Baqeer complete - Chapter 68
Baqeer complete Chapter 68: Baqeer complete Chapter 68. Ƙarfe huɗu yake tashi daga shagon yana tattare cinikin da suka yi a ranar saboda ya kai banki kafin…
3,275 words
Ƙarfe huɗu yake tashi daga shagon yana tattare cinikin da suka yi a ranar saboda ya kai banki kafin ya wuce gida, duk da mafi yawancin customers ɗin sun fi yi musu transfer akwai waɗanda suke basu cash to baya son barin kuɗi a shago shi yasa duk yamma sai ya fara biyawa banki ya ajiye kuɗin kafin ya wuce gida shi da Tanimu da yake tuƙa Baqeer ɗin duk inda zai je a motar Baqeer ɗin, sai ya kai shi gida sannan ya koma shagon sai wajen ƙarfe tara sannan ya rufe gaba ɗaya a tashi daga aiki. Shi Baqeer baya zama ya kuşan dare idan ba aiki ne dasu da yawa ba saboda bai cika son yana yin nisa yana barin Dada ba saboda tsufa da take ƙara yi kullum abubuwa da yawa da take iya yin su a da yanzu bata iyawa. Baqeer ya gyara gidan Dada sosai ya ɗaukar mata mai aiki da take yi mata ƴan aikace-aikacen gida tana kuma zama da ita kada kaɗaici ya daneta bare da ba cika zama yayi a gidan ba. Haka nan ya wadata Umma da duk wani abu da zata buƙata sai dai gidan ne tunda ya bar shi ko layin gidan bai ƙara taka ƙafarshi yake ba, su Abu da Jamila suyi ta surutun a ina Umma take samun kuɗin da take kashewa bayan ita ba sana'a take yi ba, wani lokacin idan gulmar ta ciyo su sai suce suna ganin kuɗin filin da suka sayar ne har yanzu basu gama cinyewa ba suke ci da kaɗan-kaɗan shi yasa kullum bata rasa abun ɓatarwa. Ita dai tana jin su ko kallonsu bata yi domin bata da lokacin tsayawa biyewa shirmensu. Babu yadda Baqeer bai yi ba ta bar gidansu taƙi sai dai akwai plans ɗin da yake yi yana kammalawa zai je ya ɗauketa daga gidan dan yasan tun tasowarsu take haƙurin zama a ciki ba ga mai gidan ba ba ga abokanan zamanta ba kowa ba daɗinsu take ji ba.
***** Sosai Zainab take jin daɗin zama a wajen Ummi bare da Ummi take janta a jiki, duk wani aiki idan zata yi zata sakata a gaba suyi tare, tun tana kwaɓawa har da kaɗan-kaɗan tazo ta fara iyawa. Sabuwar tarbiyya Ummi ta yiwa Zeey duk da take da kyakkyawar zuciya tana da rashin tsoro da faɗin duk abinda yazo bakinta bata duba girma ko shekarun mutum duk yadda magana tazo bakinta haka zata kwaɓa mishi ita. Akan haka sai da Ummi tayi da gaske da yawan faɗa da nasiha kafin ta samu ta daina. A harkar kitchen ma babu laifi ta iya abubuwa da dama don a yanzu wai har Ummi ta fita ta bar mata girki tayi kuma ya ciyu babu wani gyara, haka nan ɓangaren kula da gida da tsaftarshi yanzu duk Zainab ta iya. Sai take jin rayuwarta wata daban da wacce take yi da, ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali komai tana yin shi cikin ɗa'a bata yin abu da graje kamar yadda take yi ada. Tunani ɗaya ne ya kasa barin ranta shine na Baqeer, duk tsawon wannan lokacin bata manta dashi ba haka yasa taƙi bawa duk manemanta dama, har a cikin cousins ɗinta da yawa sun ce suna sonta taƙi amincewa saboda ta riga ta ƙudurce a ranta idan har ba Baqeer ba bata ga wanda zata aura ba, akan hakan ne ma suke yawan samun saɓani da Ummi don a yanzu burinta taga auren Zainab ɗin ita kuma tace idan har ba za'a aura mata Baqeer ba ta haƙura da auren.
Lokaci zuwa lokaci take ƙiran Daddy a waya amma daga gaisuwa babu abinda ke ƙara shiga tsakaninsu, ko ta neme shi da hira ma baya amsawa haka zata yita takale-takalen zancenta ta haƙura saboda baya amsa mata saboda haushin yadda ta kunyata shi a wajen mahaifin Junaid bayan sun gama magana tasa ƙafa ta bar gidan ta kuma cewa Junaid ɗin lallai yaje ya faɗawa Babanshi ya janye don baza ta aureshi ba, mahaifin nashi da kanshi ya kirashi yace abar maganar kasai tunda dai yarinya bata so. Shi kuwa Kabir kota ƙira shi ma baya amsawa saboda haushinta da yake ji na yadda ta zaɓi Ummi akan Mummy da tasha wahalarsu a faɗarshi, yadda Mummy take langwaɓe mishi tana nuna shi da Zainab ne farin cikinta don Allah kada ya guje mata kamar yadda Zeey ta gujeta hakan yasa yake ƙara jin haushin Zeey ɗin akan abinda tayi shi yasa ko ta ƙiranshi a waya tai baya amsawa.
Zaune akan doguwar kujera a parlour tana danne-danne a waya, Instagram ta shiga tana kallon hotunan ɗinki da Baqeer ya ɗora a pg ɗin shi, bi take yi tana scrolling through wani farin ciki na ratsata idan ta kalli hotunan taga wai wannan aikin Baqeer ɗinta ne, Baqeer ɗin da ake yiwa kallon nakasashe wanda ba zai iya amfanar kanshi da komai ba yau gashi yayi setting up business ɗin da ba kowa ne zai iya ba. Wani alfahari take ji ganin yadda kullum ƙara haɓaka yake yi yana samun karɓuwa kamar shi kaɗai ne tela duk wani mai ji da kanshi a kuɗi da harkar gayu to kayan *MOHBAQ* ne abun tu'ammalin shi. Manyan mutane da yawa a wurin shi suke ɗinki, wannan kaɗai abun farin ciki ne a wurinta na ganin yadda rayuwarshi tayi changing for the better.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar* Da *Ayusher Muhd*
*BAQEER* *NA*
*UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA ƊAYA*
{91}
Baqeer gaba ɗaya ya zama busy, yau suka yi cinikin gidan da ya siya ya kuma bada rabin kuɗi akan zai biya ragowar ƙarshen wata, gida ne mai masifar kyau sannan babba ne part biyu ne a gidan gate din shiga ne kawai a haɗe amma kowa bangarenshi daban, so yake ya dawo da Dada da Umma ɓangare ɗaya shi kuma ya zauna a ɗaya, Salim ma a gefenshi kaɗan ya sayi nashi gidan don yanzu soyayya ta kankama tsakaninshi da Habi, abun na bawa Baqeer dariya yanda in suna soyayya yana shigowa zai fara wayancewa, wani sa'in sai yace "Ai kawai hirar zumunci suke yi." Baqeer in yaji haka sai yace "Ai na ɗauka ta koma ƙanwarka ne ai." Tun farko Baqeer yasan da ita ne don Salim bashi da budurwa, wanda Baqeer ya tabbatar don yana son Habi ne ya hanashi yin wasu, shi kuma kunya yake ji a yanzu yace yana son Habi saboda abinda ya faru tsakanin Baqeer da Asiya, sai dai ko kaɗan wannan abun bai damu Baqeer ba don kuwa Asiya sam bata gabanshi ko tunota inba da dalili ba baya yi, shima lokaci-lokaci Salim ne ke maganarta wai Habi tace mai sun koma gidan su Bello da zama, kai kawai ya jinjina, kwanaki ma Salim ya kwashe da dariya yana bawa Baqeer labarin koro Bello da aka yi wai Asiya tayi yaji akan komawarsu gidan shine take faɗar dalilanta wanda anan suka ji, Babansu kuwa ya zuba mata ido sai gashi ko sati ba ayi ba taga gwara ta tattara ta koma gidansu Bellon a ƙalla can yafi gidansu. Ko da Baqeer yaji kai kawai ya girgiza bai taɓa musu fata mara kyau ba balle yayi murna da abinda ya samesu. Kallon gidan yayi yana tunanin abubuwan furnitures da zasu buƙata, wayarshi ce tayi ƙara ƙirar iphone 14pro max ya ɗauka tare da amsawa, wasu masu son kaya ne ready made a US suke suke so ayi musu shipping, nan ya musu bayani ya ɗauki details na yanda suke so da sizes ɗin su sannan yace nan da 7days za'a kammala saboda suna son kayan da yawa, account number ya tura musu ko minti biyar bai yi ba suka turo mishi da zunzurutun kuɗin shi, maida wayar yayi ya ajiye ya runtse idonshi tare da ƙara maida kanshi bayan hadaddiyar electric wheelchair ɗin daya siya wacce take tuƙa kanta sai dai yayi controlling ɗinta kawai da remote, ƙafafunshi na samun sauƙi sai dai har yanzu baya iya takasu, yana dai iya tsayawa ya hau kujera amma baya iya tafiya a kansu, ya canza asibiti na ganin physiotherapist don jikinshi na bashi Zee auren Junaid zata yi shi yasa sam baya son zuwa balle yaji abinda zai tada mishi hankali, fitowa yayi daga gidan Tanimu na waje yana jiranshi a mota, Baqeer ya buɗe mishi baya wanda ya kunna abinda ya sauko don wheelchair ɗin ta shiga kai tsaye. Kallon Tanimu yayi yace "Malam Tanimu kai dai ka dage baza ka zauna a shago ba kullum dai sai dai muje guri tare kaƙi yarda a nemi driver." Dariya yayi bayan ya shiga ya zauna yace "Ba komai ni hakan yafi min daɗi." Baqeer na shiga ya maida kanshi jikin kujera ya lumshe ido kamar yanda yanzu ya saba wa kanshi tunanin Zee a kusan duk sanda ya kaɗai ce, idanuwanta yake hangowa a ranar da ya ganta na ƙarshe, buɗe ido yayi a hankali sannan ya kalli waje, ko tana ina? Ya kira wayarta har ya gaji, ranar Salim har kasa jurewa yayi yaje ya tambayar mishi ko ta dawo aka ce har yanzu bata dawo ba. Murmushi mai sanyi yayi ko sai yaushe zai cireta a ranshi? Sai dai haka kawai yake ji tunaninta shike taimaka mishi yake rayuwa cikin farin ciki don ko yaya in ya tunota sanyi yake ji a cikin ranshi. Wayarshi ce ta sake ƙara ya ɗauka ma abin business ne sai yaga kiran Hadiza, ɗauka yayi suka gaisa kafin ya rufe baki tace "Ya Baqeer don Allah kana ina? Kazo gida in da hali don Allah yanzu." Cike da damuwa yace "Meke faruwa? Don yanayinta kaɗai yasa yasan ba lafiya ba, bare shi ko hanyar gidan ma rabonshi da ita ya manta bare mutanen gidan. Cikin muryar raɗa tace "Case ake yi akan kayan da Kamalu ya sato a shagon wani, to matsalar yanzu sun kawo police suna ƙoƙarin tafiya da su Umma da Baba sun ce mutanen gidan kaf sai sun yi bayani." Mamakin kalamanta ne suka rufeshi yace "Ban gane ba? Shi Kamalun yana ina?" Ta girgiza kai tana ƙoƙarin yin kuka tace "Ban sani ba wallahi, nima Umma ce ta kirani bata so ka sani ni kuma naga ba abinda zan iya yi." Tanimu ya kalla yace "Don Allah Tanimu kai ni wurin Umma." Da yake yasan gidan saboda saƙon da wani sa'in yake kaiwa ko kuma in Umma tayi musu miya yazo ya amsa. Nan suka yi sallama da Hadiza hankalinshi duk ya gama tashi, dole bazai ƙara barin Umma ta zauna a wannan gidan ba don ba zai iya ɗaukar wannan ɓacin ran ba, amma yaushe Kamalu ya fara sata haka? **** Badaru a fusace yake kallon Abu yace "Ke dai wallahi aurenki bai daɗa mini komai ba sai ɓacin rai, ɓarawo a gidana? Wallahi yau sai kin bar min gida," yayi maganar yana kallon kayan da aka fito dashi daga ɗakinta wani lace ya janyo yace "Wannan ba shine lace ɗin da aka kawo mana bara ba nazo nan gidan ina faɗan an min sata?" Bashir ya miƙawa ya kalla kafin yace "Shine." Badaru yayi mata wani kallon takaici yace "Kema dai ɓarauniyar ce ashe, dama ni ina mamakin inda kike samun kuɗi ashe kuɗin sata kuka haɗu ke da ɗanki kuke ci? Yanzu kaf shagona in aka zazzage ba za'a samu rabin kayan da aka fito dashi daga ɗakin ki ba," cikin harzuƙa yake magana, har wani kumfar baki yake fitowa da ita saboda masifa. Jamila ce ta girgiza kai tace "Abu gaskiya ku canza hali wallahi me za ayi da hakin ɗan ɓera." Wani mugun Kallo Abu tayi mata tace "Dallah Malama rufe min baki ai dai ni anga me nake yi kuma ke kanki kin san bani ke satar ba, sannan in ma kuɗin satar ne ai dake ake ci, ke waya san me ƴarki take yi a Saudia? Ko kina tunanin bamu san aurenta ya mutu ba yawon karuwanci take yi tana turo miki kuɗi?" Nan fa Jamila ta kawo bango ta nufo Abu da sauri zata cakumota, Badaru ya daka musu tsawa yace "Kun yi mini shiru ko sai ranku ya ɓaci, ƴan sandan dake waje ne suka shigo saboda hayaniyar da ake yi, Umma na tsaye a gefe tana kallonsu, police ɗin na shigowa yace "Dukansu zasu wuce dasu yanzun nan don satar da Kamalu yai babba ne bakuma zasu sakesu ba sai yazo." Jamila ce tayi saurin cewa "Officer nifa babu ruwana daka ganni nan, bani da haɗi da ita don Allah ka tafi da ita amma banda ni da yarana." Badaru ne ya kalleshi yace "Ka tafi da ita Yallaɓai mu wallahi bamu san me suke aikatawa ba sannan nima sun min sata ka ajiyesu a musu hukunci har da nawa." Kallonsu yayi ya nunawa ragowar ma'aikatan akan su kamasu duka, Hadiza ce tace "Amma ita Umma menene laifinta?" Wani kallo yayi mata yace "Ita ma wannan kayan da aka ɗauko daga wurinta ina ta samesu? Na tambayeta taƙi faɗa kuma kowa yasan bata sana'a don mijinta ma ya shaida har satar fili tayi mishi wannan ma don ta sata ba wani abun bane." Mamaki ne ya rufe Hadiza ta kalli Badaru tace "Baba baka ji kunyar bada shaida kan matarka ba?" Nunata yayi da yatsa yace "In ba so kike ranki ya ɓaci ba ki ɓacen da gani, ƙarya aka mata? Sannan ina take samun kuɗi in ba satar take yi ba?" Jamila tayi caraf tace "Satar ce ma don wallahi Malam har kuɗi dunƙulallu tana dasu ai dai baza ace har yanzu kuɗin fili take ci ba. Bashir ne yace "Ita kuma Hajiya ta fa?" Officer yace "Ita ma mai gidan ya bada shaida tana sa mai hannu cikin aljihu in har zata yi sata a aljihunshi kenan zata iya bawa Kamalu dama ta taimaka mishi yayi sata ita ma ta samu, sannan satar da yayi ba ƙarama bace bare musa ran zaku iya biya don haka dukkansu wucewa zamu yi dasu." Waje suka fito ana ƙoƙarin watsasu cikin bayan motar ƴan sandan. "Sorry to say amma banda Uwata," abinda suka jiyo kenan ta bayansu, gaba ɗayansu suka waiga don Jamila har da ture kafaɗar Badaru tana son ganin waye yayi magana da kakkausar murya haka. "BAQEER?" Gabaki ɗayansu suka ambata baki a sake, Umma kallon Hadiza tayi wacce tayi saurin kawar da kanta, ƙarasa rufe ƙofar haɗaɗɗiyar motarsu Tanimu yayi wanda yasa gaba ɗayansu suka sake buɗe baki suna bin motar da Baqeer da kallo cike da mamaki, Baqeer ya tsaya da kekenshi don ko gidan bai son gani, kallon officer ɗin yayi tare da miƙa mishi hannu alamar su gaisa, ganin motar kaɗai da kayan jikinshi da yanayinshi kaɗai yasa yasan lallai akwai maiƙo a tare dashi, miƙa mishi hannu yayi da sauri yace "Kai kuma wanene Alhaji?" Baqeer ya zaro business card ɗinshi yace "Sunana Baqeer kamar yanda ka gani ina da business mai kyau da zan iya kula da mahaifiyata, kaya da kuɗi daka gani ni nake tura mata don haka baku da hujjar tafiya da ita." Kai ya shiga jinjinawa yana cewa "Ai bata yi bayani bane shi yasa, amma yanzu kaga ai mun san babu ita a ciki." Hannu yasa ya ciro kuɗi dubu hamsin ya miƙa mishi yace "Asa kati nagode." Ɓoyewa yayi yasa aljihu yana cewa "Godiya muke, kai dai Malam baka kyauta ba tunda kasan ita ba ɓarauniyar bace miye na kiran sunanta." Badaru kam kamar an ƙamar dashi don rabonshi da Baqeer har ya manta, Jamila ce tayi saurin nufar Baqeer har tana taka ƙafar Abu tace "Ɗan albarka Baqeerun mu, ina ka shiga? Sai tunanin ka nake yi ko jiya sai da nayi mafarkinka ina ta Allah Allah na bawa Fatima labari na manta." Bai ko kalleta ba bare ya tanka mata sai kallon Ummanshi da yayi yace "Umma mu wuce?" Jamila ta kamo kafaɗun Umma tace "Allah sarki Fatima dama na faɗa miki Baqeer Allah yayi rabon arziƙinshi a duniya yanzu kinga maganata ta tabbata, to ai mu ba wanda ya kai mu farin ciki." Abu ce ta taho da sauri tace "Baqeeru don Allah ka taimaka kasa a nemo Kamalu ni tsoro nake kar naje wani abun ne ya sameshi, naji zan je police station amma don Allah ka taimaka min wannan mahaifin naku babu abinda zai yi saima ya ƙara janyo mishi masifa, don Allah ka taimakeni." Jamila ce ta ture ta gefe tace "Ahh lallai Abu ko kunya ma ba kya ji? Naga kece kika jawa Fatima har ana cewa za'a kulleta? To yanzu ba kunya shine ma kike so ɗanta ya taimaka miki? To ba dai Baqeerun mu ba." Mamaki kawai ya hana Umma magana tana mamaki yanda ko kunya basa ji duka su biyun, Badaru ya ɗan kalla kaɗan wanda har yanzu kallon Baqeer yake yi jikinshi duk yayi sanyi kamar bashi da laka, yanda Badaru yake wai yau shine ko kalma ɗaya ya kasa furtawa. Hadiza kam jan hannun Umma tayi ta cusata cikin mota sannan ta koma ciki don ta kwaso kayanta, Baqeer ne ya kauda kai yana neman juyawa, Jamila ta saki ƙaramin ihu tana cewa "Baqeer kar kayi mana haka don Allah, ni kafi kowa sanin duk abinda nayi ba'a son raina nake yi ba, kaima kasan yanda nake ji da kai a rayuwar nan, ko ka manta sanda Bashir ya dinga taimakon ka? Ai ko ba don ni ba sai ka tuna shi, da wahalhun da yayi maka, wayyo ni Jamila." Baqeer kallon Bashir yayi wanda ke tsaye yana share ƙwalla, tabbas ko ba komai Bashir ya taimakeshi, Umma ce ta fito daga motar ta kalleshi kallon da ba sai tayi mishi bayani ba yasan irin kallon. Waigowa yayi ya kalli Abu dake kuka sannan ya kalli officer yayi mishi alama daya matso gefe suyi maganaa, sunyi minti goma suna magana kafin ya amshi number mai shagon akan zasu nemo Kamalu sannan suka ja mota suka tafi. Jamila ce tace "Baqeeru Allah yayi maka albarka don Allah nima kar ka barni anan gidan ka tafi dani kaga a ƙalla Fatima ta samu abokiyar hira." Hadiza data fito da jaka bata san sanda dariya ta kwashe mata ba ta girgiza kai tana mamakin yanda mutane basa kunyar nuna zalamarsu da rashin kunyarsu a fili. Abu ce tace "Nima don Allah a tafi dani." Hadiza baki ta saki tace "A koma gidan miji ayi biyayya don Allah."
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA*
*UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA BIYU*