Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 76

Baqeer complete - Chapter 76

Baqeer complete Chapter 76: Baqeer complete Chapter 76. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

3,053 words

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

Ayusher Ce Da Umm Asghar

*BAQEER* *NA*

*UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ƊARI DA ƊAYA*

{101}

Tun Mummy tana gwada ƙiran wayar Sultan tana ringing har ma ta daina ringing ɗin gaba ɗaya. Hankalin Mummy fa ya tashi ta rasa inda zata sa kanta taji daɗi, tsoron ta ɗaya kada dai ace yaron nan cutarta yayi ya karɓe mata kuɗaɗenta da dabara. Cikin kwana biyu gaba ɗaya ta futa daga hayyacinta don ko abinci bata iya sawa cikinta, a ranar da aka cika kwana biyu ne aka yi evicting ɗinta daga hotel room ɗin data kama saboda kuɗin data biya sun ƙare kuma bata da alamar cigaba da biya. Haka nan ba don taso ba ta tattare ya nata ya nata ta bar gidan ta koma gidan Inna. Inna na ganinta tace "ke kuma daga ina?" Kawai ta fashewa Inna da kuka cewa take yi "Na shiga uku Inna, don Allah ku nemo Sultan yazo ya bani kuɗaɗena wallahi na fasa yin kasuwancin." Ita dai Inna sai kallonta take yi har tayi ya isheta sannan Inna tace "idan na fahimce ki daidai wani kika damƙawa dukiyar ya gudu da ita," kasa amsawa Inna tayi don haka Inna ta cigaba da cewa "ai daidai kenan Halima, dama wanda yaƙi ji ai baya ƙi gani ba, nan babu yadda ban yi dake akan ki koma gidanki ki kula da mijinki da larura ta sameshi ba kika toshe kunnuwanki kika ƙi ji sai yanzu da kika haɗu da mutanen duniya suka yi miki hankali ne zaki zo ki sakani a gaba kina kuka. Ai baki ga komai ba tunda kika ce ke butulu ce mai manta alheri. Duk irin yadda mutumin nan ya riƙemu amana ya ɗauke dukkan wasu nauyin mu baki duba ba kika rasa lokacin da zaki butulce mishi sai da ƙaddarar rayuwa ta afka mishi, wato yanzu ya gama yi miki amfani to bari ki ƙara gaba ki barshi." Ita dai Mummy sai kuka take yi tana jin baƙin cikin damfararta da Sultan yayi, yanzu shikenan duk abinda take taƙama dashi take ganin ita ma yanzu ta kai wani matakin rayuwa data daɗe tana yiwa kanta fatan kaiwa ya rushe lokaci vuda kamar ba'a yi ba. Kallon tausayi Inna take yi mata har sai data tsagaita da kukan sannan Inna tace "Sawunki a likkafa ki tashi ki koma gidanki ki nemi yafiyar mijinki don baki da wani rufin asiri face ɗakin ki, da Allah yasa ma ba sakin ki yayi ba ke kika ga dama kika baro gidan don wallahi baza ki zauna min anan ba ke ba bazawara ba ke ba sakakkiya ba nayi ta faman ɗawainiyarki alhali kina da gidan mijinki." Share hawayenta tayi tace "yanzu Inna sai na koma bayan duk abinda nayi mishi?"

Kallon tsaf Inna tayi mata sai daga duk ta rame ta lalace kamar ba ita, cike da tausayawa halin da ta jefa kanta a ciki Inna tace "Komawa kuwa ta zame miki dole kije ki nemi gafarar maigidanki don dai kin san baki kyauta mishi ba bayan duk alherin da yayi miki a rayuwa, baki da wani gata face ɗakin ki Halima haka zaki yi haƙuri ki tashi ki koma. Maza shiga ciki kiyi wanka ki gyara jikinki sai kizo ko tafi kin ji, Allah yayi miki albarka." Cikin zuciyarta ta amsa Ameen ɗin ta tashi ta shiga ɗakin Inna don tayi wanka kamar yadda ta umurceta.

Babu kunya haka Mummy ta koma gidan tasa makulli ta buɗe ɗakinta ta shige, babu wanda yace mata ci kanki sai ma hidimarsu da suke yi, to itama kunyar abinda ta aikata yasa ta kasa sakewa a cikin gidan kullum tana ƙunshe a cikin ɗaki bata iya fitowa, gaba ɗaya a ɗarare take da mutanen gidan duk da ma babu wanda yake shiga sabgarta a cikin su.

***** Badaru da ƴan uwanshi sun je wajen Alhaji Suleiman Ƙaraye nemawa Baqeer auren Zainab, sosai Alhaji Suleiman da nashi ƴan uwan da suka zo daga Ƙaraye suka yi musu tarba da mutunci da girmamawa, abinda ya ƙara sanyayar da jikin Badaru. Cikin mutunci da mutuntawa duka gabatar da abinda ya kawo su, babu wani ja'in'ja ko ɓata lokaci aka tsayar da magana guda ɗaya har an yanke ranar auren watanni biyu masu zuwa nan gaba. Haka suka rabu ana raha ana wasa da dariya. Bayan sun fita Badaru ya ɗan dawo ya kalli Alhaji Sulaiman yace "Ya jikin naka?" Murmushi yai ya sake mika mai hannu yace "Allah ne ya haɗa mana yaran nan dan mu sassauta wa kan mu a lahira saboda wannan gabar batada amfani." Badaru ya jinjina kai nan ya bashi hakuri shima Alhaji Sulaiman ya bashi hakuri sannan ya fito. Sosai Baqeer yayi farin ciki da jin an bashi Zeey don ma ranar da aka saka ɗin tayi mishi tsawo a cewarshi shi bai ƙi ace daga zuwa neman auren an ɗaura ba. Itama Zeey ta samu kanta cikin farin ciki don abu ne da har ta cire rai da faruwarshi sai dai da yake komai yin Allah ne sai gashi cikin sauƙi iyayen nasu sun aminta da maganar gashi har an saka rana. Kowanne ɓangare shirin biki kawai suke yi, ga Baqeer dai gyare-gyare yake yiwa gidanshi duk da sabo ne ya siya amma akwai wuraren da yake so a canja musu fasali sai kuka painti da za'a yiwa duka gidan har part ɗin su Umma. Da kanshi ya haɗa lefenshi don a yanzu za'a iya cewa yafi su Maryam sanin manyan kaya saboda harkar ɗinki da yake yi, babu irin zanin da baya gani, ya dai ɗaukesu sun rakashi amma komai da kanshi ya zaɓa ai kuwa kaya yayi mata masu kyau da tsada sosai, bai dai yi kaya irin na ƙarya ba sai dai komai mai kyau ne da inganci. Akwatina ne set biyu kowanne mai uku da kit sai suttura guda talatin da biyar amma fa duka manya sai dangin su dogayen riguna, abaya, ƙananun kaya da sauransu. Duk wanda yaga kayan sai da ya yaba don kaya ne aka yi su babu ƙaranta babu kuma fariya a ciki. Ita kanta Umma data ga irin kayan da Baqeer yayi sai data yaba sosai ta kuma ƙara godewa Allah daya ɗaukaka ɗanta gashi yanzu kullum ƙara samun cigaba yake yi. Ba wasu mutane da yawa ne masu kai kayan ba don Baqeer yace baya son gayyar mutanen nan don haka aka tsara a gidansu daga Abu sai Jamila ne masu zuwa sai Hadiza a cikin ƴan uwanshi sai kuma daga cikin ƴan uwan Badaru mutum biyu sai matar wan Umma, su kenan mutum shida.

A ɓangarensu Zeey ma sai shiri suke yi, kuɗaɗe masu yawa Daddy ya tura mata a account ɗinta yace suje da Ummi su sayi duk wasu sayayyar kayan kitchen don furniture wani interior decorations company ya bawa kwangilar zuwa su shirya mata gidan. Babu abinda ake saka Mummy a ciki, to ina ma suka ganta tunda ta mayar da ɗaki wajen zamanta. Ranar da za'a kawo lefen ma haka ƴan uwan Ummi dana Daddy suka cika gidan sai hidima ake yi, anan nema wata ƙanwar Ummi tayi magana akan bata ga Mummy ba shine aka ce mata tana ɗaki. Tashi tayi ta tafi ɗakin Mummyn, daga bakin ƙofa ta tsaya tayi knocking. Tasowa Mummy tayi ta buɗe jikinta a sanyaye don tunda taji hayaniya ta cika gidan ta sakawa ƙofarta key don tsoron haɗuwa take yi da ƴan uwan Ummi saboda wulaƙancin da tayi ta musu a yanzu kuwa da suka dawo cikin rayuwar su Zeey bata san abinda zasu yi mata ba shi yasa ta dannawa ƙofarta key. Murmushi Aunty Badi ta sakar mata don ta lura da yadda take a ɗarare, kaucewa tayi ta bata hanya ta shiga cikin ɗakin. Zama tayi akan resting chair ita kuma Mummy ta zauna a bakin gadon. Gaisheta Aunty Badi tayi sai kuka tace "mun zo tun ɗazu naga ban ganki ba shine nake tambayar ina kike aka ce kina ɗaki, sai dai kuma hakan bai dace ba a matsayinki na uwa a wajen Zainab ace ana hidimarta sai dai wasu daga waje ne zasu tsaya akai ke da kike cikin gidan kamar ba kya nan shi yasa na shigo nace kome Zainab tayi maki kiyi haƙuri zaki yi yaran ne ka haifesu baka haifi halinsu ba don haka kiyi haƙuri ki fita a tari baƙin nan dake idan yaso ko meye ma daga baya sai kuyi wannan siririn ku ne na cikin gida bai kamata wasu daga waje su sani ba".

Godiya tayi mata saboda taji daɗin yadda ta mutunta ta duk da abubuwan da tayi musu a baya, tashi tayi ta shirya cikin wani rantsatsen lace ta fita suka gaisa da mutanen da suka zo sai dai duk da haka ta kasa sakin jikinta sai take ganin kamar kowa na wurin yasan abinda tayi. Har ƴan kawo kaya suka zo suka tafi da sha tara ta arziƙin da aka haɗa musu Mummy na cikin su don duk wani abu da za'a nema ita Aunty Badi take tambaya don haka tun tana ɗari-ɗari dasu har dai ta saki jikinta aka yi komai cikin mutunci, a lokacin ne kuma ta ƙuduri niyyar samun Daddy ta bashi haƙurin abinda tayi mishi don tun dawowarta bata yarda ya ganta ba, kunyar haɗa ido dashi take yi. Da yan uwan Ummi zasu tafi da kanta taje ta basu hakuri akan kuskuren raba su Zainab datai da sharrin data dinga musu tayi haka ne saboda tana tsoron kar yaran su barta, haka tai ta basu hakuri ganin sun saki jiki sun nuna mata ba komai yasa ta ƙara samun nustsuwa.

A daren ranar ta sami Dady a ɗakin shi bayan kowa ya tafi ya kwanta, durƙusawa tayi a gaban gadon shi tana kuka tana bashi haƙurin abinda tayi mishi, to shima bai wani ja da nisa ba yace ya yafe mata don a shekarun nan nashi yana buƙatar companionship Zainab aure zata yi haka ma Kabir dole yana buƙatar abokin zama don haka ya yafe mata suci gaba da haƙurin zama da juna, sannan in ya duba wani bangaren lefin nan ba nata bane ita kaɗai shi ma yanadashi a matsayinsa na namiji sam baiyi aikinsa ba, nan ta sanar dashi damfarar da aka mata, nan ma bai nuna jin haushinsa ba yace dama dukiyar ba hakkinsu bace gwara ma da aka kwashe. Mumy tai alkawari akan bazata sake yin wani abin da bai dace ba wanda yasa hankalin Dady kara kwanciya.

Zeey na zaune a parlour ita da Kabir, tsare-tsaren biki suke yi don fa Zeey ba wasu ƙawaye ne da ita ba, dama dai Nabila ce a yanzu kuwa ko son ganinta bata yi don haka Kabir ɗin dai shine abokinta. Ƙiran wayar Baqeer ne yasa ta ajiye littafin dake hannunta tana rubuta abubuwan da suke buƙata a hidinar bikin. Ɗauka tayi cikin yauƙi tace "Ya Baqeer." Daga can ɓangaren Baqeer sai da ya lumshe idonshi saboda yadda muryar ta ratsa shi. Gyaran murya yayi saboda yadda yaji ta shaƙe kamar wanda ya daɗe bai yi magana ba sannan yace "Ba kya jin magana Sweetums bayan na faɗa miki ɓarnar da wannan shagwaɓaɓɓiyar muryar taki ke yi min ki adanata a gefe sai mun je gidanmu sannan kiyi amma kin ƙi bari ko?" Fuskarta ta rufe cikin jin kunyar abinda yace kamar yana gabanta tace "Wallahi zan kashe wayata idan baza ka bar yi min irin wannan maganar ba." Shima cewa yayi " Nima ki bar yi min magana da wannan shagwaɓaɓɓiyar muryar taki bana so." Dariya tayi tace "to na bari, ya kake yasu Ummana da Dadata?" "Duk suna nan lafiya kullum Dada sai tayi zancen ki wai yanzu kin daina nemanta." Dariya kawai tayi tace "Dada kenan, zan je ne amma ba yanzu," murya ƙasa-ƙasa yace "sai yaushe zaki ko sai kin zama Mrs. Baqeer tukuna?" "Umm," kawai tace cikin jin kunya. Sai da suka gama soyayyarsu sannan yace mata ranar Saturday zasu je Ɗambatta da wa zata haɗa su da zai yi musu rakiya. Cewa tayi "tunda weekend ne sai na yiwa Mubashir magana yazo ya raka ku," Kabir na jin abinda tace ya girgiza mata kai, "kai zaka?" Ta tambayeshi, ɗaga kai yayi alamun amsawa sai ta cewa Baqeer "To kaji wai Ya Kabir ne zai raka ku sai kace ba jiyan nan ya dawo daga Ɗambattan ba, naga alama nema yake yi ya ƙwace mini Ummi don shagwaɓar da yake yi mata ko Inaya bata yi yayi ta bata kunya cikin mutane bayan ita tana yi mishi karar ƴan fari sam baya gani."

Harararta Kabir yayi jin abinda tace, bata miye mishi ba ta cigaba da yin wayarta da Baqeer sai ma tashi da tayi zata shiga ɗakinta sai ga Mummy ta fito daga ɗakin Daddy, hannunta da karamar roba da towel da alama dundumamai gun ciwon tai, ɗauke kanta Zeey tayi ta shige ɗakinta tana ƙunƙuni. "Ke kuma ke da wa?" Baqeer ya tambayeta, tsaki tayi tace "Mummyn nan mana, ni wallahi ko ganinta bana son yi." Girgiza kanshi yayi yace "kada ki kasance daga cikin butulallun mutane mana Zainab, matar nan duk da abinda tayi muku nasan ba za'a rasa alkhairin da tayi muku ba tsawon zamanku da ita to ko don haka baki ga ya dace ki yafe mata ba, tayi laifi sannan tayi nadamar abinda tayi ke da bakin ki kike faɗa mini baki da fargabar tafiya ki bar Daddy yanzu saboda tana tare dashi tana kuma kula dashi to ai ko don wannan yaci ace an yafe mata ki manta da abinda ya faru tunda Allah yasa yanzu kuna tare da Ummi komai ya wuce don ina ganin wannan ne mafi girman laifin da tayi muku raba ku da mahaifiyarku da tayi ko?" Kamar bata so tace "umm," yace "to kin gani, don Allah ayi baƙuri a yafe mata, abinda ma kwana kaɗan ya rage miki ki bar mata gidan." Haka dai yayi ta lallashinta yana yi mata nasiha har taji abranta zata iya yafewa Mummy abinda tayi musu. Shiru tai ta kwanta akan gado tabbas duk muguntar da Mumy ta mata ta kula dasu, ta basu kulawar da ko mahaifiyarsu basuji suna nema ba. *****

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

*BAQEER* *NA*

*UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ƊARI DA BIYU*

{102}

Ranar asabar da wuri suka ɗauki hanyar Ɗambatta, Salim ke tuƙin motar sai Kabir a kusa dashi Baqeer kuma yana baya. Suna tafe suna hirarsu cikin raha da nishaɗi kamar waɗanda suka daɗe da sanin juna tun ma ba Salim da Kabir ba abota suke yi sosai yanzu. Ƙarfe sha ɗaya na safe a ƙofar gidan Ummi tayi musu, da yake Kabir ya sanarwa da Ummi batun zuwansu yasa Ummi ta tashi da hidimar tarar su. Tun daga bakin gate Mubashir da yazo gida weekend ya taro su, shi yayi musu jagora zuwa parlourn Babansu kafin yaje ya sanar da zuwan nasu, shi kuwa Kabir tuni ya shige cikin gida wajen Ummi don ƴan kwana biyun nan da bai ganta ba kewarta yake yi duk da ma kullum ne sai ya kirata a waya sun daɗe suna hira yana jaddada neman gafarar wofantar da ita da suka yi tun ma bashi da ya kasance babba ba.

Tare Ummi da Daadan su Inaya suka shiga parlourn, gaba ɗaya sai suka ƙara nutsuwa Baqeer dake zaune akan wheelchair ma ƙoƙarin zamowa ƙasa yake yi don haka nan ya samu kanshi da jin matsananciyar kunyar Ummin. Daada ne ya hanashi sauka yace mishi babu komai yayi zamanshi ai sun san yana da larura. Cike da girmamawa suka gaishe su, Ummi dai a kaikaice take kallon Baqeer tana tasbihi ga Allah cikin ranta tana yabawa da zaɓin ƴarta, duk da taji wani iri lokacin da Zainab tace mata ai gurgu ne wanda take so don babu uwar da zata so ace yau ƴarta na auren gurgu amma data ganshi yanzu sai taji wata irin nutsuwa da zaɓin ƴar tata don tasan rashin ƙafar ce kawai tayi mishi cikas bayan haka kyakkyawa kuma nutsatsen mutum ne wanda tsantsar kamalar shi bata ɓuya ba. Tashi Ummi tayi ta basu wuri bayan sun gaisa sai Daada ne ya zauna yana yi musu ƴan tambayoyi irin wanda duk uba na ƙwarai yake yiwa manemin auren ƴarshi. Mubashir da Inaya ne suka yi ta shigar musu da kayan abincin da Ummi ta tanadar musu, tashi Daada yayi ya basu wuri don yasan ba zasu sake su ci abincin a gabanshi ba. Basu bar gidan Ummi ba sai da suka yi sallar azahar bayan sun ajiye musu tsarabar drinks da ruwa da suka ciko boot ɗin motar su dashi. Daga nan gidajen ƴan uwan Ummi aka raka su duk inda suka je aka nuna Baqeer a matsayin wanda Zainab zata aura sai anyi mamakin ganin shi gurgu sai dai kuma duk wanda ya kalleshi sai ya ƙara don sun san Zeey ɗin fa ta iya zaɓe rashin ƙafar ne kawai yayi mishi cikas baya ga haka baya da wata makusa a jikin shi. Duk gidan da suka je sai Baqeer yayi musu kyautar kuɗaɗe abinda ya ƙara toshe bakin ƴan ƙananan tsegunguman da suka fara tashi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull