Kenza eBookz

Baqeer complete - Chapter 79

Baqeer complete - Chapter 79

Baqeer complete Chapter 79: Baqeer complete Chapter 79. "Um um fa Sweetums faɗi gaskiya, tunda kika ga wannan ɗan gurgun kika rasa nutsuwa har sai da kika…

769 words

"Um um fa Sweetums faɗi gaskiya, tunda kika ga wannan ɗan gurgun kika rasa nutsuwa har sai da kika nemo gidansu sannan hankalinki ya kwanta." Girgiza kanta kawai tayi tace "Allah Ya Baqeer kai ko," "Ni ko gaskiya, ai dai kin san abinda kika yi har ban san lokacin dana fara son ki ba." Wani irin kallo tayi mishi tace "I Love You Ya Baqeer." "I Love You too my Sweetums, Allah ya bar mu tare har tsufan mu." "Ameen," ta amsa tana jin wani irin shauƙi yana ɗibarta. ** Cikin hukuncin Allah Zainab ta haifi ɗanta namiji kyakkywa mai kama da uban shi sak kamar yayi kaki ya ajiye. Murna a wajen ahalinsu abun ba'a magana, ranar suna yaro yaci sunan *SALIM* saboda Baqeer yana ganin hakan kawai zai yi ya nuna mishi tarin matsayin shi a gareshi don Salim ya wuce aboki, ya tashi daga amini sai dai a kira shi da ɗan uwa. Ai kuwa yayi farin ciki sosai har ma ya rasa da bakin da zai yiwa Baqeer godiya shi kuma Baqeer yace komai yayi mishi bai biya shi tarin alkhairin shi a gareshi ba. To muma dai mun ce Allah ya bar zumunci har Aljanna. Suna ta shirye shiyen bikin Salim da Habi, Umma ta samu taje Umara ita da Dada wacce girma ya ƙara kamata, don Hajj tayi tsada sai dai a hankali, Baqeer yace wata shekarar zai biyawa Baba su kuma Jamila da Abu sai a hankali wata rana zai biya musu, yayi ƙoƙari sosai ganin ya haɗe kan ƴan uwanshi wanda suke uba ɗaya, wacce ke takaru ma a Makka ya sata ta dawo gida, Bashir na aiki sosai a wurinshi don ɗinki yake yi, Kamalu kuma an dage da zaman shago duk rawar kan nan an daina, gashi Badaru ya hana a bashi ajiyar kuɗi duk abinda aka siya ɗayan yaron shagon ake bawa. Randa Umma ta dawo daga Umara Jamila da Abu haka suka mata yi girke-girke dukkanin su burinsu su faranta mata ko Baqeer ya fara kai su makka, Maryam kuwa aiki take yi sosai shi yasa yanzu ganinta ya ragu sai dai duk ƙarshen wata suna haɗuwa a wajen Umma, Hadiza ma sana'a sosai take yi na atamfofi da laces wanda bazata ce komai ba sai hamdallah don rufin asiri kam na abinda zasu ci baya gagararsu. Badaru kam yayi sanyi don faɗa ma ba kasafai zaka ji yana yi ba dama girma yayi kawai dai rashin haƙuri ne da rashin tunani irin nashi a da, amma yanzu ya canza sosai. Baqeer har wannan lokacin ƙafar dai bata takuwa sai dai muna fatan wata rana ya taka ko da sanda ne, zaune suke a kan kujera shida Zainab, hannunshi ɗauke da Salim, ɗaga Salim yayi ya sumbaci goshinshi yace "Sweetums ya zaki yi da baki aureni ba?" Hular dake kanshi ta zare tasa a saman kanta tace "Baby Salim tambayar mana shi ya zai yi idan bai aureni ba?" Kuncinta yaja yace "Bari na tashi na koma." Dariya tayi tace "Ka gani ko? Ban san ya zaka yi da baka aureni ba kana aiki ka gudo gida don ka ganni." "Faɗa mini gaskiya addu'a kika yi mini ko?" Dariya sosai take yi yanayinta ne ya canza, wanda hakan yasa yace "What?" Yana ɗan ɗaga gira tace "Love you!" "Love you too!" Baqeer ya faɗa yana kallon Salim ta sani sarai so yake tayi magana murmushi tayi tana jin daɗin rayuwar nan tare da fatan Allah ya barsu tare.

*TAMMAT BIHAMDULILLAH*

_A nan muka kawo karshen wannan littafi namu mai suna BAQEER, muna roƙon Allah daya yafe mana kura-kuran da muka rubuta a cikinshi, ya kuma yafe muku wanda kuka karanta kuma ya bamu Ikon aiki da duka abubuwan alkhairin dake cikinshi_

_Saƙon gaisuwa na musamman da kuma godiya ga dukkanin waɗanda suka sayi littafinmu na ƴan tagwaye, mun yaba muku kuma mun jinjina muku Allah ya ƙara muku buɗi, lafiya da kuma ɗaukaka, mun gode. Allah ya haɗamu a wata tafiyar cikin aminci_

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar

*KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce

*MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari

*KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500

VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500 VIP 1000

ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130

KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull