Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 73

Baqeer complete - Chapter 73

Baqeer complete Chapter 73: Baqeer complete Chapter 73. Zee duk yadda taso bacci ya ɗauketa ta kasa ji take yi kamar in ta kwanta zata tashi ace mata…

3,087 words

Zee duk yadda taso bacci ya ɗauketa ta kasa ji take yi kamar in ta kwanta zata tashi ace mata mafarki take yi, wayarta ce tayi ƙara alamun saƙo ya shigo wanda hakan yasa ta saurin janyowa, sunan da Baqeer ya rubutawa kanshi ne kawai yasata sakin wani murmushi sannan ta mirgina tare da yin ruf da ciki ta bude, "Hmmm ban ce komai ba kar a sa ran love text na turo." Dariya ne yazo mata don har sai da haƙoranta suka fito, reply ta danna zata mishi sai ga wani saƙon, "Hmm kar ki damu an yafe miki yin reply dama dai nayi checking ne ko number na aiki ba'a canza wata ba." Saman goshinta ta ɗan buga saboda dariyar da Baqeer ya saka ta, sai ga wani saƙon yace "Hmm bacci?" Ƙiran numbershi tayi ringing biyu ya ɗauka yace "Oh ashe layin na aiki." Dariya tayi tace "Ya Baqeer Allah ka bari nifa saboda kaina na canza number." Ajiyar zuciya suka ji sun yi a tare ga mamakinta sai ji tayi ance "I miss you!" Wayar da ke hannunta ne ta nemi suɓucewa saboda mamakin abinda taji, yawun bakinta ta haɗiya cikin wani shauƙi tace "Ya Baqeer Allah ka canza." "To ke wane kike so? Wannan Baqeer ɗin ko wancan?" Kunya kalamanshi suka bata, lallai ta yarda da ake cewa maza in suna son mutum basa kunya, tace "Both ni ai kai ɗin nake so." Gira ya ɗaga don shi dama yana da tabbacin son da take yi mishi wanda hakan ne yasa yake ji dole ya bayyana mata abinda ke ranshi don shi yana da tabbacin son da take yi mishii amma ita fa? Yana ganin bai nuna mata ba balle ta samu wannan tabbacin. Katse tunaninshi tayi da cewa "Yaushe za'a kaini MOHBAQ?" Da mamaki yace "Ya aka yi kika sani?" Kafaɗa ta ɗaga tace "Da alama duk da na canza number ban iya canza abinda ke raina ba." Wani sanyi ne ya ratsashi lallai dole ya dawo da Zee kusa dashi don rashinta a rayuwarshi sai yaji komai ya canza mishi har tunani yake yaushe rabon da ya zauna yana surutu haka? Haka suka ɗan sake taɓa hira kafin suyi sallama, kowannensu zuciyarshi na cike da so da ƙauna da begen ɗan uwanshi. Bacci tayi bata tashi ba sai asuba, tayi alwala tayi nafiloli sannan tayi sallah, ɗaki ta fito tayi wurin Dady zama tayi ya idar da sallah sannan ta gaisheshi, ta ɗauko maganinshi ɗaya da aka ce ya dinga sha ƙarfe shida bayan ya sha ta kalleshi tace "Daddy akwai abinda kake so?" Kai ya girgiza sannan yace "Allah yayi miki albarka Zainab, kwanan nan ina ji rayuwata ba wani amfani da take dashi, duniyar nan sai sake bani tsoro take," ya ƙarasa maganar cike da rauni wanda kana iya ganewa ta muryarshi, kanta ta kwantar akan ƙafarshi yasa hannu saman kanta tace "Rayuwar kenan Daddy ina ga waɗanda suka mutu? Sannan kai ƙafa ɗaya wanda zamu iya zuwa waje a sa maka artificial ƙafa naga ana yi kuma mutum yana samu yayi tafiya." Kai ya girgiza alamar a'a yace "Menene amfanin haka Zainab? Ba inda zani, a yanzu ina ji nafi tsoron Allah da nadama akan ruɗin duniya da abinda ke cikinta, hakkin mutane ina zasu barni? Kuɗaɗen mutane da muka dinga ɗeba suna ina?" Ya haɗiyi wani abu daya tokare mishi yace "Gashi nan abinda na gama sata nasa sunan matar nan saboda amana ko ganinta ban yi ba balle nasa ran ko kuɗin asibitina ta biya." Tausayinshi ne ya kama Zainab ta shafi fuskarta tace "Haka rayuwa take, itama sai ka barta da duniya da kuɗin dama kai ma ba gumin ka bane kaga kenan duk abinda zata yi da kuɗin taje tayi ƙofa a buɗe take, ta shiga hakkin mu ta rabamu da mahaifiyar mu wannan shi kaɗai ne abinda bazan taɓa yafe mata ba amma sauran taje can tsakaninta da wanda ya halliceta." Kalaman Zee sosai suka saka mishi nutsuwa cikin ranshi ya ɗan yi murmushi yace "Allah yayi miki albarka, ya baki miji na gari." Ameen tace sannan ta ɗora da cewa "Daddy?" Sai kuma tayi shiru kallonta yayi yace "Ya? Ba dai har kunyi faɗa da Baqeer ɗin ba?" Mamaki ne ya kamata tace "Ya aka yi ka san na ganshi?" Sai kuma ta girgiza kai tace "Oh ni Ya Kabir." Murmushi yayi yace "In kun gama shiri kwa sanar damu yazo mu gaisa." Kallonshi tayi cike da tausayi ta ina zata iya barin Daddy cikin wannan hali tayi aure? Murmushi yayi mata yace "Ba dai har shekara zaku kai kuna ƙalula ba?" Bata san sanda tace "Daddy shekara?" Rufe baki tayi da sauri sai kuma suka saki dariya a tare kafin yace "Nasan ni kike ji sai dai karki damu Kabir na nan sannan menene bana iya yi?" Murmushi tayi sannan ta ɗaga kai jiki a sanyaye. ***** Jamila duk abin duniya ya dameta ta kalli Bashir tace "Kaga ka shirya ka kira Fatima kace saƙo ne zaka kawo mata, ita nasan zata sanar da kai inda take, to in har kaje kar ka kuskura ka taho sai kasan inda Baqeer yake aiki yanda zaka nemi ya ɗaukeka kai ma aiki kana gani gashi ka gama karatun amma aiki ya gagara." Kai ya jinjina don shi dai yanzu in dai zai samu aiki to fa lallai zai yi, sannan ai gwara wurin ɗan uwanshi ma da bare." Gyaran muryar Badaru suka jiyo da sauri ya miƙe ita kuma ta fara neman waskewa tana cewa "To adai kula bana son shirme da bin abokan banza." Sai da Badaru yazo bakin ƙofa yana waige-waige yana hura hanci ya ɗan kalli ɗakin yace "Kai Bashir in ka samo inda Yayanka yake ka faɗa min, don raini ina mahaifinshi ba zai zo ya sanar dani sana'ar da yake yi ba bayan ni nasha wahala a kanshi, dole yazo ya bani haƙuri don yasan yayi laifi." Bashir shi dai ya samu ya fito don haka kawai ba zai samu aiki Baba ya kashe mishi ba, waje yayi shi kuma Badaru maimakon ya shiga ciki sai ya fito yana hararar ɗakin Umma kafin yayi ƙwafa ya yaye labulen Abu yace "Ke har yanzu baki tattara kin bar min gida ba?" Cigaba tayi da ƙullin maganinta tana cewa "Babu fa inda zani Malam na faɗa maka aurena da kai mutu ka raba in ma ka sakeni zan yi zaman yarana ai kai kasan ba inda zani shekarar mu nawa tare? Kamalu ne kaje can kun fi kusa dashi amma ba inda zani." Kallon mamaki yayi mata kafin yayi ƙwafa ya fito waje don shi dai takaici duk ya gama isarshi burinshi kawai yasan ya aka yi Baqeer yayi kuɗi? Bayan yasan da filin shi da aka sata ne sannan da zanen daya koya mishi ne? Sam kwanan nan rayuwa bata yi mishi daɗi don shagon nashi ma yau yayi cinikin ragowar ƴan sauran abinda ke ciki ya sallami yaran shagon saboda ba komai gashi ba zai iya biyan kuɗin haya ba, in ya tuna Kamalu ne ya yasheshi gashi ko labarinshi babu, wannan abu na baƙanta mishi rai. *** Yau Baqeer daga shago gida ya dawo ga mamakinsu Umma wanka ya sake yi bayan wanda yayi da safe, Dada tana gefe suna hira tana ganinshi sai ta fara waƙar gaɗa da ake yi a ƙauye na 'saurayi zai je zance ya kasa bacci' Baqeer na jinta shi dai ya wuce ɗaki ya rufo a yanzu ba kunyar da zai ji akan son da yake yiwa Zainab, farin cikinshi ɗaya ya sayi gidan nan don haka dole ya gaggauta ayi aurensu ya ganta kusa dashi, yadin da yake ɗinkawa da style ɗinshi na daban da yake yi shi ya saka, dakakkiyar hula mai tsada ya saka ya kalli kanshi a madubi ya fito cas dashi, lallai da ace yana tafiya da sai gayun yafi fitowa, miƙewa tsaye sannan ya hau kan wheelchair ya zauna saboda baya iya taka ƙafar har yanzu. Wayarshi ya ɗauka ya kira number Zee fuskarshi ɗauke da murmushi, bata daɗe ba ta ɗauka tare da sallama, amsawa yayi sannan yace "Mu biyu zamu fita ko ana son third party?" Dariya ma abun ya bata tace "Muna buƙatar third party tun kafin wani ya ɗaura mun aure ba magabata." Duk yadda Baqeer yaso ya daure sai da yayi dariya, murmushi tayi ita kanta kafin tace "Allah Ya Baqeer tsokanar ka tayi yawa, ka shirya na fito?" "Third party ɗin fa? Kin san fa zan iya kai ki masallaci a ɗaura." Kai ta girgiza tace "Zan fito yanzu." Kai ya ɗaga kafin yace "Babu sallamar love?" Kashe wayar tayi tana dafa fuskarta da murmushin daya kasa barinta, lallai Baqeer ɗinta rigimarshi ta ƙaru da yawa, kallon kanta tayi yadda tayi kyau sosai, sanye take cikin wani dakakken lace mai tsada wanda mijin Ummi ya ɗinka mata don ko sakashi ma bata yi ba, tayi kyau sosai kyanta ya ƙara fitowa, falo ta fito jin alamun hira yasa ta nufi falon Daddy, yana zaune shi da Kabir ganin wani a zaune yasa ta kalleshi, waigowa yayi suka haɗa ido, mamaki ne ya kamata tace "J?" Dariya yayi yace "Zee in da amana ai ni ya kamata ki fara kira da kaddarar nan ta samu Daddy." Kallon Daddy tayi tace "Sorry wallahi everything was so hectic at that time shi yasa." "Sai ina?" Yayi tambayar yana kallonta, murmushi tayi tace "Secret place, anyway thanks for coming." Kabir ne yace "Kice yayanki yace kar kiyi dare, sannan ban yarda da yawo akai-akai ba." Harararshi tayi tace "Allah Daddy kayi mishi faɗa tunda yasan sirrina yabi ya hanani nutsuwa." A tare suka yi dariya, sai kuma tace "Ina Mubashir?" Kabir yace "Ya koma school da safe yace zai zo da weekends." Ƙwafa tayi tace "Lallai wato kai ya faɗa ma ni ko sanar dani bai yi ba," gwalo yayi mata ta fita fuskarta ɗauke da murmushi duk da ƙaddarar data samesu taji daɗin ganin yau ana dariya a gidan, mota ta shiga ta tsaya ta sayi fruits sannan tayi gidansu Baqeer saboda ba dama yayi tuƙi, waya tayi mishi bayan ta isa da niyyar shigowa, yana ɗauka sai aka yi rashin sa'a Umma na tsaye a ɗakin tana yi mishi maganar Maryam, jin sunan Umma yasa Zainab tayi saurin kashe wayar, fifita tayi da hannunta tare da sauke ajiyar zuciya tace "Allah ya soni ban shiga ba, wannan abun kunya har ina." Baqeer kuwa wayar yabi da kallo ba sai an faɗa ba yasan me ya faru, yace "Umma shi kenan sai dai in nayi mishi magana ina ga zamu fi samun mafita." Shiru tayi sai dai ba zata hana ba don harga Allah tana ganin yawan shiru yana cutar da mutane sosai. Daga waje ta hangoshi fitowa tayi ta ɗan jingina a jikin ƙofar tana jifanshi da wani kallo, alama yayi mata da ƙofa, kafaɗa ta maƙale alamar a'a kafin tace "Umma na nan ba yanzu ba." Ƙarasowa yayi da wheelchair ɗinshi, yace "Kika zo ɗauke mata ɗa?" Tana kallonshi tace "Da sauƙi ma tunda ɗan nata dama so yake na ɗauke shi." Baqeer ya jinjina kai yace "Eh lallai dole na tura magabatana kafin amin auren dole." Dariya ce tazo mata tasa hannu tana kauda kai tace "Allah ni wannan ko aure muka yi takura mun zaka yi da tsokana." Ƴar gira ya ɗaga mata yace "To ai matsalar a hakan kike so a shafa fatiha." Zee ta buɗe mishi ƙofa yana shiga ta rufe don wheelchair din zama take kamar kujera, shi yasa ta ɗaga kujerar baya. Gyaran murya tayi tace "Alhaji ina zamu yi?" Shima gyaran murya yayi yace "Driver muyi Hotoro." Harararshi tayi tace "Charges zaka fara biya ai." "In mun yi aure zan biya duka ki fara rubutawa." Kunyar kalamanshi ne ya kamata lallai Baqeer, shiru suka ɗan yi yana nuna mata hanya har saida suka zo, kallonta yayi yace "Thanks for waiting for me." Kallonshi tayi tace "Same, ɗazu J yazo duba Daddy." Fuska ya canza ya kalleta yace "Nima yau zani dubiyar." Dama da saninta tace "Da wuri haka?" Yana kallonta yace "Ai yanzu ba maganar wasa in zan je ma a shirye zani mu tattauna." Kallonshi tayi bayan ta tsaida motarta a daidai shagon, ta kalli shagon sannan ta kalleshi wani irin kallo suke yiwa juna na tausayin kansu da tsantsar ƙauna, cikin wata irin murya yace "Kina tunanin zan iya jinkirtawa?" Ido ya ɗan maida ƙasa yana kallon fuskarta yace "Kinyi kyau, tun ɗazu naso na faɗa ganinki yasa hankalina ya tafi wani wurin." Idanunta ta ɗago ta zuba mishi tace "Kaima, you look different." Kai ya karkatar yace "Do you fall harder than before?" Kwantar da kanta tayi a bayan kujera tafe "Maybe." Murmushi suka sakarwa juna kafin su fito, tayi mamakin ganin shagon Baqeer don kuwa babba ne sosai nan yake faɗa mata ai tun kafin ta tafi ya kama amma daga baya ya ƙara girman shagon, farin ciki sosai ta nuna don tasan shi mutum ne mai ƙoƙari matuƙa, kuma wannan alama ce ta nakasa ba kasawa bace. Guminshi ne hakkinshi ba kamar Daddy daya rufe ido suka dinga taɓa kuɗin mutane ba, aka ciyar da ita aka tufatantar da ita da hakkin mutane, lallai ita auren Baqeer rahama ne a gareta a ƙalla yanzu zata tsaftace rayuwarta da halal. Shi kanshi yaga farin cikin ta a bayyane, nan ta barshi ta tafi ganin su Tanimu sun zo, shi kuma dama so yake la'asar tayi yaje ya samu mijin Maryam, gashi yana son yaje ya duba Daddy.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA*

*UMM ASGHAR* DA AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA TAKWAS*

{98}

Sababbin designs ɗin da yake aiki akai ya zauna ya fitar, sai da ya gama har yayi uploading ɗin su cikin computer da suke aiki da ita sannan ya kira Salim ya faɗa mishi zasu fita in anjima bayan sallar magrib, bai faɗa mishi inda zasu je ba yace idan sun je ya gani duk da ma dai Salim ɗin yasan ba zai wuce gidansu Zee zasu ba. Ana yin sallar la'asar ya tashi daga aiki, daga masallaci basu koma shagon ba yace da Tanimu su tafi gidan Maryam, so yake yi suje su gama da wuri don baya so ya ɓata lokacin shi na zuwa gidansu Zainab. Suna isa bakin gate ya ɗauki waya ya kira Maryam yace mata gashi a wajen gate tazo ta shigo dashi. Tashi tayi cikin farin cikin yau Ya Baqeer ne a gidanta don ba zata iya tuna rana ta ƙarshe daya tako ƙafarshi zuwa gidanta ba tasan dai tun kafin ya samu accident ne. Fitowa tayi daga ɗaki ta faɗawa Baban Aareef dake zaune a parlourn Ya Baqeer ne yazo ya fita ya shigo dashi ciki. Shima yayi mamakin da jin Baqeer ɗin yazo gidan saboda daɗewar da yayi bai zo ba sai kuma lokacin yaji yana kunyar haɗuwa da Baqeer ɗin don duk tsawon lokacin nan bai taɓa zuwa yaje ya duba shi ba har Allah yasa ya samu lafiya ya cigaba da harkokinshi. Haka nan dai ya tashi ya fita jikinshi a sanyaye don ba zai yiwu ya barshi yana jira ba, surukuta ce sosai a tsakanin shi da Baqeer ɗin, yana girmama shi yana ganin mutunci saboda yadda yake tsaye akan al'amuran ƙannen shi ya ɗauki girman da Allah ya bashi. Yana fita ya ganshi akan wheelchair ɗin shi don tuni ya fito daga cikin motar yana jiran Maryam tazo ta shiga dashi cikin gidan, tunda uban mijinta ya dawo gidan da zama ya daina shiga kanshi tsaye saboda kaucewa gutsuri tsomar ƙananun maganganu bare daya fahimci halin mahaifin Auwal ɗin.

Yana wani sussunkuyar da kai ya miƙa mishi hannu suka gaisa shi kuwa Baqeer sai bai nuna ma yasan abinda yake yi ba. Zuwa yayi zai tura wheelchair ɗin Baqeer ya ɗaga mishi hannu ya nuna mishi remote control ɗinta yace "kada ka damu ba sai ka turani ba zata tura kanta." Ɗan murmushi yayi ya koma gefe, gaba yayi Baqeer na biye dashi a baya har suka shiga cikin gidan babu wanda yayi magana. Suna shiga Maryam ta tashi da fara'arta ta tareshi tana yi mishi sannu da zuwa, Aareef na zaune akan kujera yana kallon cartoon. Yana jin muryar Baqeer ya taso yana yi mishi oyoyo ganin shi zaune a wheelchair sai yasa yaron yayi turus yana kallon shi. Hannu ya miƙa mishi yace "zo mana Aareef, zo mu gaisa na daɗe ban ganka ba." Kasa zuwan yayi sai juyawa da yayi yana kallon Maryam, sai data ɗaga mishi kai sannan ya ƙarasa wurin Baqeer yana mamakin yadda ya ganshi haka har dai ya kasa yin shiru sai da ya tambayeshi. "Uncle Baqeer me ya sameka na ganka akan wheelchair?" Murmushi yayi yana shafa kan yaron yace "Accident nayi Aareef Mommynka bata faɗa maka ba?" Da kai ya amsa mishi yana kallon kujerar wheelchair ɗin with curiosity. "Zaka sauka ka bani na ɗana?" Dariya Baqeer yasa jin abinda yaron yace sai ya ɗaga mishi kai alamun amsawa, su kuwa iyayen sai girgiza kai suke yi Maryam ji tayi kamar ta makeshi don haushi. Korashi ciki tayi don tasan idan har yana wurin ba zai bari su gaisa da ɗan uwanta cikin nutsuwa ba wanda alamu suka nuna akwai abinda ya kawo shi, tafi bayarwa dai ko Umma ta faɗa mishi matsalarta ne shi yasa yazo. Kitchen ta shiga ta haɗo mishi ruwa da drinks ta ɗora akan tray haɗw da cups ta kawo, sai da tsiyaya mishi ruwa da kemon duka a kufuna ta ajiye a gabanshi sannan ta samu wuri ta zauna ta soma gaishe shi. Bayan nan suka cigaba da hira jefi-jefi shi da Baban Aareef, anan ne ma yake bashi haƙurin rashin zuwa dubashi da bai je yayi ba ya kawo uzurin abubuwa ne suka sha kanshi shi yasa bai samu yaje ba. "Ai babu komai," Baqeer yace don bai ga amfanin ɗago wannan maganar ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull