Batuol mamman complete novel - Chapter 5
Batuol mamman complete novel Chapter 5: Batuol mamman complete novel Chapter 5. "Ban gane masu gudunku saboda Malamijo ba, ba babanku bane?"
3,372 words
"Ban gane masu gudunku saboda Malamijo ba, ba babanku bane?"
Hannu ta dora akan bakinta kamar gaske tana ware idanu "ba dai Mairama bata yi maka bayani ba? Irin haka ai da wuri ake fada saboda toshe matsala don kada kaji a waje. Idan na koma zan fada mata gara ta sanar da kai komai da wuri zai fi. Sai ka danyi hakuri ta gama aikin furar sayarwa ne ta shiga wanka"
Wai shi za ta jawa rai, kawar da kai yayi abinsa yana kallon waje. Haka nan bata yi masa ba tun haduwarsu ta farko a gidan Gwaggonta da akayi bikin yaranta. Sai tayi ta wani kifi-kifi da idanu amma sau goma idan zai dago kai sai sun hada ido.
Yanzu da ta ji bashi da niyar tambaya sai ta sake salo. Jan hanci yaji tana yi alamun tana kuka. Dawo da hankalinsa yayi gareta da sauri.
"Ya dai?"
Goge hawayen da ko digonsu babu tayi sannan ta dan tabe baki duk yana kallonta "gara kawai na fada maka don abin zai yiwa Mairama nauyi"
Halin Malamijo kaf da yanayin zamantakewar gidansu ta kwashe masa. Hatta dangin mahaifiyar Mairama sai da ta kwancewa zani. Jinjina kai kawai yake yi yana kara tausayin Mairama sosai. Yanayin rayuwarta kusan daya da tashi wato dukkansu basa jindadi a gidan iyayensu.
Salame sai ta dauki sauyin yanayinsa a matsayin tarkonta ne ya fara kamu ta dan murmusa "nasan rashin dangin uwa lokacin aure a kusa da ciwo….." ta dan ciji labbanta "…uhmmm ni kaga dangin Innata suna garin nan kuma bikin da muka hadu ma nasu ne, Mairama kara kawai aka yi mata"
Yanzu ya gama gane manufar wannan dogon sharhin. Kaurara murya yayi ya hade rai "Salame!...."
Bai karasa maganar ba sai ga Mairama ta fito da sassarfa sanye da kayan da tayi aikin furar ta makale a bayan kyaure.
"Adda" ta kira Salame tana kunyar fitowa.
Zayyan ne ya amsa yana mai jindadin ganinta "Mairam yau a nan zamuyi tadin?"
Kai ta sunkuyar ta sake yafito Salame sai kawai tayi gaba abinta ta fice don tasan me take nema. Kusan minti goma tun bayan fitowarta take ta neman mukullin sif din bata gani ba. Baki ta saki ganin ta fice bayan tasan kiranta take. Duk sai taji ta muzanta saboda Zayyan ma ya gani kuma baiyi mamaki ba duk da bai san me take bukata a wurinta ba.
"Nima in zo bayan kyauren ne?"
"A'a ina zuwa don Allah kaya zan sauya"
Hannu ya daga ya dakatar da ita "dawo abinki nima nan kayan jikina sun sha wahala da kurar hanya amma na kasa hakuri ko masauki ban nema ba nayo nan"
Jikinta ta kalla musamman zanin taji babu dadi. Zayyan ya matsa mata akan ta fito ba zai dade ba sai dare zai dawo. Busu-busu haka ta fito kayan jikinta masu saurin nuna datti ne dama saboda haskensu.
Kanta ta sunkuyar tana kallon kasa ta gaisheshi ya amsa fuskarsa a sake. Lura yayi a takure take sai ya mika mata ledar kilishin Malamijo yace ta shiga gida sai anjima zai dawo.
Yana tafiya a hanya amma zuciyarsa ta fada kogin tunanin kalaman Salame da kuma yanayin da ya ga Mairama. Yana da yakinin Salame ko dai tana son sa ko kuma kawai bata son cigaban kanwarta ne. Ko ma meye zaiyi kokarin sanin wacece Mairama Ali kafin ya koma bakin aikinsa.
A cikin gidan kuma Mairama sake komawa tayi neman mukulli har ta hada gumi amma ta rasa ina ya fada.
Da ta gaji da nema ga rashin sanin ina Salame ta tafi sai kawai ta cire kayan jikinta taje ta wankesu. Dije ce ta kasa hakuri tace mata me take yi da daurin kirji ta fada mata bata ga mukulli bane.
"Kin tambayi Salame?"
"Ta fita"
"Taje gidan uban wa?" suka ji Malamijo ya daga murya yana fada.
Tsoro taji da tasan zai shigo gidan a lokacin bazata fada ba.
Tsawa ya sake yi mata "baki da baki ne?"
Da ya ga bata da niyyar amsawa saboda rashin sani da kuma kokarin rufa mata asiri sai ya mayar da akalar tambayar ga Dije.
Hannuwa ta yarfe "ina dakina ina zan sani, dama tunda yaron nan mai kudi ya fara zuwa daga birni naga take takenta so take tafi karfin kowa"
"Babu mai fin karfina a gidan nan, idan ta dawo a turo min ita inji da izinin wa ta fita"
Zai shiga dakinsa Mairama tayi saurin dauko masa kilishin "Malamijo gashi yace na baka"
Ledar ya karba da sauri yana lekawa. Ganin kilishi yayi gari guda ya soma dariya "soja yazo kenan Mairama"
Kanta ta kawar gefe tana murmushi ya bantaro mai dan girma kamar tafin hannunsa ya mika mata
"gashi kema ki taba, ko ya baki?"
Sai da ta karba din tace masa nasa ne kawai. Dije tuni yawu ya tsinke tayi kasake tana jiran ya bata amma sai ta ga bashi da niyya.
"Bani nawa mana zan fara aikin tuwo ne"
Harararta yayi yana kanne ido "iyayen kwadayi ungo kafin a tara min taragutsan nan su fara min kallon nama"
Wani dan guntu ya bata ta jefa a baki a kan idon Hajjo. Fitowa tayi itama tana bata rai "ko a bani ko na gayyato jama'ar gidan nan"
Bashi da zabi haka ya dangwara mata a tafin hannunta. Jefashi tayi duka a baki sannan ta daga murya tace kowa ya fito Malamijo yana rabon kilishi.
Ai kan kace kwabo sun soma taruwa mutum kadan ne basa nan. Malamijo kamar ya hadiyi zuciya haka ya rinka yafita musu yana badawa ba da zuciya daya ba.
Ana tsaka da kiran magariba Salame ta shigo gidan. Can wurin Ta Madina da taje bacin rai kawai ta karo don sosai take fushi da ita har yanzu saboda abinda tayi mata a Kano. Sallama tayi a dakin Mairama ta amsata ciki-ciki. Tsaki ta doka ta ajiye gyalenta ta fita yin alwala. Bayan tayi sallah ne Mairama ta tambayeta ko ta ga mukullin sif din.
"Ajiya kika ban ko me?"
Zuciya ta soma cin Mairama saboda ta tabbatar dazu da gangan Salame ta fita duk da tasan kiranta take yi. Wai ma me ya kaita wurin Zayyan din.
"Shikenan"
"Shikenan me?"
Maimakon amsar fatar baki sai gani tayi Mairama tasa iyakar karfinta tana jijjiga kofofin sif din tana neman ballesu. Da saurinta ta mike don ta dakatar da ita.
"Meye hakan?"
"Dame yayi miki kama? Balleta zanyi tunda mukullin ya bata in nemi kayan sawa"
"Saboda saurayinki zai zo?"
Salame tace da kaushin murya.
"Adda Salame idan wani abu nayi miki ki fito fili ki fada min amma ba ki zauna kullum kina jin haushina kina min tsaki ba. Kin sani wallahi ba don ke Addata bace …."
"Sai ki dakeni ko ba haka ba"
Wata fuzga ta kaiwa kofar sai gata ta bude ta dauko kayan da zata saka bata sake kula Salame ba. Gefe ita ma ta koma tana ta hucin kishi ganin yadda Mairama ta zage tana kwalliya saboda Zayyan.
"Aikin banza ki gama adon yace ya fasa tunda yanzu yasan daga wane irin gida ki ka fito."
A tsorace ta waiwayo "fada masa kika yi?"
Salame sai ta tsame kafarta tayi waje. Tana zaune tana jira a raba tuwon gidan na al'ada a bata nata Mairama ta fito bayan an fada mata dawowar Zayyan. Da tazo wucewa tana jin uban tsakin da Salame taja har sai da Dije ta soma sababi ko da ita take.
Hira suka yi cikin nutsuwa rabi duk shi yake maganar saboda kunya irin ta Fulani. Tana son tambayarsa game da abubuwan da take zargin Salame ta fada masa amma ta gaza. Kamar ya sani kuwa da kansa ya shiga bata labarin asalinsa da rayuwarsa ta baya zuwa yanzu. Tausayinsa taji har idanunta su ka ciko da kwalla.
"Bana so yanayin rayuwar gidanku ya sanya ki fara tunanin zan gujeki ko hakan zai shafi zamantakewarmu. Gidajen da muka fito daban, sannan gidan da zamu samarwa kanmu da 'ya'yan da nake burin ki haifa min shima daban."
Tamkar kasa ta zage ta hadiyeta taji saboda kunyar kalaminsa na karshe. Da dabara ya samu ya rinka kwantar mata da hankali da kwadaita mata irin tanadin da yake mata idan ta zama mallakinsa. Ba shi ya bar gidan ba sai tara da rabi na dare. Washegari ya sake zuwa kuma a ranar ne ya sanar da Malamijo zuwan kawunnansa idan ya koma.
"Abin da nake so da kai shine ka fada musu su taho da sadakinsu ayi komai a kare. Yaran nan sun zaunu babu dalilin ayi ta jan lokaci. Budurwa kamar Mairama ta bawa shekaru shatakwas baya harda watanni ina kallonta tana kallona. Ga yayarta ita ma zan fadawa yaron nan Salisu sai ayi a lokaci guda"
Dadi maganar ta Malamijo tayi masa yayi na'am da ita. Ana gobe zai koma yana jiran fitowar Mairama sai ga Salame da ta shiga tashin hankali sakamakon gabatowar aurenta da Salisun da bata so. Hanyar waje tayi a daidai inda yake zaune ta jefa masa takarda ta fita. Ba nisa tayi ba tana layin bayan gidansu tana jiran ya karanta wasikar yazo ya sameta.
Layuka kadan ya karanta inda take sanar dashi son da take masa da kuma jiransa da take a bayan layi idan ya amince yazo ya sameta. Mairama ce tayi sallama sai kawai ya yayyaga takardar ya dunkuleta a hannunsa.
Sun jima suna hira yana fada mata haduwarsu ta gaba ta zama tasa tana dariya a hankali Salame ta dawo kamar kububuwa. Ta kwashi awa guda da doriya tana jiransa bai zo ba. Yanzu da ta shigo takardar hannunsa ya watsa a iska ko kallonta baiyi ba. Zuciyarta kamar za ta fashe saboda bakinciki ta wuce ciki.
Bahaushe ma yasan babu wanda ya isa ya sauya kudurar Ubangiji ga bayinSa shiyasa mu kan ce wai tun ran gini….Bayan duka wasu shirye shirye da hassada daga bangaren 'yan bakinciki irin su Jume da 'ya'yanta da kuma Salame mai son maso wani, da azahar din wata asabar aka daura auren Zayyan Muhammad Tureta da Mairama Ali Gidado. Sai kuma Salisu Lawan da Ummusalma Ali Gidado. Kowacce cikinsu angonta yayi bajinta gwargwadon aljihunsa ya yi mata kayan lefe. Ko ba'a fada ba kayan Salame sun kere na Mairamu duk da Zayyan din ma baiyi kasa a gwiwa ba, amma a haka Salame ta dauko ido ta sakawa kayan Mairama a ganinta da ita su ka fi dacewa. [5/22, 10:51 PM] Sis Ruky: I *KANA NAKA…*
Shirye shiryen tarbar bakin da zasu zo suna ya kankama. Zayyan ya dage a gidan mahaifinsa za'ayi taron duk da cewa kawunansa da Mal Aminu sun ce gara ya yi a nasu saboda gudun bacin rai da ga Jume ko 'ya'yanta. Ya riga ya gama tsara yadda zai bi da su domin gujewa hakan. Gidan yaje har daki ya same ta ta hakimce tana taunar goro.
"Hutawa akeyi ne Jume? Kawarki tana gaisheki"
Tabe baki tayi tana kallonsa ya zauna a kan yagaggiyar ledar dakin "kawarsu dai wadanda aka haifawa. Ni a su wa kuma?"
Basarwa yayi ya tankwashe kafafu "dama alfarma nazo nema, ina son ayi taron sunan a gidan nan ne"
"Dama jiranka nake naga iya gudun ruwanka tun da aka fara shigowa da bokatan fenti dazu. Ita matar taka basu da dangi ne da bazata koma gidansu ba? Naga haihuwar fari ce, ya dace ace tana gaban iyayenta. Tsabagen rashin ta ido ka barta a gidanka kuna kwana daki guda."
"Cikin masu zuwa sunan akwai matar babanta da zata zauna har ayi arba'in tare da ita. Ni zan koma wani gidan a cikin barikin kafin su gama"
Maikudi ne ya shigo fakam fakam ya sami guri ya tsaya ayi zancen dashi. Zayyan ya sake fada mata yana son sauke baki da ga Nijar da kuma mutanen Sumaila a gidan nasu tunda babba ne.
"Ince ko ka ga nayi kama da baiwar gidanku da zan zauna tarbar baki. Kaga Zayyanu tun wuri ka san me kake ciki da bakinka"
Murmushi ta ga yayi maimakon ya tashi ma sai ya gyara zama "to babu matsala zan yiwa su Kawu magana. Sai abu na biyu nace idan an kawo kudin rakuman wace sana'a Maikudi zai fara?"
A tare su ka taso masa kamar zasu zaune sh. Maikudi ya zauna a gefensa yana fara'a kamar gonar auduga, hakansa zai cimma ruwa. Jume ma sai ta saki fuska kamar ba ita ba.
"An sayar da rakuman naka ne?" Maikudi ya tambayeshi da zumudi.
"Eh, zasu taho min da kudin, jibi nake sa ran isowarsu" ya bashi amsa.
Sai ga Maikudi ya tashi jiki na rawa "Bari na kira yayyenka malalatan banza su zo a fara gyara gidan nan, mu gidanmu da yake da wadatar dakuna kamar ramin bera, Jume yaushe zaki ce sai ya nemi su Kawu don iya tonawa kai asiri"
Matsowa tayi kusa da Zayyan tana dariya "shima yasan wasa nake yi masa. Ka nemi masu fentin su zo ayi a gama da wuri sai a share dakunan ayi shimfida."
Mayar da kansa wawa yayi suna ta bidirinsu yana biye musu. Maikudi da son banza harda cewa an hutar dasu yin fenti tunda su ma baifi wata uku ya rage dukkansu su ukun zasuyi aure ba.
**********
Cikin ikon Allah baki sun iso an kaisu masauki, washegari za'ayi taron suna. Zayyan ya wadata iyalinsa da duk abin da ya dace. Wani hadin kai da ga bangaren sojojin su ma sun hada masa gudunmawa sannan matayensu sun zage dasu ake komai kamar yadda su ka saba idan dayarsu ta haihu ko wani taro ya tashi. Salame da Nene Marka kanwar Malamijo a gidan zasu kwana sauran kuma duka suna gidansu Zayyan. Su Nene sun riga isowa ga yamma jama'ar gidan sun watse sai ita da Mairama da Zainab. Mami ta wuce gida Fauziyya tana fama da zazzabi. Salisu na tsayar da mota a harabar gidajen da suke jere a wurin ta fito da sauri gabanta yana faduwa ta barshi yana yiwa security din da yayi musu rakiya zuwa gidan godiya.
Ciki ta shige tana fatan yin tozali da Zayyan. Sai dai idanunta akan na Mairama su ka sauka tana shayar da jaririyarta. Wani kululun bakinciki ya taso ya tsaya mata a wuya. Mairama tayi wani mugun kyau ta ciko ko ta ina. Kallo daya zaka yi mata kasan cewa hankalinta a kwance yake. Da sauri ta cire yarinyar da ga bakin abincinta ta tashi ta fada jikin Salame tana murna da tsalle sai da Yadikko tace tayi a hankali saboda yanayin jikin haihuwa.
"Wayyo Adda Salame nayi kewarki sosai ashe kina hanya. Ina yayan namu?" Da kyar ta amsa "yana waje, ki tura mijinki ya bashi masauki"
Tsabar murna duk ta rude ma tayi hanyar daki neman mayafi sai ta jiyo muryar Zayyan din suna magana da Salisu. Salame cikin zakuwa ta juya "bari naje mu gaisa da angon karni"
Nene ce ta dakatar da ita "wa yake ta angon karni baki ga 'yar taki ba, dawo kiyi zamanki nasan zasu shigo"
Ba haka taso ba amma dolente ta zauna. Mairama ta gabatar da Zainab wadda ta tashi tana tayata hadowa su Salame abinci da sha.
Daga nan Zainab din tayi sallama ta tafi Yadikko kuma ta shiga wanka. Baby tana kwance akan wani bargon yara mai kyau Mairama ta sake komawa kitchen ta soma kuka. Har wannan lokacin Salame dama bata yi karar cewa a bata ita ba bare ta dauketa saboda bata ma son ganinta har ranta. Kukan ya tsananta Mairama tana ji ta kasa cewa ta dauketa tunda ai ba kurma bace sannan tana jin nauyin ta fito ta dauketa a ga tayi rashin kunya.
Nene tana da ga bandaki kukan ya isheta tana tunanin me ya sami yarinyar. Harara Salame ta jefa mata sannan tasa hannu tana dan taba gefen jikinta wai rarrashi. Daga sama ta bayan kujerar ta ga an zuro hannuwa an dauketa.
Waigawa tayi da sauri idanunta su ka gane mata Zayyan Tureta. Sanye yake da khakinsa ya zura hularsa cikin wani abu da aka yiwa maballi daga kafadar rigar. Yayi matukar kyau da haske aure ya sake gyara shi. A kafada ya dora 'yarsa yana shafa mata baya.
"Waye ya taba min mamana? Sojoji basa kuka fa 'Yar soja"
"Zayyan ina wuni?" Salame tace cikin sanyin jiki. Bata san zai shigo ba da ko don ta burge shi ta dauki 'yar. Tamkar bai ga mutum ba ya shareta ya shiga kwalawa Mairama kira. Tana tsaye dama daga kofar kitchen din duk abinda Salame tayi ta gani tunda kujerar ta bata baya ne. Mamakin wannan mummunan canjin daga 'yar uwarta take yi. Ashe ko me ya hadasu tun kafin suyi aure bai kare ba har yana son shafar 'ya'ya. Hawaye taji ya soma sauko mata tana kallon bayan Salame a inda take zaune kamar gunki saboda yadda taji kunyar abinda ta yiwa jaririyar a gaban babanta.
Hawayen nata Zayyan ya gani ya matsa gareta da dayan hannun da yake shafa babyn ya janyota jikinsa da karfi ya rungume da hannu daya.
"Kada na sake ganin kin bar min yarinya ita kadai a falo. Idan babu kowa ki goyata ki shiga kitchen din…kinji"
"Kayi hakuri baza'a kuma ba, na ga Adda tana wurin ne" tace tana karbarta daga hannunsa. Salame ta juyo kamar mai ciwon wuya tana neman kalaman wanke kanta.
Kamar bai ji ba sai cewa yayi "Taimaka ki hada min abinci da zan tafi dashi inda zamu kwana da Salisu. Zan kaishi yayi sallah da wanka na dawo na dauka. Amma ki fara cikawa wannan sojar ciki"
Hannunta daya ta dora a gefen ido tayi masa salute "Yes Sir"
Matsowa yayi yana neman sumbatarta ta goce tana dariya. Mutuwar zaune Salame tayi. Shi kuwa Zayyan da biyu yake yi don ji yayi ya kara tsanarta. Ba don ta hada jini da Mairamansa ba da sai ya saka ta a guardroom ko na sa'a daya ne ya huce kukan 'yarsa.
Da ya fita Mairama ta kawo mata sauran kayan abincin batare da ta sake yi mata magana ba ta zauna bawa 'yar nono.
"Ki kwashe ba ci zanyi ba don yanzu ba komai ke zauna min a ciki ba"
Wai nan so take ta sanar da ita itama tana da cikin. Sai Mairama ta gwada mata halin matar soja da ta fara koyon yadda yake juya zance musamman idan ya fuskanci abu kake son sanar dashi da dabara don ka bashi haushi. "Adda yaya hanya? Ya zaman Kano?"
Sai da Salame ta kara kallonta irin baki ji me nace dinnan ba sannan ta chanja zancen tace lafiya. Zaman kurame su ka koma har Nene ta fito tana tambayar me ya sami baby dazu take kuka. Babu wadda ta amsa mata a cikinsu duk sun daure fuska sai ta kyale su ta sa tv a gaba tana kallon tashar NTA.
Zaman ne ya ishi Salame ta tashi ta shiga daki wai zata yi wanka. Mairama ta bi bayanta taji ko akwai abin da zata bukata. A tsaye ta sameta tana karewa dakin kallo tana tabe baki.
"Af...ke fa gadon da Malamijo yayi mana dashi aka kawoki ko? Amma naga labulayen kamar sababbi ga TV ma a falon da firij. Kin fara sana'a ne ko Zayyan din kike tatikewa?"
"Yo Allah na tuba Adda mace da mijinta har sai kinji yaya ake kudi ke fita har a gyara mata gida? Dadin zama ne kawai da iya tafiyar da miji"
Ta fadi haka ne saboda gorin da Salamen ke shirin yi mata. Ita kuma Salame sai ta dauka cin fuska ne ko ta gane ta son sa.
"Ki dai bi a hankali maza basu da tabbas. Canja mace a wurinsu ba wata tsiya bace"
Zaro idanu Mairama tayi da mamaki. Har fatan aurenta ya mutu kuma Salame take yi? Indai haka ne dole ta kama kanta don bata ga me ta tsare mata ba da take nuna mata hassada irin haka. Kowa ya shaida mijinta yana da kudi ta rasa gane bakincikin na meye.
Karfe goma na safe a gidansu Zayyan tayi musu. Anyi taron suna na kayatarwa don Zayyan ya sakar musu yadda zasu fita kunya. 'Yan uwansa mutan Agadas sunyi masa halacci duk da rashin mahaifiyarsa sun zo da yawansu tare da gudunmawa mai yawa. A cewarsu basu sami bikinsa ba dole a fanshe yanzu. Gashi jaririya ta gaji sunan 'yar uwarsu.