Baqeer complete - Chapter 71
Baqeer complete Chapter 71: Baqeer complete Chapter 71. ***** Tunda Baqeer yazo ya ɗauke Fatima hankalin Badaru ya tashi, ya kasa gasgata abinda idanunshi…
4,152 words
***** Tunda Baqeer yazo ya ɗauke Fatima hankalin Badaru ya tashi, ya kasa gasgata abinda idanunshi suka gani wai Baqeer ne yazo gidan cikin kyakkyawar shiga ga ƙatuwar mota, kenan cigaba yayi da aikin zanen babu shi? Yanzu don rashin imani irin na ɗan yau shine da hannun nashi ya warke bai nemeshi sun cigaba da yin harkar tare ba shine don rashin amana ya tafi yake yin abun shi shi kaɗai ba tare da ya nemeshi ba, ya mance duk tarin alherin da yayi mishi ya fifita shi a cikin ƴaƴanshi amma yanzu da yayi kuɗi uwarshi kaɗai ya sani. Wannan baƙin cikin ne yasa abu kaɗan zaka yiwa Badaru sai ya hau faɗa yana zage-zage tun ba Abu ba don yake jin haushi gana satar da Kamalu yaje yayi banda Allah ya tufa asiri Baqeer ya hana a tafi dasu watakila da har yanzu suna police station ga kuma na tayashi ɓoye kayan da yake zuwa kasuwa yana sace mishi da tayi shi yasa ko gilmawarta ya gani ya dinga surfa mata zagi kenan, to itama da yake lallaɓawa take yi shi yasa bata biye mishi sun yi rigima ba kamar yadda suka saba yi da. Daga Abun har Jamila abun duniya ya taru yayi musu yawa, sun rasa ta yadda aka yi Baqeer ya zama wani babban mutum haka daga ganin shi anga wanda yake cikin wadata da kwanciyar hankali. Ta yaya za'a ce duk wani alheri da zai samu a cikin gidan sai dai Baqeer ya samu bayan suma sun da ƴaƴan nan, anya kuwa babu wani abu da Fatima tayi don ɗanta yafi nasu ɗaukaka da kuɗi kuwa? Kai gaskiya ma haka ne don in ba hakan ba sai kace shi kaɗai ne ɗa a cikin gidan, su miye sa nasu ƴaƴan basu zama wani abu ba har yanzu sai shi da ko shekara biyu bai yi da barin gidna ba zai dawo yayi irin wannan kuɗin, to ko dai sata yake yi? Wata zuciyar ta Jamila ta kitsa mata hakan sai dai ta kasa yardar wa kanta Baqeee zai yi sata watakila dai wata sana'ar ya kama da kuɗin filin shi da Fatima ta ɗauke ta kai mishi. Har kamar ta tashi taje ɗakin Abu su tattauna don tunda abun nan ya faru basu zauna wuri ɗaya sun yi maganar ba ga kuma tijarar da Mallam yake yi musu kullum tasa kowaccen su ta kama kanta ta tsaya a iya ɗakinta kawai.
***** Har Daddy ya ƙari zamanshi a asibiti ya fito Mummy bata je ta ganshi ba. Hidimar gabanta kawai take yi da dukiyar shi data dinga sawa yana canjawa zuwa sunanta a cewarta saboda siyasar shi ne kada ya samu matsala, ko bincike aka zo ba za'a ga ya tara wani abu da yawa ba bare hakan ya kawo mishi cikas. Ranar da aka sallame shi suka koma gida ma basu sameta a gidan ba, sai Zeey ce ta turashi zuwa ɗakin shi akan wheelchair daya koma amfani da ita yanzu, bayan nan ta shiga kitchen ta shirya mishi abinci. Faten acca tayi mishi da yaji hanta da ganyen ugu. Tana ƙara tsaftace wajen ne bayan ta gama girkin Kabir ya shigo kitchen ɗin, kallonta yayi yaga yadda take aikin cikin nutsuwa kamar ba Zeey ɗin daya sani ba, kai shi sai yace ma tunda ta dawo yaga wata irin nutsuwa a tare da ita wacce sam da bata da ita. Lallai Mummy ba ƙaramin cutar su taso yi ba banda Allah ya kiyaye watakila so tayi su lalace ta yadda baza su iya amfanar kansu da komai ba. Ita Ummi da yake uwa ce ai gashinan a zaman shekara guda kacal da Zainab tayi a wurinta ta koyar da ita duk wani abu daya kamata ace ƴa mace mai shekarunta ta iya ga kuma tarbiyya da tayi mata wacce sam ba'a basu irinta ba tsawon shekarun da suka ɗauk aa cikin gidansu, komai suka yi daidai ne idan laifi suka yi sai dai ma Mummy tayi ƙoƙarin taya su ɓoyewa kada Daddy ya sani, a wancan lokacin gani yake yi duk duniya babu mai ƙaunarsu irin Mummy shi yasa ko mahaifiyarsu basu wani damu da ita ba ashe ita tana da manufarta tayin hakan sune basu sani ba. Ƙarasawa yayi cikin kitchen ɗin yace "Har yau na kasa sabawa da ganinki kina aiki, sai nayi ta mamaki ina tambayar kaina wai shin da gaske wananan Zeey ɗin ce dana sani da ko ruwan zafi bata iya dafawa ba." Dariya tayi tace "Ai dai wallahi anso a cutar dani Allah ya kiyaye da haka zan tafi gidan miji ban iya komai ba. Baka san abun haushin bama sai idan Inaya tayi aikin dana kasa yi Ummi tayi ta min gori tana faɗa babu shiri na tashi na koyi hidimar gida sannan na huta da faɗan Ummi lokacin da taga na daina yi mata kwaɓa." Shima dariyar yayi yace "Ina so naje naga Ummi sai dai ina jin nauyinta sosai, sam bamu kyauta mata ba tun ma ba ni da nake da wayo sosai lokacin da ta bar gidan ifan ke baki tuna wasu abubuwan ba ni ya kamata ace na tuna." Ajiye duster dake hannunta tayi ta kamo hannunshi tace "Ya Kabir Ummi bata yi fushi da kai ba kullum tana zuba ido ganin ta inda zata ganka don haka ka ture duk wasu tunanukan da zasu iya hanaka zuwa wurinta kaje ta ganka, lokacin zaka san ba'a yi mata adalci ba da aka rabata damu sannan kuma aka hana mata ganin mu." Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace "In Sha Allah zan je bari dai Daddy ya ƙara samun sauƙi sai mu saka time ki rakani," ɗaga mishi kai tayi alamun amsawa sannan ta cigaba da aikin daya tarar da ita tana yi. Bayan ta gama ta ɗauki tray ɗin data haɗawa Daddy abinci ta nufi ɗakinshi. Sai da ta ƙwnƙwasa ya bata izinin shiga sannan ta tura ƙofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama, lokacin yana kwance akan gado gaba ɗaya duniyar nan bata mai daɗi sai dai a yanzu bamai bashi mamaki kamar Mumy, sai dai bai sa abin a ransa ba yana ganin da mutuwa yai fa? Ƙoƙarin miƙewa yake yi amma ya kasa don haka kawai ya koma ya kwanta, ajiye tray ɗin tayi akan bedside table sannan ta kamashi ta taimaka mishi ya zauna, pillow ta ɗauka tasa mishi a bayanshi tana yi mishi sannu. Abincin ta zuba mishi sannan ta miƙa mishi plate ɗin tace "Daddy gashi da kaina na dafa maka, ci kaji yayi daɗi." Karɓa yayi yana murmushi, sai da ya i abincin yaji taste ɗin shi sannan ya kalleta yace "Da gaske ke kika dafa wannan abincin?" Ɗaga kanta tayi tana dariya, girgiza kai yayi yace "gaskiya yayi daɗi, hala karatun chef Ummin taki tasa kika yi a Ɗambattan." Cikin jin daɗin yabon da Daddy yayi mata tace "Babu wata makaranta dana shiga Daddy Ummi ce ta koyar dani duk wasu ayyukan cikin gida har na iya." Jinjina kai yayi yace "Ta kyauta, kinga yanzu bani da haufi idan na aurar dake don nasan kin iya duk wani abu daya dace macen ƙearai ta iya." Sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba si yanayinta daya canja daga farin ciki zuwa damuwa. Sosai Daddy ya kalleta sai ya ajiye plate ɗin hannunshi ya riƙo hannayenta yace "Kiyi haƙuri Auta nasan ban kyauta miki ba kin kawo wanda kike so na koreshi na hanashi aurenki, a wancan lokacin gani nake yi abun kunya ne ace na ɗauki ƴata na bawa gurgu gashi kuma ɗan Badaru mutumin da tun tasowarmu babu wata jituwa a tsakaninmu sai gashi tun ba aje ko ina ba Allah ya nuna mini iyakata, idan rashin ƙafa ce tasa na hana Baqeer aurenki to gashi nima na gamu da larurar wacce tafi tashi ma don shi ai da ƙafafuwan shi takawar ce kawai baya iya yi ni kuwa an yanke ƙafar ma gaba ɗaya ta tafi kenan ba zata sake dawowa ba."
Tunda Daddy ya fara maganar nan Zeey take kuka, sai taji wani irin rauni ya lulluɓeta gana tausayin Daddy gana tausayin kanta. Hannu Daddy yasa ya goge mata hawayen yace "ki daina kuka kin ji auta, idan kuna tare har yanzu ki faɗa mishi ya turo iyayenshi ayi maganar aurenku don a yanzu bani da wani buri bayan naga na aurra daku daga ke har Kabir, siyasar dana ƙwallafa rai akanta ma ina kwance anyi zaɓen primaries ganin ga larurar data sameni yasa ƴan ƙarƙashina duk suka koma wajen abokin takarata don haka duk shi suka zaɓa shi jam'iyya ta tsayar a matsayin ɗan takarar senator ɗin."
Kanta a ƙasa tace "Bama tare dashi Daddy tun wancan lokacin ya rabu dani," tayi maganar muryarta na rawa alamun kowanne lokaci zata iya fara wani kukan. Dafata yayi yace "Kada ki damu kin ji idan har da gaske yake son ki to zai dawo barazanar da nayi mishi bata isa ta raba soyyyarku ba sai dai idan dama can ba sonki yake yi ba." Ɗagowa tayi ta kalli Daddy idanunta cike da hope akan abinda ya faɗa, ɗaga mata kai yayi yana bata tabbacin dawiwar Baqeer wajenta. Wani farin ciki ne taji ya kamata sai take ganin kamar ta samu Baqeer ta gama tunda Daddy yayi na'am da soyayyarsu. Shi kuwa Dady yanzu gani yake kamar babu komai cikin rayuwarshi banda yaranshi, saboda kaddarar data sameshi, sai yake ji gwara ya gyara kuskurensa tunda ga ishara nan ya fara gani tun yanzu.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA*
*UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA BIYAR*
{95}
Inna ce ta kalli Mummy cike da mamaki tace "Kina nufin hatsari yayi amma baki ma san halin da yake ciki ba? Sannan kizo kice min umara zaki? Wani irin ibada ne wannan Halima?" Murmushi tayi tana kallon Inna kai kace ba faɗa ake mata ba tace "Inna kenan, to ni in na zauna acan ma me zan yi mishi, gwara naje nayi mana addu'a kila Allah ya sassauta, ni ban san me yasa ba na gaji da murmushin ƙarya da nake yi sai nake ji yanzu komai ya isa bazan iya ba bare jinya." Cike da takaici Inna ke mata wani kallo kafin ta ajiye kulun da take saƙa tace "To wallahi wannan karan ba dani ba, wani irin mugun hali ne wannan? Mutumin daya riƙe mu hannu bibbiyu kika rabashi da matarshi, kika sa ya dinga biya ma ƴar ki kudin makaranta ba tare da saninshi ba har ta zama abinda ta zama yanzu sannan kice baza ki iya jinyarshi ba?" Ganin yadda Inna take faɗa yasa tace "Inna don Allah kinga karki kawo min ƙabali da ba'adi, sanda nasa aka maida ke Hajiya ai baki ce mun haka ba." Baki kawai Inna ta buɗe tana mamakin kalaman da Mummy ke furta mata, muryar Nabila ce ta katse mata tunani da cewa "Ai ba ita tace ki maidata Hajiyan ba, sannan in ma maidata Hajiyan ne ai da badon ita ba kema baki isa ki zama ba," ta ƙarasa maganar cike da tsiwa da takaicin kalaman Mummy. Miƙewa Mummy tayi fuskarta a murtuke don har mayafin kafaɗarta na faɗuwa tace "Nabila how dare you?" Kanta tsaye tace "Ke da kike faɗawa Inna baki yi tunanin zata ji zafi ba? Ko kuwa mu muka saka kije kiyi yawon banza har ki same……." Marin da Mummy ta zabga mata ne yasa ta yin shiru sai waigowa da tayi tana mata wani kallon raini, jikin Mummy har wani rawa yake yi saboda mamakin abinda take ji, Nabila? Yarinyar da akanta tayi komai saboda tana so ta bata rayuwa mai kyau? Duk da tsanar da tayi mata saboda tsautsayin daya faɗa mata a can ƙasan ranta tana son taga ta zama wani abun ba tare da gori ba. Bazata taɓa mantawa ba tana makarantar da tayi diploma ranar da suka yi graduation suna ta murnar gama makaranta, to saurayin da take so malamin makarantar ne, yace tazo suyi magana kafin ta tafi gida, haka ta sulale ta gudu wurin shi ba tare da ta sanar da su Inna da suka zo mata taron ba, lokacin tana ji da rawar kai, matan babansu biyu Inna da Dada, ita Dada tana da yara da yawa ita kuma Inna duk inta haihu sai ɗan ya koma sai data yi haihuwa shida sannan Allah ya bar mata Halima, shi yasa ta ɗauki son duniya ta ɗaura mata, ita kuma ta taso cike da rashin kunya don bata ganin kowa da gashi sai Innarta, gata ta iya yiwa maza wayau don su bata kuɗi bawai don tana sonsu ba, wani sa'in haka zata kira a rikice wai zata asibiti kai Babanta sai sun turo kuɗin ta cinye, to shi wannan Malamin da gaske take sonshi don akan shi tasha yin faɗa da class mates ɗinta tana ganin ita kaɗai ta dace dashi, yau kuwa tunda taji yace tazo ta lallaɓa ta gudu tana ganin yau dai zai furta mata kalmar ƙauna tunda dai ta gama school duk da tasan akwai maganar wani akanta don Babanta yayi alƙawarin bayar da aurenta ga ɗan abokin shi, da zuwanta ya shiga da ita ɗaki ya fara yi mata zance soyayya da yadda ya daɗe yana sonta, da kuma kunyar sanar da mutane yake saboda ita dalibarshi ce, jin haka yasa ta ƙara tabbatar da soyayyar shi, haka ya dinga mata daɗin baki har sai da ya keta mata budurcinta, bata damu ba don gani take yi ai aure zasu yi, haka ta dinga biye mishi suna shan shagalinsu sai dai har sama da wata bai je ko kofar gidansu ba, ita ke zuwa inya kirata bata auni ba sai da cikin jikinta yayi wata hudu sannan ta fahimci ma bata al'ada sam a lokacin fa hankalinta ya tashi nan ta rikice tayi gwaji pt sai ga ciki, Inna ce ta fara fahimta ta tsareta da tambayar haka ta sanar da ita tana kuka, sai dai me? Duk yanda aka yi Malam ya amsa yace bai san zance ba shi hasalima aurenshi saura sati biyu a lokacin, haka suna ji suna gani ya sawa idanunshi toka yace in suka yi misi sharri ma ƙara zai kai su, Inna kuwa tsoron mutane su san abun kunyar daya faru yasa ta yin shiru, nan fa Halima tsoro ya kamata tayi kuka har ta gaji, gashi Dada sai tayi ta binta da kallo tana son tasan ƙibar da tayi da yawan saka hijab da take yi na menene. A lokacin da mahaifin Halima ya frga da cikin jikinta ne yace sai dai ta fita ta bar mishi gida ita kuma Inna tace in dai ya kori Halima sai dai ya haɗa ya koresu gaba ɗaya don babu inda ƴarta budurwa zata tafi ta barta, shawara ta bawa Inna akan su je ƙauyen Innar in ta haihu sai su dawo sai dai bayan sun kama hanya ta kalli Inna a tsorace tace "Inna ina ga mu bar ƙasar in na haihu, yanzu muje inda ba'a san mu ba muce ni matar aure ce hijira muka yi bayan na haihu babyn ya ɗan tasa sai muje wani gari muce abinda na haifa naki ne in yaso in muka ga babyn ya girma ko shekara biyu ne sai mu dawo kinga ba wanda zai gane." Da wannan shawarar suka shigo garin Kaduna suka kama haya da kuɗin gadon Inna na fili da suka saida bayan ta haihu, Nabila na shekara biyu suka dawo Kano don a lokacin zaman Nigeria ya fara yi musu daɗi suna ganin gwara ta ƙara ko shekara biyu ne, Inna sam auren ma sai taji bai dameta ba don Halima na fita ta samo kuɗi, bayan sun dawo Kano ne suka kama haya anan ne kuma ta ga rayuwar Ummi wanda ta fara kwaɗaituwa da inama ita ce? Ta sani sarai yara dasu ake cutarka shi yasa taja su Zainab a jiki ya zama kafin ma Ummi taji matsalar su sun sanar mata. Dawowa tayi daga ƙaramin tunanin data tafi tana kallon Nabila wacce har yanzu itama tana tsaye a kanta. Inna ce tace "Dukanku ya isa haka, wannan wani irin abin kunya ne?" Tayi maganar cikin raunanniyar murya, wani abu Mummy ta haɗiya ta fito daga gidan ba tare da tayi magana ba, Nabila kusa da Inna taje ta rungumeta kawai tasa kuka, Inna ma hawaye kawai take sharewa wannan wani irin rayuwa ne? Nabila tana kuka tace "Inna ki yafe min wallahi nasan ina son Kabir amma ƙaryar ciki da nayi kawai fansa nake son ɗauka akan Mummy ganin ta banzatar dani taje tana neman suna wurin yaran da ba nata ba, nayi dana sanin haka don daga ɗaukan fansa kan Mummy soyayyar Kabir ta mamayeni har na aikata abinda nayi, ki yafe min." Kai kawai Inna ta girgiza don bata san me ma zata ce ba, wannan wani irin bala'i ne? Tashi kawai tayi ta koma ɗakinta ta kulle ta baza tagumi lallai son zuciyarta ne ya ja mata don a zamansu sun yi niyya ne in Halima ta haihu su koma yanzu gashinan ita rayuwar ma ba daɗi take yi mata ba, tsoronta ta mutu ƴan uwanta basu sani ba, bare mijinta da kila ma baya raye. ***** Kabir ne ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Salim kafin ya ɗau robar ruwa ya kwankwaɗa yace "Yanzu ba yanda zamu yi mu haɗa su? Ya kake gani in muka yi amfani da matsayin mu? Kai ka kira Baqeer ni na kira Zee muce mu haɗu anan?" Salim ya jinjina kai yana dariya yace "Haka zamu yi am sure in dai sun haɗu tofa tsumar ƙauna zata tashi." Hannu suka sake yin musabaha wai deal ya haɗu, Kabir yace "Karfa ka manta an jima ƙarfe biyar na yamma." Salim ya jinjina kai alamar gamsuwa yace "Kai ma kar ka manta." Da haka suka yi sallama duk sunaji sun ƙosa gobe tayi. Baqeer kuwa kallon mai gidan yayi bayan ya amshi takardun gidan yace "Nagode sosai," ya dawo mota Tanimu ya tuƙa suka koma gida. Yana shiga gidan yaji muryar Umma na cewa "Koma dai menene kar ki yiwa Baqeer magana yanzu, don na kula yanzu a wuya yake sam bashi da haƙuri sai ya maida abun wani abu, aiki ai ba dole bane." Dada ce ta cafe da cewa "Tunda ya rabu da Zainab ya zama mara fara'a ga saurin fushi, ni amma Maryama dole ne aikin nan? Ki zauna kiyi biyayya kamar yadda muka yi." Kekenshi ya tura zuwa cikin gidan, Umma ce ta kalleshi a ranta tana fatan Allah yasa bai ji ba, kallon Maryam yayi wacce tayi saurin goge ƙwallarta tace "Ya Baqeer sannu da zuwa, ni yanzu nake shan labari wai da gaske Zainab budurwarka ce?" Wani abu ne ya taso mishi ya ɗan motsa baki zai yi magana Dada tayi caraf tace "Tsohuwar budurwa dai ko? Yo ni Baqeeru kama taɓa zuwa zance?" Ji yayi kalaman Dada kamar sun ƙara taso mishi da ƙaunar Zainab, murmushin yaƙe kawai yayi yace "Hajiya Dada kenan," yayi maganar yana juyawa maimakon ya shiga ciki, Umma ce tace "Ina kuma zaka?" Yace "Abu zan amso Umma ba daɗewa zan yi ba," yayi maganar yana murmushi. Waya ya yiwa Tanimu akan ya taimaka ya kaishi wani guri, ba musu ya dawo don dama ba abinda zai yi a gida, gidan Maryam suka nufa don yana son yin magana da mijinta ya sani ba sai an faɗa ba mahaifin mijin ne ya hana aikin, don ya daɗe shi ke shirya su in sun yi faɗa lallai ya daina sakin fuska tunda har Maryam ta gwammace faɗawa Umma akan shi bayan bata yi, wayar Salim ce ta shigo ya ɗaga nan ya sanar dashi wai akwai wani mutumi da yazo yana son ganinshi a Gusto wai yazo daga Abuja ne zai wuce, ajiyar zuciya yayi sannan yace yana zuwa. Zainab kuwa tana riƙe da kaskon turaren wuta tana yi suna waya da Inaya, dariya kawai take yi saboda tambayar da Inaya ke mata, Mummy ce ta shigo tana matse ƙwalla tana kiran Kabir tana cewa "Kabir kana ina? Nikam ina Senate ɗina tun bayan kwanciyarshi nima zazzabi ya rufeni daga asibiti nake kwanana bakwai ana yi mini ƙarin ruwa…" ganin Zee ne yasata yin turus, Zee ta kalleta ta kawar da kai ta cigaba da wayarta kamar bata ganta ba, kai tsaye ɗakin Daddy ta nufa tana cigaba da matse ƙwalla. Ta kai hannu zata buɗe Zee ta riƙe handle ɗin, da mamaki ta kalli Zee tace "Auta oyoyo Allah yayi kin dawo ya jikin Senate? Har yanzu jiri nake ji." Bayan wuyanta Zee ta shafa tare da waigawa sai kuma ta juyo tace "Wa zai mayar dake asibiti?" Tayi murmushi tace "Na warke ai." Kai Zee ta girgiza tace "Ahh a hakan?" Da yake Mummy bata shirya barin gidan yanzu ba sai cewa tayi "Zainab please kar mu tsaya sa'in sa." Hannu tasa ga mamakinta key ta ciro cikin aljihun wandonta, a gaban Mummy tasa key a kofar ɗakin sannan ta girgiza mata key ɗin tasa a aljihunta tace "A gaida Inna, kar ki manta ki kwashi kayanki," tana kai nan ta maida waya kunnenta suka cigaba da hira da Inaya, a fusace Mummy ta fice ta bar gidan. Kabir ne ya fito daga ɗaki yana dariya ashe tunda ta shigo yazo fitowa ya jisu da Zainab yace bari ya ƙyalesu, kallonta yayi yace "Bani key ɗin zan zauna wurin Daddy please taimaka ki amso mini saƙo wurin wani abokina a Gusto yazo daga Abuja zai wuce ni kuma Daddy na buƙata ta kinga har text yayi min, kallon shi tayi kafin tace "Kai dai baka so na huta wallahi," tayi maganar tana bashi key ɗin bata wani canza kayanta ba kawai abaya tasa baƙa a sama tayi rolling tare da sa sun glasses ta fito. Baqeer ne ya fara isa ya shiga sai dai bai ga inda mutumin yake ba, gashi waiters har sun bashi wurin zama, ruwa ya sha yana duba agogon hannunshi na apple watch, ganin har minti ashirin ga Salim yaƙi ɗaukan wayarshi yasa kawai ya yanke shawarar tafiya gida, turo electric wheelchair ɗinshi yayi yana zuwa jikin ƙofar fita ya ja ya tsaya saboda abinda idanunshi da zuciyarshi suke hango mishi, Zee ce tafe ɗauke da waya a kunnenta da alama Kabir take kira ganin bai ɗauka ba yasa taja tsaki tana waigawa idanunta ya sauka akan abinda zuciyarta ta daɗe tana muradin gani, nan da nan zuciyoyin mutanen biyu ta karye, kallon juna suke kamar yau suka fara ganin juna, wasu mutane ne suka zo shigowa ɗaya saura kaɗan ta buge Zee, Baqeer da sauri ya mata alama da hannunshi akan ta matsa, matsawa tayi tana waigawa sannan ta sake maida ido kanshi, wani abu ya haɗiya yana jin kamar yaje ya rungumeta sai dai ya sani wannan lokacin akwai saura. Takowa ta fara yi shima yana turo kekenshi har suka haɗu a tsakiya, hawaye ne suka gangaro saman kuncinta ta saki wani murmushi wanda kana gani kasan kuka ke neman ƙwace mata tace "Ya Baqeer?" Ji yayi sunan ya ratsashi don abinda ya dade yana begen ji kenan, murmushi ya sakar mata yace "Zainab!" Ido ta runtse ta sa bayan hannunta ta goge bayan idonta tace "Ka canza." Ta nuna kekenshi tana dariyar dake ɗauke da gudun hawaye, kai ya daga mata yace "Hmm ba kya nan lokacin." Kai ta sake jinjinawa tana share ƙwalla tace "Umm bana nan." Kallon juna suka yi suka saki murmushin da su kansu sun san na missing ɗin juna ne. Kai ya nuna mata alamar su zauna, kai ta jinjina ba tare da ta musa ba suka wuce suka zauna. Menu aka kawo musu ya miƙa mata tare da ɗaga mata kai yace "Yi mana order." Ta saki murmushi sai kuma tasa hannu biyu ta rufe fuskarta hawaye na zubo mata tace "Ya Baqeer kasan Daddy yayi hatsari?" Tausayinta ne ya rufeshi ya cire tissue ya miƙa mata yana cewa "Umm naji." Amsa tayi tace "I am really scared in ya bar duniyar nan fa? Ya zanyi? Ina zani?" Ido ya zuba mata yana jin ƙauna da tausayita na dawo mishi sabo fil yace "Ko mu fita?" Kai ta ɗaga don ba abinci ne a gabanta ba ganinshi ya gama ƙosar da ita kuma tana son kaɗaicewa da Baqeer.