Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 4

Batuol mamman complete novel - Chapter 4

Batuol mamman complete novel Chapter 4: Batuol mamman complete novel Chapter 4. Hularsa ya turo gaba "abi miji sau da kafa shine shawarata gareku. Banda…

3,369 words

Hularsa ya turo gaba "abi miji sau da kafa shine shawarata gareku. Banda tsiwa ko rashin kunya sannan ayi ta hakuri. Duk wadda ta kaso aurenta babu abinda ya shalleni ah to. Allah bada zaman lafiya ku tashi ku tafi kada ayi dare Mairama tana da nisa. Birnin Shehu kwai dan karen tafiya daga nan kamar za'a ya da shege"

Wannan magana ma sai da ta taba ran Salame. Babu wanda ya damu da cewa ita ke son Zayyan har ake wani zancen nisan garin. Haka su ka fito suna ta kuka, kowacce da abinda take yiwa. Salame kukan rabuwa da masoyi take yi don tasan an riga an cuceta an rabata da Zayyan. Mairama kuwa kukanta bai wuce na rabuwa da 'yar uwarta da gidan nasu duk da ba dadinsa suke ji ba, sai kuma fargabar sabuwar rayuwar da zata fara.

Akori kura biyu ke biye da motocin daukar amaren na kayan dakinsu da aka samu Malamijo yayi. Gadaje daidai ne da saitin kujeru da kuma kayan kitchen. Gidan Salame aka fara tsayawa a Kofar na'isa babban gida ne mai bangare uku na Salisu da 'yan uwansa. Yadikko da Hajjo su ne zasu tsaya a nan ayi jere tare da 'yan uwan Ta Madina. Basuyi mamaki ba ganin har sunyi jeren katon gado a daki daya da kwaba da madubi masu kyau daidai da zamani wanda Ta Madina da 'yan uwanta suka yi. A falon ma sunyi mata kujeru manya da suka fi na wajen Malamijo an malale kasan da leda mai ado da ta dace da labulen da suka yi mata. Kayan da suka zo dasu wani daki guda aka nuna musu suka jera kujerun da gadon ya dauke su tsaf saboda ba wani yawa garesu ba.

Kannen Ta Madina suna aiki suna yabawa su Yadikko magana wai kudin Malamijo bai tsinana musu komai ba. To su din ma basu tanka ba tunda idan anbi ta barawo abi ta mabi sawu.

Dije da Inno su ne jagora a tafiya kai Mairama nata gidan. Yamma likis suka isa Allah Yasa ba wata gayya ce ba basu fi su biyar ba. Sanin cewa idan ya kaisu gidansu Jume sai ta saka shi jin kunya ya nemi alfarmar kanin babansa zai saukesu a gidan kafin su yi jeren. Nan su ka kwana ana ta tarairayarsu. Mami matar Captain Mustapha ita ma tayi abinci mai yawa suka je aka yi taro a gidan. Jume ko zuwa bata yi ba amma 'ya'yanta mata sun je suna ta yada magana wai kalen dangi ya guji nasa asalin. Haka nan 'yan uwan Mal.Muhammadu sun je da yawansu.

Da safe Hadir ne yaje daukosu aka kaisu gidan da aka bawa Zayyan a bangaren gidajen da suke cikin barikin. Daki daya ne kato da bandaki a cikinsa sai falo madaidaici da kitchen karami. Bata zo da komai ba sai iya kayan da Malamijo yayi mata. Anyi jere lafiya a daren aka kawo amarya dakinta su kuma suka koma Sumaila washegari.

Zaman Zayyan da Mairama abin burgewa ne da sha'awa ga duk wanda ya sansu kuma yake mu'amala dasu. Babu abinda ya rageta dashi ta fannin soyayya da kyautatawa. Ita ma a nata bangaren tana binsa sau da kafa da biyayya da tattali. Yanayin gidansu yasa ta iya girki bashi da matsala ta wannan fannin ma.

Satinsu biyar da aure Zainab ta tare matar Hadir. Mami dadi ya isheta ga hausawa 'yan uwanta a kusa duk da nasu gidajen suna bangare daban. Sunfi girma da kyau. Su Mairama kuwa layinsu daya da Zainab. Hade kai suka yi suna zaman gaskiya da bawa juna shawarwari. Mami ce babba amma Zainab duk ta fisu wayewa. Mairama kuwa dama albarkacin boko ta san wasu abubuwan amma kifin rijiya ce. Idan suna hira abin dariya, Mairama kana jin hausarta zaka gane bafillatana ce, Zainab sakkwatanci ziryan ita kuma Mami Hausar Katsina.

Yau juma'a Mairama tana cikin girki kafin dawowar Zayyan taji sallamar Awwab. Kowa yasan dan gidanta ne na gaban goshi. Zainab har ta gaji da mita ta kama kannensa Zahra da Fauziyya a matsayin nata.

Kitchen din ya shigo ya sameta tana yanka salad.

"Anti kawo in yanka"

"So ka ke Anti Zainab ta shigo ta soma tsokanarka ko" tace tana murmushi.

"Mami tace in gaisheki kuma zata zo kiyi mata kalba anjima"

"Kaje kace mata nace sai ta shigo sannan ka dawo ka ci abinci"

Fita yayi zai tafi ya ga ta biyo bayansa a guje ta shige bandaki tana kakarin amai. Awwab ya rasa me zaiyi sai kuka yana mata sannu. Ita ke fama da matsananciyar tashin zuciya da amai kamar zata fitar da kayan cikinta amma kuma ita ke bashi hakuri saboda yadda ya gigice mata.

"Awwab ka dena kuka mana" tace cikin rashin kuzari.

Kuka yake sosai "to ki dena aman"

"Na gama muje ka zuba abincin idan kaci sai ka tafi"

Kallonta yayi tana dafa bango tana daga kafa da kyar. Hannunta ya rike har kan kujera yace "In fadawa Mami ko Anti Zainab?"

Da sauri ta dakatar dashi "a'a kada ka fadawa kowa na ji sauki"

"To kiyi dariya in gani"

Dariya ya bata ya kafeta da ido wai tayi dariya. Motsin mutane suka fara ji daga waje ya tashi da sauri ya bude kofar. Zayyan ne da wani security soja sun kinkimo katon kwali ga wasu kwalayen biyu kuma a kasa daga gefe. Yana ganin Awwab yace ya je ya fadawa Mairama ta koma daki zasu shigo da kaya. Ta ji me yace kafin Awwab din ya dawo ta koma ciki ta kwanta.

Suna shigo da kayan ya fadawa Zayyan tana amai. Nan fa hankalinsa ya tashi ya bishi dakin bayan sun gama shigo da kayan.

A kwance take tana jin ya shigo ta tashi zaune.

"Mairam me ya same ki?"

Sai da ta harari Awwab ta bashi amsa "ulcer ta ce ta tashi tun dazu da na sha coke kirjina ke suya"

"Shine baki taba fada min kina da ulcer ba suk sati nake ajiye miki crate din minerals? To anyi an gama"

Bata da wata ulcer a iya saninta amma ta ki jinin asibiti. Kitchen din yaje ya zubo abinci.

"Nasan baki ci ba, tashi"

Wani aman taji ya taho mata daga ganin abincin ta daure "Awwab baici ba ka bashi zan ci anjima"

"Nima bazan ci ba sai kinci" Awwab din yace yana marairaicewa.

Zayyan ya janyo hannunsa ya zauna a kusa dashi da kyar ya samu ya karba yana ci yana mata hira.

"Kayi min kwacen mata kirikiri yaron nan"

Mairam ta soma dariya da Awwab ya dage sai ya fada masa me yake nufi. Sai can yamma ya tafi ya fadawa Maminsa bata da lafiya. Taso zuwa amma tunda Zayyan yana gida sai ta hakura sai gobe. Sai dare Zayyan ya bude kwalayen da suka zo dasu. Daya firinji ne madaidaici mai kofa daya amma da freezer daga sama. Sai kuma TV da bidiyo duka sababbi. Mairama godiya harda kuka don murna.

Bayan kwana biyu kullum tana fama da amai da jiri ya kaita asibiti aka basu tabbacin ciki ne da ita. Tamkar ya hadiyeta don farinciki. Gani yake yanzu zai sami abinda zai kira nasa, jininsa sosai.

**********

Lokaci yana tafiya al'amura suna faruwa garesu. Captain Mustapha ya sami karin girma zuwa mukamin Major bayan ya dawo daga wani aiki da aka tura shi Warri. Zayyan da Hadir kuma sun zama Lieutenants. Cikin Mairama yana da wata shida amma idan ka ganta sai ka rantse bazata kara kwana ba zata haihu. Su Mami sun gama sadakarwa 'yan biyu ne a cikin. Bata wani laulayi sosai sai cin abinci akai akai tayi bulbul ta sake kyau da cikowa. Kwakkwaran motsi idan tayi Zayyan ya rinka cewa yaya akayi. Zainab ma cikin gareta wata uku amma ita laulayi yake saka ta don bata iya komai yanzu sai kwanciya duk ta rame abin tausayi. Mazajensu na fita suke tarewa a gidanta su taimaka mata da aikin gida. Mami tayi ta kokarin hana Mairama amma bata ji, tafi ganewa motsa jikin dama kuma haka ake so ga mai juna biyu.

Yau litinin suna tare a gidan Zainab su Awwab suka dawo daga makaranta. Tun da suka ga gidan a rufe sun san inda Maminsu ta tafi sai suka bita. A falo suke zaune suna hira yau Zainab din jikinta da kwari ba kamar kwanaki ba.

Kowa yana cin abinci an hadawa yaran a tray karami na silver iyayensu su ma sun hada tare. Zainab ce ta kula da Awwab gabadaya idanunsa suna kan Mairama. Idan ta yamutsa fuska sai yayi kamar zaiyi kuka. "Awwabu ya aka yi ne kake ta kallon mamanka?"

"Anti baki ga cikinta ba kullum yana kato kamar na maman Ebere"

Mami ta tuntsire da dariya "kai kuma baka son cikinta yayi irin na maman Ebere din ne?"

Ya gyada kai "saboda fashewa zaiyi watarana, haka Ebere tace na mamansu ya fashe a asibiti."

Zahra ta kai masa bugu a kafada "Kai Hamma haihuwa zatayi fa mu sami baby" Hamma shine sunan da Mairama tace su rinka kiransa dashi don da fari Awwab kawai suke cewa.

Maminsu ya kalla a tsorace "kinji tana rashin kunya Mami, ni dai ba ruwana"

Tsokanarsa Zainab ta shiga yi tana cewa Mairama danta yakware a wautar 'yan fari. Da abun ya ishe shi sai ga hawaye Zahra da Fauziyya aka sami na yi. Mairama ta janyo shi kusa da ita.

"Kyalesu baby zan dauko maka a asibiti idan nawa cikin ya fashe kai kadai zaka rinka dauka."

Wata dariya ya saki da ta kara masa kyau da nuna kuruciyarsa yana murna, har da yiwa su Fauziyya gwalo. A haka rayuwarsu take tafiya komai nasu cikin aminci tamkar 'yan uwa na jini.

Ranar da nakuda ta kama Mairama Zayyan sun tafi gidan gwamnati shugaban kasa zai kawo ziyara. Nauyi da kunya ya sanya ta kasa fada masa tun gabanin asuba da ta fara ciwon har ya fita. Gashi abu yafi karfinta zamani ba na waya ba bare ta nemi taimako. Allah ne ya kawo mata Awwab tana cikin wannan matsanancin halin ta daure tace yaje gida ya kira Mami kuma ya tabbata ta taho yanzun nan. Ya kusa shekara tara a lokacin shiyasa duk da bata fada ba jikinsa ya bashi ba lafiya ba.

A guje ya koma gida sai gasu cikin mintuna kalilan. Tana ganinta tace ya fita ta shiga daki ta taimaka mata su fito kawai ta fara nishi. Mami ta san babu yadda zatayi tun da ta hango kai yana neman fitowa a take Allah Ya sako mata karfin zuciya ta karbi haihuwar santaleliyar yarinyar da Mairama ta haifa.

Tubarakallah yarinyar akwai girma da kiba taci ta koshi tun a ciki ga kyau. Kukan da ta chanyara ne ya sanar da gidan da yake jikin nasu an sauka. Matar gidan bayerabiya ce suna kiranta Maman Dolapo ta shigo da sallamarta domin su ma musulmai ne. Awwab aka tura ya kira Zainab itama tazo suna ta murna aka dora musu ruwan wanka. Yarinya tana ta wutsil wutsil kakkarfa da ita.

Mami girman yana gareta ita ta yiwa Mairama wanka. Jaririya kuwa Maman Dolapo ta roki alfarmar a barta tayi mata irin nasu na yarbawa. Babu wanda ya hana saboda zaman mutumci suke yi da ita. Sun kuwa ga wanka ba irin wanda suka saba ba. Ta wanke yarinyar nan sosai ga mamakinsu harda manja mai kyau ta dauko daga gidanta ta shefe jikin yarinyar ta mitstsiketa sosai sannan aka fara wankan da kyau ana fitar da datti da maikon manjan. Ko da ta gama yarinya kana tabata jikin nan subul ta kara wani haske kamar jini ya fito. Lallausan kayan sanyi aka sanya mata lokaci na damuna sannan akace Mairama ta bata nono. Nan fa ake yinta kunyar jama'a ko karbarta ta kasa. Zainab ta kamata ta maidata daki. Zata rufe mata kofa Awwab yayi kekam dole ta barshi ya bi bayan mamansa ana musu dariya.

Babu abinda makota basu yiwa Mairama ba. Daki ta shiga tayi kukan rashin dangin uwa da basu damu da ita ba. Da kanta ta nemi Zayyan akan bata son zuwa gida wanka saboda ta sani ba wata kulawa da zata samu. Bayan auren nasu sunje sau daya bata ji dadin gidan ba ko kadan. Wani kallo na kyashi ake watsa mata, Yadikko ce kadai mai janta a jiki. Malamijo kuwa zubar da girma yayi gaban Zayyan yana fada masa yadda yake cikin mawuyacin halin kula da iyali. Allah Yasa sunyo musu tsaraba irin ta Sakkwato amma duk da haka sai da ya bashi kudi. Kurewar lokaci yasa basu tsaya a gidan Salame ba. Abin da bata sani ba da gangan Zayyan yayi haka don ko kadan baya kaunar yadda Salamen take yiwa matarsa ita kuma bata gani. Ba su suka dawo gida ba sai daya saura na dare. Lokacin kowa ya watse hatta Mami ta tafi saboda yara sun fara bacci. Mairama da jaririyarta ma baccin suke jiki ya gaji ga wankan da suka sha. Ko ina a gyare tsaf gidan ya bude kofar dakin a hankali don kada ya tasheta ko fitila bai kunna ba. Kayansa ya cire yaje yayi wanka ya fito yana komai a nutse don baya son damunta. Duhun dakin yasa garin neman robar mai ya tunkudu wani abu daga kan madubin ya fado da karfi. Karar ce ta tashi baby din yaji ana inya inyaa.

Hanyar kofa ya nufa da fari ya ajiye sojancin na wucin gadi, sai yaji muryar Mairama tana cewa shhhh. Da mugun sauri ya kunna fitila idanunsa a kan gadon. Kyakkyawan gamo yayi. Masoyiyarsa abar kaunarsa ya gani tare da baby kunshe cikin shawul fari tas.

Zuciyarsa ce tayi wani irin nauyi ya tako gaban gadon a hankali ya zauna a gefenta. Murmushi ta sakar masa kafin ta dora masa jaririyar a kan hannuwan da ya miko mata. Rungumesu yayi tare yana fidda numfashi da sauri. Mairama sai ta soma hawayen farinciki ta kara shiga jikinsa yana yiwa baby addu'a. Sun dauki lokaci a haka kafin ya bude fuskarta tana tandar baki.

"Yunwa take ji ko?" ya kalli Mairama

Karbarta tayi ta juya masa baya zata shayar da ita ya hawo gadon ya zagaya gabanta "kada ki cuceni da kunya"

Ba yadda ta iya yana ta kallonsu cike da sha'awa kamar wani zai ce ba nasa bane. Bai iya tashi ba har ta gama ya ga babyn tayi bacci ita ma idanu sun fara rufewa.

Kwanciya ya gyara musu ya dauko darduma ya shimfida yana nafilar godiyarsa ga Allah. Duk gajiyar da ya kwaso ranar babu wani bacci da ya iya yi sai gadinsu har asuba tayi. A masallaci Major Mustapha da Hadir su ka yi masa barka tare da sauran abokan aikinsu ana taya shi murna. Papa Dolapo ya tsokane shi wai Allah Yasa dai ba mai kiriniya bane kamarsa akayi dariya.

Aikinsu bai kare ba zasu koma gidan gwamna. Kafin su tafi Major Mustapha da Hadir su ka je gidan ganin baby da kuma yi mata addu'a. Zayyan ya dan taba Hadir yana yi masa magana da ido. Ya san zancen shiyasa ya dubi Major din.

"Sir kaine zaka rada mata suna fa, kayi mata huduba"

Wani iri yaji yadda yaran nan suke matukar girmama shi tamkar yayansu na jini "wane sunan zan saka mata?"

Shiru Zayyan yayi sai ya koma ciki da sauri wurin Mairama a daki.

"Mairam bamu tsayar da shawarar suna ba ga Major can yana jira"

"Sunanta Alheran" tace tana gyara daurin zaninta.

"Nace sunan Innarmu ta Sumaila zamu fara sakawa"

"Don Allah Sojana sunanta Alheran, idan na sake haihuwa sai a saka sunan Innar"

Muhawara suke yi sosai ya gaji ya karbi nata "baki da wani suna da kike son a saka mata? Suna biyu nake son a saka"

Sarai ta fahimce shi, a dole yana son bata dama ita ma ta sanyawa yarinyar suna. Sai dai duk yadda take son saka sunan innarta tana ganin shi yafi dacewa da ya fara sakawa. Bata yi dogon tunani ba tace "Radhiya".

Murmushi kawai yayi ya fita ya sanar da Major sunan 'yarsa Alheran Radhiya Zayyan Muhammad Tureta. Hadir yace "mutumina wannan sunaye haka"

" 'Yar soja ce, ya kamata a komai ta fita daban" ya bashi amsa yana magana a hankali kada a ji.

Major Mustapha ya gama yi mata huduba sannan yace ya maidata ciki suyi shirin tafiya bakwai ta kusa.

Kwanaki hudu da haihuwa duk wanda ya kamata ya sami labarin haihuwa daga danginsu ya sani. Tasha Zayyan yaje ya bada sakon wasika zuwa ga Kawunsa Ghoumar domin a sanar da sauran dangi abinda aka samu. Sai wasikar ta isa akan gaba suna shirin zuwa saboda aurensa da yazo da gaggawa basu sami damar halarta ba. [5/22, 10:51 PM] Sis Ruky: F Sai da ya nemi izinin fita na kwana biyar, da kyar kuwa bukatarsa ta biya saboda ba kasafai ake son suna yin nesa da barikin ba. Ranar da zai tafi sai da ya bi ya sallama da Captain Mustapha. Yanzu alakarsu tamkar wa da kani ga kuma yaransa sun mayar da Zayyan uba na biyu. Shi Captain Mustapha asalinsa da Katsina ne daga shi har matarsa don auren gida ma su ka yi.

Asubancin fita yayi ya shiga cikin gari gidajen dangin Mal Muhammadu. Daga can ya wuce tasha sai Kano.

Yayi sa'a masu kilishi sun fito ya sayawa Malamijo. Shi dai a dan zamansu na farko bai hango komai a tattare da shi ba sai barkwanci.

Kwanakin da suka gabata Salame ta dami Mairama wai me ya hana Zayyan dawowa saboda Salisu ya matsa lamba kuma Malamijo ya riga ya bashi. Ganin akwai kudi yaron ya kara shiga ransa. Salame so take ta tabbatar Zayyan bazai dawo ba sai ta amince masa ko babu komai zata huta. A haka tana tsoron saurin amincewa ya dawo a bashi Mairama ita kuma ta rasa. Akwai ranar da ta tambayi Mairaman ko ta fadawa Zayyan yanayin gidansu.

"Kinsan boye-boyen babu amfani gara yasan wa zai aura kada Malamijo ya nuna masa hali"

Bata rai Mairama tayi "yau da kanki Adda Salame kike cewa Malamijo zai nuna hali? Ni dai soyayya bazata sa na kwashe sirrin gidanmu na kaiwa saurayi ba. Idan bai aureni ba shikenan ya gama sanin komai nawa. Kuma ko yaya Malamijo yake ai babanmu ne dole mu so a mutunta shi"

Waskewa Salame tayi amma a ranta tana ganin ta sami hanyar rabasu "irin wannan sharhi ba wani abu nake nufi ba, abar maganr dai"

Yau kamar daga sama sai ga dan aike wai ana sallama da Mairama inji Zayyan.

Wanka take yi lokacin ta gama aikin fura Salame ce taji sakon. Jikinta har bari yake tsabagen murna ta fada dakinsu da sauri. Kaya ta sauya da sauri ta shafa hoda harda janbaki ta sako daya daga cikin kayan da Ta Madina ta dinka mata. Komai da azama take kada Mairama ta fito ta sameta. Tazo fita ta koma ta cire mukullin sif din kayansu bayan ta kwashe duk wani kayan sawa ta saka a ciki ta jefa a karkashin sif din ta fita tana dariyar mugunta.

Bata yiwa kowa sallama ba don basa tsakar gidan ta fice zaure. Dama niyarta da an tambayeta ina zuwa tace wurin Innarta zata je.

Kamshin turare wanda Salisu ya kawo mata zuwansa na karshe ya fara ji kafin ya ganta. Ta gumbuda turaren sosai kuwa a ransa yaji dadi ba Mairamansa bace take wannan aika-aikan. Fuska ya saki yana mata murmushi. Ta sunkuyar da kai tana 'yar dariya don jin kanta take kamar yau take sallah saboda ganin Zayyan.

"Babban bakonmu barka da sauka, yaya hanya?"

"Lafiya kalau Saude ya mutanen gida"

Wani abu taji ya soki zuciyarta, wato ku sunanta bai rike ba. Bata nuna damuwar a fuska ba sai ma wani kasha murya da ta tsiri yi "Salame dai ko, baka ma rike sunana ba saboda baka damu dani ba"

Banbarakwai yaji zancen nata "Afuwan kada ki fadawa Mairama tace ta fasa na yiwa Addarta ko ince Addarmu laifi"

"Ba wani abu ai, ita ma bata soma fada ba yadda ta matsu tayi auren nan. Allah Ya dube mu, masu gudunmu saboda Malamijo zasu sha kunya"

Zayyan mutum ne mai saurin dago ina mutum ya dosa idan suna magana, yanzu ma tuni ya fahimci akwai abinda Salame take son fada masa tun hirar bata tsawaita ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull