Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 75

Baqeer complete - Chapter 75

Baqeer complete Chapter 75: Baqeer complete Chapter 75. "A yanzu ɗinki nake yi ina da shagon ɗinki a Hotoro sannan muna shirin buɗe wasu barnches ɗin ɗaya…

3,727 words

"A yanzu ɗinki nake yi ina da shagon ɗinki a Hotoro sannan muna shirin buɗe wasu barnches ɗin ɗaya a Zoo road ɗayan kuma a Gadon ƙaya," ya bawa Daddy amsar tambayarshi. Jinjina kai Daddyn yayi yace "yanzu a hakan kana iya ɗinki? I'm sorry fa kawai ina mamakin jin yadda kake iya yin ɗinki ne." Murmushi kawai yayi don bashi ne na farko daya fara yi mishi irin wannan tambayar ba, wanda ya ganshi akan wheelchair sai yayi mamakin ta yadda ake yake iya yin ɗinki. "Yawanci kekunan namu electric ne wasu ma are computerized don haka aikin yana zuwa mana da sauƙi, a yanzu kuma da nake da ma'aikata ban fiye hawa keke ba sai dai nayi designing na kuma yi yanka su kuma sai su haɗe kayan." "Masha Allah," kawai Daddy yake cewa don he's really impressed da yadda Baqeer ɗin yayi mishi bayanin, lallai tabbas bahaushe yayi gaskiya da yace babu nakasashe sai kasashe shi dai Baqeer gashi nan nakasa bata hana shi tashi ya nemi na kanshi ba abinda ya kamata ace mutane masu disability sun yi koyi dashi kenan su tashi su nemi na kansu sai a daina yi musu kallon ƙasƙantattun mutane. "Wanda ya kaɗeka fa ko har yanzu ba'a sameshi ba?" Zeey ce tace "Daddy bakasan...." da sauri ya kalleta ya girgiza mata kai alamar a'a sai akai dace itama kallonshi take yi don haka tayi shiru ba tare data ƙarasa faɗar abinda tayi niyyar faɗa ba, shima Daddyn yaga lokacin daya girgiza mata kan sai ya ɗauke kanshi kamar bai gani ba. "A'a ba'a sameshi ba, ni kam ma tuni na yafe mishi don tuni na karɓi ƙaddarata a yadda tazo min don haka ko tunawa ma bana yi." Ya bawa Daddyn amsar a nutse don a ganinshi babu wani amfanin faɗa mishi Kabir ne ya kaɗeshi bayan Kabir ɗin yayi nadamar abinda ya aikata har ma yaje ya nemi gafararshi sannan bayan tashin hankalin da suke ciki baisan ya ƙara musu wani, balle ko badan komai ba ko dan darajar Zainab ai da matsayinta a gunshi ya kamata a bar maganar. Shi dai Kabir har ya sha jinin jikinshi yayi kif da ido yanajin yanda abin zaizo, sai yaji shiru hakan yasa ya kalli Baqeer wanda kalamansa yasa ya ji zuciyarshi ta karye, girma da darajar Baqeer suka karu a idanshi, kai kawai ya sunkuyar bai iya cewa komai ba. Sun daɗe tare da Daddyn bayan ya gama yi mishi duk wasu ƴan tambayoyi da ya dace yayi mishi sai yace ya bashi auren Zainab duk lokacin da ya shirya sai ya turo magabatan shi a tsayar da magana. Anan parlourn Daddy da Kabir suka fita suka basu wuri sai sannan ya ware ya kalli Zeey, sosai kwalliyarta tayi mishi kyau. Ɗage mata gira yayi yace "Amarya to ya? Kina ji dai Daddy yace ya bani ke ko yanzu na shirya nazo na ɗauke ki na mayar dake wurin Umma." Rufe bakinta tayi tana dariya tace "la'ila, yaushe aka yi hakan ina zaune ban ji ba? Ko kuwa kai kaji Salim?" Girgiza kanshi yayi yace "Ahh kaga mutum? To nima dai ban ji ba watakila kuma a mafarki yaji hakan yayi tunanin da gaske haka Daddy yace." Harararshi Baqeer yayi yace "To ɗan baƙin ciki, tukunna ma waya sa da kai daka wani tsomo bakin ka, magana ake ta tsakanin miji da mata idan ka shiga ma kai zaka ji kunya." Baki buɗe Salim yake kallon shi, ƙwafa yayi yace "gobe ma rana ce, ina zaune zaka zo ka sameni da wata buƙatar lokacin zaka san ni ka yiwa rashin mutunci." "Ni ba akwai inda kace zaka ba? Don Allah tashi ka tafi zamu tattauna da Sweetums ɗita." "Kai Ya Baqeer," Zeey tace tana dariyar faɗansu. "Ai ki rabu dashi Zainab, nima zan rama ne ai." Da sauri Baqeer yace "sai dai ka rame," tashi Salim yayi zai bar wurin Baqeer yace "idan kaje kace ina gaida Habi don nasan duk baƙin ran nan da kake yi akan yau na hanaka zuwa wurinta ne." Da mamakin yadda aka yi ya sani Salim yake kallondhi, ɗan taɓe baki Salim ɗin yayi yace "Wai kai ka ɗauka duk abinda kake yi ban sani ba ne, ƙyaleka nayi ka gama ɓoye-ɓoyenka don dole dai akwai ranar da zaka sanar mini tunda ba'a ɓoye za'a yi auren ba." Kasa magana Salim yayi, da ƙyar ya iya cewa "Hmm taya za'a yi nace ina sonta bayan abinda ƴar uwarta tayi maka." Katseshi Baqeer yayi da cewa "to miye a ciki don kana sonta, Habi ai ba Asiya bace besides that ni na daɗe da mantawa da wata Asiya a rayuwata bayan Allah yayi mini mafi kyakkyawan sakamako da my Sweetums to kuma me zai dame ni." Wani murmushin farin ciki Zeey ta saki jin abinda ya cewa Salim, duk da tasan Baqeer yana sonta amma bata ɗauka son da yake yi mata ya kai girman haka ba. Girgiza kanshi kawai yayi ya fita ba tare daya ƙara cewa komai ba, ba zai yiwu yaje wurin Habi a yanzu ba don tara ta wuce sai dai ko gobe kawai dai ya basu wuri ne don su tattauna shi yasa ya tashi ya fito. Salim na fita Zeey ta kalli Baqeer a shagwaɓe tace "Ya Baqeer," sosai yaji ƙiran sunanshi da tayi ya ratsa shi. Ƙasa-ƙasa kawai ya kalleta ya girgiza kai don bata san yadda duk tayi mishi magana da wannan muryar tasirin da take yi a jikinshi ba. Cigaba tayi da cewa "Me yasa ka hana na faɗawa Daddy Ya Kabir ne ya kaɗeka?"

Da mamaki yace "Ke yanzu idan aka ƙyaleki sai kije kina faɗa, abinda ya riga ya wuce ai ba'a dawo dashi baya don haka ko ba Daddy ba please kada kije kina faɗa don ni ko Umma ban taɓa faɗawa ga wanda ya buge ni ba ko Baba ma hasashe ne kawai yake yi amma baya da tabbacin Kabir ne ko bashi bane ni kuma ba faɗa mishi zan yi ba don haka please a rufe wannan maganar kada a ƙara dawo da ita don tuni na yafe mishi tun ma kafin nasan ɗan uwanki ne shi." Idanunta ne taji sun cika da ƙwalla, nauyin da ƙirjinta yayi tun ranar da tasan Kabir ne yayi sanadin gurguncewar Baqeer taji ya yaye tamkar an sauke mata wani gungumemen dutse da aka sa aka danne ƙirjinta dashi. Cikin rawar murya tace "Nagode Ya Baqeer." "No, thank you, for believing in me even when I didn't believe in myself, for loving me the way I am despite all my flaws. Thank you for being there for me when I needed it the most, I don't know what I would have done without you. I will forever be grateful for having you in my life. I love you so much Sweetums."

Bata san lokacin data buɗi baki tace "I love You too Ya Baqeer, fatana har kullum Allah ya bar mu tare cikin aminci har ƙarshen rayuwarmu." "Ameen Habibty," ya amsa mata yana jin wani irin shauƙin sonta yana ratsa duk wata jijiya dake harba jini zuwa zuciyarshi. Bai dan wane irin do yake yiwa Zainab ba abu ɗaya ya sani rayuwarshi is incomplete without her. Sun daɗe suna tattauna suna tsara yadda suke so bikin su ya kasance, ita tace tana son yin events shi kuma yace a'a dinner kawai zasu yi, ba zai hanata yin wasu events ɗin ba idan tana so amma shi dai dinner kawai zai je. Da ƙyar ta lallaɓa shi ya amince zai je mata kamu amma daga shi yace ba zai je komai ba to itan ma ta yarda babu jayayya tunda dai ta samu ya amince zai je kamu da dinner ɗin ai shikenan. Da ƙyar suka iya rabuwa shima sai da Kabir ya leƙo yace mata Daddy yace ta shiga gida haka nan sannan suka haƙura suka yi sallama ya tafi bayan ta rakashi harabar gidan inda motarshi take, sai da taga fitarsu daga cikin gidan sannan ta koma ciki tana jinta kamar tana yawo akan gajimare don shauƙi.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA*

*UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ƊARI*

{100} Mummy ce ta sauke ajiyar numfashi ta kalli yaron da bai wuce shekaru talatin ba da yake gabanta tace "Sultan ka tabbata kuɗin zai ninku?" Murmushi ya sakar mata yace "Haba Aunty ban san me yasa kike tantama ba a gabanki da kuma kanki kika tura 1m ko kwana biyu ba ayi ba aka turo miki 1.5m to imagine in kika saka 100m nawa za'a baki? 150m kenan." Lissafi tayi tunda ta saida gidaje uku tanada 200m to zata juyesu kawai in yaso in aka ninko mata kuɗin sai ta haɗa ta tafi Dubai ta saro manyan kaya ta buɗe ƙaton shago a Abuja, daga Inna har Nabila tunda basu zaɓe ta ba suje can suyi rayuwarsu itama zata yi tata, wahalarsu da tasha da ta isa. Katse mata zance yayi da cewa "Ba dai tunani kike yi ba? Ni yanzu kalleni? Ko ba gidanki na siya da kuɗin da na samu ba?" Murmushi tayi mishi tace "Na yarda fa, kazo muje bank sai na tura musu kuɗin ka zama shaida." Dariya yayi yace "Dadina dake kin san abinda kike so shi yasa bana so wannan garaɓasar ta wuceki, don daga mutane sun gano abinda ke faruwa to fa rubdugu za ayi daga nan kuma sai wanda Allah yaci da rabonshi, kin san turawa suna son suga suna taimakawa wanda yake nema." Kai ta jinjina alamar gamsuwa tace "Muje?" Miƙewa yayi yana yi mata tafi yace "Sai babbar mace ai ku irinku ba'a ja daku, ga kyau ga aji ga kuɗi." Ji tayi ya ƙara fasa mata kai, nan suka je bank babu wani jan lokaci ta tura kuɗin nan cas sannan suka yi sallama akan daga kudin sun shigo zata kirashi ta bashi la'ada. Hotel ɗin data kama ta wuce tana shiga ta kwanta akan gado tana sauke numfashi ta rasa me yasa kwanan nan sai tai ta yin haki ta tabbatar saboda bata wahala ne yanzu gashi kwanan nan sai fita take yi tana ta ƙoƙarin saida filayenta tun kafin Alhaji Sulaiman yazo mata da shirmen banza. *** Wata irin tsaftatacciyar soyayya ce ke ƙara shiga tsakanin Baqeer da Zeey, Baqeer yau yake so ya yiwa Umma magana akan sa ranarshi da Zee da kuma son zuwa Dambatta yaje ya gaida mahaifiyarta da ƴan uwanta, tunda yaji su a waje suna hira ya fito yana murmushi ganin yadda suke zaune suna hira gwanin sha'awa, Umma kana ganinta zaka san tana cikin kwanciyar hankali don har canzawa tayi ta murmure, ita kanta Dada dake mitar Umma ta koma ganin yadda ta ke murmurewa yasa ta ɗan yi shiru don ta fahimci lallai Umma zaman gidan Badaru haƙuri kawai take yi tasa a ranta gwara ta ɗan huta kaɗan sai ta sake maganar komawar, yana ƙarasowa ya gane maganar Maryam suke yi hakan yasa yace "Umma tazo ne?" Kallonshi tayi fuska a sake sosai tace "A'a magana muka yi a waya da safe, tace ta kira ka bata sameka ba wai Baban mijinta ne zai tashi akwai wani karamin gida da ya saya mishi zai koma can, kamar har aure ma suke son yi mishi." Dariya Dada tayi tace "A'a to ni dai kar ma yace yana sona don ina da zawara na ehe." Baqeer duk yadda yaso ya dake sai data sashi dariya yace "Ya taimaki kanshi, dama ni sam banga dalilin barin mahaifinshi a gidan da matarshi take ba, sam ba tsari." "Kai dai ba gashi kaje ka sa an koreshi ba, sai hankalinka ya kwanta, sai maganar aiki tace ya bada takardunta." Sosai abun ya yiwa Baqeer daɗi har hakan ya bayyana a fuskarshi yace "Umma kenan dai saura ni." Dada ta riƙe haba tace "Ahaf ni dama nasan ba iya jira zaka yi ba, to ni kam Baqeeru ko dai kawai nazo ni kadai na wakilceku a ɗaura ne." Hannu yasa ya shafi bayan kanshi yana cewa "ko zaku yiwa Kawu Halliru magana?" Kallon mamaki suka yi mishi, ganin wanda yake magana yayan Umma ne, fuskar ta ce ta canza ta gyara zama tace "Kana nufin ba Babanka bane da yan uwanshi zasu nema maka auren?" "Babana a ina? Ni bana buƙatar shi ma a wurin ɗaurin auren ya sha zamanshi." Sosai Umma ta tamke fuska tace "Ba kuwa zai yiwu ba sai dai in ba son auren kake yi ba, babu mai nema maka aure sai mahaifinka, duk laifin Badaru mahaifi mahaifi ne, sannan a iya sanina dashi duk fitinarshi a cikin gida take sai kuwa abokin faɗanshi mahaifin Zainab amma banda mu bana ji akwai wanda yake samun matsala dashi ba tare da dalili ba, shima mahaifin nata shi ya fara tsoksnoshi kawai dai Badaru rashin haƙuri ne da faɗa da yayi mishi yawa shi yasa aka fi ganin laifin shi," bata jira me zai ce ba ta cigaba "Dan haka dole kaje ka sanar dashi." Baqeer kasa magana yayi din zuciyarshi har wani zafi take yi yana ji shi gaskiya babu abinda zai haɗa shi da Badaru, Dada ce ta katse mishi tunani da cewa "Baqeer uba fa uba ne sannan ka duba kyautatawa da kaunar da ya nuna maka kafin ka tuna rashin kirkin da yayi maka." Har yanzu dai bai yi magana ba sannan kuma babu ma alamar zai yi, Umma ce tace "Sannan maganar Bashir ina ganin ka kira shi yazo ya fara aiki ko ya ya ne dai ƙaninka ne na jini in babu mu dole su kake dasu." Kai ya ɗaga kawai ba tare da yace komai ba, tasan halin Baqeer hakan yasa tace "Kana da numbershi?" "Eh Umma zan kira." Ga mamakinsa sai ji yayi tace "Kirashi." Shi abun ma dariya ya bashi kamar wani yaro? Sai dai ya ya iya haka nan ya kira wayar ba tayi ringing biyu ba ya ɗauka cike da zumuɗi yana gaishe shi, amsawa yayi sannan yace "Zan turo maka address na shagon mu sai kazo da yamma." Cike da jin daɗi yace to. Komawa ɗaki yayi sai yaji duk ranshi ma ya ɓaci kenan dole sai ya sanar da Badaru? Umma kuwa yana barin wurin ta kira Baffa wato yayan Badaru nan ta sanar dashi maganar auren Baqeer da kuma yarinyar Alhaji Sulaiman ce, shi kanshi Baffa sai da yayi mamaki don yasan ƴar tsamar dake tsakaninsu sai dai ya sanar da ita zai je da kanshi suyi magana. Nan yayi mata godiyar kayan abinci da Baqeer ya aiko musu, daɗi ne ya kamata kafin suyi sallama ta kashe wayar Dada na cewa "Kin yi daidai don Baqeer in aka biyeshi haka zasu yi ta zama da mahaifinshi kuma ita rayuwa ba'a ajiye iyaye. *** Baffa kuwa da rana yasa yaronshi ya kawoshi don ya girma ba sosai yake fita ba, ƙin shiga yayi yace Badaru ya zo suyi magana, ya dade yana yi mishi nasiha akan rayuwa da kuma haƙuri da ake da rayuwa sannan ya nuna mishi kuskuren fifita Baqeer fiye da ƴan uwanshi da yayi wanda gashi nan shine ya raba mishi kan iyalinshi da kuma babban abu na rashin yarda da ƙaddara da yayi, jikin Badaru ne yayi sanyi don kwanan nan sam rayuwar bata yi mishi daɗi jiya da yaje asibiti saboda ciwon kai da yake fama dashi aka gwada jininsa gani aka yi jininshi ya hau nan likita ya bashi magani ya dawo gida, ga kwankwasonshi tunda Kamalu ya hankaɗe shi har hau ciwo yake yi mishi lokaci-lokaci, sai da suka gama magana sannan ya sanar dashi maganar auren Baqeer da ƴar gidan Alhaji Sulaiman, a fusace Badaru ya miƙe yace "Kaga Yaya bafa zai yiwu ba kafa san meke tsakanina da mutumin nan don haka ba dai yarona ba." Kallon takaici Baffa yayi mishi yace "Kenan duk abinda nake sanar da kai baka ji ba? To ita Uwanin da kuke faɗa akanta ma ta daɗe da barin duniya kuma ku da kuke raye kuma ba dawamma zaku yi ba." Jikin Badaru ne yayi wani sanyi ya kalli Baffa kafin ya koma ya zauna, Baffa yace "In ma zaka gyara rayuwarka dats iyalanka ka gyara tun kafin wanin abun ya sameka ka rasa wanda zai tausaya maka a cikinsu." Haka ya tafi ya bar Badaru da dogon tunani, ji yayi hawaye ya ciko idonshi lallai ya tafka babban kuskure shi yasa sam rayuwarshi baya ganin daidai, yanzu ga Kamalu an nemeshi an rasa, shi dai yanzu ya fara tsoro Allah dai yasa ba wani abun bane ya sameshi. Bashir ne ya fito da alama fita zai yi, Badaru ya kalleshi yace "wurin Baqeer ɗin zaka?" Kallonshi yayi yana neman wayancewa, "in kaje kace ina son yin magana dashi," Badaru ya faɗa yana shiga cikI, ɗakin Fatima yaje ya zauna yana tunanin abubuwan daya aikata, lallai rayuwarshi gaba ɗaya bai tafi da ita akan hanya mai kyau ba. Haka ya fito sukuku yaje masallaci, agoggo kawai yake dubawa yana jiran isowar Baqeer, Abu yau ita ce da girki gashi gidan babu komai, ta rasa yadda za ayi tayi mishi magana saboda ko fuska bai bada ba, haka tayi tuwo tayi miyar kuka daga garin kuka sai ruwa da gishiri a ƙalla dai aci. Bashir yana shago yazo nan yace ya fahimci ya shagon yake in yaso sai yaga me zai fara koya, anan ne shi kuma ya sanar dashi kiran da Badaru yake yi mishi, kalaman Umma ya tuna wanda yasa yasan tabbas ba zai iya ƙin zuwa ba, da la'asar ya kira Tanimu suka je, tun a waje yaga mutum biyu da alama cikin fushi suke, ga Badaru a tsaye yana kallon su babu alamar ma yana da ƙarfin yin faɗa, Baqeer na ƙarasowa yaji yana cewa "Bani kuɗina haka kawai ba zai yiwu ka amshi kayan abinci da zummar bani kuɗi ba gashi har sati uku baka biya ba, nifa matsalata da matsiyata kenan basu san hallaci ba……" "Kai kuma a wani ɓangare za'a saka ka?" Baqeer yayi maganar yana ƙarasa turo kekenshi, kallonshi suka yi idanunshi na kan mutumin yace "Nawa ne kuɗin naka?" "Dubu biyu." Takaici ya kama Baqeer wai akan dubu biyu ake ciwa mahaifinshi zarafi, miƙa mishi dubu biyar yayi ya amsa kuma ko kunya babu ya fara godiya kafin ya juya. Badaru kallon Baqeer yayi yana tuno cin zarafin daya dinga yi mishi, ji yayi ƙwalla ta sake ciko idonshi ya kauda kai yace "Mu shiga ciki." Shima Baqeer bai musa ba suka yi ciki, Jamila kam tana ganinshi ta rikice tama manta ɗanta ne sai gani tayi ta rusuna tace "Sannu da zuwa ina wuni?" Mamaki ya kama Baqeer yace "Me kike yi hakan? Ɗanki ne fa ni." Sai kuma ta hau matsa ƙafa tana cewa "Wai na daɗe a zaune ne naji kafata tana amsawa." Abu ta fito ita ma tace "Sannu Baqeer, ya labarin Kamalu?" Kai ya girgiza kafin yace "Na dai basu kuɗin mutumin nan to amma shi ɗin ne har yanzu ba labari inda ya shiga In Sha Allahu zaku ji alkairi." Tace "Mun gode mun gode." Ɗakin Umma suka je ba komai a falon sai tabarma da pillow da bargo wanda bargon yake na Badaru kenan yana shiga ɗakin? Zama suka yi duk suka yi shiru kafin Baqeer ya gaisheshi ya amsa yana cewa "Kafarka fa har yanzu dai?" Kai ya jinjina kafin yace "Ina dai iya tsayawa akanta amma bana iya takata, da alama ba zata taku ba ko kuma ba yanzu ba." Kai ya ɗaga sannan yace "Ashe Zainab kake so?" "Eh!" Ya faɗa kawai, Badaru jiki a sanyaye yace "Shi mahaifinta ya amince?" "Eh!" Yanzun ma ya faɗa kawai Iska ya ɗan sauke kafin yace "Nine dai mafaɗaci kenan? Tunda har ka nemi izininshi amma ni ka kasa neman nawa." Hannayenshi Baqeer ya haɗe yace "A'a na ɗauka baka damu da yadda nake rayuwa bane." Kallonshi yayi sannan yasa hannu ya shafi cinyarshi yace "Ka yafe mini Baqeer lallai nayi kuskure kuma ban kyauta ba." Ba wani dogon nazari yace "Na yafe maka Allah ya yafe mana gaba ɗaya." Yana cewa ameen Abu na shigowa da kwanon abinci, amsa Baqeer yayi duk da ba ci zai yi ba, mamaki ne ya kamashi ganin wata irin miya wacce kana gani kasan ɗaci ma zata yi, ajiyewa yayi sannan yace "Baba ko muje a sayi kayan abinci?" Badaru ji yayi kamar yayi kuka lallai bai kyautawa kanshi ba, yanzu gashi nan gurgun dai shine gatanshi, kasa magana yayi sai Baqeer da yace "Kamar gwara muje tare saboda a siyo abinda ya dace." Haka suka fito Tanimu ya jasu a mota, a hanya Badaru ke tambayarshi me yake yi, ya sanar dashi, nan ya sake tambayarshi maganar auren da kuma sanda suke so aje gaisuwa, Baqeer yace susa rana zuwa wani satin sai suje. Haka suka siyo kayan abinci suka dawo, murna a wajen Abu da Jamila kuwa ba'a cewa komai, nan suka yi sallama da matan gidan suka fito, Badaru ne yace "Fatima fa? Yaushe zata dawo?" Shiru Baqeer yayi yana kallon Baban don bai san me zai ce ba. Ganin haka yasa yace "Shi kenan ta huta kafin ta dawo." Jikin Baqeer ne yayi sanyi ganin har ya gane me yake nufi, dama fa tun da haka suke da Babanshi kafin yayi magana yasan me zai ce saboda tsabar shaƙuwar da suka yi. **** Jikin Mummy ne ya fara rawa ganin sai kiran numbar Sultan take yi ba'a ɗauka ba, farcen hannunta ta fara ci hankalinta a mugun tashe, yanzu ya zata yi? Wa zata nema? Ina zata sa kanta? Har gidan data saida mishi taje wai ake ce mata shima ya saidawa wani gidan data tambayi nawa aka siya sai mai gidan yace 80m bayan ita a 30m ta sayar mishi, nan fa hankalinta ya tashi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull