Baqeer complete - Chapter 77
Baqeer complete Chapter 77: Baqeer complete Chapter 77. ***** A hankali Mummy ta turo kofar ɗakin Zainab hannunta ɗauke da babbar leda, bayanta wata mata…
2,141 words
***** A hankali Mummy ta turo kofar ɗakin Zainab hannunta ɗauke da babbar leda, bayanta wata mata ce hakan yasa Zainab kallon Mumy ɗin, jiki a sanyaye tace "Zainab mai gyaran jiki ce, zata dinga zuwa daga nan har biki tana gyara ki." Kallon Mummy tayi ta ɗaga kai alamar to don tasan Mummy na sonta har cikin ranta da alama buri ne yayi mata yawa yasa take tunanin basu ne a gabanta ba. Yawun bakinta ta haɗiya har sai da Mummy ta kai bakin ƙofa zata fita sannan tace "An jima zan zo sai muyi maganar shirye-shirye sannan kice Nabila tazo bai kamata ayi biki tana can ba." Ƙwalla ce ta cikowa Mummy a ido, kai ta jinjina mata don ta kasa magana, da sauri ta juya ta shiga ɗakin Daddy rungumeshi tayi ta fashe da kuka tana ƙanƙame dashi, bayanta kawai yake shafawa don ya kula abubuwa ne suka yi mata yawa, ɗagowa tayi jiki a sanyaye tace "Senate ku yafe min don Allah wallahi na sani da sanina na ɓoye Nabila don kar ku gujeni sannan na ɓoye neman da yan uwan mahaifiyarsu ke musu saboda ina tsoron rasasu, amma wallahi har cikin raina ina sonsu, nayi kuskure ku yafe min, duk na ɗauka mugunta nake yi musu amma wallahi har cikin raina a matsayin ƴaƴana na ɗauke su don Allah ku yafe min," ta ƙarasa maganar tana kuka, shafa kanta yayi yace "Halima ya isa haka nan, son zuciya ba abinda bays janyowa na sani tsakani da Allah kike sonsu don akwai abubuwa da dama da kika yi wanda uwa ce kaɗai zata iya yiwa ɗanta." Kallonshi tayi tace "Maganar Kabir dana ɓoye akan Baqeer? Senate nayi laifi ka yafe min wallahi lokacin ni na bashi shawara akan mu ɓoye maka kada mu bari ka sani, ka yafe min, komai nice na tsarashi." Shiru yayi yana kallonta haka kawai yaji zuciyarshi na tsoron tambayar abinda ke faruwa, don tabbas ko bata ƙarasa ba ƙwaƙwalwarshi ta kai mishi abinda ke faruwa, fuskar Baqeer ce ta dawo mishi sanda ya ke girgizawa Zainab kai akan kar tayi magana ko wannan ya isa ya tabbatar da inda kalaman Mummy suka nufa. Wannan dalilin yasa yaji son Baqeer ya ƙaru mishi tare da tabbatarwa da lallai zai kular mishi da Zainab har bayan ranshi. *** Ana jibi ɗaurin aure Badaru yazo gidan Dada, don Umma tace baza su koma sabon gidan Baqeer ba gwara yasa matarshi su zauna ita zata koma wurin mijinta in yaso ɓangarensu ya barshi sanda suka je sa sauka su ko kwana ɗaya ko biyu tunda duk gari ɗaya ne, bai musa ba don ya fahimci Umma duk rigimar Badaru da alama tafi son zama dashi. Dada ta daɗe a zaune tana yi mishi nasiha tare da nuna mishi kuskuren abubuwan da yake aikatawa, ya kuma amshi laifinshi ya kuma bada haƙuri, bayan nan ta tashi ta bar musu falon shi da Umma. Shiru suka yi kafin yace "Zaki zo mu koma? Kinga ai ba'a yi biki uwar ango tana wani wurin ba." Kai ta jinjina tace "Shi kenan sai mu tafi nima nasan bai kamata ba." Kallon ta yayi cike da tausayinta yace "Fatima ina ga bayan biki ki koma gidan Baqeer da zama ni sai na dinga zuwa ran kwananki." Da sauri tace "A'a gwara mu zauna a gidan mu suma mu barsu suyi rayuwarsu," ta ƙarasa maganar tana kauda kai, murmushi yayi don ya fahimci me take son ce mishi nan ya juyo yace "Na sani ba zaki yarda dani ba don tunda hali nane ba fasawa zan yi ba, ni nasan ba komawa kike son yi ba burinki dai kiga kin bar Baqeer yayi rayuwarshi don kin san in dai ina zuwa zan iya komawa halina nada." Shiru tayi don maganar gaskiyar kenan ba wai bata yarda dashi bane amma fa hausawa sun ce mai hali baya fasa halinsa shi yasa ta kasa yarda dashi. Haka suka fito ya kwaso mata kaya da yake Hadiza tazo suka wuce tare anan zata kwana ita da yaranta, Maryam kuma tace da safe zata ƙaraso. **** Bahaushe yace rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya. A ranar asabar sha bakwai ga watan April aka ɗaura auren Muhammad Baqeer Badaru da Zainab Suleiman Ƙaraye akan sadaki naira dubu ɗari biyu. Bakin Baqeer a wannan ranar ya kasa rufuwa saboda tsananin farin cikin daya tsinci kanshi a ciki, haka yayi ta gaisawa da waɗanda suka zo don taya shi murnar auren rabin ran nashi da yayi. Kallon Salim yayi yace "Abokina kaga fa mu yanzu mun bar sahun gauraye sai kusan inda kuka nufa." Dariya yayi yace "Wai ya labarin Siddarth har yanzu ba'a ganshi ba?" Ajiyar zuciya yayi yace "Wa ke nan?" Haɓarshi Salin ya taɓa yana dariya yace "Kamalu mana kai dai ka gode Allah baya kusa aka yi bikin da ban san me zai faru ba." Cike da rashin fahimta Baqeer ya kalleshi sai kuma yace "Yana prison next week za'a sallameshi bana son faɗawa kowa ne shi yasa nayi shiru, satan wayoyi suka haɗa gang suna yi to gaba ɗayansu an kamasu aka kullesu ance sai sunyi zaman gyaran hali na wasu watanni wanda wani satin zai ƙare za'a sakesu." Kai Salim ya girgiza yace "Gaskiya ba'a yiwa Siddarth adalci ba Roshni tana nan tayi aure za'a sha romon soyayya yana amsa romon yunwa." Baqeer ganin bai gane me yake nufi ba yasa ya girgiza kai. Gidan su Zainab suka wuce don za ayi hotuna da yamma kuma za ayi dinner. Tunda suka iso yake ɗan kallon gefe da gefe yana neman matarshi, Nabila ce ta fito ta gaishesu tace tana zuwa. Sanye take da black lace anyi kwalliyar da golden shi kuma yana sanye da white shadda anyi kwalliya da golden kallon juna suka yi a hankali suka sakar ma juna murmushi, Inaya ce tace "Ya Baqeer baka ganni ba?" Kallonta yayi yana dariya yace "Little Zee kinyi kyau." Haka suka sha hotuna Baqeer yana ji kamar ya sungumi matarshi su tafi ai gaskiya da yana da ƙafa tabbas a mota zai sata ya tuƙa sai dai kowa ya haƙura da dinner ɗin. Habi anci kwalliya za'a dinner, don Salim har gida ya kawo mata kati uku yace ta bawa wasu in tana so, Asiya ce data zo gidan ta kalleta duk ta rame ta canza sai ƙaton ciki wanda da alama an kusa haifeshi, Habi sai sha'awa take bata don kayan sawarta yanzu kana gani kasan masu tsada ne, yawun bakinta ta haɗiya tace "Habi nima da ina da pass da na rakaki bikin ko banza kaci kasha." Kallonta tayi tace "In zaki ki shirya muje ina da pass." Da sauri ta kalleta tace "Da gaske? Bikin wanene?" Kai Habi ta girgiza tace "Ke dai me ya dameki in zaki kawai ki shirya." Daɗi ne ya kama Asiya atamfar jikinta ta bari kawai tayi ɗan gyare-gyare a fuskarta suka fito, mota ya turo ɗaya daga cikin yaran shagonsu na ɗinki yazo ya ɗauke su, sai murna take akan ko banza zata je taci abinci mai daɗi a hanya ta kira Bello sai data kira sau hudu ya ɗauka ta sanar dashi zata biki to kawai yace ya kashe, sam zaman aurensu baya yi mishi daɗi a dole yake zaune da ita, balle yanzu da zata haihu yana ji zamanta dashi kamar ya zama dole. Sun isa ganin Salim yasa Asiya tayi saurin samun wuri ta labe tana mamakin me ya kawo Salim, gani tayi Habi ta bishi suna hira suna dariya, jikinta ne yayi sanyi don da alama shine saurayin, wanda ta hango akan kujera ne yasa ta murza idanunta tabbas Baqeer ta gani, mamaki ya kamata, ya canza ya canza sosai ya ƙara kyau da fresh, ga wata haɗaɗɗiyar mace a kusa dashi, hawaye ne suka zubo mata, ji tayi baza ta iya zama ba ta fito ta tari adaidaita ta koma gida, sai data isa ma ta tuna ba kuɗin da zata bada, sai ta tuna da kuɗin da Habi ta bata nan ta biya ta shiga ciki. Baqeer a wurin dinner ya ɗan matso yace "Sweetums yaushe za'a gama ne? Nifa na gaji so nake mu wuce muhallin mu." Harararshi tayi tace "Bari na faɗawa Ummi saƙonka." Ido ya zaro yace "Bar shi kawai I can manage." Haka aka gama taro, ganin Habi yasa Baqeer ya sanar da Zee gafa Habin Salim, Kabir a wurin dinner yaga wata junior ɗin su Zainab wacce a take yaji ta kwanta mishi don haka bai sanya ba ya gabatar da kanshi inda yayi sa'a a take ta amsa tayin soyayyarshi, Nabila dake zaune akan kujera tana ganin duk motsinshi, tana kallo sanda yaje yana gabatar da kanshi wurin yarinyar, share ƙwallarta tayi don tasan duk son da take yiwa Kabir ba zai taɓa zama nata ba ta riga ta ɓata rawarta da tsalle, ji tayi zaman wurin ya isheta ganin yadda suke magana kamar sun daɗe da sanin juna, haka itama ta bar wajen tana share hawaye. An kai amarya kai tsaye Baqeer yace su Salim su tafi daga shi har Kabir wai sun gaji bacci zasu yi. Ɗaki ya shigo Zee tana jiran taji yan siyan baki sai taji shiru, kanta ta ɗago kaɗan tana son ganin me ke faruwa cikin ɗakin hannunta taji an kamo an ɗaurata akan cinya, kallonshi tayi tare da yin murmushi ta ɗan daki ƙirjinshi kaɗan tace "Allah ka lalace Ya Baqeer." Kafaɗa ya ɗaga yace "Wai matsalar ma baki ga komai ba tukun." Kallon shi tayi tace "Kamar...." Kawai sai jin bakinshi tayi cikin nata, wani irin yanayi ta shiga wanda bata taɓa ji ba wani abu ne yake tsirga mata har tsakiyar kanta, shi kanshi ji yayi zuciyarshi tana wani irin bugawa da sauri, sun fi minti biyar suna sumbatar juna kafin su haɗa goshinsu guri ɗaya, ya haɗiyi yawun bakinshi yace "Muyi sallah kici abinci ko?" Kai ta ɗaga don ta kasa magana sam, tana neman miƙewa ya maidata kan cinyarshi sannan ya fara tafiya da keken hanyar banɗaki har suka shiga sannan yace "Take responsibility." Tace "Da nayi me kenan?" Kunnenta ya matso yace "Na birkita min tunani da kika yi, wannan gurgun gaskiya ba zai yarda ba." Murmushi tayi tace "Allah kai ko?" Tayi maganar cikin shagwaba, idanu ya runtse yace "Sweetums please ayi mini haƙuri da shagwaɓar nan muyi sallah kici abinci tukun." Haka suka yi sallah ta buɗe kaza zata ci ya buɗe baki cike da kunya ta kalleshi. Gira ya ɗaga mata ta saka mishi a baki, ci tayi ta ɗauko zata kara mishi ya girgiza mata kai alamar a'a tana kaiwa bakinta ko sashi a ciki bata yi ba ya haɗe bakunansu biyu ya ɗauki naman daga cikin bakinta, ita kam Baqeer wai haka yake dama? Ko kuwa yanzu ne ya koyi wannan abubuwan? Don ita gaba ɗaya ya gama birkitata tun kafin ma ayi nisa...... Sai da suka ƙoshi sannan ya sake yi musu addu'a suka shafa. Kallonta yayi yace "Na gaji, mu kwanta?" Da sauri tace "Bari na shiga toilet ina zuwa." Bata jira amsarshi ba tayi toilet tana sauke ajiyar zuciya, turaren da Umminta ta bata ta ɗauko ta shafa a cinyoyinta sannan ta kalli madubi tana sauke ajiyar zuciya kafin ta fito, tsayawa tayi kawai tana kallonshi ganin ya cire rigar shaddar ya bar wando da vest, kallonta yayi yace "Ƙaraso mana." Bata tanka ba ta tsaya tana kallonshi, murmushi yayi yace "Bacci zamu yi ni ba abinda zan yi miki matsoraciya kawai." Jin haka yasa ta ƙaraso tana cewa "Ni dai ba tsoro nake ba kawai kai ɗin ne ke bani mamaki." Kwanciya suka yi akan gado rigingine ya sauke ajiyar zuciya tare da janyota ya ɗaura kanta saman kafaɗarshi yace "Sweeetums thank you for always been there for me." Ɗago da fuskarta tayi ta kalleshi, idanuwansu na hade da juna yace "Ni me za'a ce min?" Murmushi tayi tana neman maida kanta ƙirjinshi yasa hannu ya ɗago haɓarta kallon juna suka sake yi a hankali ya kai bakinshi cikin nata, salo yake yi mata wanda ya birkita tunaninta itama tana iyakacin ƙoƙarin ta wajen maida mishi da martani....
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar
*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce
*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari
*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500
VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500 VIP 1000
ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130
KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 +234 903 056 9336
*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*
*BAQEER* *NA*
*UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ƊARI DA UKU*
Last Page❤️ {103}