Baqeer complete - Chapter 70
Baqeer complete Chapter 70: Baqeer complete Chapter 70. Hannun ƙofar ya saki tare da zubawa ƙofar ido, kalaman Nabila ne suka dawo dashi daga hayyacinshi…
3,269 words
Hannun ƙofar ya saki tare da zubawa ƙofar ido, kalaman Nabila ne suka dawo dashi daga hayyacinshi "Koma menene Kabir nake so, in har da gaske kina so na kamar yadda kika ce to kisan yanda kika yi na aureshi, shi nake so kuma shi nake son aura." Mummy ce ta katseta a fusace tana cewa "Sanda nake ta ce miki a'a ki bari kin ji magana ta? Ko har yanzu baki san shirmenki bane ya samu cikin situation ɗin da muke ciki yanzu? Da kin barni ni nasan yadda zan yi ki aureshi tunda ba aure ne ya haramta tsakanin ku ba amma shirmenki da gaggawa yasa kika lalata komai, banda dai ni nasan takan komai da yadda zan gyara abu da tuni kin kashe mini aure, to sa'a ta ɗaya Alhaji Sulaiman a tafin hannuna yake, sai yanda nayi dashi daga shi har yaranshi, ba boka ba Malam amma duk a tafin hanuna suke, ita kanta wacce ta nemi yi mini gardama na rabata da mahaifinta," tayi tsaki sannan ta cigaba "Amma da yake ke sam baki da haƙuri gashi nan kin rasa Kabir ɗin, da kin bi maganata sanda nace a'a da yanzu sai yanda kika yi dashi, ko kina tunanin lokacin da kike munafircin kyawawan halaye duk ba training nake yi miki a fakaice ba?" Nabila kallon Mummy kawai take yi cike da mamaki kafin tace "Ke ba son su kike yi ba ni kuwa Kabir son gaskiya nake yi mishi, kuma Allah in kina so hankalina ya kwanta ki san yadda kika yi na mallakeshi." Tsaki Mummyn tayi tace "A yanzu ko zai aureki bazan baki shi ba don kuwa babu dalilin da zai sa ki aureshi, primary election ɗin ma har sun faɗa ya faɗi, gashi yana asibiti yayi accident na kira driver ɗinshi naji meke faruwa saboda bani da time na yawon asibiti yake sanar dani ƙafarshi kamar ta samu matsala, to faɗa min me yake dashi da zan bashi ke? Bayan rabin dukiyarshi tawa ce." Kabir duk yadda yaso ya daure akan abubuwan da kunnenshi ke jiyo mishi kasawa yayi ji yayi ƙafafunshi na neman kayar dashi ƙasa, da sauri ya dafa bango sannan ya fara jan ƙafafunshi yana tafiya kamar wanda bashi da laka, zuciyarshi bazata iya tsayawa ya gama jin abinda kunnenshi ke jiye mishi ba, waje kawai yayi ya shiga mota, ko tankawa mai gadi dake tambayarshi har ya fito bai yi ba, da ƙyar ya iya sawa motar key sannan ya bar layin. Kalaman Mummy ne ke sake mishi rito a zuciya wanda yake ji kamar ana sake dawo mishi dasu cikin kunnuwanshi, da ƙyar ya isa asibiti sai dai ya kasa fita daga motar kawai ya zauna yana tunanin wannan rayuwa, taya zata riƙesu shekara da shekaru ta dinga irin wannan furucin? Ya daɗe a haka kafin wayar Zainab ta shigo wayarshi, da sauri ya ɗauka yace "Kin iso?" Hankalinta a tsananin tashe tace "Ya Kabir kuna ina? Gamu yanzu mun shigo." Kwatancen inda zata sameshi yayi mata sannan suka yi sallama, basu fi minti uku ba sai gasu sun iso lokacin yana waje yana jiransu. Da sauri-sauri gudu-gudu ta ƙaraso idanunta taf da ƙwalla tace "Ya Kabir ina Daddy?" Wani abu ya haɗiya tare da kallon Mubashir sannan yace "Muje." Nan suka shiga ciki, duk ta rikice kawai Daddy take son gani, Kabir ne yace "Zainab akwai ragowar payments da bamu yi ba wanda ni kuma babu ragowar kuɗi a wurina." Mamakin kalamanshi ne yasa ta kalleshi sai dai bata da lokacin wannan hakan yasa ta miƙa mishi card ɗinta ta sanar dashi pin sannan tace "A ina Daddyn yake?" Nan ya sanar da ita ɗakin ita dai hankali a tashe take tafiya, Mubashir ne yabi bayanta. Kabir sai daya biya ragowar kuɗaɗen sannan ya dawo inda Daddy yake. Tunda Zainab taga halin da Daddy yake ciki take kuka, kuka kawai take yi, a hankali ya ɗan motsa hannayenshi sannan ya buɗe ido kamar mai jin bacci ya saukesu a kanta, wani murmushi yayi mata na tausayi sannan ya maida idon ya rufe da alama dai maganin da drip ɗin da aka saka mishi akwai na sa bacci, kallon Kabir tayi tana hawaye ta kalli ƙafar da aka naɗeta da bandage tace "Ya Kabir ya zamu yi?" Kai ya girgiza alamar rashin sani kafin ya share ƙwallar shi yace "Ina ji duk alhakina ne ya sauka akan Daddy, Zainab na shiga uku…." Ya ƙarasa maganar yana dafa bango don shi kaɗai yasan me zuciyarshi take ji a wannan lokacin. Fitowa tayi daga ɗakin tace "Ya Kabir zo." Bai musa ba yabi bayanta har sun kai bakin ƙofa ta kalli Mubashir tace "ƙanina ɗan zauna anan kaɗan yanzu zan dawo." Cewa ƙanina da tayi yasa Kabir ƙara kallon yaron, wani abu ya haɗiya don yanzu kam ya tabbatar yaron nada haɗi da Ummi ko ba ɗanta bane yasan yaron dai wani nata ne. Fitowa suka yi suka zauna daga gefe, kallonshi tayi tace "Ina Mummy?" Kalmar Mummy da tace yasa ya kalleta ji yayi wani abu ya tsaya mishi yace "Zainab ashe matar nan ba tsakani da Allah take son mu ba." Yanayinta ne ya canza tace "Ba dai wani abun tayi maka ba?" Kai ya girgiza zuciyarshi na zafi ya sanar da ita abinda ke faruwa." Hawaye Zee ta goge tace "Ya Kabir me yasa kaga na bar gida ban ƙara waiwaye ba? Na gane halayenta ne kuma kai da Daddy kun kasa bani dama na sanar daku wannan dalili yasa naƙi dawowa." Nan ita ma ta kwashe komai ta sanar mishi, mamaki duk ya hana Kabir magana, sai hawaye kawai da yake ta zubo mishi saboda tashin hankalin da yake fuskanta wurin matar da yafi yarda da ita a duniya fiye da kowa. "Zainab na faɗa miki alhaki ne, na yar da Ummi gashi nan abinda ya sameni, ya zan yi? Wannan daya kawoki wanene?" Murmushi tayi tace "ƙaninka ne wanda baka sani ba." Kai ya kauda yana maida kwallar dake neman zubowa yace "Wacce muka yi waya fa?" Tace "Ita ma." Ido ya runtse, tausayinshi ya kamata tace "Ya Kabir ka girma yanzu don Allah, yanzu dai kana ganin yadda rayuwa ta zo mana, matar nan haka ta dinga zuga Daddy yana kwaso kuɗin da ba nashi ba na gomnati yanzu kaga ko zuwa ta dubashi bata yi ba." Kwafa yayi yace "Rayuwa ce tayi abinda ranta ke so." Haka suka koma ɗaki suna ji suna gani aka shiga da Daddy aiki, takaicinta ɗaya da bata dage wajen sanar da Daddy da Kabir halin Mummy ba har sai sanda aka zo lokacin da abu ya riga ya ƙure. Mubashir ne ya siyo musu ruwa ya miƙawa Kabir ɗaya, kallonshi yayi idanunshi sun ciko hannu ya miƙa mishii alamar musabaha, Mubashir shima ya miƙa mishi, ji yayi zuciyarshi na ƙara karyewa kawai sai ya rungumeshi. ***** A hankali Baqeer ya kai hannu saman goshinshi da yake ji kanshi nayi mishi ciwo, Tanimu ne ya kalleshi yace "Ya Baqeer ka koma gida ka huta don Allah, ni zan kula da ayyukan da ake yi anan." Kallonshi yayi sannan ya kalli kayan mutanen da yake taso a gama haɗa musu don yana da buƙatar wasu kuɗin ya haɗa da na hannunshi ya biya ragowar kuɗin gidan, in yaso a hankali ayi funitures ɗin da ya kamata, zai sake magana Tanimu yace "Don Allah kaje ka huta." Murmushi yayi yace "Kai ma ka iya magiyar Salim ko?" Kai ya sadda ƙasa yana shafa bayan kanshi, tare suka fito suka shiga mota akan in ya kai shi zai dawo shagon shi. Kanshi ya maida jikin window yana kallon mutane, motar data gifta ta gefensu ya kalla da kuma sauri ya kalli number motar, sai dai bai iya duba number sosai ba ta wuce, kai ya girgiza tunowa da yayi ba ita kaɗai bace mai irin motar, sannan in da sabo ya saba ganin irin motar yana duba plate number yaga ba nata bane, ido ya ɗan lumshe sannan ya buɗe yana tunanin anya bai fi son Zainab akan yadda take sonshi ba kuwa? A wani shagon Rufaida yoghurt ya tsaya ya ɗan yi siyayya sannan suka wuce, ya bawa Tanimu nashi shi kuma ya shiga gida. Hadiza tayi wankin ragowar kayan Umma wanda aka zubar a waje suka ɗan ɓaci, gaisawa suka yi yace "Maimakon ki bari in za'a kai wanki a haɗa?" Tace "A'a ba komai, dama ɗazu muka zo ni da Maryam to ita ta koma saboda nemanta da mai gidan yake yi shine nace bari na ƙarasa kafin na tafi." Kai ya jinjina yace "Yanzu dai ba matsala ko?" Dariya tayi tace "Inafa matsala ai Ya Baqeer yanda kasan ba Baban su Husaini ba haka yake min, nan nan yake dani tunda yaga ina samun kuɗi sosai, sannan kaga saida atamfofi da nake online ɗin nan shima ba ƙaramin taimaka min yake ba, ni dai kam ba abinda zance maka sai fatan Allah ya kara lafiya ya kawo mace ta gari." Bai amsa a fili ba sai dai yace Ameen a ranshi. Mayafi ta ɗauko ta yiwa su Umma sallama sannan ta tafi. Dada ce suna gaisawa tace "Ni kam Baqeer auren mahaifiyarka kashe mata shi kayi ko me? Ita ta biyeka kai kuma banga kana da niyyar maidata ɗakinta ba." Kai ya kauda yace "Da wannan auren da babu shi duk daya ne." Baki Dada ta saki kafin tace "Koma dai menene ka maida ta ai dai ɗakinta shine darajarta." Kallonta yayi sosai yace "Dada bafa zata koma ba, ni gidan dana siya ma na kusa gama biyanshi maidaku can zan yi." Kallon mamaki suka yi mishi, ya shige ɗaki ba tare da ya ƙara cewa komai ba, Dada ce tace "Fatima nima ba son zamanki da Badaru nake yi ba amma aure da ƴaƴa kun riga kun zama ɗaya." Murmushi ta yiwa Dada tace "Ke kika san mun zama ɗaya Dada amma ba Badaru ba, ni ba kashe aurena zan yi don ɗana Allah ya azurtashi ba kawai dai bazan koma bane har sai yayi nadama ya canza hali." Jin haka yasa Dada kallonta, tabbas Badaru bashi da imani ita kanta tana bada shawarar ne a matsayinta na uwa wacce tasan hakan bai dace ba, amma me za ayi da auren Badaru? *** Asiya ce ta kalli Mama da ta miƙo mata wake tace wai ta surfa ta wanke za'ayi alale, kamar ita? Ai ita ko a gidansu bata daka bare hannunta yayi kanta. Kauda kai tayi gana gyara kwanciya tana cewa "Mama bana jin daɗi kin sani don haka bazan iya surfe ba gaskiya," ta ƙarasa maganar tana gyara kanta. Ajiye mata waken tayi tace "Sai ki zaɓa ko aikin dana saka ki ko kuma ku tattara ku nemi gidanku." Komawa tayi ta zauna don kuwa tasan bata da wurin zama banda nan ɗin don ko banza yafi gidan su, bata son tuna wahalar da tasha a komawarta wai kamar ita zasu yi ta bawa ɗumame shima sai dai ta ɗumama da kanta, gashi itace ne, da farko kayanta na lefe taso siyarwa sai dai ba dama don kuwa Bello ya taho dasu nan gidan, dole ta tattara ta taho ai ko banza nan ɗin ana ci asha kuma gidan yafi na iyayenta. Haka nan ta amsa kamar zata yi kuka tana daka tana ƙunƙuni. **** A hankali Daddy yake bin ɗakin da kallo, idanunshi ne suka sauka akan Zainab dake gefen gado ta kwantar da kanta a kusa da ƙafar shi, hannu ya kai yana son taɓata kawai yaga ta ɗago, da sauri ta dawo inda yake tace "Daddy ka farka? Ya kake jin ka? Wurin yana yi maka zafi? Akwai inda kake jin ciwo?" Murmushi yayi yace "One at a time Auta, slowly." Hawaye ne suka zubo mata tace "Daddy kayi haƙuri na tafi na barka, gashi abinda ya sameka, ka sani?" Kai ya ɗaga mata alamar eh, tare da lumshe ido yace "Kina tunanin zasu min aiki babu izinina ne? Ni nayi signing lokacin Kabir yaje gida ya dawo." Murmushin tausayin kansu yayi yana ƙoƙarin riƙota da sauri ta mika hannunta ta kamo nashi tasa kuka. Lallashinta yayi har ta tsagaita sannan yace "Rayuwar kenan, sannan laifina ne dana bari diabetes ya shigeni haka ba tare da sanina ba ban kuma duba canjin da nake ji a jikina ba saboda hankalina yana kan siyasa, sannan ko na sani ma me zan yi Zainab?" Hawaye ta share ta ƙara riƙe hannunshi tace "Am sorry Daddy." "Me kike ci a Dambatta da naga kin canza haka?" Fuskarta ta shafa tace "Kai Daddy." Gefe ya kalka ya ɗan dubi ƙofa, Zee jikinta ya bata Mummy yake nema hakan yasa tace "Tazo ɗazu komawa gida tayi ta huta," tayi maganar cike da son janye tunaninshi. Maida kallonshi yayi kanta yace "Ba ita nake nema ba Kabir nake jira, da alama tunda na kwanta bata zo ba." Da mamaki Zee ta kalleshi tace "Daddy me kake nufi?" Murmushi yayi yace "Tunda aka yi aikin ina farkawa lokaci-lokaci sai dai bana iya magana saboda ƙarfin allura, a iya tsawon farkawar da nayi ban ga wata mace ba bayan ke." Jikin Zee ne yayi sanyi don bata son yi mishi ƙarya, gashi Kabir da Mubashir sunje gida jiya ma suka ga bata gidan. Bai yi magana ba hakan yasa ta juya don ta kira nurse., da kallo kawai ya bita. **** A shagon Baqeer da aka yi mishi kwatance Kabiru ya tsaya, ido ya runtse tare da sauke ajiyar zuciya, bai ga ta zama ba dole ne yazo ya nemi yafiyar Baqeer, yana ji kamar laifukanshi ne suka sauka kan Daddy, mamaki yake yi yadda aka yi shagon dashi kanshi yasa yi kaya kusan kala biyar a wajensu ashe shagon Baqeer ne, fitowa yayi daga mota ya tsaya a jikin ta inda kana gano cikin shagon, Baqeer yana zaune sanye da riga da wando yasa table a gaba yana yanka, wuyanshi ɗauke da tape sai gefen kunnenshi da yasa pencil, ɗagowa yayi ya kalli waje ta glass door ɗinsu, idanunshi ne suka sauka kan Kabir.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*
*BAQEER* *NA*
*UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA HUƊU*
{94} Sosai ya kalleshi yana mamakin abinda ya kawoshi nan sai kuma ya juya ya cigaba da aikin shi cikin ranshi dai cewa yayi "To ina ruwana tunda dai nasan ba wurina yazo ba." Kabir ya daɗe a tsaye a wurin yana tunanin ta yadda zai fara fuskantar Baqeer bayan abinda yayi mishi, haka nan ya ƙarfafi kanshi ya daure ya tura ƙofar shagon ya shiga. Tanimu na ganinshi ya taso ya tare shi da fara'arshi yana welcoming ɗin shi don babu laifi suna da kyakkyawar mu'amala da customers ɗin su. Bayan sun gaisa da Tanimun ne yace mishi wurin Baqeer yazo. Raka shi yayi wajen da Baqeer yake aikin yanka ya ɗauko mishi kujera ya ajiye kafin yaje ya kawo mishi ruwa da drink duk ya ajiye mishi sannan ya tafi ya bar su. "Assalamu alaikum," Kabir yace don duk tsawon lokacin da ya ɗauka a wurin Baqeer bai yi alamar yasan da tsayuwarshi ba. "Ameen Wa'alaikassalm," shima ya amsa mishi ba tare daya ɗago ya bar abinda yake yi ba. Ɗan shiru Kabir yayi yana jinjina ta yadda zai fara faɗin abinda ya kawo shi duk da bai ga fuska a wajen Baqeer ɗin ba sai dai kuma bai ga laifin shi ba don tun dama can su ɗin ba abokai bane ga kuma abinda yazo yayi mishi bayan ya kaɗeshi da mota sannan ya gudu ya bar wurin ko fita bai yi yaga a halin da ya saka shi ba. Ɗan gyaran murya yayi dai kuma yace "Zuwa nayi na baka hakurin abinda nayi maka duk da dai babu abinda hakan zai canja, don Allah kayi haƙuri ka yafe min, bani da wani excuse akan abinda nayin don haka ma bazan kawo uzuri akan hakan ba. Fatana ka yafe min don Allah ba don ni ba nasan in har ba yafe mini kayi ba bazan taɓa ganin daidai a rayuwata ba." Saurarenshi kawai Baqeer yake yi yana jin ciwon abinda yayi mishi yana dawo mishi kamar a lokacin abun ya faru. Idan yace bai ji ciwon rasa ƙafafunshi da yayi ba kowa ma yasan ƙarya ne to amma idan ya duba yaga alherin da hakan ya janyo mishi a rayuwa sai ya gode Allah don ya tabbatar da hakan bata faru ba Badaru ba zai taɓa barinshi yayi pursuing dream ɗin shi na zama tailor ba, watakila da har yanzu yana can Badaru na juya rayuwarshi yadda yake so bai isa ya yankewa kanshi hukunci ba dile sai abinda yace zai ayi.
Ɗagowa yayi ya kalleshi yace "Kada ka damu abinda ya riga ya wuce babu amfanin dawowa dashi baya, Allah ya yafemu gaba ɗaya." Farin ciki ne ya cika zuciyar Kabir don bai tsammaci samun afuwa daga Baqeer ɗin da wurwuri haka ba, godiya yayi tayi mishi har sai da yace ya isa haka nan sannan ya bari. Ƙara gyara zama yayi na wasu ƴan dukkansu kuma sai suka yi shiru don babu wani sabo a tsakaninsu, sai da ya tashi zai tafi sannan yace "You didn't ask me about her, ko har ka manta da ita?" Ya ƙarashe maganar da sigar tambaya. Da sauri Baqeer ya ɗago ya kalleshi jin ya taɓo mishi abinda ke ƙunshe cikin ranshi. Ɗan kawar da kai yayi ya basar kamar bai ji abinda Kabir ɗin yace ba. "Bai tsaya sauraren abinda zai ce ba ya sake cewa "Ta dawo fa although bata san zan zo nan, zan ce mata kana gaisheta," ya ƙarashe maganar da tsokana duk da babu wani sabo a tsakanin shi da Baqeer yana so wannan awkwardness ɗin ya rabu dasu. Ɗan murmushi kawai Baqeer yayi sai dai duk da haka bai yi magana ba sai ma ɗaukar scissors da yayi zai cigaba da yankan kayan da Kabir ya tarar dashi yana yi.
Ƙara nutsuwa Kabir yayi yace "Nagode sosai I really appreciate it, baka duba kuskurena ba ka yafe min duk da na aikata maka ba daidai ba, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi." Hannu Baqeer ya miƙa mishi suka yi musabaha sannan yace "Kada ka wani damu ya riga ya wuce kuma ni dama ban taɓa riƙe ka a raina ba." Wayarshi ya miƙa mishi yace idan baza ka damu ba ka bani number ka ma riƙa gaisauwa." Karɓa Baqeer yayi ya saka mishi number sai shi kuma yayi flashing Baqeer yaga tashi number sannan suka yi sallama ya tafi yana ayyana wani abu cikin ranshi. Haka Kabir ya fita yana jin daɗi don sai yaji kamar an suke mishi wani gungumemen dutse daga kanshi, ashe haka hakki yake duk yabi ya dabaibaye rayuwarka ya hana ka samun cikakkiyar nutsuwa. Yana fita Baqeer yabi bayanshi da kallo cikin ranshi yana cewa "Ai ko don Zainab dole na yafe maka tunda ka kasance ɗan uwanta." Duk da haka yayi mamakin abinda ya faru daya canjawa Kabir ɗin tunani har ya nemeshi ya nemi yafiya a wurinshi.