Baqeer complete - Chapter 69
Baqeer complete Chapter 69: Baqeer complete Chapter 69. {92} Kallon cikin motar Umma take yi tana ƙara godewa Allah da irin baiwar da yayi wa ɗanta, da…
2,322 words
{92} Kallon cikin motar Umma take yi tana ƙara godewa Allah da irin baiwar da yayi wa ɗanta, da Badaru ya koreshi saboda yana ganin babu wani sauran amfani da zai yi mishi sai korar ta zame mishi alheri gashi yanzu sanadin hakan Allah yayi mishi arziƙin da ba lallai yayi ba idan a gaban Badaru yake. Shiru tayi a cikin motar ta kasa cewa komai sai Hadiza da Tanimu ne suke ta hirarsu sai jefi-jefi Baqeer ke saka musu baki har suka ƙarasa gidan Dada. Yanzu ya zama dole yayi ƙoƙari ya cikawa masu gidan can kuɗaɗen su don ya samu a shirya gidan cikin lokaci tunda gashi ya ɗauko Umma a lokacin da bai gama shiryawa ba, da farko da ya bari ne sai ya gama cika musu kuɗin gidan an zuba furniture kafin yaje ya ɗauko Umman to kuma sai wannan al'amarin ya faru da yasa dole ya rabota da gidan. Gaba ɗaya suka shiga gidan Dada da Baqeer yasa aka gyara aka mayar dashi na zamani sosai kamar ba gidan tsohuwa ba. Ganin suna shigowa da kayan Umma yasa tace "Ke kuma lafiya? Ina Badarun kika tattaro kika dawo gida?" Zama tayi akan tabarmar da Dadan ke zaune kafin tace wani abu Baqeer yace "Na rabota da wancan gidan ne Dada ba zata sake komawa ba." Kallon mamaki Dada tayi mishi duk da tasha jin shi yana zancen zai ɗauke Fatima ya rabata da zaman gidansu ba sau ɗaya ba sau biyu ba amma bata taɓa tunanin zai aiwatar ba, duk tunaninta yana dai faɗa ne saboda takaicin halin uban su ashe shi da gaske yake yi, murmushi tayi ta girgiza kai tace "In banda abinka Baqeeru ta yaya zaka rabo mace daga gidan aurenta mijinta bai saketa ba, a ina ake yin haka saboda Allah?" Yana tafiya ɗakin shi ya bata amsa da "Za'a fara akaina, ni dai na ɗauko ta kuma baza ta koma ba," yayi shigewarshi ɗakin shi. Hadiza ce tace "Allah Dada Baban ne baya da kirki, yanzu haka idan kin ji abinda yayi ba zaki sake ganin laifin Ya Baqeer ba." Harararta Dada tayi tace "Kome yayi ai dai uban ku ne har kike cewa baya da kirki." Ƴar dariya Hadiza tayi tace "Hhamm Dada kenan, wai fa zuwa nayi gidan na tarar an ɗebo musu ƴan sanda Kamalu yayi sata shine Baba yake bayar da shaida akan Umma wai ta sace mishi takardun filinshi a haɗa har da ita a tafi bayan takardun filin da yake magana akai na Ya Baqeer ne ba nashi bane." "Allah ya kyauta," kawai Dada tace ta juya tana amsa gaisuwar da Umma take yi mata. Tashi Hadiza tayi ta kwashe kayan Umma ta kai ɗakun Dada, sai da ta shirya kayan tsaf sannan ta fito tayi musu sallama zata tafi gida saboda yamma tayi ta baro yara a gida. Hadiza na fita Umma ta tashi ta shiga ɗaki, ta rasa tunani guda ɗaya da zata kama sai take ganin al'amarin kamar a mafarki sai dai idan ta ɗaga ido ta kalli Baqeer yau bayan wani tsawon lokaci Allah ya ƙara haɗa su zama a muhalli guda sai tasan cewa ba mafarki take yi ba.
*****
Zaɓe yana ta matsowa saboda haka hankalin kowanne ɗan takara ya tashi, kowa burin shi ace yau shi yayi nasarar lashe kujerar daya fito nema. Primary Elections za'a yi a jam'iyyar su Daddy don haka hankalin shi ya kasa kwanciya domin abokin takarar shi na neman saye ƴan jam'iyyar da kuɗi duk da shima ba baya ba wajen yi musu ɓarin kuɗin duk don ya samu su zaɓe shi a matsayin ɗan takarar jam'iyyar tasu. Yau sun fita yawon campaign a wani ƙauye basu baro garin ba sai dare. Suna tafe a hanya motocin campaign ɗin sai zura uban gudu suke yi a titi suka yi wani mummunan accident. Haka mutane suka yi dafifi akan su ana ta fitar da mutane daga cikin motocin da hatsarin ya rutsa dasu, wasu sun rasu wasu sun ji munanan ciwo, a cikin waɗanda suka ji ciwo har da Daddy don wani ƙarfe ne ya coke shi a cinya ya ɓullo ta ɗaya ɓarin cinyar abun babu kyaun gani. Sai da ƴan road safety suka zo sannan aka fara zuba su a mota za'a bar wutin dasu don wurin da suka yi accident ɗin daji ne. Haka aka kwashe su aka yi asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dasu a ɓangaren accident and emergency. Kabir na kwance har ya fara bacci yaji wayarshi na ringing, haka ya tashi yana tsaki ya ɗauki wayar sai yaga ashe Daddy ne ke ƙiran shi. Cikin muryar bacci yace "Hello Daddy," sai yaji wata murya da ba ta Daddyn ba ta amsa. Ai tuni yaji ya wartsake jin wayar ba'a hannun Daddy ba, da ƙyar ya nutsu suka gaisa da mutumin sannan mutumin ya faɗa mishi maƙasudin kiranshi da yayi. Tuni hankalinshi ya tashi yana tambayar mutumin "Yanzu ina Daddyn? Da fatan dai bai ji ciwo ba?" "Eh to, yana nan accident and emergency na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano idan kun zo zaku ganshi." Hankali a tashe ya zari makullin motarshi ya fita, har ya isa harabar gidan ya tuna bai sanar da Mummy ba don haka ya koma yayi knocking a ƙofar ɗakinta. Cikin bacci taji ana ƙwanƙwasa mata ƙofa, sai da ta ɗauki wayarta ta duba lokaci sannan tace "kai waye anan?" Saboda har lokacin ba'a daina buga ƙofar ba. "Mummy nine," jin muryar Kabir yasa ta duro daga gadon ta ɗauki hijabin sallarta ta saka sannan ta buɗe ƙofar tana cewa "Kabir lafiya kuwa yanzu da dare?" Idanunshi sun yi jawur saboda tashin hankalin yace "Yanzu aka kirani a waya wai an kai Daddy asibitin Aminu Kano sun yi accident a hanyarsu ta dawowa daga campaign, har na fita zan tafi na tuna ban faɗa miki ba shine na dawo."
Tuni itama ta rikice tace "Subhanallahi nima gani nan zuwa bari na shirya." Juyawa yayi ya tafi da kamar ya tsaya jiranta ta shirya ɗin kamar yadda tace sai kuma yaji ba zai iya ba gaba ɗaya hankalin shi yayi gaba gara yaje yaga a wane hali Daddyn yake ciki idan yaso ta iske shi a asibitin. Gudu kawai yake yi akan titi bare da titin ya kasance babu kowa saboda dare da ya fara yi babu yawaitar motoci a titun. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙarasa asibitin, yana shiga cikin accident and emergency ɗin ya kira number Daddyn, mutumin na ɗauka yace mishi gashi yazo sai yana ɗan ɗaga hannu, daga nesa mutumin ya ganoshi yayi waving ɗin shi back. Da sauri Kabir ya ƙarasa wurinshi yana zuwa yace "Ya jikin Daddyn? Ina fata babu wata babbar matsala." Hannunshi mutumin ya kamo yaja shi wajen kujera suka zauna yace "Mu ɗan jira su anan likitocin na dubashi har yanzu," hannu Kabir yasa ya riƙe kanshi yana jin tashin hankalin shi na ƙaruwa, a yanzu burinshi kawai yayi ido biyu da Daddy watakila idan ya ga a halin da yake ciki ya samu ƴar nutsuwar zuciya. Dafa shi mutumin nan yayi yace "Ka kwantar da hankalin ka In Sha Allah zai samu lafiya, kai dai kayi tayi mishi addu'a Allah ya sauƙaƙa mishi ya tashi kafaɗunshi." Kasa ki amsawa Kabir yayi, suna zaune a wurin babu wanda ya fito wurin su har lokacin sallar asuba yayi suka tashi suka fita amsallacin cikin asibitin suka yi sallah suka dawo. Har wannan lokacin likitocin basu nemesu ba, gaba ɗaya Kabir ya ɗaga hankalinshi gani yake yi Daddyn ya mutu kawai faɗa mishi ne basa so suyi. Sai can wajen ƙarfe shida na safe sannan ɗaya daga cikin likitocin ya fito, mutumin na ganinshi ya gane shi don haka yayi wa Kabir magana suka tashi suka ƙarasa wurinshi. Yana ganin wannan mutumin daya kasance ɗaya daga cikin yaran Daddy na amana ya yafito su, kallon Kabir yayi yace "And who are you?" Mutumin ne ya amsa mishi da "Mahaifin shi ne mara lafiyan ai." "Oh okay, to ku biyo ni," yaja su zuwa wani office. Bayan sun zauna ya kalli Kabir "muna buƙatar kuyi signing akan wannan form ɗin don zamu shiga dashi surgery," ya miƙa mishi consent form. Karɓar takardar Kabir yayi yace "Ya jikin Daddyn? Meya sameshi da har sai anyi mishi aiki?" Ya tambayi likitan ba tare daya duba takardar ba. Ɗan kallonshi Doctor ɗin yayi yace "Mahaifinka is diabetic gashi kuma ƙarfe ya shige cinyarshi ya ratattaka ƙashin wurin da ba zai gyaru ba don haka dole zamu yi amputating ƙafar don idan aka barta ruɓewa zata don ƙashin wurin ya tashi a aiki babu ta yadda za'a iya gyarawa." "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun," kawai Kabir ke ambata, dafe kanshi da yake jin yana wani irin sara mishi yayi. Ya ɗauki wasu ƴan mintuna yana cikin halin ruɗani kafin da ƙyar ya iya buɗe baki yace "Yanzu ina Daddyn yake? Zan iya ganinshi?" Cike da tausaywa suke kallonshi Doctor yace "Me zai hana, idan kun shirya muje ku ganshi sai kuyi ƙoƙarin biyan kuɗin aikin dan a samu a shiga dashi akan lokaci."
Zubewa kawai Kabir yayi a ƙasa saboda yadda yaga Daddy ya koma wani iri kamar wanda aka canjawa halitta gaba ɗaya kamannin shi sun juye. Da ƙyar ya iya tashi ya ƙarasa gaban gadon murya na rawa yace "Daddy," duk da Daddyn ba jin shi yake yi ba saboda har yanzu bai dawo cikin hayyacinshi ba. Ya daɗe a tsaye a wurin yana kallon Daddy hawaye duk ya cika mishi ido saboda tsabar tausayi. Da ƙyar ya iya barin wurin ya fita don ya koma gida ya ɗauko atm card ɗin shi sannan ya dawo ya biya kuɗin aikin da za'a yiwa Daddyn bayan ya bar wato Mallam Nuhu mutumin da ya ƙira shi a wurin don ba zai yiwu abar Daddyn shi kaɗai ba duk da bai san inda kanshi yake ba. Sai wannan lokacin ma tunanin rashin ganin Mummy ya faɗo a ranshi bayan tace mishi gata nan zuwa tun lokacin da yaje ɗakinta ya faɗa mata Dady na asibiti yayi accident. Kallan time yayi a jikin wayarshi sai yaga har ƙarfe goma sha biyu da rabi tayi, rasa abinda ya kamata ya fara yi yayi. Tunani yayi ya kamata ya kira Zeey ya sanar da ita duk da fushin da yake yi da ita na barin su da tayi ta koma wajen Ummi.
Zeey na kitchen tana girkin rana lokacin da ƙiran Kabir ya shigo wayarta, a lokacin wayar tana hannun Inaya tana yin game don haka bata lura da shigiwar kiran ba sai gani tayi ta danna ok. Ganin ta masa ne yasa ta kai wayar kunnenta tayi sallama haɗe da cewa "Ya Kabir Aunty Zeey bata kusa bari na kai mata," saboda yadda Zainab take zaunar da ita tana bata labarin Kabir yasa take ganin kamar tasan shi, shi yasa da taga shi ya kira kawai ta amsa. Shiru yayi yana tunanin wacece ita kuma wannan yarinyar? Ba dai? Kafin ya gama tunanin da yake yi yaji muryar Zeey tana cewa "Ya Kabir sai yau kaga damar nemana bayan duk ƙiran da nake yi maka baka ɗauka, ai wallahi ba don Inaya ta amsa ƙiran ba da nima sai naja maka class kafin na ɗauki wayarka." Cikin wata irin cunkusashiyar murya Kabir yace "Daddy ne Zeey, Daddy yayi accident yana asibiti ance za'a yanke mishi ƙafa." Da ƙarfi Zeey tace "What? Garin yaya? Yaushe hakan ta faru ban sani ba?" Ai tuni ta fara kuka jin wai za'a yankewa Daddynta ƙafa. Ihun da tayi ne yasa Ummi fitowa daga ɗaki da sauri don tasan tabbas ba lafiya ba. Tana shigowa taga Zeey na kuka ta e "lafiya? Meya faru?" Zuwa tayi ta rungume Ummin tana cigaba da kukan, cikin kukan take faɗa mata abinda Kabir ya faɗa mata. Itama ji tayi hankalinta ya tashi amma haka nan ta daure ta zaunar da Zainab tana rarrashinta har ta samu ƴar nutsuwa. Tashi tayi ta kalli Ummi da idanunta da suka yi kozai-kozai tace "Tafiya zan yi Ummi, zan je naga a halin da Daddy yake ciki." Ɗaga mata kai tayi alamun amsawa sai kuma tace "Bari na ƙira wo Mubashir ku tafi tare don bazan yarda kiyi driving a wannan halin da kike ciki ba. "To," kawai ta cewa Ummin don ba zata iya yi mata musu ba.
Kabir kuwa suna gama yin magana da Zainab ya tashi motar shi ya tafi gida yana tunanin abinda ya hana Mummy zuwa asibitin har yanzu kuma ko a waya bata kurashi taji halin da ake ciki ba bayan tasan abinda ya faru tunda sai da yaje ɗakinta ya faɗa mata kafin ya bar gudan ya tafi asibitin. Daga wajen gate yayi parking don baya so ya ɓata lokaci ya shiga gudan, direct ɗakin shi ya wuce ya ɗauki atm cards ɗin shi da duk wani abinda zai buƙata. Har zai yi ficewarshi ya koma asibitin sai kuma yayi tunanin watakila fa Mummy ba lafiya ba tunda har ta kai yanzu bata nemeshi ba don haka ya juya ya koma ɗakinta don ya dubata sai dai abinda kunnuwanshi suka jiye mishi yana dosar ƙofar ɗakin yasa ya daskare a tsaye a wurin....Me kunuwansa suke jiyemai? Anya ba mafarki yake ba?
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA*
*UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA UKU*
{93}