Batuol mamman complete novel - Chapter 16
Batuol mamman complete novel Chapter 16: Batuol mamman complete novel Chapter 16. Bayan kwana biyu da zuwan su Major Kano suka shirya harda su Zainab sai…
3,375 words
Bayan kwana biyu da zuwan su Major Kano suka shirya harda su Zainab sai birnin Shehu. Da yake Zainab 'yar gari ce dadewa bata sa ta manta hanyar gidan ba. Sun so bata saboda gyare gyaren da aka samu kadan. Sojan da ake turowa kudi ya riga ya bar garin ma ta banki yake turawa MaiKudi kudin.
Alhamdulillah gida ya cika da yara ko ta ina. Ibrahim yana tura Hadir gefensa Major ne yana fada masa dawowar Awwab nan da kwana goma.
Matan ne suka fara shiga aka amsa musu. Sun gaisa Mami ta tambayi Jume wata yarinya ta nuna musu dakinta.
"Fada mata abokan aikin marigayi ne da iyalansu suka zo"
Yarinya ta ruga sai gasu sun fito tare Jume tana musu marhabin da lale. Tabarmi uku aka shimfida musu suka zauna aka gaisa.
"Jama'a ina kuka shige duk shekarun nan ba'a jin duriyarku?"
Kunya ta kamasu duk da kowa dai da nasa uzurin. Sun dan yiwa Jume bayanin da zata iya fahimta Major yana dariya yace "ina Alheran ne?"
"Wai, 'Yar soja ai tana rugar Barkindo, da yake dai akwai bikin yayarta 'yar wajen Mubaraka nasan suna tafe in Allah Ya so"
Kallon juna suka shiga yi sai Mami ta gyara tambayar "aka ce mana bayan Mairama tayi aure ita ta dawo nan wurinku"
Itama nema suke su juya mata kai ta kwalawa Matar Badaru kira "kinji wai 'Yar soja suke cigiya ni duk ban fahimci zancen ba, nasan Badaru yana ciki turo min shi ya musu bayani."
Tsayawa tayi suka gaisa sannan taje ta dawo tare da maigidanta. Shima ya gaisa dasu a mutumce Major yayi masa bayanin yadda suka yi da sojan da yake turo musu kudi akan cewa Mairama tana gidan miji, Radhiya kuma tana nan.
Badaru ya rike baki abin da daure kai "Yallabai gaskiya ka binciki mutumin da yayi maka karairayin nan tun wuri"
"Ban fahimceka ba"
Mami da Zainab har sun fara damuwa ganin yadda iyalan gidan su ka canja fuska su ma.
Badaru ya gyara zama ya soma yi musu bayani "zancen da nake muku Mairama tayi akalla shekara shida ko ma fi da makancewa, Radhiya da Zayyan kuma suna tare da ita a can wurin dangin babarta. Sai dai mutumci irin nata wallahi har ila yau tana turo mana yaran idan sun sami hutu"
Kuka wiwi Zainab da Mami suke yi. Zuwa yanzu sai dai su ce sun ga jiya sun ga yau a auren soja. Makanta, yanzu ace Mairama ta makance babu ido.
A sanyaye Major yace "ban tari numfashinka ba, wane Zayyan kake magana a kai?"
Jume tace "Zayyanu karami kanin Radhiya"
Mami ta zaro idanu "aka ce mana ta haihu jariri babu rai"
A fusace Jume tace "wai uban waye ne da wadannan karairayin? Yarinya tana fama da lalura da rashin miji anbi an dabaibayeta da karya. Rashin waiwayarta da kuka yi yafi komai damunta, bata da masaniyar inda kowa yake cikinku gashi dangin ita mahaifiyar Zayyanu suma shiru rabonmu dasu tun sunan 'Yar soja"
Zuciyar Major tuni ta kawo wuya ya daga waya zai kira dan sakon nasa sai ga Maikudi ikon Allah. Su Maikudi an karo wulakanci yana shiga yana fita duk wata yana jin 'yan chanjinsa a aljihu. Saboda son zuciya ma sai ya dena 'yar fafutukar da yake tunda dai albashin nan yana shigowa babu fashi.
"Yauwa Maikudi gara da Allah Ya dawo da kai da yanzu."
Idanunsa akan bakin ya kula akwai maiko a tare dasu "hee...hee baki muka yi a gidan ne. Sannunku da zuwa."
Matarsa ya shiga kwalawa kira "ya naga babu ko 'yar mantina dinnan a gabansu? Wannan ai halin karanta ne. Waye nan a cikin yaran azo a nemo musu abin sha mai sanyi"
Ran Jume ya fara baci tace "to dan ayi jikan na'isa, mu duk bamu iya ba sai kai. Ni zo ka jiye min baki ke neman Radhiya wai an fada musu a gidan nan take"
A take kuzarinsa ya fara raguwa "ki fada musu inda take su je mana"
"Mutanen nan fa abokan Marigayi ne, shi wannan yace ya dauki lokaci yana aiko da kudi kuma ance a gidannan ake karba" Badaru ya kara masa haske
Abinka da munafuki gumi ya soma yi kamar an kwara masa ruwa "indai don Allah suke yi sai abar tone tone su sake mata kyautar tunda sun dawo. Ni bari na shiga ciki na gaji"
Wani irin kallo Major da Hadir ke yi masa. Ashe Jume ma tasha jinin jizkinta. Ai kuwa bazata barshi ba indai haka ne. Kankace ido tayi ta kaurara murya
"Maikudi kada kace min kana da masaniya akan maganar da mutanen nan suke yi"
Ja da baya ya soma yi a tsorace "Ni kuma? Daga shigowata? Uhmm nayi nan akwai mai son ganina a waje" kafin su farga ya fice da sauri.
Yau da ace Hadir na da lafiya Maikudi sai ya yabawa aya zakinta. Major ma tashi ne dai baiyi ba amma ko ciki daya suka fito da Zayyan sai ya nuna masa yayi kuskure.
"Ku tashi mu tafi" yace dasu gabadaya.
Jume tana kuka matan gida da Badaru suna salati suke basu hakuri.
Babu alamun wasa a fuskarsa yace "Ku bani nambar waya da zamu nemi kwatancen inda Ummin Awwab take. Shi kuma wancan kafin na turo masu kama shi a fada masa nasan iya abinda na turo saboda haka ina bukatar kudin nan...da gaggawa"
Ransa yayi matukar baci ne yaki amincewa da masaukin da Jume tace ayi musu a gidan. Giginya hotel suka yi masauki washegari sai ga Badaru da sassafe ya kira yace zaiyi musu rakiya har Rugar Barkindo.
**********
Saboda yanayin matsanancin zafi da ake fama dashi yau gidan har Ardo suna zazzaune a karkashin katuwar darbejiyar da ta yiwa tsakar gidan inuwa suna taba hira.
Yammaci ne na asabar Radhiya tasan cewa Zakari zai zo kawo wani sabon maganin ciwon ido da aka rubutawa Mairama a asibitin Bauchi inda yake aikin lab wato dakin gwaji. Gyaran nono ta gama wanda ta cire man shanu sannan ta je tayi wanka.
Shiryawa tayi cikin riga da skirt ta saka hijabinta iya gwiwa don zuciyarta tana raya mata yau kawun nata zai fada mata abinda idanunta suke ganin yana boyewa...soyayyarta.
Har kofar gidan Ardo aka rako su Major suka firfito kowa da nasa tunanin. A yayin da rayuwa tayi ta garasu ita Mairama kauye ta fado. Kauyen ma ruga da abubuwan cigaba suka yi mata karanci fiye da ko ina.
Fitowarsu ke da wuya sai ga Emzee nan da wani abokinsa sun dawo daga kiwon shanun Ardo. Sanda ce a wuyansa amma shirt da dogon wando ya saka suna ta hirarsu ta samari.
Ba Major da Hadir ba, hatta Mami da Zainab sai da gabansu ya fadi da ganinsa. Wannan banda haske babu ta inda zaka ce ya baro mahaifinsa.
Kawunsa ya hango ya yi saurin barin abokinsa ya taho "Kawu Badaru yaushe ka iso"
"Tare da bakin Umminku nake. Yi maza ka shiga kayi mana iso"
Gaishe su yayi cikin gurbatacciyar hausarsu ta tsantsar fulani ya shiga ya fada musu. Mairama ta auna ta auno ta kasa gane su waye zasu zo nemanta tare da Badaru.
Radhiya da ta tabbatar zuwan bakin zai hanata sakewa da Zakari ta shiga tura baki. Innawuro tace tayi shimfida sannan aka ce su shigo.
Zainab da Mairama kowacce wai dakewa take yi kada suyi abin kunya a gaban 'ya'yansu amma da sauri suka shiga gidan.
Mairama tana zaune akan tabarma ga sandarta a gefe ta yafa mayafi kalar kayanta. Daga bayanta kuwa babu tantama Alheran Radhiya ce wadda ganin 'yan gayu suna shigowa yasa ta manta da batun Zakari ta shiga washe baki.
Mairama tana ji Innawuro tana yi musu barka da zuwa amma yaran kadai ke amsawa. Manyan kuwa Mairama suke kallo da take ta murmushi a hankali a zatonta babu mai ji tace "Ke su waye ne sai kamshi nake ji"
Mami a gabanta ta zauna tana kuka ta kama hannunta da makanta bata hanata ayyuka irinsu yin fura ba da nata lallausan hannun. Zainab kuwa a gefenta ta zauna ta rungumo Mairama a jikinta. Rasa gane me yake faruwa ita da kowa na gidan suka yi.
Radhiya da ta kurawa Major da Hadir idanu ta saki ihu kamar an tsunguleta.
"Yasin Ummi na ganesu na hoton nan ne"
Mami tasa hannu ta shafa fuskar Mairama tace "Ummin Awwab"
Duk da bata gani sai da idanunta suka kara girma gabanta ya tsananta faduwa, baki na rawa tace "Mami??? Ke duba hotunan akwai wannan a ciki?" Ta fada tana kankame hannun Mami kamar zata kuma tafiya.
"Ai shikenan tunda baki ce a duba dani ba" Zainab tayi maganar da wasa cikin kukan da yaci karfinta.
Mairama fashewa kawai tayi da kuka su ukun suka rungume juna suna hawaye sauran jama'ar wurin suna tayasu mazansu da matansu.
[5/22, 10:51 PM] Sis Ruky: Mairama ta ga gata da ya amsa sunan gata a Rugar Barkindo. 'Yan uwa ke tururuwar ganinta har ana fadan gidan wa zata zauna. Ardo yayi tsalle ya dire yace matarsa ce zata dauka ai ita ce mace. Dole sauran suka amince aka barwa Innawuro.
Idan manya ko dattijai cikin danginsu sunzo sai ayi ta kallonta ana cewa kaza dinta irin na Mairo ne. Murmushi kawai take yi don ko hoton mahaifiyarta bata taba gani ba. Sun tausaya mata da jin labarin rasuwar mijinta ga makanta.
Radhiya da Emzee sai gasu cikin 'yan uwa sa'anninsu ana ta nishadi. Abinci da nama anci an ture. Kafin sati ya zagayo jikinsu ya fara nuna kwanciyar hankali da koshi.
Mairama kullum cikin godiya take ga Allah da Ya dawo mata da dangin mahaifiyarta. Ba jimawa sabo ya kullu sosai a tsakaninsu baki daya. So da tausayawa suke nuna mata da 'ya 'yanta. Ardo ke cewa su duka marayu ne ababen dubawa.
Bata cuci kanta ba ta roki alfarmar su Radhiya su koma makaranta. Tare aka nema musu JSS 1 ita da Emzee da ya gama aji biyar. Ita a makarantar kwana ta gwamnatin jaha ta mata shi kuma jeka ka dawo ta maza. Ranar da dan gidan Baffa Habubakari ya kawo takardun tubure musu Radhiya tayi da kuka wai bata so.
"Karatun kike yiwa haka Radhiya?" Innawuro tace tana kokarin bata baki.
"Dama saboda bama cin abinci mu koshi ne fa Ummi ta kaini makaranta inyi kudi"
Mairama kunya ta isheta tasa hannu tana nemanta "haka muka yi dake? Kuji min yarinya"
"Da naga ko nama bama ci irin na gidan Baba Kallamu shine nayi zaton haka ne" ta mayar mata da amsa tana shure-shure.
"Idan bata yi ba ai ba'a kirata jikar Ali ba" Innawuro tace tana dariya.
Radhiya ta turo baki "Malamijo muke kiransa mu dai"
"Ina yaga malanta sai bakar rowa da mammakon tsiya"
"La la lahhhh baban Ummi ne fa"
Ardo yana jinsu yana rubutu a jikin allo yace "da kyau 'yar albarka ki kare masa kinji ko. Duk tsiyar naka ai naka ne Innawuro"
Dariya rigimar Radhiyan ke bata tace "kasan ni ba bakuwar zafi bace Allah Ya baki hakuri. Nima kizo na baki labarin 'yar uwata Mairo. Ga kyau ga kirki kamar wata dan daren goma sha hudu"
Idanu Radhiya ta bude sosai da mamaki "wata dai irin na sama Innawuro?"
"Akwai wata a kasa ne?" Mairama ta fada tana jin kamar ta mangareta.
"Tabdi, Ummi kenan Innar taki a mulmule take kamar wata. Ga Malamijo kamar tsolon rake. Mu dai Allah Ya taimakemu ke daidai kike."
Mairama ta fusata ta fara wawurarta "Karami dauko min yayarka ko ka janyo min ita. Yau tambotsan nata harda iyayena kuma"
A guje ta tashi "Ardo don Allah ba Innawuro ce ta fada ba."
Innawuro ta dauko muciya "bari na mulmule ki kema sai aji dadin kiranki jikarta"
Hanyar waje tayi tana gudu wai ita gidan Malamijo zata koma.
Mairama ta daure fuska "da ya fi miki mu ma mu huta. Kuma karatu ki ma fara shiri sai kinyi"
Dawowa tayi da baya tana murza yatsan kafarta a cikin kasa tana tura baki "to don Allah ki kaini soja irin na babana indai kina so nayi karatu"
Gaban Mairama ne ya fadi ba shiri sai ga hawaye. Innawuro da ta dauki abin wasa tana biyewa Radhiya ta shiga bata hakuri tasan bazai wuce mijinta ta tuna ba.
Radhiya ma sai ta soma kuka tana cewa tayi hakuri zata yi karatun ko wanne ne.
**********
Alheran Radhiya Zayyan Tureta irin fitinanun daliban nan ne marasa tsoro ga kin ji. Duk inda akace 'yan aji daya sunyi laifi to in sha Allahu Radhiya tana cikinsu. Kan kace kwabo tayi kaurin suna tsakanin dalibai da malamai. Kirikiri tace sunanta 'Yar soja haka babanta yake kiranta daga Mairama ta bata labari. Shikenan makaranta suka santa da wannan sunan. Anyi sa'a tana dan taba karatun babu laifi.
Wata rana suna layin dibar ruwa suna ta hayaniya irin ta 'yan makaranta ta dage tana ta zuba.
"Allah Ya kaimu siniya wallahi zan warwasa a makarantar nan. Duk wasu jiniya a lokacin sun shiga talatin a hannuna"
Kawarta Ruqayya tace "ke 'Yar soja so kike yadda muke tsinewa su senior Jummai kema a tsine miki?"
"Ke baki gane ba. Lokacin kannen su senior Jummai mai tafiyar agwagwa ne a makarantar. Ramuwa zan zauna yi"
Wata tace "ai kuwa nima zan so, rannan fa kwai tace nayi mata a karkashin gadonta"
Radhiya ta daka tsalle "inama nice wallahi, na samu na sassaka mata kashi mai waaaaaari"
Dariya suke duniya sweet kampo sai ga senior Jummai ta taho da tafiyar catwalk dinta da su Radhiya suke yiwa lakabi da tafiyar agwagwa. Ta gama jinsu tsaf suna bayan ginin da famfon yake.
Idonta ya kyallo mata ita sai kawai ta canja hirar amma saboda tsoro muryarta har rawa take yi.
"Allah Yasa senior Jummai tace in zama daughter dinta a makarantar nan. Daga ranar wanki da debo ruwanta duka zan rinka yi"
Sauran sai suka fara mamakin me take nufi tunda dai haduwa suka yi ana zaginta. Yadda tayi maganar ne idanu har sun ciko da hawaye yasa Jummai da sauran seniors din dariya. Kawayen Radhiya ciki ya duri ruwa. Ita kanta a tsorace take. Jummai ta dafa kafadarta kamar ta saki fitsari don tsoro sai ji tayi tace daga yau kada wani ya sake ko da aiken daughter dinta ne.
Kowa yayi mamaki harda kawayenta tace Radhiya tana burgeta saboda ko me za'ayi mata sai ta aikata abinda tayi niya. Idanunta kawai zaka kalla kasan fitina da rigima suna dawainiya da ita.
Wata kungiya da aka bude a makarantarsu SS wato School Soldiers a nan aka samu kanta. Da jikinta da zuciyarta take wannan aikin na kare hakkin dalibai. Gashi da kayan makarantarsu riga da zani ne amma an basu hula irin ta sojoji mai lankwashewar nan suna sakawa akan hijabansu. Radhiya jin kanta take kamar sojar gaske. An kamanta gaskiya da amana sannan an gurji seniors masu hana sababbin dalibai sakat. Idan kaji ana Officer 'Yar soja a makarantar zaka rantse wani babban soja ne saboda yadda ake shayin shiga tarkonta. Zaman SS shine babban jindadinta a makarantar.
A haka aka yi karatun cikin ikon Allah tayi nasarar fita da credit bakwai. Emzee kuma duka taran ya haye. Sai dai ko kadan a yadda ilimin ya tabarbare bazaka hada makarantar gwamnati dake kauye da wadda take birni ba.
***
Tana jin shigowarsa dakin nata tayi saurin rufe ido kamar mai bacci. Murmushi kawai yayi yana kada kai. Zainab bazata taba canjawa ba indai tare dashi ne. Shekarun da suka yi a matsayin ma'aurata bai sa ta canja komai daga yadda ta faro ba. Akan doguwar kujera irin ta hutawar nan ta dakin ya zauna sannan ya soma yi mata magana.
"Tashi magana zamuyi"
Kin motsawa tayi sai da taji yace bari ya hawo gadon ya tabbatar ko idonta biyu.
Juyowa tayi a hankali tana jin kunyar ya gano karyarta. Bata son yadda take yiwa Musa amma zuciyarta ta kasa rissina.
"Shawara nazo nema"
"A wurina?" Ta tambaya mamaki yana bayyana a fuskarta.
"Eh, aure nake son karawa sai dai na kasa tsayar da shawara akan na dawo da mamansu Aisha ko na auro wata daban"
"To ni me kake so nace? Ka auri wadda tafi kwanta maka"
Fuskarsa ta nuna ba haka yaso ba kuma shima bai boye ba yace "zan so kiyi min rigima irin wadda kowace mace take yiwa mijinta a lokacin da ya tashi yi mata kishiya"
Cikin yanayin rashin damuwa don har ranta ita bata ga abin rigima ba tace "saboda me?"
"Saboda nasan cewa ko yaya Zainab ta damu dani kamar yadda na damu da ita. Sai dai nafi kowa sanin zaman hakuri kike yi a gidan nan. Na tauyeki na hanaki walwala da jindadin zama da wanda kike so"
An tabo inda yake mata kaikayi sai hawaye sharrr tana gogewa da bayan hannunta.
Musa yana jin kukan har ransa amma yasan ba nasa bane na wani ne "kinyi hakuri sosai Zainab, naso ace mun haihu don in samu abinda zan cigaba da garkuwa dashi in ki rabuwa dake amma Allah bai kawo ba. Sai nace zan barki ko don su Aisha. Yanzu kuma gashi suna shirin aure nan da watanni kadan. Ina ganin kamar bani da sauran dalilin cigaba da zama sanadin kuncinki"
Kukan Zainab sai ya koma mai sauti. Tana tausayin Musa bisa soyayyar da yake mata. Tayi iya yinta amma zuciyarta taki amsarsa a matsayin masoyi.
"Kayi hakuri da dukkan bata maka da nake yi, zanyi kokarin gyarawa"
Murmushi yayi mata yana mika mata takardar hannunsa "ni na gyara mana matsalar ina fata Allah Yasa nayi abinda ya dace. Zainab na sakeki saki daya"
A gigice ta kalle shi hawayenta yana karuwa. Idan ya saketa fa kenan babu sauran shamaki tsakaninta da Hadir. A gaggauce ta bude takardar sai ta kula guda uku ne a hade da stapler. Daya takardar saki, daya check na miliyan biyu, dayar kuma takardar mallakar wani gida ne a Kano da ya saya mata dan madaidaici. Dago kai tayi sharbe da hawaye harda majina.
Cikin nutsuwarsa yake magana daki-daki "tukwicin kulawar da Aisha da Anisa suka samu daga gareki ne. Bana son fada amma yabon gwani ya zama dole. A kanki na yarda ba sojoji bane kadai jaruman kasata harda matansu. Soyayyarki ga baban Ibrahim ita tafi komai kara miki kima a idanu na. Nayi zaton kudina zai sa ki manta da wanda yake talaka mai nakasa amma bakiyi ba. Kin so zama da mutumin da bautar kasa ta nakasa farincikinku domin cikar soyayya. Nagode da lokacinki da kika ara min muka zauna tare"
Maganganun sunyi mata tsauri sun taba mata zuciya. Tashi yayi zai fita Zainab ta taho da sauri ta rungume shi tana kuka. Bata taba yi masa haka ba idan ba shi ya nema ba sai yau.
"Allah Ya faranta maka fiye da yadda kayi min Abban Aisha. Ka yafe min duk laifukan da nayi maka a zamanmu tare"
Dago kanta yayi kana ganin damuwa a cikin idanunsa "yanzu dai ki soma hada kayanki kafin na chanja shawara"
Da hawayen take murmushi "nagode"
"Nima nagode" yace ya sa kai ya fita yana jin a ransa kamar an sauke masa wani kaya mai nauyi. Ya dade yana tsoron hakkinta kada ya kama shi saboda son zuciyarsa yau Allah Ya bashi iko ya rabu da ita ba don yana so ba.
Ajiyar zuciya ta saki bayan fitarsa ta mika godiyarta ga Allah sannan cike doki ta kira Ibrahim.
Labaran tara na NTA ya kunnawa Hadir yana gefe game ya dauke masa hankali a wayar kiranta ya shigo. Murmushi yayi ya dauka.
"Hello Mama"
Hadir ya juyo ya kalle shi sai kuma ya dauke kai. Ina ma zai iya tambayar lafiyarta da yayi.
Daga daya bangaren tace "Ibrahim yaya su Umma?"
"Lafiya kalau, ya su Anti Anisa da Baba?"
"Su ma lafiya kalau. Ibrahim nace me kake so gift din graduation ka ki fada min kamar wata surukar ka ko, na kula ko hira baka son yi dani" tayi karamar dariya.
"Ina naga fuskar" yace a zuci. Ita da bata sakin jiki da kowa bare ayi batun hira. Daga gaisuwa sai ta fada kogin tunane tunanenta ta bar mutum zuru. Yana mamakin yadda idan yaje hutu take hira da su Anisa duk da ba wata hirar kirki suke yi ba.
"Ya kayi shiru ne?"
"To kiyi hakuri zan gyara"
"Shikenan, ina babanka?"