy gwamna? Ƙaramin mutum kuke san maidani?"
"Wallahi kuwa Yallaɓai, accident yayi sai kuma abu yazo da tsautsayi ya rasa ƙafafun shi gaba ɗaya."
"Mts... Allah dai ya bashi lafiya amma ni damuwata ta yadda zan nemi wani contestant ɗin a tsakanin yau da gobe wanda zai maye gurbunshi kawai tunda ko be karye a hannu ba ƙafafunshi sun tashi daga aiki, taya zai shiga taro irin wannan akan keken guragu, wallahi Mallam Badaru ya ɓata mini rai don daya faɗa mini da wuri da tuni nasan abun yi, gashi mun riga mun aika sunanshi." Ya ƙarasa maganar rai a ɓace.
Dukkansu shiru suka yi kowa da abinda yake tunani a cikin zuciyarshi, Bello ne yayi ƙundunbalar cewa "Yallaɓai idan babu damuwa nace ko ni ba sai na wakilcemu? Tunda dai nima na iya zanen nan, asali ma abinda ya haɗa abotarmu da Baqeer ɗin kenan."
Wata nannauyar ajiyar zuciya Yallaɓai ya sauke kafin yace "Kuma fa haka ne Bello, ni ba na manta ba ashe kaima duk harkarku ɗaya, matsalar da za'a samu kawai wajen canja suna ne tunda mun riga mun miƙa sunan Baqeer a matsayin wanda zai wakilcemu, shi yasa ma abun ya dameni don sai da lokaci ya ƙure sannan aka samu wannan canjin amma In Sha Allah zan yi ƙoƙarin ganin an gyara komai ya koma da sunanka, kai dai ka zama cikin shiri don koyaushe zan iya nemanka, fatana kar canza sunan ya zama matsala.
"To Yallaɓai nagode Allah ya ƙara girma" yace cikin tsantsar farin ciki irin wanda bai taɓa tsintar kanshi a ciki ba "Yallaɓai in kana ganin sunan zai jawo matsala ina ganin ba matsala bane tunda ai dama da initials ake amfani to nima kuma sunana Bello Bala kaga Muhammad ɗin kawai za'a ƙara mini daga gaban sunan, kuma duk wani namiji ai Muhammad ne, ko ba haka ba?"
Wata irin dariyar farin ciki Yallaɓai ya saki ganin ya samu mafita yanzu-yanzu kamar ba shine ke tunanin neman replacement na wanda zai maye gurbin Baqeer ɗin da ke neman kassara shi ba.
(Wani abokin dai sai Allah, ga dai Bello ba kunya ba tsoron Allah, ga kuma mahaifin da ya kasa duba halin da danshi yake ciki.)
Baqeer #Shalele #Asiya # RayuwadaKaddara #Hawayena
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 - Uku 1200 - Biyu 1000 - Ɗaya 500 -
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
Promo zai kare zuwa wani satin, garzaya kisai naki🙌🏻💃🏻
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
BAQEER🦼 NA UMM ASGHAR DA AYUSHER MUHD
RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TARA
Dandano......
{9}
Yallaɓai yana kashe waya Bello ya daka wani irin tsalle tare da yin ƙaramin ihu, lalai ba shakka rayuwa zata fara masa da ɗi yanzu, masu mai gani-gani su shirya ganin abinda zai zama yanzu. Sako ne ya shigo wayarshi na Yallabai akan wai ya tura samples na zanen dayai ya gani dan ya sake tabbatarwa akan ba matsala. Ajiye wayar yai ya durkusa ƙasan gado yana jawo zanukan da yai, wanda kusan kowane ya ɗaga sai yaga Baqeer ne ya tayashi ko kuma Baqeer ne ya nunamai yanda zaiyi, tsaki yai yace "Nuna min yai ai ba shiya zana min ba." Kallan initial na sunanshi da ya saba amfani dashi yake wato BB da sauri yasa pencil ya ƙara M a gaba nan danan da ɗi ya ƙara rufeshi ba shakka Allah ne ke sanshi da rahama, shafar zanen yai yanajin wata nutsuwa na sake zuwa mai, yau ina mutanen dake ganin zane ba inda zata kaishi? Wanda ciki harda mahaifinshi? Dole ya shayar dasu mamaki dan bazai sanar dasu ba sai yaje ya ciyo gasar da za'ai a Abuja nan ne fa zai nuna ma duniya shi ɗin wanene. Haka ya ɗau hotuna kala-kala ya tura nan da nan Yallabai yamai reply akan komai yayi sai sun haɗu gobe.
******
Kallan ɗakin tai cike da jin daɗi a hankali ta ke sake takawa ciki, wani sanyi na sake ratsata, ta baya taji an dafata, ba tare da ta juyo ba ta saki murmushi tace "Senate Allah yayi autata zata dawo." Kai ya girgiza yace "Ke dai wallahi san yaran nan ya miki yawa, ina fitowa da naga ban ganki ba dama nasan kina nan, ba last year tazo hutu ba?" Waigowa tai tace "Hutun wata ɗaya ne fa kacal? Yanzu kuwa fa? Kaga dai wannan karan inta dawo shikenan ba komawa." Kai ya girgiza yana kallan yanda tasa aka canza komai na ɗakin, kallanta yai yace "Nabeela ce zataje airport ɗin?" "Eh nace taje dan kasan halinta in taga ka tura yaran nan shi kaɗai bamusan me zata aikata ba." Yana ɗan jinjina kai yana cewa "Sam bansan meke damun yarinyar nan ba, ace wai ita ba'a isa a hadata da wani ta kulashi ba? Tunda kike da ita kin taɓa ji tace tanasan wani? Ita bata kawo ba sai taurin kan tsiya." Hannunta ta saƙala cikin nashi tace "Calm down please my Senate, kasan Zeey abubuwa ne suke mata yawa, ita bawai auren bane bataso kawai....." Hannu ya ɗan daga mata alamar tai shiru yace "Nidai Allah tana dawowa ki sanar da ita ko ta kula wannan ko karta kulashi a shekarar nan zan aurar da ita, sam banasan yarinya mace ta min girma haka a cikin gida, tun yaushe nake san aurar da ita amma abu yaki yiwuwa?" Sanin halinshi yasa ta nemi janye maganar da cewa "Yau ne zakuyi meeting ɗin da kace?" Fara tafiya yai yana fita daga ɗakin yana cewa "Yau ne, nidai ki faɗawa Nabeela taja mata kunne kindai san wannan ɗan wanene bansan shirme." Zatai magana yace "Da zatai rabin hankalin Nabeela da ba haka ba." Daga nan bai jira tace wani abu ba ya wuce, itadai sam batasan ya zatai ta nusar dashi akan ya rage tsauwalawa Zeey ba.
*** Baqeer tunda Mama ta fita ta barshi a ɗaki yake zaune a gun, banda ƙoƙarin riƙe pencil dayake tayi babu abinda yakeyi, ganin yafi awa ɗaya yana abu ɗaya yasa ya runtse ido, yanajin wani irin kunci a zuciyarshi wanda kawai yacigaba da samun kansa da addu'ar Allah ya ɗau ranshi ya huta da wannan bakin cikin, Fatima ce ta shigo jiki a sanyaye tace "Baqeer bari na roki Bashir ya taimaka ya kaika bandaƙi kai alwala azahar tayi." Kamar wanda aka daɓa masa wuka a zuciya haka yaji kalamanta, shikenan shi yanzu komai sai an taimaka mai yayi kenan? Kasa magana yai har sai da ta fita ya ciji kasan leɓensa yana sake runtse idanuwansa. "Bashir baya nan, sannan banaji sanda na haifi ɗan akwai gadan zaki sashi wahalar nakashashen ɗanki." Kalaman da Jamila tace kenan wanda yasa Fatima hadiyar yawo a ranta tace "Inama yanada kani namiji?" Abu ta kalla tace "Abu dan Allah naga kamar Kamalu ya shigo ko zaki mai magana?" Baki Abu ta buɗe tace "Kamalun saninshi ne bakiyi ba? Sai kije da kanki ai kinsan ɗakin shi." Kamalu shine mai bin Baqeer a gun mahaifinsu, sam ba jituwa tsakaninsu, tunda yaga Baban yanasan Baqeer sosai sai ya kangare ba wanda ya isa ya sashi balle ya hanashi, har zargin shaye-shaye akemai sai dai tsoronshi yasa inba Baba ba bamai masa magana. Wani tunani ne yazo mata wanda yasata juyawa ta koma ɗakin tana murmushi tace "Baqeer bama sanan amma na ƙira Salim yace dama gashi nan zuwa." Kai kawai ya ɗaga dan yasan akwai abinda ya faru faɗane kawai batai ba, hanyar fita tai ya daure yace "Umma dan Allah aran wayarki." Cikin sauri ta miƙa mai, ya fara ƙoƙarin sa hannu dama zai amsa, da sauri ta ɗau ra mai akan cinyarsa ta fita ɗakin zuciyarta na sake karyewa, gaba ɗaya intaga Baqeer a haka sai taji hawaye, Baqeer ɗinta wanda a koda yaushe yake cikin ji da ita wai shine a wheelchair. Wayar ya ɗauka da hannun hagu ya sa number Asiya ya ƙira, tana zaune suna cin abincin rana itada Habi, ganin ƙiran da number da bata sani ba yasa ta ɗaga, tace "Hello!" Baqeer ya haɗiyi wani abin yace "My love!" Dam gabanta ya faɗi dan kuwa tasan waye, cak ta kame ta kasa magana, Baqeer ya daure ya sake cewa "My love am so so......" Kashe wayar tai da sauri tana maida hakki ta maida kallanta kan Habi wacce take cewa "Wenene? Ko Baqeer ne?" Abincin ta cigaba da ci tace "In ma shine sai me? Kinga ni dan Allah ki kyaleni ke in hakan ta faru dake ki tabbatar baki bar mutum ba." Habi cike da takaici ta tsame hannunta tace "Butulci dai babu kyau." Wata muguwar harara Asiya ta zabga mata ta ɗauke kanta.
**** Baqeer kuma kasa sauƙe wayar yai daga kunnenshi mamaki gaba ɗaya ya kasa barinshi, kodai Asiya tausayinshi ne yasata shiga wani hali? Ba shakka abinda ya faru dashi ta gani yasan tana cikin wani hali.
Salim bai daɗe ba sai gashi nan ya taimaka mai yai alwala yai sallah sannan Fatima ta kawo musu abinci, da kyar yai loma uku yace ya koshi. Suna zaune a ɗakin Baqeer yace "Salim dan Allah tunda kuma shiri da Habi ko zaka taimaka ka fita dani waje kasa Habi ta ƙira mana Asiya in mata magana? Na tabbatar tana bukatar wanda zai taushasheta, in har ta ganni nasan zata yarda da kaddarar data samemu." Salim yace "To shikenan." Anan ya ƙira Habi yace bayan magriba sai su haɗu kusa da shagon Sidi.