Baqeer complete - Chapter 74
Baqeer complete Chapter 74: Baqeer complete Chapter 74. Gyara zamanshi yayi akan wheelchair ɗin sannan ya kalli Auwal sosai yace "wurinka nazo akan maganar…
2,559 words
Gyara zamanshi yayi akan wheelchair ɗin sannan ya kalli Auwal sosai yace "wurinka nazo akan maganar Maryam." Kallonshi yayi sosai, shi dama tunda ya ganshi yasna dole akwai abinda ya kawo shi don tun da can baya zuwa musu gida haka nan sai idan sun samu saɓani shi da Maryam ko shi ya kira shi ko ita idan ta kirashi amma yawanci ma shine yake kai ƙararta. Gyara zamanshi yayi yace "wani abu Maryam ɗin tace anyi?" Kallonta Baqeer yayi yace "maimaita abinda kika ce yayi miki." A nutse ta buɗe baki ta fara magana, duk wata matsala da take da ita a zamanta da Baban Aareef da mahaifin shi yau sai data faɗawa Baqeer harda shigo mata da yake yi ɓangarenta kanshi tsaye akan hakan yasa yanzu ta daina zaman parlour kwata-kwata, a ƙarshe tace "to yanzu aiki ne ya sama min tun kwanaki don ya daɗe da yin alƙawarin zai barni nayi aiki saboda na faɗa mishi ina da sha'awar yin aikin, har nan ya kawo mini offer ina ta murna sai da ya fita sallah ya dawo yace wai wannan maganar a barta saboda sun yi magana da Baffa, nace ya faɗa min wacce magana ce suka yi da zai sa a hanani aiki bayan ansa min rai yace wai maganarsu ce shi da mahaifinshi nace to ai nima ta shafeni tunda akai na aka yi. Haka nan dai na haƙura da aikin ba don naso ba, nace mishi to tunda ba zai barni nayi aikin ba ina so zan koma makaranta nayi masters nan ma yace a'a ni kuma zaman haka ya isheni idan suka fita daga gidan nan haka zan yini ni kaɗai har sai sun dawo don haka nace mishi ina so zan fara snacks na sayarwa tunda abu ne ina daga cikin gida zan yi yace babu damuwa hakan shawara ce mai kyau kawai yana fita sai dawowa yayi yace wai batun sana'ar nan a haƙura kawai don shi baya son mutane suyi ta shigo mishi gida suna fita yanzu kuwa ina fara sana'a za ayi ta sintirin shigo mishi ana gane mishi sirrin cikin gida ni kuwa nace ita ma sana'ar da zan yi Baffan ya hana to kuwa in dai ba za'a barni nayi sana'a ba sai a ƙyaleni na fita nayi aiki don ba zai yiwu komai nace ina so ba sai an kushe shine yace wai ina yiwa mahaifinshi rashin kunya ni kuma Ya Baqeer gani nayi ba Baffa nake aure ba don me yasa zai dinga shiga rayuwata sai mun gama tsara magana da mijina sai ya rushe kuma ace bazan yi magana ba alhalin ni ake cuta," ta ƙarashe maganar muryarta na karkarwa alamun kuka take ƙoƙarin dannewa.
Tunda ta fara maganar duk suka yi shiru suna saurarenta har sai da tayi shiru sannan Baqeer ya kalli Auwal yace "haka aka yi?" Gyara zamanshi yayi yace "Eh Ya Baqeer sai dai kada ka manta Baffa mahaifina ne dole nayi mishi biyayya akan duk abinda yace ita kuma Maryam sai tace ba haka ba to tana nufin sai abinda take so zan bi na take ra'ayin mahaifina." Shiru Baqeer yayi yana auna maganganun da dukkansu suka yi, kallon Auwal yayi yace "Da farko dai wacce magana take yi akan mahaifinka yana shigo mata har nan da gaske ne?" Don duk cikin maganganun da Maryam tayi wannan ya fi ɓata mishi rai. Shiru yayi ya kasa amsawa. Sai ya cigaba da cewa "da gaske ne kenan tunda kayi shiru, to maganar gaskiya dole ka dakatar da mahaifinka daga shigo mata cikin gida tunda shi ɗin ba muharraminta bane kai ko muharraminta ne bai dace ya shigo mata ba tunda bai san a wane irin yananyi zai risketa ba bayan haka ita ɗin yanzu baliga ce babu dalilin da zai sa don tana aurenka mahaifinka ya dinga shigo mata ɗaki, idan kuma baza ka iya hanashi shigo mata cikin gida ba sai ka canja mata muhalli don aure take yi ba bauta ba, idan bata sake a cikin gidanta ba a ina ake son taje ta sake. Sannan kuma maganar sana'a da tayi ina ganin kayi haƙuri ka ƙyaleta tayi tunda dai baka son aikin kuma ta haƙura idan yaso sai ka gindaya mata sharuɗɗa akan yadda kake son ta tafiyar da kasuwancin nata."
Sosai yaji ranshi ya ɓaci sai dai yayi shiru bai katse shi ba har ya gama magana, cikin ɗaurewar fuska yace "Ni bazan iya cewa Baffa ya daina shigowa cikin gidan nan ba don dani da abinda na mallaka duka mallakin shi ne baya da wani iyaka da duk abinda na mallaka ba kuma zan iya canja mishi gida ba bayan nasan ba wani da zai kula dashi gareshi ba tunda mahaifiyarmu ta rasu ba kuma wata matar gareshi ba." Rai a ɓace Baqeer ya mayar mishi da "Bashiv da iyaka da komai naka face Maryam don kuwa ba a garin gaɓa-gaɓa muke ba mu musulmai ne ba kara zube muke rayuwa ba, idan har ba zaka dakatar da mahaifinka daga shigo mata ɗaki ba to lallai kuwa zan tafi da ita gida don bazan barta ta cigaba da zama da kai bata da sakewa a cikin gidanta ba tana fargabar kowane hali take ciki za'a iya shigo mata. Ke Maryam ɗauko mayafinki mu tafi don ba zaki cigaba da zama a gidan nan ba."
Da sauri Auwal ya tare shi ganin har Maryam ta miƙe zata tafi ɗaukar mayafin kamar yadda Baqeer yayi mata umarni. "Kayi haƙuri Ya Baqeer don Allah kada ka tafi da ita yanzu dai me kake so ayi nayi alƙawarin yi maka in har zaka bar mini Maryam." Kallon kada ka raina mini hankali Baqeer yayi mishi yace "zaɓi ai yana wurinka tunda na faɗa maka su, inma dai ka canja mata muhalli ko ka hana mahaifinka shigo mata wuri dai kuma batun sana'a daka hana lallai idan har baza tayi aiki ba dole ka barta ta nemi na kanta saboda halin rayuwa ba'a san me gaba zata haifar ba bayan haka kuma ita ma tana da iyaye tana da ƴanuwan da zata so tayi musu hidima da guminta ba sai ta jira abinda ka bata ba."
Haka nan ya amince da duk abinda Baqeer yace ba don yana so ba sai don yasan ba kowacce mace bace zata ɗauki abinda Maryam ɗin ke ɗauka ba. Zama da Baffa ne bata so to zai gyara mishi tsohon gidansu ya koma idan yaso sai ya nemi wata matar yayi aure, su dama tun bayan rasuwar mahaifiyarsu ai auren suka so yayi shine yaƙi shine kuma dalilin da yasa ya dawo dashi nan saboda acan ɗin babu kowa ko wajen abinci babu mai bashi amma yanzu ya zama dole ya koma ko ba zai yarda yayi auren ba idan yaso sai su nemi wanda zai dinga zama dashi suna biyanshi abinci kuma ko daga nan ko gidajen ƴan uwanshi sai a dinga girkawa ana kai mishi. Haka Baqeer yayi musu sallama ya tafi bayan ya cika Maryam da kyautar kuɗaɗe ya kuma ce tayi tunanin sana'ar da take son yi shi zai bata jari ba sai ta tambayi Baban Aareef ba.
***** Bashir na fita daga gidan ya dannawa number Umma ƙira, abinda ba zai iya tuna ranar da yayi hakan ba don fa iyayen su sun koya musu rashin ganin girmanta tun suna yara shi yasa kusan dukkansu yaran gidan suka rainata don ma ba shiga shirginsu take yi ba shi yasa duk abinsu basa iya yi a gabanta. Bayan ta ɗauka ne ya gaisheta sai kuma yace "Umma dama gaininki nake son yi don Allah." Duk da tayi mamakin jin wai Bashir ke son ganinta hakan bai hanata cewa tana gidan Dada yaje can ya sameta ba, kwatancen gidan tayi mishi don ba taɓa zuwa yayi ba. A wurin ya tari adaidaita ya faɗa mishi inda zai kai shi cike da fatan dacewa da abinda zai je nema. A ƙofar gidan Dada mai adaidaitan ya ajiye shi kamar yadda Umma tayi mishi kwatance don dama gidan ba wani wahalar ganewa ne dashi ba. A ƙofar gidan ya tsaya ya kira Umma a waya yace mata gashi ya ƙaraso sai tace mishi ya shigo kawai. Suna zaune a tsakar gida ita da mai aikin Dada suna haɗa abincin rana don tunda Umma ta dawo gidan ta karɓi aikin girkin sai dai mai aikin ta tayata da ƴan wasu abubuwan. Zama yayi akan tabarmar da Umma ta shimfiɗa mishi ya shiga gaisheta cike da girmamawa abinda da sam basa yi mata. Da fara'arta ta amsa tana tambayarshi lafiyar mutanen gidan yace mata duk suna nan ƙalau Jamila ma tace a gaisheta. Murmushi tayi tace tana amsawa jin wai yau Jamila ce ke aiko mata da saƙon gaisuwa.
Ɗan shiru yayi yana juya ta yadda zai fara faɗa mata abinda ya kawo shi sai da taga baya da alamun zai ce wani abu sannan tace "Wacce magana ce kace zamu yi? Kada kaji komai ka buɗe bakinka ka faɗa mini ni uwa ce a wurinka." Ɗan gyara zamanshi yayi yace"Dama Umma cewa yayi don Allah ko zaki yiwa Ya Baqeer magana ya bani aiki a shagon shi tunda na gama makaranta aiki ya gagara samu bare aiki a ƙasar nan da ya zama na masu hanya sai kuma mai tsananin rabo." "Haka ne,"Umma tace. "Baqeer ɗin baya nan yana shago amma In Sha Allah idan ya dawo zan faɗa mishi nasan ba zai rasa wajen da zai ajiye ka ba." Godiya yayi ta yiwa Umma don yasan tabbas Baqeer zai bashi aikin don baya taɓa tsallake umarnin Umma.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA*
*UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA TARA*
{99}
Baqeer na komawa gida wanka kawai yayi ya shirya cikin wani tsadadden men lace kalar sky blue da ya yiwa special ɗinkin shi da wa kanshi kaɗai yake yin designs ɗin. Dark blue ɗin hula ya saka sai baƙaƙen takalma ƙirar kamfanin baertozzi da ya saka. Turarukanshi ya fesa da ba'a iya tantance sunayensu saboda ba guda ɗaya yake amfani dashi ba a lokaci guda, ya kan fesa a ƙalla turare uku zuwa biyar don haka ba'a taɓa iya tantance wane kalar turare yake amfani dashi. Yana fitowa Dada ta sa ka guɗa tana tsokanarshi tace "Iye wannan wankan dai daga gani zance zaka," shi dai murmushi kawai yayi. Ta cigaba da cewa "to idan kaje kace ina gaisheta da kyau da kyau, na kuma gode da kayan marmari." Bai iya amsawa Dada ba ganin Umma zaune a wurin, ita kuwa Umma sai daɗi take ji don tasan macen ƙwarai ce kawai abinda Baqeer ɗin ya rasa a yanzu, fatanta da burinta bai wuce na ganin aurenshi da zuri'arshi ba sannan tunda taga sun koma tare alama ce ta Dady ya sauko kenan. Sallama yayi musu ya fita inda Tanimu yake jiranshi don ya faɗa mishi dama kada yayi nisa zasu sake fita bayan magriba. Buɗe mishi motar yayi ya shiga ya zauna sannan ya zagaya ya shiga mazaunin direba yaja su suka bar wurin. Sai da suka hau titi sannan yake tambayar inda suka nufa, "Unguwarsu Salim zamu je don nasan yanzu yana can yana jiranmu, ban ɗauka zamu daɗe sosai a gidan Maryam ba sai gashi mun kai kusan magriba acan." Suna shiga unguwar ƙiran Salim na shigowa wayarshi, yana ɗauka Salim ɗin yace "haba Baqeer taya zaka sani na zauna ina faman jiranka amma har yanzu baka ƙaraso ba." Ɗan tsaki Baqeer ɗin yayi yace "To Malan gamu nan mun shigo cikin unguwar, a ina zamu sameka?" "Ina majalisar su Audu, please kuyi sauri don ina da wurin zuwa nima tun kafin kuma kace wani abu ba zance zani ba." "Kaji da gulmarka,da ɗin ta dai unguwarsu ɗaya." Baqeer yace ya kashe wayar bai jira jin me Salim ɗin zai sake faɗa ba. A majalisar su Audu suka tsaya, sai da Baqeer ya gaisa da ƴan zaman majalisar da suka kasnace tsofffin abokanshi sannan Salim ya buɗe gaban motar ya shiga Tanimu yaja motar suka bar wurin. Basu tsaya a ko ina ba sai ƙofar gidan su Zeey, horn ya danna maigadi ya taso ya buɗe gate don dama Zeey ta sanar dashi zuwansu tace kada yayi nisa su zo suna ta yin horn babu mai buɗe musu ƙofa don shima akwai ɗan banzan yawo idan yaso tun ma ba yanzu da Daddy yake kwance baya da lafiya ba. A harabar gidan Tanimu yayi parking motar, basu fito ba sai da Baqeer ya ƙira Zeey a waya ya sanar mata da isowarsu. Ƙara gyara fuskarta tayi sannan ta fita wajen Daddy da yake zaune a parlourn shi da Kabir, a shirye yake tsaf zuwan su Baqeer kawai yake jira don tun bayan da suka rabu ɗazu tana dawowa gida ta sanarwa Daddyn cewa zai zo ya gaishe shi shi yasa ana yin sllar magriba ya shirya ya fito parlourn ya zauna yana jiran zuwan nasu. Faɗa mishi tayi su Baqeer ɗin sun iso, Kabir ne ya tashi ya fita don ya shigo dasu ita kuma ta tura Daddyn zuwa sitting room ɗin shi inda yake amsar baƙin shi. Bata jira shigowarsu ba ta koma ciki don ta haɗo musu kayan motsa bakin data tanadar musu.
Kabir na gaba suna biye dashi a baya a haka suka ƙarasa parlourn na Daddyn. Sanda suka samu labarin rashin lafiyar Daddyn basu ɗauka yayi sanadin daya rasa wani ɓari na jikinshi ba, sai duk jikinsu yayi sanyi da yanayin da suka sameshi a ciki. Zama Salim yayi a ƙasa shi kuma Baqeer na daga kan wheelchair ɗin shi sai dai russunawa da yayi ya gaishe da Daddyn alamun girmanawa. Bayan sun gaisa yana tayi musu ƴan tambayoyi duk don su saki jikinsu ya kuma wanke kanshi daga abinda yayi musu wancan zuwan da suka yi gidan. "Yanzu wacce sana'ar kake yi ko har yanzu paintings ɗin dai kake yi?" Ya tambayi Baqeer don fa duk son da Zainab take yi mishi ba zai ɗauketa ya bashi ba idan har baya da ƙwaƙwarar sana'a duk da ma dai yanayin shigar jikinshi bata yi kama dana mara aikin yi ba. Ya buɗe baki zai amsa mishi kenan Zainab ta shigo, wani kallo yayi mata ya sakar mata kyakkyawan murmushin da yasa ta kusa rasa nutsuwarta, ajiye tray ɗin data ɗora kayan tayi akan center table sannan ta juya zata bar parlourn sai dai kuma Daddy bai barta tayi hakan ba sai cewa da yayi ta dawo ta zauna. Daga ƙasa ta zauna a kusa da ƙafar Daddyn tana satar kallon Baqeer da shima ya kasa ɗauke idanunshi daga kanta. Gyaran murya Daddy yayi abinda ya tunatar dashi a inda yake tuni ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana jin kunyar Daddyn na yadda ya kasa ɗauke idanunshi daga kan Zeey.