Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 67

Baqeer complete - Chapter 67

Baqeer complete Chapter 67: Baqeer complete Chapter 67. ***** Baqeer tunda Zee ta tafi ya turo ƙofa ya rufe ɗakin shi, abincin data bashi ya tura gefe don…

3,090 words

***** Baqeer tunda Zee ta tafi ya turo ƙofa ya rufe ɗakin shi, abincin data bashi ya tura gefe don ko alamun yunwa ma baya ji, ko idanuwanshi ya runtse sai ya dinga ganin Zee tana yi mishi murmushi, hannu yasa ya ɗan matsa saman girarshi sannan ya janyo takarda ya fara sketch, yi kawai yake yi kamar wanda ake zubowa basirar, ji yayi hannunshi na ɗan zafi hakan yasa ya ajiye pen ɗin tare da dafa saman kanshi dake ciwo, maimakon ya daina sai ya janyo shaddar daya siyo kawai ya bajeta ya sauka daga kan kenenshi ya fara yankawa, sai daya gama fitar da komai sannan ya ajiye scissors ɗin tare da duba agoggo, magriba yaga tayi ya turo kekenshi ya fito. Dada tana ganinshi tace "Anga dama an fito? Banda shirme in kana sonta da gaske ai ba haƙura zaka yi ba, sannan ko kunya ka shige ɗaki ka barta ta tafi gida da kanta." Shi dai bai ce komai ba sai bandaki kawai daya wuce. Bayan yayi sallah ya ji zuciyarshi ta kasa nutsuwa sunan Zainab ya kalla cike da damuwa ya danna kira ai dai ko ba komai ta cancanci kulawar shi don yadda ta bar gidan nan yana tsoron wani abun ya sameta, da sauri ya kashe kafin wayar ta shiga ya kifa kan wayar tare da sake wani dogon numfashi, yadda yake jin zuciyarshi na zafi ko Asiya da suka dade tare bai ji rabin abinda yake ji akanta ba bayan sun rabu. Wayarshi ce yaji ta fara ƙara da sauri ya ɗauka yana fatan Allah yasa Zainab ce, ga mamakinshi Umma ce yanayinshi kaɗai zaka san ba haka yaso ba sai dai Umma ce ita kanta yana son jin muryarta. Ɗauka yayi bayan sun gaisa cike da kulawa tace "Baqeer dama Zainab sonta kake yi?" Yawun bakinshi ya haɗiya kafin yace "Ba dai Baba ya huce akan ki ba? Umma don Allah ki kwashe kayanki daga gidan nan zan zo na ɗaukeki," yayi maganar a ɗan hasale. Cikin sanyin murya tace "Ba maganar da muke yi kenan ba, taya zaka nemi janyowa kanka magana Baqeer? Kafi kowa sanin wanene Alhaji Sulaiman ka kuma san abinda zai yi akan yaran shi, ka sani ko da ƙafafunka ma ba baka Zainab zai yi ba." Baqeer ji yayi wani abu ya tokare mishi a maƙoshi, mikin da yake ƙoƙarin dannewa na neman tasowa, muryarshi ce ta ɗan sarƙe yace "Umma ban sani ba wallahi, sanda kuma nasan ita wacece nayi nisa da har nake jin zan iya gwada sa'a ta, duk wannan lokacin a matsayin ƙawar Maryam kawai na santa, ta canza kama sannan ban ma taɓa kawowa Zainab dana sani zata kula dani haka ba. Umma ita ce wacce a dalilinta nake zaune cikin kwanciyar hankali yanzu, na tabbatar Allah ne ya kawo min ita cikin rayuwata a lokacin da nake buƙatar wanda zai fahimceni, wanda zai nuna min hanya ya hanani faɗawa wani hali, Umma tunda nazo gidan Dada nake roƙon Allah ya ɗauki raina na huta sai dai ita ce ta nuna min kuskurena ta kuma sani fara sana'ar da nake yi yanzu, ni....ni!" Kasa cigaba da magana yayi kawai sai ya runtse ido yana haɗiyar wani abu mai ɗaci da yaji ya tokare mishi maƙoshinsa. Umma tausayin ɗan nata ya kamata, lallai da ta sani tun sanda tasan Zainab ce data tuntuɓeshi kila da lokacin bai mato a sonta kamar yanzu ba don kalamanshi kaɗai sunsa tasan yana sonta sosai. Murmushi yayi na yaƙe yace "Baba yayi halin nashi ko?" Cike da tausayin ɗan nata tace "Babu komai ni faɗanshi baya damuna, kai kuma In Sha Allahu Allah zai dubeka ya baka lafiya zai kuma baka wacce iyayenta zasu soka." Murmushi kawai yayi don Ameen ɗin ma ji yayi ya kasa cewa don in dai aure ne to da Zainab kawai yake son zama, ɗan shiru yayi kafin yace "Don Allah Umma karki sadaukar da farin cikin ki saboda ni, babban burina a duniyar nan na faranta miki shi yasa babu amfani na ganki cikin ɓacin rai, ki bar gidan kamar yadda yace miki kizo mu zauna, ni hankalina zai fi kwanciya in kina nan zan kuma fi maida hankalina wurin sana'a ta, sau da dama barin Dada ita kaɗai baya mini daɗi ta kawo girman da take buƙatar wani tare da ita," ya ƙarasa maganar yana rage murya zuwa rashin jin daɗi. Ta sani sarai duk abinda ya faɗa daidai ne hakan yasa tace "Shikenan zan yi tunani skai." Cike da jin daɗi ya amsa mata sannan suka yi sallama. Number Zainab ya sake dubowa ya kwantar da kanshi a bayan wheelchair ɗin yana tunani, sai dai baya ji yana da ƙarfin iya kiran ta. **** Yau kwana huɗu kenan da tafiyar Zee Ɗambatta sosai suka ƙara shakuwa da Ummi da Inaya, shi kanshi Mubashir da bashi da yawan magana sosai sai da Zee tayi ƙoƙarin janshi a jiki, ko waya Abba yayi haka Inaya zata yi ta bashi labarin abubuwan da suka yi da Aunty wanda abun ba ƙaramin daɗi yake yi mishi ba, yana son Ummi sosai shi yasa yake jin daɗi ganin tana cikin farin ciki, yaso Ummi da farko sai dai bai sanar da ita ba saboda shi abokin yayanta ne, in yazo wurin abokinshi yana ganin Sulaiman yazo zance, wannan dalilin yasa bai sanar da kowa son Ummi da yake yi ba, yaja bakinshi yayi shiru har tayi aure shima yai aurdnshi, sai dai aurenshi bai daɗe ba matarshi ta rasu a wajen haihuwa ta koma ita da babyn da ta haifa, wannan dalilin yasa ya ajiye batun aure ya maida hankali wurin aikinshi, shekarar matarshi huɗu da rasuwa auren Ummi ya mutu, yazo Ɗambatta hutu ya ganta wannan dalili yasa ya sanar da yayan Ummi don baya son ya sake bari ya huce, bayan aurensu Ummi ta haifi Mubashir daga nan kuma sai ta dinga ɓari babu haihuwa, ƴan uwanshi suka fara canza mata saboda suna son yayi aure suna ganin aikin da take yi ne kila yasa ma cikin yaƙi zama. Ƴar uwarshi suka bashi akan ya aura yace fir ba zai aureta ba, sai dai Ummi ta nuna mishi rashin dacewar hakan, daga baya ya amince da auren sai da aka zo daf da auren suka gane ashe akwai wanda take so, auren shi kawai zata yi saboda yana da kuɗi amma ba wai don ta rabu da saurayinta ba. Ba ƙaramin ɓacin rai ya shiga ba yaci zarafinsu akan kar wanda ya kuskura ya ƙara yi mishi maganar ƙara aure matarshi ta isheshi baya buƙatar ƙari. Tun daga nan Ummi ta samu salama suka daina ƴan maganganu, daga baya Allah ya bata cikin Inaya, wanda ganin tasha wahala sosai wajen haihuwarta yasa yace to haihuwar ta isa haka su biyu sun isa, da kanshi ya zaɓawa Inaya sunan Zainab don ya san tsananin son da take yiwa ƴaƴanta kawai dai kawaici take yi take kauda kai. Shi yasa yanzu ya tabbatar Ummi na cikin farin ciki wanda hakan shi kuma ba ƙaramin daɗi yake yi mishi ba. Yau Ummi ce a kitchen ita da Zainab da Inaya, aikin girki ake taya Ummi, sai dai Zainab duk ta zama ƴar kallo tana tsaye tana ganin yadda Inaya ke taya Ummi yanke-yanke amma ita tana farawa Ummi tace ba haka ba. Baki ta turo tace "Ummi to wai ita wannan ƴar mitsilar ya aka yi take iya yin wannan yankan ƙanana?" "Kema haka nan zaki koya kuma ga naki nan kada na kuskura naga kinsa Inaya ta miki." Baki ta turo ta shiga daddagewa tana yankawa, ganin ta yanka daidai yasa ta daka wani tsalle ta kalli Ummi tace "Ummi Ummi kalla, wallahi ni nayi." Kai kawai ta girgiza ganin yadda take murna kamar wacce tayi wani abun kirki. Sosai Ummi ke ƙoƙarin janta a jiki da kauda mata tunanukan da take yi, sai dai duk sanda tazo kwanciya sai tayi kuka ta gaji saboda tunani da rashin Baqeer tana ji son Baqeer ya zama jinin jikinta, tunda tazo Daddy bai nemeta ba in ta kira kuma yana amsa gaisuwarta yake kashe wayar ko dama baya bata suyi magana, Mummy kuwa ko waya basu sake yi ba balle da Ummi ta bata labarin yadda ta shiga jikinta dasu har ta auri Daddy wannan dalili yasa ta ƙara tabbatar da makircin Mummy.

**** Baqeer kuwa ya tattara komai ya sashi a gefe, duk da Zainab na cikin ranshi amma ya danne bai bari a gane, shagonsu sun kammala gyarashi da sanya kayan aiki, yin aiki da mutanen nan ba ƙaramin alheri yake samu ba, hakan yasa yace ko ya buɗe shagonshi zasu cigaba da aiki tare, wani idea ne yazo mishi na yanda yake fitar da ɗinkin maza, style ne wanda ba'a taɓa ganin irinshi ba, sai suka yi meeting akan yanda zasu ƙayata ɗinkin ya karɓu a wurin mutane, Salim ya bada shawara akan su haɗa shi kamar gift su dinga sayawa kayan huluna da takalmi suna ɗaurawa a social media, designs ɗin jikin hulunan su suke bayarwa ayi musu sai suyi wa kayan aiki irin shi, keken da zai yi aikin sun yi sa'a ba irin wanda zai taka bane, yana daga zaune zai yi dan shi kaɗai yasan yanda yake son style ɗin ya kasance, kuɗin siyan injin aikin suka maida hankali wurin haɗawa don kuwa yana da tsada sosai, gashi baya so su je wani wurin suyi aikin wani yaga idea ɗin ya sace, dole su zasu fara in suka fara tallanshi wasu suka kwafa a kalla kowa yasan sune dai asalin masu abun. **** Yau Bello tun cikin baccinshi yake ji ana buga ƙofa, miƙewa yayi don sam basa kwana ɗaki ɗaya da Asiya, ganin ƙazantar ta na neman illa tashi yasa ya nemo mai aiki take zuwa safe da yamma tana gyara gidan ta tafi, Asiya sam bata damu ba sai ma wani halin banza data tsuro mishi in taga an gyara gidan sai ta ɗauki abu ta saida ta gayyato ƙawayenta suzo ayi ta hira ana koɗa jin daɗin da take yi a makeken gidan nan. Tsaki yayi jin buga ƙofar tayi yawa, ya fito yana murza ido don dama yau zai sake fita neman aiki ko Allah zai sa a dace, kwanan nan kuɗin cefane ma mahaifinshi ke basu. Ƙofar shigowa ya buɗe don yasan Asiya nacan na baccin asara, idanunshi ne suka sauka kan mai gidan daya basu haya, gaban Bello ne yayi wani mugun faɗuwa, ba dai har sun cinye kuɗin hayar su ba? Tabbas tun wancan watan yake ganin kiran mutumin yana ignoring gani yake yi surutun banza zai yi mishi. Yanda mutumin ke kallonshi ne yasa jikin Bello ƙara yin sanyi.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*

*BAQEER* *NA*

*AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN*

{90}

Murya na rawa yace mishi "Yallaɓai barka da asuba." A wulaƙance mutumin ya kalle shi yace "Kai ba wannan ya kawo ni ba," hannu ya miƙa mishi yace "Bani." Kallonshi yayi ya kalli hannun da yake miƙo mishi yace "Me zan baka?" Gabanshi yana dukan uku-uku don yasa yau dai ƙaryarshi ta ƙare. Wani irin kallo yayi mishi yace"Kuɗin hayata ko makullan gidana." Duk da yasan abinda ya kawo mutumin kenan sai da yaji wata irin faɗuwar gaba ta ziyarce shi, yanzu idan aka koreshi daga gidan nan ina zai je? Cikin ƙasƙantar da kai yace "don Allah kayi haƙuri zuwa..." Ɗaga mishi hannu mutumin yayi ya dakatar dashi daga abinda yake cewa yace "Tun wancan watan hayarka ta ƙare don rainin wayo ina ta kiranka a waya kayi banza ka rabu dani ko bin bayan ƙiran baka yi ba sai yanzu ne zaka wani karkace wuya zaka yi min ƴar murya, to bazan lamunta ba idan kana so ka cigaba da zama a gidana ka biya kuɗin haya idan ba haka ba kuwa ka tattara ya naka ya naka ka ƙara gaba ina da mutanen da zan sa a gidana."

Karkata kai yayi ya hau bawa mutumin haƙuri don yasan idan yace ya fita ya bar mishi gidanshi baya da wurin kamawa, "Dan Allah kayi haƙuri Yallaɓai kayi min lamunin kwana biyu In Sha Allah zan kawo maka kuɗinka har gida." Haka nan dai yayi ta bawa mutumin haƙuri har ya samu ya haƙura akan idan kwana biyu ta cika bai biya shi kuɗin hayar gidanshi ba zai fita ya bar mishi gida. Mutumin na tafiya ya juya ya shige cikin gida yana tunanin abun yi, yanzu a ina zai je ya samo wannan iyayen kuɗaɗen a cikin kwana biyu shi ba aiki ba shi ba wata sana'a ba. Ɗakin shi ya shige ko wanka bai yi ba ya canja kaya ya ɗauki makullin motarshi wacce da ƙyar ya samu Asiya ta dawo mishi dashi hannunshi ya fice daga gidan yana tunanin inda ya kamata ya fara zuwa. Tunani yayi gara yaje ya samu mahaifin shi watakila akwai taimakon da zai iya yi mishi. Bai damu mahaifinshi a gida ba fon haka ya bi bayanshi zuwa kasuwa. Ya yiwa mahaifinshi bayanin abinda ke tafe dashi. Wani irin kallo yayi mishi yace "To yanzu ya kake so ayi?" Ɗan shiru yayi yana sunkuyar da kai don sai yanzu yaji takaicin zuwan shi gaban mahaifin nashi bayan ko lokacin da zai kama hayar gidan sai da ya hanashi amma yaƙi ji, to amma idan ba Baban ba wurin wa zai je ya faɗi damuwarshi? Kanshi a ƙasa yace "Kayi haƙuri ka yafe min Baba, ban kasance ɗa na ƙwarai a wajenka ba duk abinda ka haneni dayi shi nake yi, wallahi nayi nadamar abubuwan da nayi tayi, ka taimakeni na samu na biya kuɗin hayar In Sha Allah zan yi ƙoƙari na biyaka cikin lokaci." Tsaki Baban yayi yace "Dame zaka biyani idan na ɗauki iyayen kuɗi da yawa tsababa na baka kai da ba aiki kake yi ba ba sana'a ba?" Da sauri yace "Ai ina neman aiki In Sha Allah ina sa rai da zan samu da an fara biyana zan yi ƙoƙarin haɗa maka kuɗin ka." Kallon baka da hankali Baba yayi mishi sai kuma yace "To ita motar da kake yawo da ita miye amfaninta da baza ka sayar ka biya kuɗin hayar ba?" Ai bai san lokacin da ya ɗago ya kalli Baba ba, taya zai ce ya sayar da motarshi motar da ita kaɗai ta rage mishi, kai gaskiya a'a ba zai taɓa yiwuwa ba sam ya sayar da motarshi. "To idan ba zaka sayar ba sai ka tattara ka bar musu gidansu idan yaso ka dawo gida ku buɗe ɗakinka na da ku zauna a ciki." Tashi yayi jiki a saluɓe ya bar wajen Baba, zai dai yi ƙoƙari daga nan zuwa kwana biyu yaga ya haɗa kuɗin hayar ya biya idan kuma hakan bata samu ba dole Asiya tayi haƙuri su tattara su koma gidansu da zama idan yaso sai su sayar da kayan ɗakin da yayi mata yaja jari tunda gidan nasu ɗaki ɗaya ne babu inda za'a zuba duka waɗannan kayan a ciki.

***** *BAYAN SHEKARA GUDA*

A cikin shekara guda data gabata Baqeer yayi nasarar buɗe shagon shi na ɗinki mai suna *MOHBAQ TAILORING SERVICES*, sosai Allah yasa mishi albarka a ciki ta yadda kullum cikin samun sababbin customers suke. Designs ɗin ɗinkunansu idan har suka yi maka baka taɓa ganin su a ko ina sai a jikin wanda suka yiwa irin shi. Saboda yadda suke tsara designs ɗin su yasa ba kowa ke iya kwafarsu ba masu gwadawar ma sai dai su kamanta amma ba dai suyi shi sak da sak irin yadda suke yin nasu ba. Sosai shagon shi ya samu karɓuwa saboda bayan kaya da mutum zai kawo su ɗinka mishi har da ready-made suna ɗinkawa daga kayan maza har na mata babu wanda basa ɗinkawa kuma duka styles ɗin da suke yi Baqeer ne ke ƙirƙirar designs ɗin su kuma yaran shagon sai su ɗinka yawanci ma shi yake yin yankan da kanshi ko shi ko Tanimu, ganin yana samun kuɗi sai ya zuba irin machines ɗin da yake buri, wasu irin machines ne da suke amfani da computer. Hoton designs ɗin da ake so kawai za'a saka shi zai ɗinka maka automatically don haka aikin yake zuwa musu da sauƙi, idan machines ɗin suka yi zanen surfanin da suke so su kuma sai su haɗe kayan. Bayan shi da Tanimu da ya kasance kamar manager a wurin ya ƙara samun wasu yaran da suke yi musu aiki saboda yadda suka samu karɓuwa ayyuka na yi musu yawa.

A yanzu haka ƙoƙarin buɗe wani branch ɗin yake yi. Shi dai a rayuwa babu abinda zai ce sai Alhamdulillah, yasan da ace har yanzu yana gaban Badaru ba lallai ya tsaya da ƙafafun shi yadda yake a yanzu ba, watakila da har yanzu yana nan yana paintings ɗin da kaso saba'in cikin ɗari na abinda yake samu na Badaru ne, abinda yake bashi bai wani taka kara ya karya ba wanda a ciki yake yin duk wasu buƙatun shi har ma ya ɗauki nauyin Umma da kuma ƙannenshi. Abu ɗaya ya kasa mantawa a cikin shekara ɗayar nan data wuce shine Zainab da soyayyarta, har yau ya kasa cireta daga cikin ranshi gashi ko kiranta yayi a waya baya samunta, ba sau ɗaya ba dau biyu ba yaje har gidansu sai mai gadi yace mishi bata nan tayi tafiya idan kuma ya tambayeshi inda ta tafi sai yace shima bai sani ba sai dai har yau bai cire rai da sake dawowarta cikin rayuwarshi ba hakan nema yasa ya kasa bawa wasu matan damar shiga rayuwarshi don a yanzu da Allah ya azurtashi sai ya zamanto ko nakasar tashi ba'a kalla shi ɗin dai kawai matan suke kallo ko kuma yace ƴan canjin hannunshi suke kallo, sai dai kuma sun makaro domin babu wani sauran gurbin ƴa mace a cikin zuciyarshi gaba ɗaya Zeey ta kankane tayi kaka gida, babu wata ƴa mace da yake iya kallo da sunan soyayya.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull