Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 78

Baqeer complete - Chapter 78

Baqeer complete Chapter 78: Baqeer complete Chapter 78. Kuncinta yaja yana kallonta, cike da jin kunya ta shige jikinshi a hankali ya kai bakinshi saitin…

3,052 words

Kuncinta yaja yana kallonta, cike da jin kunya ta shige jikinshi a hankali ya kai bakinshi saitin kunnenta yace "Madam a sake yi mini kiss ɗin nan please sai naga duk na zama alawar lollipop." Hannu tasa ta maƙalƙale shi ta sake shigewa jikinshi tace "Allah kai dai ba zaka bari ba ko?" "Ina fa zan bari gaba ɗaya an tashi kaina?" Yanayin maganar shi ne ya canza yace "Thank you Sweetums for marrying this disab....." hannu tasa ta rufe mishi bakinshi wani kallo take yi mishi mai cike da so da ƙauna, wani abu ne yaji ya tsirga mishi a hankali ya fito da harshen shi ya fara wasa dashi a saman tafin hannun data rufe bakin nashi dashi, wani yanayi ta fara ji wanda ya sata ƙoƙarin zare hannun, a hankali ya sako hannunshi ya riƙe ƙugunta wanda hakan ya hanata tashi daga kanshi, idanunta lumshe tana jin wani abu na ratsata, miƙewa yayi dsga kwanciyar da yake zuwa zama har yanzu hannunshi na riƙe da ita hakan yasa ta kasance a saman cinyarshi fuskarsu na fuskantar juna sai dai idanuwanta na ƙasa, juyawa tayi tana san barin kan cinyar tashi, hannu yasa ya zagayo dasu saman dukiyar fulanin ta a hankali yace "Please karki matsa mijin naki ba zai iya gudu ya kamoki ba!" Yayi maganar cikin dashashiyar murya, waigowa tayi saboda yanayin da take ji yasa duk jikinta ya mutu, cikin wani yanayi yana wasa da hannunshi yace "Kiss me please!" Yawun bakinta ta haɗiya sannan ta matsa tare da kai bakinta saman leɓenshi, wani irin sumbata yake mata wanda yake nuna tsantsar buƙatuwar shi gareta, yana sumbatarta ya sauke rigar da ke jikinta, wani irin numfashi yake fitarwa a hankali ya saukar da bakinshi saman dukiyar fulaninta, nan ta fara sauke wani irin nishi don wani yanayi ta tsinci kanta a ciki mai wuyar fassarawa, kwantar da ita yayi ya mirgina samanta yana sarrafata cikin yanayin da shi kanshi yasan bata cikin hayyacinta, ganin yadda ɗakin ya ɗauki nishin junansu yasa Umm Asghar da Ayusher lallaɓawa suka bar ɗakin wannan abu sirrinsu ne... Kunya ce ta kamata hakan yasa tayi saurin jan bargo ta rufe kanta, Baqeer dake kwance kusa da ita har yanzu yana maida numfashi ya sa kanshi kan wuyanta wanda yasa ta lumshe ido ya sumbata sannan ya rungumota, shigewa jikinshi tayi yasa hannu ya shafi saman kanta, so take ta miƙe ta shiga wanka amma kunya duk ta isheta, wash yace yana ɗan matse ido, hankali a tashe ta juyo tace "Menene? Ko ƙafarka ce?" Ta tambaya ganin abinda ya faru tasan zai iya yiwuwa ƙafar tayi ciwo, kai ya girgiza yana runtse ido, cike da kulawa tace "Menene don Allah?" Hannu yasa ya riƙo gefe da gefe na fuskarta kallonshi tayi yace "Sweetums kin wahalar dani." Baki ta buɗe ganin gata nan da ƙyar take juyawa amma wai ita ta wahalar dashi bayan shi ya wahalar da ita, gira ya ɗaga mata yace "Ya? Ba haka bane?" Kai ta kauda tana murmushi, rungumota yayi yace "Murmushin me kika yi?" Har yanzu tana murmushi tace "Hango rayuwata da kai nake yi da alama komai sai an tsokaneni za'aji daɗi." Ajiyar zuciya yayi yana wani canza yanayin fuska yace "Matsalar kenan, yanzu ya zamu yi? Gashi ni babban burina naga na tsokane ki." Bakinshi ya kai ya sumbace ta yace "one year da nayi ina jiranki duk sai na fanshe barina da aka yi." Ya zata yi da Ya Baqeer? Ita sam bata san yaushe ya lalace haka ba, kamar yasan me take cewa sai ji tayi yace "Ni kaina ban sani ba, shi yasa you have to take responsibility don ke ce nan kika maidani haka." A tare suka saki murmushi yau dai kunyarshi take amma tabbas zata fanshe abinda yake yi mata, kasancewar ƙafarshi ba iya takata zai yi ba dole ita ta sakko da ƙyar don ma ya tafi da ita a hankali bata sha wuya sosai ba, bargon ta yaye ta rufe jikinta dashi, ta barshi anan ta shiga toilet, yana kallon yanayin tafiyarta wanda hakan yasa yaji tausayinta ya kamashi, saukowa yayi ya hau wheelchair ɗin shi, ya kalli bedsheets ɗin da suka ɓata, yaye shi yayi don har ga Allah bai taɓa tantama dama akan Zeey ba, nan yabi bayanta zuwa banɗakin, sam bata kula dashi ba saboda ƙarar ruwan da ke taruwa cikin bathtub, in ta tuna abinda ya faru ɗazu sai tayi murmushi, hannunta taji an janyo an juyo da ita, kallonshi tayi a kunyace tace "Da ka bari na gama." Kai ya girgiza alamar a'a yace "bayan wahalar dake da nayi ni ya kamata nayi wannan." Hannu yasa a cikin ruwan har sai da ya haɗu ya mata alama da ta shiga, kai ta girgiza tace "Ka fara shiga in ka gama zan zo." Ido ya ƙifta ya nuna mata bath ɗin da idonshi, ita kunya take duk da sun zama ɗaya amma bata shirya wanka a gabanshi tun yanzu ba, baki ya buɗe yace "Ba dai har kin fara son round 2 ba?" Ido ta zaro da sauri tace "Allah ni ka daina yi mini haka." Shima maimaita abinda tace yayi kafin ya ɗora "to in ba haka bane shiga." Shiga tayi tana runtse ido saboda zafin ruwan da take ji yana ratsata, turo keken shi yayi daf da ita ya janyo shower gel yasa a loofah sannan ya kai hannu jikinta, haka ya dinga romancing ɗinta da kumfar wani irin yana yi take ji wanda bazata iya fassarawa ba, sun daɗe a toilet ɗin bayan ta gama tana neman fita sai cewa yayi wai ƙafarshi in ya shiga bath ba zai iya fitowa da kanshi ba, haka ya shigo yasa ta wanke shi sannan suka buɗe rariyar ruwan ya fita shower ɗin ta ciro ta miƙa mishi akan yayi wankan tsarki nan yace ita zata yi mishi ita dai haka tayi cike da jin kunya tana yi yana kissing ɗinta kafin nan suka fito. **** Wata irin tsaftatacciyar soyayya ce ke gudana tsakanin Zee da Baqeer don dama honeymoon ɗin sati uku ya ɗauka da wata ma yace Salim yace kai Malam sati biyu fa ake yi, yace to shi uku zai yi. Yau tana kitchen tana haɗa breakfast, tunani take yi da ace ada tayi aure lallai da zaman gidan Baqeer bai mata daɗi ba tunda lokacin babu abinda ta iya, potato omelette tayi da stir fry na beef, daga cikin ɗaki taji yana kiranta "Sweetums!" Yadda ya ke kiran ne yasa ta nufi ɗakin da sauri bayan ta rage gas ɗin, a zaune ta ganshi akan gado yana ganinta ya ɗaga mata gira yace "Ba morning breakfast?" "Yanzu nake yi wai na ɗauka bacci mafa kake yi?" Turo kekenshi yayi yazo inda take yace "Bafa wannan ba breakfast ɗin dana fi so." Dariya ta ɗan yi tace "Ka fito ga Baba nan yazo ku gaisa." Ido ya zaro yace "Da safen nan?" Tace "Eh shi yasa nake ta sauri nama ɗauka kaji zuwan nashi ne." Yanayinshi ne ya canza, tayi mishi gwalo, ƙwafa yayi yace "Ai dai gobe ba zuwa zai yi ba." Tace "Ina ka sani kila ma kaga Kabir ko Bashir." Gira ya haɗe yace "Matsalar fa zama kusa da unguwar dangi kenan, gaskiya we need to move." Tare suka fito ga mamakinshi ba kowa a falon, kallonta yayi ta kwashe da dariya tace "Baba ina kwana?" Fuska ya tamke sosai ta sake yi mishi gwalo tace "1-0." Kai ya jinjina yace "Kai? Lallai dole na fanshe," yayi maganar yana neman kamota, da gudu tayi kitchen yabi bayanta da kallo yana murmushi. ** Kamalu yau za'a sakeshi don haka ana yi mishi waya yace zai zo da kanshi, yafi son yaje da kanshi ya ɗauke shi ya kawoshi gidanshi yayi mishi faɗa sosai kafin ya maidashi gida, haka ya cewa Zainab zai fita zai dawo da baƙo, kafin ya fita shi ya ɗan tayata yanke-yanke sannan ya shirya Tanimu yazo suka fita. Kamalu duk ya canza ya rame fuskar nan duk ta motse saboda wahalar gidan yari, ganin Baqeer yasa ya fara sum sum da kai, nan Baqeer yace ya shiga mota su tafi, a mota basu yi magana ba don baya son ko Tanimu yaji abinda ke faruwa, Zee tana ɗaki sanda suka iso, tayi kwalliya cikin lace wanda aka yi mata ɗinkin buba, tayi kyau sosai bata yi wani kwalliya ba sai ɗan kwalli data sa a idonta ɗaurin Zarah Buhari tayi, tunda Kamalu ya shigo yake bin gidan da kallo, wai gidan Baqeer? Ina ma shine? Haka suka shiga gashi an zubawa Zee tsadaddun furnitures wanda suka ƙara gyara gidan, fitowa tayi bayan Baqeer ya kirata, idanun Kamalu ne suka sauka kan hotonsu dake manne a bangon falon idanunshi ne ko kuwa mai kama da ita ne yake gani? Matar da yake ta mafarkinta a gidan yari har duka yaci akanta ranar da ya fara mafarkin aurensu ashe wani gardi ne a kusa dashi ya fara ƙoƙarin manna mishi kiss ai kuwa ya zabga mishi mari ya rufeshi da duka, inaa mafarki yake yi, kalaman Baqeer ne ya katseshi jin yace "Sweetums da kanki? Ai kawai kice Habiby zo ka ɗauki tray ɗin nan." Kamalu ne ya juya idanunshi suka sauka akan Roshini, ƙamewa yayi a zaune don ji yayi kamar an zare komai na jikinshi har tayi mishi magana ma bai ji ba sai da Baqeer yace "Kamalu?" Ido ya ƙifta ya haɗiyi yawu kawai ya miƙe da sauri yace "Baqeer bari naje gida." Kallonshi yayi yace "Menene?" Zainab da yake ta san me yake sai ji yayi tace "Ka zauna mana ai gidan wanka ne." Kallonta yayi yana ji kamar ya saki kuka, fitowa yayi cikin sauri don sam bai kula ma takalmi daban daban ya saka ba ɗaya nashi ɗaya na Baqeer haka ya fito ya nufi gida, kawai a hanya sai ji yayi hawaye ya zubo mishi, har ga Allah duk ƙaunar da yake yiwa Zee ashe amanarshi zata ci ta auri Baqeer? Abu tana ganinshi ta saki ihu duk ta rikice saboda murna, shi dai komai na rayuwa ya tsaya mishi. Baqeer da kanshi yazo gidan ya sashi a ɗaki yayi mishi faɗa sannan yace "Zai sake zuba kaya shagon Baba in yaso ya dinga zama, don Kamalu bai yi karatu ba sannan Baba kaɗai ne zai iya sa mishi ido akan lamarinshi. **** Kwanaki sun shude rayuwa ta canza abubuwa da dama sun sauya, ciki kuwa har da Mummy wacce yanzu ta canza gaba ɗaya, to babu ma yalwar arzikin da zai sa ta yin bushasha sai dai rufin asiri da suke dashi ko fita ba tayi in ba da dalili ba, Kabir yayi aure yasa matarshi anan gidan ɓangaren su shi da Zainab da Nabila ya kasance ɓangaren shi da matarshi yanzu, matar yar boko ce don likitace, ita tasa Kabir ya maida hankali ya koma makaranta yin masters ɗinshi don da wasa da son harkar chilling da abokai ya hanashi maida hankali ya cigaba. Aurenta yasa abubuwan Daddy sun sake zuwa musu da sauki don yawanci treatment ɗin da bashi da wuya a gida take yi mishi. Inna kuwa ta je ƙasarsu sai dai yawanci mutanen da suka bari sun rasu haka dai suka nemi yafiyar wanda suka samu sannan ta dawo, Nabila kuwa ta samu wani mai madaidaicin ƙarfi ta aura a cikin samarinta da taƙi kulawa saboda Kabir sai da taga da gaske fa Kabir ba aurenta zai yi ba sannan ta haƙura ta fitar da miji tayi aure, balle da taga matar da Kabir ɗin ya aura tasan lallai yayi mata nisa. Dada kuwa jikin tsufa yau lafiya gobe ciwo hakan yasa Zainab ta dawo da ita nan wurinsu wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Baqeer ba, Umma taso ta ɗauketa sai dai tasan zaman gidan ba zai yiwa Dada daɗi ba, shima yana ta ƙoƙari akan ƙafafunshi wanda yake fatan nan gaba zasu warke don har yanzu baya iya tafiya dasu da wheelchair yake amfani. Shago kuwa sai dai ace masha Allah don kuwa har sun buɗe wani branch a Kaduna inda Tanimu ya koma can da zama shi kuma Baqeer ya ɗauki driver in kuma da Zainab ne sai su fita tare, Baqeer yaso ta fara aiki don baya son tauye mata hakki sai dai ta nuna ba yanzu ba gani take yi bai kamata su bar Dada ba sannan tana ganin Baqeer na buƙatarta sosai ya zai yi in ya dawo gida bata nan? Wannan dalilin yasa shima bai matsa ba don haka sai ta fara business ɗin shigowa da unique fabrics masu kyau Baqeer na ɗinka ready made daga na mata har na maza, yawanci kayan matan tare suke zama su ƙirƙiri styles ɗin shi kuma sai yayi sketching, na mazan ma takan taya shi ƙirƙirar design ɗin a inda suka gano Zainab is very creative kawai dai bata iya zanen bane, daga haka suka fara designing kaya very unique da idan ba a wurinsu mutum ya saya ba bai isa yaga irin styles ɗin su ba.

Watansu shida da aure sai ga Zeey da ciki, murna a wajen waɗannan ma'aurata abun ba'a magana, kusan kowa daya kamata yasan da batun cikin nan sun faɗa mishi don yadda suke ta ɗoki da murna, ita dai Umma sai dai ta kallesu ta girgiza kai idan taga yadda suke giringiɗishi da rawar kai akan cikin. Haka suka yi ta rainon cikin su cikin kwanciyar hankali kuma inda Allah ya taimaki Zeey bata yin wani laulayi sai ɗan abinda ba'a rasa ba.

***** Asiya da Bello na zaune a layin ganin likita sun kawo ɗansu da baya da lafiya. Kallon asibitin Bello yake yi yana jinjina ta yadda zai fara biyan kuɗin asibitin gashi tun ba'a je ko ina ba ɗan abinda ya riƙo ya tafi a wajen buɗe folder. Tsaki ya saki yana jin takaicin nurse ɗin data turo su wannan asibitin da kana gani kasan na masu hannu da shuni ne. Kallon Asiya yayi yace "wai shi likitan dole sai anan asibitin za'a iya ganinshi ba zai yiwu a ganshi a asibitin gwamnati ba? Nifa bani da kuɗi kin sani daga ganin wannan asibitin kuwa kin san za'a kashe kuɗi."

A kaikaice ta kalle shi cikin ranta tana tir da wannan halin rashin babu na Bello, ace wai kuɗin asibitin ɗansu ma sai yayi mita akai kamar shi ya yanke wa talauci cibiya. A daƙile ta amsa mishi da "kana jin dai abinda nurse ɗin tace sai muyi ta zuwa wancan asibitin bamu samu ganin shi ba saboda shine babban likita a wannan ɓangaren in har muna son ganin shi dole dai nan ɗin zamu zo idan kuma kana ganin baka da kuɗi a barshi sai mu koma gida musa yaron a gaba muna kallo har Allah yayi ikon shi akan shi." Bai ƙara cewa komai ba sai wani tsakin daya kuma yi. Kamar ance ɗaga kanka ka gani kawai sai hango Baqeer yayi akan electric wheelchair ɗin shi Zeey na daga gefenshi hannayen su cikin na juna suna fitowa daga cikin asibitin sai murmushi suke yi kana ganin su kasan basu da wata damuwa a rayuwa. Hannu yasa ya mutsitsika idon shi sai dai tabbas Baqeer ne yake gani, gaba ɗaya ya canja ya zama babban mutum kana ganin shi kaga wanda hutu ya zauna a jikin shi, ga matarshi da nesa ba kusa ba ta kerewa Asiya a komai. Juyawa yayi ya kalleta sai yaga itama ashe su take kallo idanunta sun tara ƙwallar ɓakin ciki, kaico da dana sani dafa yanzu itace kusa dashi. Tabbas ba ƙaramar asara ta tafka ba da barin Baqeer data yi gashi tun ba'a je ko ina ba Allah yayi mishi sakayya, ita ta guje shi saboda ya gurgunce sai gashi ya samu matar data fita a komai, Bellon data komawa gashi nan yanzu baya da komai sai kame-kamen rayuwa suke yi, tasan a yanzu Baqeer yayi mata nisan da har abada bata isa ta kamoshi ba.

Shima Bello a cikin ranshi yana jinjina yadda yau Allah ya mayar da Baqeer bayan duk abinda yayi mishi, yasan da ace bai butulcewa Baqeer ba da yanzu wannan arziƙin dashi za'a ci don duk wani alheri da Baqeer ya samu a rayuwa shine mutum na farko da yake fara janyowa ciki amma shine yayi mishi halin ƴan adam ya munafurce shi ya guje mishi a lokacin da yafi buƙatar kasancewar shi a tare dashi, yayi watsi da abotar shekara da shekaru son zuciya da kwaɗayi suka rinjaye shi ya aikata cin amana mafi muni ga abokin shi gashi nan yanzu inda rayuwa ta kawo shi, Asiyar da yake ganin kamar ita ce koma shi yayi mishi ƙwacenta ta zame mishi ƙarfen ƙafa don a yanzu dai da suka fara tara zuri'a bai isa yace zai yakice ta ba bayan haka ma wacce mace ce zata yi haƙurin zama dashi da wannan baƙin talaucin da yayi mishi katutu. Kiran sunan ɗansu da aka yi ne ya katse su daga tarin dana sanin da suka tafi suka tashi suka shiga ɗakin ganin likita, waiwayawa Asiya tayi ko zata sake ganinsu sai dai taga wayam babu su babu alamar su don tuni suka fice daga cikin asibitin ma.

***** Suna zaune a mota Zeey ce ke tuƙawa shi kuma hannayenshi sun kasa tsayawa waje ɗaya sai tsokano ta yake yi. "For the last time Ya Baqeer ka bari idan dai ba so kake yi na watsar damu ba, tom," tayi mishi maganar a shagwaɓe idanunta na kan titi don bata son abinda zai yi distracting ɗinta daga tuƙin da take yi. Ɗauke hannunshi yayi kamar yadda ta buƙata sai kuma yace "tunda yarinya taga sardeden saurayi ɗan kyakkaywa gaba ɗaya tabi ta sukurkuce ta rasa nutsuwa duk da yake gurgu sai data san yadda tayi ta janyo hankalinshi ya fara sonta sannan hankalinta ya kwanta."

Rufe bakinta tayi tana dariya tace "yau kuma nan wurin ka tafi? Ai dai wallahi kasan wuce nan, abinda ma kai ka fara nuna min soyayya a fakaice daga ka ganni a gidan Dada sai ka gurguro kekenka ka wani ajiye mini gift bag har da su kyautar rose flower, sarai kuma kasan me kyautar rose take nufi don haka kai ne ka ganni ka fowler mini har sai da kayi yadda kayi na afka maka shine yanzu zaka zo kana wani zance."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull