Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 66

Baqeer complete - Chapter 66

Baqeer complete Chapter 66: Baqeer complete Chapter 66. (😞🥺😟)

3,040 words

(😞🥺😟)

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*

*BAQEER* *NA*

*AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA TAKWAS*

{88}

Tsayawa kawai Daddy yayi yana kallon Zeey ganin yadda take ta dariya kamar wata sabin kamun hauka. Sai da tayi dariyarta ta isheta sannan ta tsagaita, wato Mummy tunda ta gane ita wacece shine zata yiwa Daddy bariki a gabanta ko, ita dariya ma ta bata ganin yadda ta haƙiƙance tana nuna damuwarta a fili. Da ace da ne da idanunta basu buɗe tasan asalin wacece Mummyn ba da tayi mamakin yadda lokaci guda ta juya magana amma yanzu ta gama ganeta sarai sai abun bai wani bata mamaki ba, tasan fiye da hakan ma zata yi in dai Mummy ce. Wani kallo yayi mata yace "Gidan uban wa zaki da kike haɗa kaya?" Turo baki Zeey tayi idanunta ƙyar babu alamun tsoro tace "Wajen uwata zan koma tunda dai ba za'a aura min wanda nake so ba ni banga amfanin zamana anan ba." Hannu Daddy ya ɗaga zai kwaɗa mata mari sai Mummy tayi saurin riƙe hannunshi tace "Haba Senate ya zaka mareta bayan kasan auta yarinya ce har yanzu ba wani sanin daidai tayi ba, don Allah kayi haƙuri abi abun nan a hankali. Ke auta bashi haƙuri kullum ina faɗa miki ki daina yin musu da mahaifinki."

Wani kallo Zeey ta watsa mata kawai ta cigaba da haɗa kayanta, a fusace Daddy yace "Ki tattare kayan nan ki mayar dasu cikin wardrobe don babu inda zaki je, kuma ki sani nasa ranar aurenki da Junaid sati huɗu masu zuwa don bazan yarda ki zubar min da mutunci da ƙimata ba." Itama ƙara tamke fuska tayi tace "Ai na faɗa maka wallahi bazan aureshi ba sai dai nayi ta zama a haka babu aure in har ba zaka aura min Baqeer ba sai ka shirya ganina a cikin gidanka, ai tun farko na faɗa maka ni bana son Junaid bazan aureshi ba ka dage sai anyi to sai kasan yadda zaka yi dasu don ni dai bazan taɓa auren mijin da bana so ba." Ƙara yunƙurowa yayi zai kai mata duka Mummy ta sake tare shi ta hanashi kaiwa ga Zeey ɗin. Sosai ranshi ya ɓaci duk da yasan halin Zainab bata iya yin shiru idan anyi mata abu amma bai ɗauka zata tsaya a gabanshi yana faɗa tana faɗa ba. Juyawa yayi zai bar ɗakin don idan ya tsaya zai iya lahanta ta da duka sai ji yayi tace "Kuma na faɗa maka bazan zauna a gidan nan ba don kada ma kuje kuna yawon nemana ah to." Tsaki kawai yayi ya fice Mummy ma tabi bayanshi suka bar ɗakin. Cigaba tayi da zuba kayan a cikin akwatin, sai da ta tabbatar ta ɗauki duk wani abu da tasan zata rinka buƙata sannan taja akwatinta ta fice. A parlour suka kusa karo da Kabir. Kallonta yayi fuskarshi ɗauke da mamaki yace "Ke kuma ina zaki?" Wani irin kallo ta watsa mishi ta ratsa gefenshi ta wuce don shi kanshi haushin shi take ji, sai take ganin kamar shine sanadin wannan halin da take ciki don watakila da bai nakasta Baqeer ba da duk hakan bata faru ba. Bama zata ga ana wulaƙanta shi ba bare har tausayin shi ya ginu a zuciyarta, da kuma Badaru bai koreshi daga gidanshi ba. Watakila ma da yanzu sun yi aure shi da Asiya. Tana yin wannan tunanin taji wani abu mai nauyi ya sauko ya tokare a ƙirjinta, bugun zuciyarta ya ƙaru fiye da ƙima, numfashi ta dinga yi akai akai har ta samu bugun zuciyarta ya dawo daidai. Tana fita a harabar gidan taga Junaid ya nufo inda take yana murmushi. Ƙara tamke fuskarta tayi ta cigaba da tafiya zuwa wajen motarta, buɗe motar tayi ta jefa akwatin a baya sannan ta rufe. Daidai lokacin Junaid ya ƙaraso inda take. "Hajiya Zeey kin yi wuyar gani." Wani kallo tayi mishi ta saki tsaki ciki-ciki don bata so yaji saboda tana ganin mutuncin shi kawai dai halin shi na naci ne bata so tunda tace bata yi ba sai ya haƙura ba amma ya dage shi a dole sai ya aureta gashi tana ganin kima da darajarsa. Cigaba yayi da cewa "Kin ji abun farin cikin da yake tunkaromu ko? Su Daddy sun saka ranar aurenmu, In Sha Allah nan da four weeks kin zama mallakina." Yatsina fuska tayi tace "Idan ma mafarki kake yi gara ka farka don ba tun yau ba na faɗa maka ni bazan aureka ba to yau ma ina ƙara faɗa maka bazan aureka ba, idan har ban samu Muhammad wanda nake so ba sai dai na haƙura da aure don haka tun wuri ma gara kaje ka faɗawa waɗanda ke da alhakin sanya ranar auren nace bana yi su warware." Ta buɗe motarta ta shige ciki ba tare da ko kallon Junaid ta ƙara yi ba. Kamalu daya faki idon maigadi ya samu ya shigo gidan don ya faɗawa Roshni ɗin shi ya gama haɗa lefe ta faɗi ranar da za'a kawo don so yake yi ayi komai da komai lokaci guda ba sai anyi ta kai komo ana zuwa ana dawowa ba, ganin ta fito ya fito daga bayan motar daya laɓe, yana wani gyara kwalar riga, da sauri ya koma bayan motar ya sake laɓewa ganin saurayi ya nufi Zee ɗin, har ya fara auna cin zarafin da zai mai indai yace yanasan Roshini dan kuwa kowa yasan Roshini ta Saddarth ce, sai dai kalaman Zee sun sa ya zauna dabas a ƙasa. Sakin baki yayi yana kallon Zeey da saurayin da ta gama yagawa, tabɗijam idan har zata iya kallon idanun wannan tsalelen saurayin tace bata son shi to shi kuma a wa da zai yi tsammanin zata so shi. Lallai Roshni ta wuce da saninshi, sai dai duk da haka gara ya gwada sa'arshi don bai san inda za'a dace ba. Wa ya sani ma ko shine Muhammad din? Tunda dai kowa yasan Kamal ma ana cemusu Muhammad Kamal. Ƙarasawa yayi jikin motar yace "My Roshni!" Wani banzan kallo tayi mishi taja wani irin tsaki don sarai ta gane waye Kamalun ɗan uwan Baqeer ne, shi bai san duk haushin ƴan gidansu take ji ba saboda abinda ubansu ya yiwa Baqeer bare wannan mahaukacin da sam bata sakashi a layin masu hankali. Har zata shiga mota sai kuma ta kalleshi tace "Na ɗauka nace in neman taimako kake a bakin ƙofa zaaka tsaya ko?" Kallan kanshi yai da irin wankan dayai na gayu ya buɗe baki zai sake magana kawai yaga ta shiga motarta tayi reverse kafin ta danna wani mahaukacin horn, a guje maigadi ya taso ya buɗe mata gate ɗin taja motarta ta fice daga gidan a guje. Kallon wurin data bari Junaid yayi ya juya ya nufi motarshi don bai ga tsaiwar me yake yi ba a wurin kuma sai jin muryar Kamalu yayi yace "Ah to tun wuri gara ka kiyayi Roshni don ba sa'ar yinka bace." Ai juyowa bai yi ya kalleshi ba ya cigaba da tafiyarshi, duk da ranshi a cunkushe yake da maganganun da Zainab ta yaɓa mishi sai da yayi dariya din ya fahimci kamar shima wancan jakin son Zeey ɗin yake yi. Har sai daya zo kusa dashi a mota ya sake mai wani kallan takaici ya kalli kafafunsa da suka sha wani tsohon takalmi, kai ya girgiza, Kamalu ganin irin kallan daya mai yasa ya harsuko yana kumfar baki yana cewa "Dallah Malan ware ko banza wacce kake so bata sanka ni take so Muhammad Kamal ɗan gata sarkin iya soyayya." Shidai Junaid wucewa yai kawai ya dinga jin dariya na zuwa mai, duk kuwa da bacin ran da yake ciki.

***** Tunda ya dawo wani abu bai shiga tsakaninshi da Asiya ba duk da a matse ya diro ƙasar amma annakiyar ƙazantar data haɗa tasa yaji sam baya son kusantar ta, to ita ma bata cikin yanayin daɗin rai tunda yace mata ba zasu koma ba shi yasa bata damu da rashin nemanta da bai yi ba. Yau sai ya tashi da tsananin buƙatuwa, haka nan ya daure ya shiga ɗakin Asiya ya tarar da ita a kwance tayi shame-shame sai shaƙar bacci take yi. Hannu yasa ya toshe hancin shi warin dake busowa daga toilet na hautsina mishi ciki. Kallonta yayi yaga yadda take bacci hankalinta kwance ga alama ita wannan warin daya cika ɗakin baya damunta. Ƙarasawa yayi jikin window ya bubbuɗe don iska ta shigo ko ya samu warin ya fita. Juyawa yayi ya kalli ƙofar banɗakin sai ya ganta a hangame, runtse idonshi yayi ya janyo ƙofar ya rufe banɗakin don baya son ma idanunshi suyi mummunan ganin da zai hana mishi zaman lafiya.

Tsaki yaja yana jin takaicin shigowa ɗakin Asiya da yayi sai dai yanayin daya tsinci kanshi a ciki ne ba zai iya haƙuri dashi ba idan ba ya fitar da abinda ya taru a mararshi ba. Ƙarasawa yayi gaban gadon ya ɗan bubbuga pillown da take kwance akai, shi kanshi pillow case ɗin yayi baƙi ƙirin da dauɗa if he's not mistaken kamar tun wanda aka shimfiɗa ne da aka kawota gidan bata canja ba. Tashi tayi tana mutsitsika ido, ganin Bello tsaye a kanta yasa ta haɗe rai tace "Malan lafiya zaka tashe ni ina bacci?" Wani irin wari ne ya buso fuskarshi data buɗe baki tayi magana, ai tuni zuciyarshi ta tashi yaji cikinshi na wani irin hautsinawa ɗan abinda yaci yana neman dawo mishi.

A sukwane ya fice daga ɗakin, yana shiga ɗakinshi ya faɗa toilet ya fara kelaya amai, tuni ɗan abincin da yaci ya fice sai kakarin kawai da yake yi. Daya tuna warin bakin Asiya sai yani wani aman ya yunƙuro mishi gashi cikin shi babu komai. Da ƙyar ya samu aman ha tsaya ya fito yana sauke numfashi, haba wannan masifa har ina? Shi yanzu da wanne zai ji fisabilillahi? Ga rashin aikin yi ga mata ƙazama Allah ya bashi, duk inda ya juya baya jin daɗi ya rasa inda zai saka ranshi yaji daɗi. Ƴar buƙatar data shigar dashi ɗakin Asiya ma tuni ta kama gabanta tayi nata wuri don a yanzu sai yaji ko ɗan yatsanta ba zai iya riƙewa bare har ya haɗa jiki da ita.

Allah ya taimaki Baqeer da yanzu shi ake yiwa wannan ƙazantar shi da baya son ƙazanta ko misƙala zarrati. Koda yake hakki ne shima yake bibiyar shi hakkin abinda ya yiwa Baqeer gashinan yana ɗanɗana kuɗarshi a hannu. Dana sani iya dana sani Bello yayi ta akan abinda ya yiwa Baqeer gashi nan tun ba'a je ko ina ba yaga sakamakon abinda ya aikata.

***** Tunda ta hau titi take sharara gudu fatanta kawai ta ganta a gaban Ummi ta kwanta a kafaɗunta tayi kukan baƙin cikin da yake damunta, tayi kukan rabata da masoyinta da ake nema ayi, tayi kukan yaudararta da soyayyar bogi da Mummy tayi, tayi kukan tausayin abinda ɗan uwanta na jini ya jawa Baqeer, tayi kukan abubuwa da yawa data rasa a rayuwarta saboda riƙon taɓararru da Mummy tayi mata. Hannu tasa ta ɗauke hawayen daya zuba daga idanunta, duk ta tuna yadda Mummy ta dinga raina musu wayo tana ƙara nesanta su da mahaifiyarsu suna jin haushinta sai taji zuciyarta ta ƙuntata, ta rasa laifin me suka yi mata data yi musu irin wannan zaluncin ta shiga tsakaninsu da mahaifiyarsu tasa mahaifinsu ya hana su zuwa inda take ya kuma hana ƴan uwanta zuwa su gan su. Ribar me Mummy taci da duk tayi hakan bayan basu aikata mata laifin komai ba. Hukuncin Allah ne kawai ya kai Zainab Ɗambatta lafiya don bata da wata nutsuwa haka nan tayi tuƙin har Allah ya kaita garin lafiya. A wani wajen sayar da layin waya ta tsaya ta sayi sabon layin mtn aka yi mata register ta biya ta bar wurin. Dole ta canja layi idan har tana so ta nesanta kanta daga Baqeer, tana jin nauyinshi tana jin nauyin ƙara haɗa ido dashi sabida abinda Kabir yayi mishi, gashi Daddy yayi rantsuwa ba zai aura mata shi ba, ita kuwa baza ta iya aurenshi ba har sai Daddyn ya amince da batun auren da kanshi, a yanzu kuwa tasan abu ne mai wahala yayi hakan, bata so ta cigaba da jin muryarshi ko ta ganshi don tasan rabuwarsu zata yi musu matuƙar wahala.

Tana yin parking motarta a ƙofar gidan Ummi, Inaya na dawowa daga makarantar islamiyya. Tana ganin motar Zeey ta tsaya a ƙofar gidansu ta rugo a guje tana murna. Sauri tayi ta goge hawayen fuskarta ta fito daga motar tana dariya, buɗe hannayenta tayi Inaya ta shige jikinta ta rungumeta. "Aunty Zeey ashe zaki dawo da wuri?" Ta tambayeta tana ɗaga ido ta kalli fuskarta, ɗan ɓata fuska tayi ganin yadda fuskar Zainab tayi jajawur da kumbura saboda kukan da tayi. Cike da kulawa tace "Aunty Zeey me aka yi miki? Kuka kika yi ko?" Girgiza kanta tayi tace "A'a abu ne ya faɗa min a ido shine yayi tayi min zafi amma yanzu ya fita." Ɗaga kai Inaya tayi alamun ta fahimta, suna riƙe da hannun juna suka shiga cikin gidan. Tun daga harabar gidan Inaya ke ƙwalawa Ummi kira tana ceqa "Ummi fito ki gani Aunty Zeey ta dawo," har suka ƙarasa cikin parlourn. A tsaye a bakin ƙofar kitchen suka tarar Ummi ta zubawa ƙofar parlourn ido tana so taga shin da gaske ne abinda taji Inaya na faɗa ko kuwa. Zeey na shigowa taga Ummi kawai sai ta ruga a guje ta rungumeta tana sakin wani irin kuka mai ciwo, hannu Ummi tasa tana bubbuga bayanta a hankali dan tabbas tasan wani abu ya sake faruwa.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce* Da *Ayusher Muhd*

*BAQEER* *NA*

*AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA TARA*

{89} Ummi bayan ta kawai take shafawa har sai da ta gaji da kanta ta tsagaita da kukan, Inaya kam tana gefe tayi tsuru duk zuciyarta ba daɗi ganin Zee na kuka, ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta kamo hannunta tana cewa "Inaya ki je ki cire kayan islamiya ki watsa ruwa kizo kici abinci." Ba musu tayi ciki su kuma suka shiga ɗaki, da yake Zee ta saba shigewa jikin Mummy sai take jin yau ɗumin jikin tata mahaifiyar take so, kanta ta kwantar akan cinyar Ummi tana maida kukan dake neman ƙara tasowa, Ummi ce ta daure tace "Ki kwanta in kin ware anjima sai muyi magana," tayi maganar tana zare jikinta don ta kula Zee na buƙatar kaɗaicewa, da sauri Zee ta riƙota tana girgiza kai tana cewa "Ummy karki tafi don Allah, gaba ɗaya duniyar nan bata mini daɗi wurinki kaɗai nake sa ran samun sauƙin abinda ke damuna." Kallonta Ummi tayi ta dawo kusa da ita ta zauna ta kamo hannayenta tare da juyo da ita saitinta tace "In ɗan adam ya shiga damuwa me yake cewa?" Wasu hawaye ne suka zubo tace "Nayi addu'o'i Ummi kawai zuciyata ce nake ji kamar zata buga." Kallon da Ummi ke yi mata ne yasa tace "Allahumma inni a'udhu bika minal-hammi wal-Ḥuzni, wal-ajazi wal-kasli wal-bukhli wal-jubni wa ḍala'id-dayni wa ghalabatir-rijal." Lumshe ido tayi, Ummi ta saki murmushi kaɗan kafin tace "Ke da Halima ne?" Kai ta girgiza sai kuma hawaye ya sake zubowa tace "Ni da kowa ne ma Ummi wanda nake so an hanani aurenshi, Daddy ya takura sai dai na auri Junaid kuma ni bana sonshi," ta kalli Ummi tana jin wani zafi a ranta tace "Ummi don yana gurgu shikenan sai ya zama abun ƙyama?" Mamaki ne ya bayyana a idon Ummi tace "Gurgu ne?" Zee ta jinjina kai tana goge fuska tace "Kema nasan ba yadda zaki yi ba sai dai wanda ya ja mishi abun...." Sai kuma tayi shiru don bata son ta ɓata Kabir a wajen Ummi tun kafin ma su haɗu, ita dai Ummi baza tayi ƙarya ba amma tabbas ba zata yiwa yar ta fatan auren gurgu ba, Zee ta kalleta sai kuma tayi shiru kawai don bata son ta ɗagawa Ummi hankali daga zuwa, kai kawai ta girgiza alamun babu komai tana ciza ƙasan leɓenta. Ummi ta shafi saman kanta tace "Ki tashi kiyi sallah kici abinci naga babbar jaka kika zo da ita a hankali sai mu tattauna." Kai ta ɗaga alamar to, hakan yasa Ummi fita, tana maida ƙofar ta rufe ta bi ɗakin da kallo cike da tausayin Zee tabbas abubuwa da yawa sun faru sai dai da alama na saurayin yafi damunta, a hankali zata kula da yarta za kuma ta gina shaƙuwar da suka rasa, kuskuren da tayi a baya na barin Halima ta gaje mata yara ba zata sake makamancinshi ba yanzu. Zee kuwa a ɗakin alwala tayi bayan tayi sallah ta kwanta akan sallayar ta zubawa wayarta ido, number Baqeer take nema bayan ta goge komai dake cikin wayar ɗazu, wayar ta ɗaura akan kirjinta tana jin wani raɗaɗi na rashinshi na damunta, kalaman Badaru ne ke sake dawo mata, ashe yayanta ne duk ya janyo mishi wannan bala'in? Ta runtse idanuwanta wanda suka ƙanƙance saboda kukan da tasha.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull