Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 72

Baqeer complete - Chapter 72

Baqeer complete Chapter 72: Baqeer complete Chapter 72. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

2,597 words

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* [2/6, 08:44] Ayusher: *BAQEER* *NA*

*UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA SHIDA*

{96} A jikin motarta suka tsaya Baqeer nata kallonta, gaba ɗaya sai yaga ta canja mishi, ga wata irin nutsuwa da take da ita yanzun. Wani irin farin ciki ne yake ratsa zuciyarshi, yau dai gashi ga abar son shi a zahiri ba'a irin mafarkan da yake yawan yi ba sai idan ya farka yaga ashe mafarki yake yi. Ƙasaitaccen murmushi ya sakar mata yace "Kin dawo daga tafiyar kenan?" Itama murmushin ta sakar mishi kwatankwacin wanda yayi mata, haka nan take jin kunyar shi yau. Cikin wata irin murya tace "Umm na dawo, ya aka yi kasan bana nan?" Tace tana kallon fuskarshi sai dai ta kasa haɗa idanunta da nashi. "Matsoraciya ce ke ai ban sani ba." Yar hararar tsokana tamai tace "Allah a'a, sannan indai ansan bana nan kenan nemana akaje ba'a sameni ba?" Kai ya ɗan kauda yana murmushi mai sanyi yana cewa "Hmm maybe, kila naje bakya nan ance kinyi tafiya, maybe kila na ƙira wayar bata shiga ba." Da mamaki ta juyo tana kallon shi jin wai yayi ta zuwa yana nemanta, ita ai ta ɗauka ya rabu da ita kenan tun daga abinda Daddy yayi mishi ashe dai bai manta da ita Aaaba, sai taji wasu hawaye na neman cika idonta, ɗaga idonta sama tayi tana ƙoƙarin mayar dasu ciki don bata son tayi kuka a gabanshi. Sai da ta samu hawayen suka koma sannan tace "Ɗambatta na tafi wurin Ummi, wayata kuma na canja number ne." "Saboda ni kika canja number?" Yayi mata tambayar muryarshi tana ɗan rawa don yaji babu daɗi da yaji wai ta canja number ne, kenan don kada ya kira ya sameta a waya shi yasa ta canja layi. Da sauri tace "No ba haka bane Ya Baqeer nayi ne saboda hakan zai fi mana sauƙi wajen mantawa da juna don nasan mawuyacin abu ne iyayen mu su bari muyi aure a wancan lokacin sai dai hakan da nayi bai rage komai na daga yadda nake jinka a cikin zuciyata ba sai ma kewa da tunaninka da basu taɓa barina na huta ba." Wani daɗi yaji da jin yadda take jaddada soyayyarta a gareshi, kallonta yayi sai yaga kamar ta gaji da tsayuwar don haka yace ko zaki shiga daga cikin motar ki zauna naga kamar kin gaji," kallonshi tayi sai ta girgiza kai alamun a'a don bata son abinda zai shiga tsakaninsu a yau ɗinnan. Shiru suka yi kamar ba zasu sake magana ba sai kuma yace "Da kikaje can kin manta dani?" Waigowa tai ta kalleshi, idanuwansu suka haɗu da juna, idanunta na kanshi yace "Ba haka bane?" Kai ta girgiza haryanzu idanunsa na kanta, ya dan waiga kaɗan gefe yace "In nace ban taɓa son wata mace kamar yadda nake jin son ki a raina ba zaki yadda?" Wani abu ne taji ya sauka daga saman kanta har kafafunta, idanuwanta ta zuba mai wanda suke tara kwalla, hannunsa yasa cikin aljihu yana cewa "Maganganun Daddy basu ban tsoro ba sai ma ƙara min ƙarfin gwiwa da suka yi wajen son ganin na mallake ki, tafiyar da kika yi ce abinda yayi min cikas don ni ban ɗauki rashin jituwarsu da Baba abinda zai hanani aurenki ba zan aureki with or without his consent, bana jiran ya bani izinin aurenki don bashi zai zauna min dake ba, Daddy ne dama matsalar shima kuma na shirya ɗaukar duk wani ɓatanci da zai fito daga wurinshi idan har zai haƙura ya bani aurenki."

Wani murmushin farin ciki ne ya suɓuce daga bakinta, cikin yanayi na jin kunya ta goge kwallarta tace "Shima Daddy ba matsala bane don a yanzu ya amince na kawo wanda nake so zai aura min ni kuma kasan kai ne..." sai tai shiru tana ta rufe fuskarta saboda kunyar yadda ta iya tsayawa a gabanshi tana fallasa mishi asirin zuciyarta. Ya kalleta yace "Faɗa min nine me?" Kai ta girgiza tace "Kaima kansani." Shima kai ya girgiza yace "Bansan komai ba, a faɗa min ko daga haɗuwa na fara rubuta bashin da aka fara bina." Kallanshi tai tace "Zaɓina, kai nake so da kai nake da burin kasancewa har ƙarshen rayuwata." Dariya yayi kunyarta na ɗaya daga cikin abubuwan dake burgeshi da ita, duk da Zainab take sakaltacciya tana da kunya sosai abinda yake ƙara mishi jin sonta don ya kasance yana son mace mai kunya, kuma yanasan mace wacce zata faɗi abinda ke ranta shiyasa santa yai kane-kane a ranshi.

"Yanzu dai an bani go ahead naje naga Daddy kenan?" A kunyace ta ɗaga mishi kai alamar amsawa, "In Sha Allah zamu je, sai kuma a bani number da aka canja saboda ni," ya ƙarashe maganar da tsokana. Dariya tayi ta miƙa hqnnu ta karɓi wayar da yake miƙo mata, number ta daddana ta miƙa mishi yayi saving, sai da ya fara kiranta don taga tashi number sannan yayi saving number da *Sweetums*. Kallanshi tai tace "Allah ka canza," tai maganar cike da shagwaba, kallan daya mata ne yasa tai saurin cewa "Ya Baqeer ina Dada?" kewar Dada na daga abun da yafi damunta a zamanta a Ɗambatta, sai sannan tasan ashe ba ƙaramin sabo tayi da Dada ba. "Tana nan lafiya ƙalau, kullum sai tayi maganarki." "Allah sarki Dada sosai nayi kewarta wallahi, don Allah kace ina gaisheta." Ɗaga mata kai yayi alamun amsawa. Kamar kada su rabu haka suke ji sai dai kuwa hakan ya zame musu dole don magriba ta kawo kai, kallon agogon hannunshi yayi sai sabbab ya tuna ashe fa fitowa yayi da niyyar zuwa gidan Maryam suyi magana da mijinta sai dai yanzu lokaci ya ƙure ba zai yiwu yaje musu gida da fare ba sai dai kuma gobe. Haka suka yi dallama da Zeey ta shiga motarta yana kallonta har sai data bar wurin sannan shima ya shiga tashi motar Tanimu yaja shi suka koma gida, daga shi har ita sun manta da wasu mutane da suka zo gani tunda suka haɗu da junansu shikenan suka manta da komai.

***** Da farin ciki Zeey ta koma gida, tana yin parking lot Kabir ya fito daga cikin gidan zai tafi masallaci sallar magriba, sai sannan ta tuna ashe fa shi ya tura ta taje ta karɓo mishi saƙo ita shaf ta ma manta da abinda ya fitar da ita ganin Baqeer da tayi yasa ta mance da komai. Fitowa tayi daga motar shima yana ganinta ya nufo wurinta da sauri yace "To ya?" Harararshi tayi tace"Ka duba wayarka ka gani sau nawa na ƙira ka, kawai ka tura ni wuri baka bani number ba don haka kada kaga laifina da ban karɓo maka saƙon ka ba." Ɗan sosa kanshi yayi yace "Share wannan batun don Allah, kun dai haɗu ai ko?"

Ɗaga gira tayi tana kallonshi sai kuma tace "Baka ji abinda nace ba, ni banga abokin naka ba don ban san shi ba kai kuma kaƙi ɗaukar wayarka shi yasa nayi tahowata gida." "Da Baqeer nake nufi Zeey, I mean kun haɗu da Baqeer a wurin?" Baki buɗe ta tsaya tana kallonshi mamaki ƙunshe a fuskarta, ya aka yi yasan ta haɗu da Baqeer? Kada dai ace? Dariya yasa yace "Yup, nine nan na haɗa ina fatan dai kun yi sorting out issues ɗin ku." Girgiza kanta kawai tayi sai dai bata jin haushin abinda yayi ba sai ma ƙara jin ƙaunarshi da tayi cikin ranta don yayi mata abinda ta kasa yiwa kanta wato neman Baqeer su daidaita duk da tun farko it ta datse alaƙar dake tsakaninsu. Anan wurin ta wuce ta barshi taƙi bashi amsar da yake son ji, itama sai ta wanashi kafin ta faɗa mishi. "Come on mana Zeey," yace yana ɗan bubbuga ƙafafun shi a ƙasa. "Kana nan wurin har a tayar da sallah baka tafi," tayi shigewarta cikin gida. Sai da ta fara leƙa ɗakin Daddy ta ganshi yana zaune akan wheelchair ɗin shi yana sallah sannan ta wuce ɗakinta ita ma tayi sallar. Yau wani irin farin ciki take jin kanta a ciki bata jin akwai wani abu kuma da zai ƙara ɓata mata rai, dama Baqeer ne damuwarta kuma Allah ya dawo mata dashi cikin rayuwarta tana kuma da tabbacin Daddy zai aura mata shi a wannan karon. Ta idar da sallar kenan tana naɗe abun sallar Kabir yayi knocking a ƙofar ɗakin, sai data bashi izinin shigowa sannan ya tura ƙofar ya shigo. Kamo hannunta yayi suka zauna akan gadon kafin yace "Please Zeey ki faɗa mini ya kuka yi dashi." Ƙwace hannayenta tayi tace "Sai ka faɗa mini yadda aka yi kasan zai je wurin daka turani, tukunna ma tsaya kenan babu wani abokin ka da zai bada saƙo tsarani kawai kayi fon naje wurin?" Gira ya ɗaga alamun amsawa. Girgiza kanta kawai tayi sai kuma tace "Haɗuwata dashi came to me as a surprise don ban tsammaci ganin shi a wannan wurin ba sam. Mun yi magana dashi ya nuna interest ɗin shi a kaina har yanzun despite abinda Daddy yayi mishi yace ma zai zo ya gaishe da Daddy, so abinda ya faru kenan." Jinjina kai Kabir yayi yace "Ni dama nasan zai dawo wuyarta baku haɗu ba an farfaɗo da tsohuwar soyayya shi yasa muka haɗa plan da abokin shi Salim muka tura ku Gusto shi akan zai ga customer ke kuma nace kije ki karɓo mini saƙo, gashi nan kuwa shirinmu ya tafi bisa tsari yanzu sauranmu shan biki, iyye waya ga Zeey amarya." Harararshi tayi sai dai kuma ta kasa ɓoye farin cikinta don haka dariya ta ƙwace mata duk yadda take so ta basar ta kasa. Haka Kabir yayi ta tsokanarta sai da taga zai dameta ta koreshi daga ɗakinta ta sawa ƙofar key ta rufe, kwanciya tayi akan gadonta tana tunanin Baqeer da taga gaba ɗaya ya canja mata ya zama babban mutum, kana ganinshi kaga wanda yake cikin wadata da walwalar rayuwa abinda ya ƙara saka mata nutsuwar zuciya duk d tasan yadda shagon shi ya zama so successful saboda tan bin su a duk kafafan sadarwa na social media tana ganin irin cigaban da suke samu kullum tana kuma alfahari da hakan, tun ma ba idan an ƙoda shi ba sai taji kanta ya fasu tana jin wia Baqeer ɗinta ne wannan Allah ya ɗaukaka shi haka.

***** Sai da Zeey ta bar wurin sannan ya shiga mota Tanimu yaja suma suka bar wurin, suna hawa titi Tanimu yace "Zamu je can inda kace zamu ne da farko kafin oga Salim ya kira ka?" Girgiza kai yayi yace "A'a mu tafi gida kawai dare yayi, mun je gobe." Jinginar da kanshi yayi a jikin kujera ya lumshe idanunshi, Zeey kawai yake gani da sassanyan kallon da take jifan shi dashi da kuma murmushin ta mai sa zuciyarshi ta narke cikin ƙaunarta. Wani tunani yayi da yasa shi buɗe idanunshi ya ɗauki wayarshi ya ƙira number Salim. Kamar wnda yake jiran kiran kuwa tana fara ringing ya ɗauka. Baqeer naji ya ɗauka yace "Kai dai wallahi anyi ɗan iska, dama kasan abinda ka shirya shi yasa nayi ta ƙiran wayarka kaƙi ɗauka." "Ban burge ka ba kenan?" Shima ya mayar mishi daga can ɓangaren. Tsaki Baqeer yayi yace "Ai dai kasan amsarka, amma ta yaya hakan ta faru? Ya aka yi kasan zata je wurin a daidai wannan lokacin?" Ƴar dariya Salim yayi yace "Ina zaune a majalisa yayanta yazo ya sameni akan yana don haɗaku kai da Zeey ya nake ganin za'a yi, to anan muka haɗa plan ɗin turaku wurin a daidai lokaci ɗaya, amma kafin na amince sai da yayi min rantsuwa akan bada wata manufa zai yi hakan ba kawai yana so ya gyara kuskurenshi na baya, baka taɓa faɗa mini shi ya bugeka ba amma."

Shiru Baqeer yayi yana jinjina wai Kabir ne ya tura Zeey wurin don su haɗu su daidaita tsakanin su, Kabir ɗin da babu wata jituwa a tsakaninsu tun suna ƙanana sai dai kuma ba abun mamaki bane duba da yadda yabi shi har shago don ya bashi haƙurin kaɗe shin da yayi. "Babu amfanin faɗan ne shi yasa kuma nima ban gama tabbatar da shi ɗin bane sai ranar da muka je gidansu Babanta yayi mana wulaƙancin nan." Lokacin da suka shiga unguwarsu har an shiga sallar magriba don haka ya cewa Tanimu ya tsaya a masallaci suyi sallah sai su ƙarasa gidan gaba ɗaya. Sai da suka yi har sallar isha kafin su tafi gida. A parlourn Dada ya tarar dasu it Dada Umma suna kallon tashar arewa 24 suna cin tuwo. Bayan sun gaisa yake tambayar Umma ina Maryam sai tace mishi ai yana fita itama ta tashi ta fita gida, ɗaga kanshi kawai yayi cikin ranshi dai ya ƙudurce gobe da safe suna fita gidanta zai fara zuwa kafin ya ƙarasa shago don dole a shiga maganar ta da uban mijinta idan har mijin nata yana son cigaba da zama da ita dole mahifinshi ya ɗauke idonshi daga sabgar gidanta don ɗan shi take aure ba shi ba da zai bi ya takura rayuwarta. Dada ce ta kalleshi tace "Kai kuma lafiyatka tunda ka shigo kake ta faman washe haƙora?" Kallonshi Umma tayi, ashe ba ita kaɗai ta lura da fara'ar daya shigo da ita gidan ba. Murmushi yayi yace "Wai ke Dada komai kika gani sai kin yi magana ne?" Taɓe baki tayi tace "Kai dai ka sani, idan tayi wari ai zamu ji ne. Zaka ci abincin ne a kawo maka ko ba yanzu," girgiza kanshi yayi yace "A ƙoshe nake bazan ci ba Dada," don farin cikin da yake ciki ya ƙosar dashi baya jin zai iya saka wani abu a bakin shi. Juyawa yayi zai bar parlourn sai da ya kai bakin ƙofa sannan yace mata Zainab na gaisheki. Yayi ficewarshi tun kafin ƙwaƙwalwarta ta gama processing wacce Zainab ɗin, yana fita ya jiyo muryarta tana tambayrshi "A ina kaga Zainabun? Shi yasa ka shigo babu wannan ɗaɗɗaurewar fuskar daka tsiri yi yanzu?" Shi dai yana jinta bai amsa mata ba har ya shiga ɗakin shi yana tunanin kiran Zeey a waya don bai gaji da ganinta ba ɗazu kawai don ya zama dole su rabu ne yasa ya ƙyaleta ta tafi.

*

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* [2/6, 11:40] Fatima Eshak: *BAQEER* *NA*

*UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA BAKWAI*

{97}

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull