Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 3

Batuol mamman complete novel - Chapter 3

Batuol mamman complete novel Chapter 3: Batuol mamman complete novel Chapter 3. Tabarma aka shimfida musu a zure shi kuma yana daga kan wata kujerar karfe…

3,319 words

Tabarma aka shimfida musu a zure shi kuma yana daga kan wata kujerar karfe ya baza riga don ya cika ido. Gaishe shi suka sake yi Hadir yayi masa bayanin komai game da zuwansu da bukatar idan 'yan matan sun amince ayi komai da wuri musamman saboda su basa samun damar fitowa daga barikin suyi dogowar tafiya batare da dalili ba. Yawonsu baya wuce cikin gari kada a nemesu sunyi nisa.

"Ku kwantar da hankalinku Kano dai ba bakuwata bace sannan a can birnin Shehun ma akwai wanda na sani don na taba zuwa garin. Kunsan wani mai kilishi a hanyar Dange shuni? Yana nan wani dan firit haka yace min asalinsa ma mutumin Zaria ne. Kila zai iya tuna ni don naji dadin kilishinsa na sayi da yawa lokacin…"

Duk sun dauka wata alaka zai ce tsakaninsu ko karin bayani sai suka ji zancen yakare, Zayyan sarkin dariya tunda yace mai kilishi dan firit ya daga kai ya kalli Malamijo sai kawai ya kunshe dariyarsa kada ya jawowa kansa. Sun ji dadi ya ce ya basu yaran sai su fara shiri. Tashi yayi yace su jira zai turo su ko gaisawa suyi tunda su Zayyan a ranar zasu koma Sakkwato. Kusan a shirye Mairama take kira kawai take jira yayin da Salame ta nade akan katifa wai zazzabi ke damunta. Mairama tayi mata sannu ta bi bayan kanwarta da ta sanar da ita Malamijo yace taje wurin bakin.

Sai da tazo bakin kofar da zata sa da ta da zauren da suke, kunya ta hanata shiga. Da Hadir ya hangota, ya fara zolayarta cewa ko sune bata son gani bari su basu wuri. Kai a kasa ta rufe fuska ta shiga ta gaishesu. Salisu yana cigiyar gimbiya Salame ta sanar masa bata da lafiya. Yanayin fuskarsa ya nuna baiji dadi ba.

"Ki dai taimaka min naga alama so take ta saka min ciwon zuciya"

Zayyan da Hadir ne suke kwantar masa da hankali har suka fita don a bar Zayyan suyi magana da Mairama. "Mairam tafiya ba sallama ko?"

Kanta a kasa ta amsa "kayi hakuri"

"Nayi tunda zuwan nawa ya haifar da da mai ido gashi an bani ke"

Wata matsananciyar kunya ce ta shigeta ta sake dukar da kai. Shima yasan a hanya suke shiyasa bai ja ta sosai ba yace zaiyi kokarin dawowa kafin magabantansa su zo. Yau a hanya suke suna sauri. Wata leda ya mika mata, yayi yayi, taki karba sai ya tashi ya barta a wurin. Iyakarta bakin kofa tayi musu sallama da kyakkyawar addu'ar tafiya. [5/22, 10:42 PM] Sis Ruky: C Washegari yaje wurin Mal Aminu ya fada masa yadda suka yi da shawarar da ya yanke game da kudin. Goyon baya ya bashi suka yi sallama ya kwashi dukiyarsa sai Kano gidansu Hadir.

***********

"Ka koma ka fadawa wadda ta aiko ka na fada na kara 'yata bazata tafi kwadayi gidan kowa ba." Cewar Malamijo yana karkada dan jikinsa duk don ya nuna da gaske fa yake.

Yaron wanda ya kasance kanin Salame da suka hada uwa ya tashi ya bar wurin Salame na zubar hawaye. Wata tsawa Malamijo ya daka mata ta shi babu shiri jiki na bari.

"Kwalamammiya tashi ki bani wuri. Ku babu mijin babu wata sana'ar kawo dari da kwabo sai dai aci a cika min shadda da bayan gari. Mtww Kallamu kwoi mugu, ya rinka rudata sai da na kaiku bokon banza bokon hofi gashi ban ga komai a kasa ba"

Mairama da ke wanki a tsakar gidan ya nuna da bakinsa da yake turawa saitinta "ke kuma sai bakin hali ba uhm ba uhmm uhmm kinbi kin tsaneni ina mahaifinki. Ko rokona abu ba kya yi. To duk jarabar mutum dai ba'a sake uba. Nine nan dai uban naki don ko makaho ya shafaki ya shafani yasan akwai jini. Da namiji kika fito ma sunana zan maida miki Yasin"

Wankinta ta cigaba tana yi hawaye na diga a cikin bokitin ta jiyo muryar Yadikko daga dakin girki.

"Ka dai ji kunya Malamijo, kana abu yana damunka shine ka rasa da wadda zaka rinka wannan magana kamar wata sa'arka sai 'yar cikinka. Rashin roko tayi min daidai. Masu yi din banda bakar magana me kake tsinana musu bayan sun gama keta billensu"

Hularsa ya turo gaban goshi a karkace "mutum dai ya shiga taitayinsa dani don ni dadewa bazata sa na kasa sallamar 'yan hamayya ba"

Daidai nan Nene kanwarsa da ta kawo musu ziyara daga wani kauyen Gaya inda take aure ta idar da sallah. Magana take da niyyar yi masa akan yadda yake yi da gidansa duk da dai ba yau farau ba suka ji an banko kofar gidan.

Ta Madina ce babar Salame ta shigo ko sallama babu "gani nazo da kaina a bani 'yata Malamijo ko in nuna maka ba kai kadai aka haifa a watan tijara ba"

Tuni tsakar gidan ta kaure da 'ya'ya da matansa an fito kallo. Salame jikinta har bari yake tana kuka.

"Yanzu ke baki ji kunyar shigo min gida ba? Koda shike naji labarin yanzu ma zawarci kike kina neman mafaka"

Daga murya tayi cikin fada ta nuna shi da yatsa "Ali ba tsoronka nake ji ba. A bani 'yata biki zamu na 'ya'yan 'yar uwata a Kano"

"Bazata ba" yace a takaice. Fada Innar Salame ta soma yi Nene ta sa baki "Ke Salame wuce ki hado kaya kizo ki bi mahaifiyarki. Malamijo idan baka bari yaran nan suna rabar dangin iyayensu mata za'a sami matsala nan gaba"

Wani karkataccen kallo ya bita da shi kafin ya kada baki yace "ke da kika lallabo cin arziki ina ruwanki da iyalina bayan baki san zafin haihuwar ba?"

Jikinta ne yayi sanyi ta dukar da kai "Malamijo ni???"

Shima sai yaji nasa jikin ya saki don kuwa yana ji da Iyalle ko a cikin dangi "ba haka nake nufi ba. Ke Salame zo ki bi uwarki kuma sati guda na bada aka dara ban yafe ba"

Innar Salame tana tsaye tana karkada kafa daya tana jiranta ta fito. Mairama tana rakube a jikin bango wurin da suke shanya tana jin inama ita ce zata je wurin dangin tata mahaifiyar. Sai dai ina zata sami wannan damar. Mutanen da suke fulanin tashi basu nan basu can. Auren ma da Innarta anyi ne kawai saboda sauke bashin da Malamijo yake bin babanta a lokacin. Hangota Innar Salame tayi sai taji yarinyar ta bata tausayi. "Mairama kema ko zaki bimu ne?"

Malamijo yayi wani tsalle sai gashi a gaban Mairama "wannan kuma kinyi tsararo Ta Madina, babu inda zata je"

Iyalle da kanta tazo taja hannunta ta kaita dakinsu "hada kayanki ki bisu zanyi maganin abin"

A tsorace Mairama ta hada kayan saboda gudun kada ya hanata tafiya. Basu dade ba a dakin Yadikko ta kwala musu kira suka tafi dakinta. "Ni da Nene mun roka muku alfarma ya bari kuyi kwana goma. Idan kunje ku tabbatarwa da kanku bazaku wuce lokacin da aka dibar muku ba"

Murna a wurin Mairama kai kace bikin na dangin tata mahaifiyar ne. Salame kuwa har ta gama tsoro bai bata damar sakin jiki ba.

Da zasu tafi kashedi Malamijo ya rinka yanka musu kusan minti goma yana abu daya. Nene da Yadikko sunyi masa shigar sauri sun kuma hade masa kai ba don haka ba Ta Madina bata isa ya bata Salame harda karin Mairama ba.

**********

Kano ta Dabo tumbin giwa, birnin na Kano a yau yayi manyan baki daga garin Sumaila wato Salame da Mairama. Wata unguwa da basu san sunanta ba suka wuce zuga guda ta 'yan biki daga Sumaila. Yadda Mairama ta saki jiki cikin mutanen sai ta baka mamaki da tausayi. Tun tasowarsu ita dai bata taba zuwa wani wuri da zata ji dadi da sa'anninta ba sai makaranta. A can ma ba wani sakin jiki gareta ba saboda tana ganin kowa yafi karfinsu. Gasu dai da uba mai kudi amma daga kayan makaranta da akwati baya basu komai. Dan siyayyar nan ta provision sai dai su gani a kwanar wasu. Shiyasa an rainasu sosai musamman Salame da sunanta ya dace da halinta. Anyi Kamu a ranar da suka sauka da daddare inda amare aka kunshesu a daki tsakiyar 'yan mata kawayensu da 'yan uwa, dangin angwayen su ka zo aka feshesu da turare.

Washegari kuwa lanchin (luncheon) za'ayi a filin wani katon gida mallakar kanin baban amaren biyu.

Salame ta sami kaya kala biyar sababbi, biyu daga yayar innarta uwar amare sai uku daga Ta Madinan. Guda ta cire a ciki ta baiwa Mairama tace ta saka kada ta fita daban tunda su dai ba wasu suturun arziki na shiga taro garesu ba. Mairama sai murna da godiya ta sanya atampar da akayi mata dinkin riga da zani buba anyiwa rigar cin baki da irin lace dinnan na adon kaya a wuya da hannaye. Tayi kyau abinta gwanin sha'awa haka itama Salamen. Motoci bus bus ne aka haya suka rinka kwasarsu aka kaisu wurin bikin.

Salame tana manne da kanwarta duk da cewa dai tana sakin jiki da 'yan uwanta suna hira. Teburinsu su bakwai ne da yake a zagaye yake suna fuskantar juna ana ta tsokanar wata cikinsu da tayi saurayi daidai kofar shigarsu gidan. Karaf idanun Salame suka sauka akan Zayyan ya nisa suna magana mai matukar mahimmanci da Hadir. Daya daga cikin angwayen dan uwa ne ga Hadir din.

Iyayensu maza ciki daya suka fito. Shiyasa da Zayyan ya iso Kano aka sanya shi cikin abokan ango. Cinikin fili suka gama kafin zuwansu nan a unguwar gandun albasa. Shi dai Zayyan ya ga wurin babu gidaje sosai amma dillalin yana ta cika masa baki cewa nan gaba kadan unguwar zata hade harma a rasa filin saidawa. Shima da yake ba mazauni ba sai ya amince ya biya kudi bisa shawarar Hadir. Zancen gini kuma a hankali zasu yi tunda har yanzu ko rabin kudin da aka bashi bai taba ba.

Takardun filin ne kwafi biyu da sa hannayensu ya mikawa Hadir daya yace gata nan ya ajiye masa shi kuma zai aje daya a wurinsa. Sai da suka gama komai duk motsinsa akan idon Salame sannan su ka koma cikin samari 'yan uwansu. Ba karamin tafiya yayi da imanin Salame ba lokaci guda taji sonsa ya game zuciyarta.

Mairama kuwa an sami sake hira tayi hira an kawo abinci kowa plate dinta shake da jallof din shinkafa da yankan naman sa da aka soya sai salad, tumatir da albasa. Wayyo dadi jikinta har tsuma yake kuma wai aka kirga su aka sake ajiye musu ledar tsire ga kuma lemon kwalba. Kar kaso ka ga idanun Mairama hankalinta yayi kwano na Salame kuma yayi kan Zayyan da bai san da zamanta a wurin ba.

Police band suna wakarsu amma kusan kowa abinci yake ci babu 'yan rawa. Kwalbar fanta chapman Mairama ta faki ido ta daga tana kwankwada asalin dadi da sanyi yana ratsata ta manta da kunyar idanun jama'a. Bata samu ta sauke kwalbar mai 35cl ba sai da ta shanye shi tas. Daga lokacin da ta soma waige ta tabbatar babu mai kallonta har zuwa sanda ta ajiye kwalbar Zayyan yana gani. Baki ya rike yana kallon yadda ko da ta shanye sai da ta sake daga kwalbar ta kwakkwafeta a bakinta. Kasa cin nasa abincin yayi komai tayi sai yaji ya burge shi shi kadai ya rinka murmushi. Teburin kusa da nasu Mairama ne duka matan dama su uku ne su ka tashi a tare. Mairama tana ji suna cewa sallama zasu yiwa amaren su tafi. Tana ganin sun bace cikin jama'a ta wayance ta tashi da kwalbar lemonta ta ajiye a wurin ta dauki wata mirinda da ko rabinta ba'a sha ba. Plate din nasu ma basu wani ci sosai ba ga nama sun bari. Kamar ta dauka shima sai dai ta hakura lemon yafi mahimmaci a gareta. [5/22, 10:42 PM] Sis Ruky: E *TUN RAN GINI…*

Tana shiga daki ta sami Salame a tsaye sai safa da marwa take saboda zulumi. Yanzu shikenan abinda take so sai ta hakura dashi saboda Mairama. Gaskiya bazata iya ba domin son da take masa ba kadan bane. Kuma ma dai ai ita ce ya kamata yaso tunda danginta ne, Mairama kara kawai akayi mata. Ta nisa a cikin tunani taji Mairama tana mata magana.

"Adda jikin ne dai? Ko na sanar da Yadikko a fadawa Malamijo?"

Hade rai tayi ta koma ta zauna akan tabarma "ke yanzu banda rashin kamun kai me ya kaiki dadewa wurin saurayi daga zuwansa na farko? Mutumin da ba wani saninsa ki ka yi ba don iya zubar da aji."

Kwarai Mairama tayi mamakin kalaman Salame don a iya sani da kuma shaidar da za'ayi mata a gidan tafi kowa saukin kai da dadin mu'amala. To amma meye ya kawo wannan zantuka haka? Kasa daurewa Mairama tayi ta koma bakin katifarsu ta zauna ita ma.

"Adda Salame wai me nayi miki ne haka don Allah? Kwana biyu kenan sai kiyi ta harara ta kina fada min maganganu"

"Ji rainin wayo ki min kwace kizo kina min dadin baki" tace a ranta amma a zahiri sai ta daure tayi mumushi "gani nayi daga yin saurayi kin haukace a kansa ko tunanin idan kin bar gidan nan da wa zan zauna ba kya yi?"

Jikinta sai yayi sanyi ta sake matsowa kusa da Salamen "kai Adda me ya kaiki wannan tunanin? Shine kike ta fushi…ohh ni wallahi duk kin tayar min da hankali na damu. Kema ga Salisu ba sai mu bar gidan tare ba."

Turo baki Salame tayi "dena min zancensa wallahi baiyi min ba, ke dai kinyi sa'ar Zayyan kawai kina murna"

Rarrashinta Mairama ta soma yi a zatonta da gaske tunanin rabuwarsu a gaba ke damunta. Sauran kannensu mata babu sa'anninsu, maza biyar ne su ke binsu. Koda Salisu ta shiga yi tare da bata sakon gaisuwarsa ta yi tsaki da gaske dai bata son zancensa.

"To na bar zancen nasa Allah Ya kawo wanda ya fishi alkhairi. Shima yace na gaisheki da jiki kuwa"

"Shi wa?" Salame ta fada cikin gatsali wanda Mairama duk ta sawa ranta duk a cikin rashin son su rabu ne.

Tambayar kunya ta bata ta soma inda-inda ba ta san da me za ta kira shi ba. Sunansa dai da wahala ta iya fada a yadda take matukar jin nauyinsa.

Zungurinta Salame tayi da kafa tana mata wani irin kallo mai tattare da kishin da ake kokarin sakayawa. "Zayyan kike nufi?"

Kai ta gyada ga mamakinta sai ta ga fuskar Salame ta washe sosai tana murmushi "ashe bai manta ni ba. Me yace? Ina nufin da yaya ya baki sakon? Ki gaishe da Salame yace ko me?"

Dadi taji ganin sauyi a tare da yayarta ta kuwa biye mata tana fada mata yadda yace da zai bada sakon gaisuwar. Har dare ranar Salame motsi kadan sai ta tuna wai Zayyan yace a gaisheta, sai taji wani dadi yana ratsata.

**********

Matafiya sun sauka a cikin garin Sakkwato lafiya. Ba wata gajiya su ka yi ba don sun dade da fara sabawa da wahala suna jure mata sosai. Gidansu Zayyan su ka wuce zai dauki kayansa da ya bari sai su koma barrack dinsu.

Gidan yanzu dama daga Jume sai Maikudi, Rayyan da Badaru wadanda sune Zayyan yake bi dukkansu babu mai aure. Matan kuwa Fiddausi, Mubaraka da Hafsatu duk suna dakunansu. Kwasar tuwo Jume take yi Badaru yana zaune akan turmi da ya kifa sai Maikudi kwance a kofar daki yana faman firfita su ka ji sallamar Zayyan din.

Babu wanda ya amsa masa cikinsu sai harara da suke binsa da ita. Dakinsa ya wuce kai tsaye ya dauko jakar kayansa a ransa yana bakincikin halayyar 'yan uwan nasa. Ba haka ya bar jakar ba alamu sun nuna an bude an yamutsa masa kaya wurin neman abin da yake zaton kudi ne, sai dai ko kwandala bai bari a ciki ba. Ratayo abarsa ya yi ya fito ya kulle dakin.

"Sai Allah Ya sake dawo damu ni zan wuce" yace daga tsaye yana dan rissinawa Jume.

Maikudi ya tashi zumbur yana kallonsa, ita ma Jume ta juyo da kujerar da take zaune a kai yadda za ta fuskance shi da kyau.

"Zayyanu ni zaka wulakanta a gidan nan? In baka umarni saboda ba uwarka bace sai kasa kafa ka take. Kwana nawa ina sawa a dubo ko gidan Aminun ka makale babu kai babu labari sai yau. Shine har kake da bakin cewa zaka wuce."

Baya son ya kai ga yi mata abinda zai zo yana nadama nan gaba ga darajarta na matsayin wadda ta rike shi kuma matar babansa, da idan ya fada mata wata maganar ko hanyar da ya bi bazata so ta sake bi ba.

"Jume Kano naje biki ba maganarki naki ji ba"

Maikudi ya dawo kusa dashi ya miko hannu kamar wanda ya bawa ajiya "ina kudin da tace ka karbo a wurin wancan tsohon munafukin?"

"Yanzu aminin Baba kake kira munafuki?"

"Kaga kafin ka fara dogon surutu bani kudin ka wuce bana son rigima da al'murun nan" Jume ta fada tana kara tamke fuska.

Dago idanu yayi ya zube mata a kanta sai gashi jikinta ya yi lakwas. Rayyan da Badaru ma kowa ya sha jinin jikinsa. Maikudi ne kawai hankalinsa bai kai wurin ba.

"Jume!"

"Eyye" ta amsa a dan tosrace.

"Kudi dai gadona ne ni kadai kamar yadda a gabana aka bawa kowa nasa..."

"Kai, rashin kunya za ka yi mata a gabanmu?" inji Maikudi.

"Idan na fahinceka Zayyanu kudin ne ba za ka bani ba saboda ban isa in nemi abu a wurinka in samu ba?"

Tausayi ta bashi yadda ta hakikance akan rashin gaskiyarta bata ko tunani sai son bukatarta ta biya. Hannu ya zura cikin aljihun wandonsa ya zaro naira dari 'yan ashirin guda biyar ya mika mata.

"Ga wannan ku kara cefane" yace cike da nutsuwa, bai kuma jira cewarta ba ya fice waje inda Hadir yake jiransa.

Yana fita Maikudi ya warce kudin a hannunta yana jaddada mata tasan yadda zata yi ta karbo musu ragowar idan ba haka ba shine zaiyi ajalin Zayyanu sai ya ga ta inda zaiyi amfani da kudin.

"Banza shashasha to sai ka dawo, kafin kayi ajalin nasa shi zaiyi naka. Har mamaki kake bani yadda kake manta zuciyar Zayyanu da kuma kasancewara soja. Yanzu idan yasa aka kamaka duk duniya bana jin kana da wanda zai fito da kai. Nima kaina tsoronsa nake ji dan jakar uba, daurewa kawai nake ina masa barazana. Amma muje zuwa sai na dawo dashi tafin hannuna. Uwarsa ma mai suna kamar na tsuntsaye bata iya karawa dani ba"

**********

Sati uku da dawowarsu a tsukun lokacin iyayen Hadir sun zo daga Kano an daidaita maganar aurensa da Zainab. Kullum ya dawo ya ishi Zayyan da labarin hirarsu ko maganar biki. Ranar da ya bishi kuwa yadda ya kula suna son juna musamman Zainab da duniya bata ganin kowa da gashi sai Hadir sai yaji muguwar kewar Mairama.

Ranar lahadi ya samu da babu training sosai ya fita yaje ya sanar da Mal Aminu da mutum biyu cikin 'yan uwan mahaifinsa game da auren da yake nema. Sunyi farinciki da alkawarin bayan ya koma Kanon ya fadawa mahaifin yarinyar zasu je bayan sati daya da zuwan nasa. Godiya yayi musu ya nemi matar Mal Aminu mai suna Gwaggo Ladi matar da ta maye masa gurbin uwa wurin kulawa da bashi abinci da sauran abubuwa lokacin da kowa ya gane gashin kuman da Jume take yi masa. Kudade ya bata da yake so a fara siyayyar kayan aure ta yadda idan zasu tafi zasu je ne a shirye saboda nisa. [5/22, 10:51 PM] Sis Ruky: G *….TUN RAN ZANE*

Hakan take domin kuwa yau ne za'a kai amaren dakunansu. Dakin Yadikko aka tarasu Malamijo ya shigo zaiyi musu nasiha ta karshe safiyar lahadi. Kallonsu yayi daya bayan daya sannan ya juya wurin Yadikko.

"Me ake cewa ne idan za'a kai amarya?"

"Ko addu'a ai ka yi musu"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull