Batuol mamman complete novel - Chapter 6
Batuol mamman complete novel Chapter 6: Batuol mamman complete novel Chapter 6. Mutan Sumaila ma sun sha kallo ganin irin suturar da Zayyan ya wadata…
3,360 words
Mutan Sumaila ma sun sha kallo ganin irin suturar da Zayyan ya wadata Mairama da su na fitar suna. Abin nasu ya burge sosai musamman da wata kanwar innar Zayyan ta kawo kayansu na gargajiya na kabilarsu ta Tamasheq ta bawa Mairama.
" 'Yata ga wannan ku saka ke da maigidanki da jikarmu ayi hoto. Dashi nake son tafiya saboda wadanda basu zo ba su ganku."
Mairama sai godiya take su Zainab suna tayata. Riga ce fara kamar buba ta zarta gwiwa da kadan gaban ta sha aiki da shudin zare sai zani shudi. Ga kuma sarkoki da yari duka irin nasu da abubuwan sakawa a ka. Mami ce ta karbi Radhiya yayin da wasu 'yan mata biyu kusan sa'annin Mairama su ka ja ta dakin da su ka kwana. Da taimakonsu ta shirya komai su suka yi mata. Abin hannu da na wuya da kunne harda hanci kowanne yayi mata cif. Na gashin kuwa sai da daya ta yi mata kalba kananu guda uku-uku a gefe da gefen kunnenta ta zubo mata dogon gashin irin nasu sannan aka dora mata shi ya zauna daga gaba kai kace wata sarauniya ce. Hatta fuskarta kwalliyarsu aka yi mata leben nan ya sha fenti yayi baki. Da yake fara ce ba karamin kyau tayi ba ta saje dasu. Wata guda ta soma ji daga tsakar gidan aka dora mata shudin yadi irin na zanin wani irin yafawa yadda suke yi sannan su ka rike mata hannuwa aka fito da ita.
Turus tayi ga wata irin kunya kamar sabon aure da su ka hada idanu da Zayyan. Yayi kyau har bata san yadda za ta kwatanta ba. Shima kayan gargajiyar ne a jikinsa na ciki farare babbar rigar da kuma rawani duka shudi.
Kanta a kasa shi kuwa ya zuba mata idanu, manya cikin 'yan uwan nasu suna ta guda. Da shirinsu suka zo da sunan yi masa nasu bikin. Taro ya kayatar da jama'a ba kadan ba duk da iyakarsu cikin gidan. Salame tamkar ta bude ido ta ganta a matsayin Mairama. Ganinsa cikin wannan kaya ba karamin sake fama mata ciwon son sa da yake nukurkusarta yayi ba.
Mai hoto aka kira yazo akayi ta dauka. Gwaggon Zayyan tace suyi su uku zata kai hoton gida. Days suka dauka a tsakar gidan a tsaye tana rike da Radhiya shi kuma a gefenta. Dayan kuwa dakin Innarsa yace su shiga a kan tsohon gadonta ya zauna da 'yarsa a hannu ita kuma a kusa dashi. Daga nan ta kira danta Awwab ta dora masa kanwarsa tana tallabe da kanta daga bayansa ta dan duka aka yi musu sannan Zayyan ma ya shiga.
Ranar idan ka gansu dole su baka sha'awa. Mutan Agadas har irin abincinsu sun dafa duk na bikin dansu Zayyan da murnar haihuwar Alheran Radhiya.
A gidan maijego ta kwana ranar tare da danginsa ana ta bata labarin 'yan uwansu da irin yawan danginsu. Gwaggon Zayyan tace mata cikin gurbatacciyar hausarta da ace Zayyan ba soja bane gida Nijar suka so komawa dashi bayan rasuwar Mal Muhammadu.
"Idan ya sami saukin aiki ku kawo mana ziyara kinji Mairama. Zayyan dan gata ne saboda yana zagaye da dangi masu kaunarsa saboda maraicin uwa. Da mahaifinsa ya amince min naso tun rasuwar Alheran na dauke shi."
Hawaye ta ga dattijuwar tana gogewa shiyasa taji zuciyarta ta karye "In sha Allahu zamu zo"
"Allah Ya nuna mana"
Mairamu a ranar tayi kwanan farinciki da bakinciki duka lokaci guda. Soyayyar da ta samu daga wurin dangin mijinta ta tsaya mata a rai tayi matukar farinciki. Sai kuma tunanin dangin Innarta da babu wanda zata iya nunawa tace nata ne ta wannan bangaren. Sun manta da ita da shafin rayuwarta saboda rashin uwa da tsanar da suka yiwa Malamijo akan rikon sakainar kashin da ya yiwa 'yar uwarsu a gidansa.
Asubar fari aka fara tashi saboda masu shirin komawa. 'Yan Sumaila ne farkon tafiya aka bar Nene zata zauna wanka idan sunyi arba'in su tafi Sumailan tare. Mutan Agadas ma kaf sun gama shiri wai basa son dorawa Zayyan nauyi idan suka cigaba da kwanaki. Kawunnansa biyu ne a cikin tawagar Ghoumar da Sidi. Shatara ta arziki suka yi masa kyautar kudi da irin abin amfani nasu na can. Kamar kada su tafi haka Mairama taji har kofar gidan inda bus guda biyu zasu daukesu tayi musu rakiya.
Daga nan gidanta ta koma tare da Yadikko da Salame su ma a ranar zasu wuce.
Manya akwai kaifin tunani da hangen nesa. Cikin kankanin lokaci Nene ta gane manufar Salame akan Zayyan. Tasha mamaki ba kadan ba saboda a da tana yi mata kallon wadda zata iya sadaukar da komai domin farantawa kanwarta. Ashe abin ba haka yake ba. Ta ciki na ciki ne. Jan bakinta tayi ta tsuke bata tona ba sai dai ta jasu su biyun tayi musu fada akan sabon yanayin alakarsu.
"Nene gara da ki ka kula, ki tambayeta idan na mata laifi ne na bata hakuri"
Kallon Salame Nene tayi ta dauke fuska tare da janyo jakar kayanta tana shan kunu.
Nene tace "Salame idan ma da sabani na kula kece kike jansa. Tun zuwanki ina lura dake ko da wasa wallahi baki dauki Radhiya ba."
Saurin kallon Mairama tayi don kuwa hakan ne. Mairama tuni ta gane shiru kawai tayi.
"Nene bana jindadi tunda nazo garin nan shiyasa. Mairama Allah Ya baki hakuri...shikenan ko" tace a kagauce tana son fita daga dakin.
"Juna biyun shine zai sa ki kasa daukar 'yarki? Ki dai yiwa kanki fada don rayuwa bata da tabbas"
Mairama bata ma tanka ba ganin za ta rana musu wayo. Da zasu tafi Salisu ya kawo kudi ya bayar a sayawa Radhiya kaya harda cewa inji mamanta Salame. Godiya suka yi masa sun san kuma kara ce kawai yayi amma babu wani inji Salame.
Sun shiga gidan Nene ta goya Radhiya ta shige daki wai garin akwai sanyi. Ga gida mai daki daya tana rufo kofar Zayyan ya rungume Mairama harda ajiyar zuciya.
"Na wahala Mairam, na wahala sosai"
"Taron jama'a ko?" Tace tana kokarin kwace jikinta kada Yadikko ta fito.
"Wane jama'a, a kaina suke? Rashinki ne ya addabeni."
Murmushi tayi ta sunkuyar da kai ya dago habarta "dadina da mutum kunya. Yaci ace mun wuce wannan matakin fa, ga 'yar soja can kina gani"
"Ni dai kazo ka tafi kada ta fito ta sameka"
"Kin yarda zaki yi min irin kwalliyar jiya idan ta tafi?"
"Na yarda"
Rungumeta ya sake yi sosai "Ina sonki Mairam, shigowarki rayuwata ya sanyani farinciki mara misaltuwa. Karo na farko naga da dangin Innata su ka zo da yawa haka saboda ni. Kuma duk a dalilinki ne da kyautar Alheran da kika yi min. Nagode"
"Ina fatan Allah Ya bani ikon cigaba da kyatata maka Sojana. Kayi min komai a rayuwata. Ka rabani da kunci da bacin rai. Ka zame min miji, aboki kuma dan uwa"
Kashe mata ido yayi "ina ma daga ni sai ke a gidan nan kike wannan kalaman"
Ta gano manufarsa ta shiga dariya a hankali. Kofar dakin aka taba ya tashi a guje ya fice ita kuma ta dake fuska kada Yadikko tace me suke yi. [5/22, 10:51 PM] Sis Ruky: H **********
"Kasan Allah Malamijo idan naje Sakkwato haka zikau Allah shi tsinan"
Fuskarsa a murtuke kamar zai kai mata duka ya tashi daga kwanciyar da yayi " wai ni dake waye ya haifi yarinyar nan ne eyyee?"
Yadikko ta galla masa harara "kaine ubanta wanda na sani da ana sakewa wallahi bana jin ko tsinken ashanar gidan nan zai so a alakanta shi da kai. Me kake yiwa yaran bayan haihuwarsu? Nan haka muka kaita gidan miji abin kunya babu wani kayan arziki wai kuma 'yarka ce, kai da garin nan kowa ya shaida arziki gareka"
"Sa ido, sa ido…kowa zaiyi ya bari tunda ba da uban mutum muke kiwon ba"
"Ba sai ka zageni ba, gaskiya ce dai dole na fada maka. Mairama baka fitar da ita kunya da biki ba dole kayi bajinta ita ta fara kawo maka jika a gidan nan. Ka kuma hada da gara tunda ba'ayi musu komai ba da bikin. Salame ba don mahaifiyarta tana kusa ba itama da haka za ta tare ba garar"
Malamijo ya mike yana kada hannuwa yana kumfar baka saboda an bukaci kudi "garo ba gara ba, idan sai na bada kudi kunyi mata gara zaku je don Allah kuyi zamanku na yafe. Yo dangin uwarta ma suka bace bat a doron kasa basa waiwayarta tunda ta rasu balle ku"
"Laifin waye to idan bana ka ba? Kowace mace ka gani kana so saboda zalama. Kuma ba dole su bace ba. Kayi auren biyan bashi tana haihuwa kace ka saketa kuma sai sun biya rabin kudin. Tsoro yasa sun gudu bakinciki kuma ya kashe yarinya karama ta bar marainiya"
Yadikko kin hakura tayi sai da kyar da sudin goshi Malamijo ya bata dubu uku da kuma tinkiya guda daya "gashi nan a tafi a kaiwa 'yar kunama kafin na fara ganinki cikin bacci na. Ke dai da mayya ce da tuni na dade a tukunya"
Warce kudin tayi a hannunsa "fadi ka kara, aradu da ina maita da tuni an dade da raba gadon ka"
Hanjin cikin Malamijo ne ya kada da gaske furucinta ya bashi tsoro. Ko dai mayyar ce ne? shiyasa kullum baya gaba sai dai baya kamar kudin guzuri.
**********
Kwance take akan doguwar kujera a falonta lokaci lokaci ta dago kai ta tsartar da miyau a duk inda ta ga dama tana faman yatsina fuska. Salisu ne ya shigo da langa cike da gurasa da tsire irin wanda take so.
"Salame tashi kici abincin" Kallonsa tayi ta watsar tana kokarin zubar da wani yawun ya taho da sauri ya mika mata kurtun da ya ciko da kasa "zuba a nan kinji don Allah Salame na" yace da rarrashi.
Kamar bazata zuba ba sai kuma ta tofa ya mayar ya ajiye jiki na rawa ya miko mata langar ta amshe ta soma ci don yunwa take ji dama. Ta dauko yanka na biyu ya saki fuska yana dariya "yau da albishir na dawo, me zaki bani tukwici?"
"Rike kayanka indai sai na bada wani abu zaka fada"
Baiyi fushi ba don ya saba da halinta. Bata boye masa kiyayya har yanzu da take dauke da ciki na wata biyu. Tsiyarta take tsulawa a gidan tana cin karenta babu babbaka kawai don tasan Salisu yana masifar son ta.
"Mairama ta sauka yau kwana hudu an sami mace"
Naman da take shirin hadiya ne ya makale mata a makoshi ta soma tari. Ruwa ya bata ko kalla bata yi ba bare ta karba.
"Me kace?"
"Mairama…."
"Dakata malam, wannan har wani labarin fada ne?"
Mamaki ya kama shi "ke, Mairama kanwarki nake nufi"
Zuciyarta ce take tafasa da bakin kishi. Yanzu Mairama har ciki Zayyan yayi mata ta haihu. Saboda shi tafi wata uku Salisu bai sami kanta ba sai da ya hada da fin karfi. Rigima sosai suka kwasa kamar auren bariki tana ta yi masa Allah Ya isa. Ganin babu sarki sai Allah daga baya ta hakura ba don tana son sa din ba sai don kawai ba ta hango mafita daga kaddararren aurensa ba. Da ciki ya bullo kamar ta zare don bata kaunar komai tsakaninsu lokacin da za ta kasha auren ta nemi hanyar shiga gidan Zayyan. Indai soyayya na saka hauka, kan Salame ya dade da kwancewa akan mijin kanwarta. Kuka ne ya kwace mata mai cin rai da zuciya. Mairama ta rigata samun abinda take muradi. Salisu ya tsaya kallon ikon Allah yadda take kuka haikan.
"Yanzu meye abin kuka bayan kema kina da cikin nan" a tunaninsa ko don ta riga ta haihuwa ne.
"Allah Ya sauwake nayi kuka don ta rigani haihuwa" tace cike da tsiwa.
Tsareta yayi da idanu "to kukan me kike yi?"
Gabanta ne ya fadi ta soma inda-inda "banda abin Mairama da kwarewa a rashin kunya daga auren sai ta bashi kanta. Wannan ai zubar da mutumci ne. A lissafina sai nan da kwana hudu ma zamu cika wata tara da aure amma gashi ita ta haihu. Anya ma kuwa cikin nan…."
"Ke Salame! Shiga taitayinki. Kanwar ta ki kike neman jifa da kazafi saboda wani shirmenku na banza da hofi. Na dade da kula ko sunanta na ambata ko agidan ku aka ambaceta sai fuskarki ta sauya. Idan ma wani abin ne ya hadaku ki shirya jibi zamu wuce Sakkwaton sai ku sasanta"
Kallon wulakanci ta jefa masa duk da taji tsoron tsawar da yayi mata "ba zani ba idan ka matsu da ganinsu kaje kai kadai"
Ransa ne ya soma baci shima "na fasa a gobe ma zamu tafi, haba yarinya mai nutsuwa da kunya baki da aiki sai na kusheta da jifanta da bakaken kalamai"
"Da kasan tana da halayen kirki me ya hana ka nemi aurenta ka barni na auri wanda nake…."
Tasss taji saukar mari a kumatunta sai da ta ga haske, rai a matukar bace Salisu ya nunata da yatsa "bar ganin ina lallabaki wallahi sai nayi miki shegen duka a gidan nan. Ke wace irin mutum ce ne? Kina ta abubuwa ina kawar da kai to amma tura ta kai bango tunda har jininki baki raga musu ba. Ki shirya gobe zamu tafi sannan ki tashi ki hada ruwan omo da dettol ki bi duka gidan nan ki goge min. Su bayan kofofi da kujeru duka ki tsaftace min gida ko ina warin yawu ya isheni. Idan na sake kamaki kina tofa yawu nan ba a wancan abin ba wallahi jikinki ne zai gaya miki. Tashi ki bani wuri ni"
Ba karamin tsorata tayi ba ta kai mai hakuri bango. Tsoro ne da ita tun da can, soyayyar Zayyan da ta bari a zuciyarta da kyashin kanwarta su ne suka maidata haka. Jiki na rawa ta tashi yace ta dawo sai ta gama cin abincinta tukunna. [5/22, 10:51 PM] Sis Ruky: ....ALLAH NA NASA
"Ummin Awwab me yake damunki ne kwanakin nan sai wata rama kike yi kamar wadda za'a yiwa kishiya"
Dago kai Mairama tayi jiki a sanyaye "Mami ni kaina na rasa gane dalilin wannan rama. Kuma ke shaida ce ina cin abinci sosai"
"Kinbi kin dashe kinyi fayau. Jiya ina ji baban Radhiya yana fadawa Hadir wai kinki bari ku je asibiti. Baki ga yadda ya damu ba fa"
Mairama tayi shiru ita kanta ramar da take yi tana damunta. Dadinta ma dai Radhiya kullum kara habbaka take. Suna wannan hirar Fauziyya ta shigo da Radhiya tana nishi anyi daukan rungumarni mu fadi.
Kafin su shigo kukan Radhiyan ne ya isar da zuwansu. Mairama ta girgiza kai tana takaicin wannan kukan banza na Radhiya. Tana jaririya babu ruwanta amma yanzu rigima da kuka ga fada duk ta iya. Idan ta raina girman mutum ya dauketa sai yakushi tana doke doke duka wataninta tara a lokacin. Zayyan dariya yake yace 'yar Soja bata daukar raini. Wasu lokutan kuma sunanta na gaskiya yake kira idan yana jin nishadi. Har ta gane indai taji Alheran tasan babanta ne.
A cinyar Mairama ta ajiyeta ta kalli uwar tasa dariya. Zainab tace "kunji min mara kunya ko? Mu da take gani kullum yanzu dariyar ma sai mun roka. Dadinta dai har Awwab bata yiwa"
Homework yake yi a gefe yana jin tsokanar da ake masa ya taso ya kinkimeta yana cewa "Ummi wallahi tayi nauyi da yawa ki dena bata abinci"
Me zasu yi banda dariya kuwa. " to sarkin wauta, an taba hana mutum abinci saboda kiba ne?" Cewar Mami
Shi dai bai ga aibun maganarsa ba ya dauketa gashi siriri sai tsayi da yake faman yi ya tafi dakinsu Zahra. Kayan wasa ya baje mata yana cewa sai tace Ummi da Daddy. Gajiya tayi da wasan ta soma rigima sai ya dauketa. Duk da haka kukan take masa ya sabata yana haki "gaskiya kin fiye kuka Alheran dinnan"
Kamar taji me yace kuwa ta kai masa duka a fuska harda yakushi. Zafin da yaji a gefen idonsa na hagu yasa shi sakinta tim a kasa ta fasa wata gigitacciyar kara. Zainab da Mami ke rige rigen shiga dakin ya dafe gefen idonsa da yake jini ko ta kanta bai bi ba a kasan. Zainab tayi saurin daukarta yayin da Mami babu tambayar ba'asi ta dauke Awwab da mari.
"Me kayi mata take wannan kukan?"
Shima kukan yake sosai Mairama ta taho ta rike shi murya na rawa ya nuna mata wurin "yakushi na tayi fa"
"Sai kayi mata me?" Mami ta kuma tahowa kamar za ta doke shi.
Da karamar murya ya amsa "Faduwa tayi daga hannuna"
Takaici ne ya kamata kuma wai Mairama tana kare masa. "Bari Daddynku ya dawo sai na fada masa" ta koma ga Mairama rai a bace "ke kuma kin karbi yarinyar nan kin rarrasheta ko kuwa"
Mairama tace to yau abin harda ita. Karbarta tayi ba shiri an tabo Mami yau ta fara shayar da ita amai ya taso mata da gudu tayi bandaki. Abu kamar wasa sai gata ko tashi da kafafunta ta kasa. Mazajen nasu ba ma sa cikin barrack din an turasu wani training cikin jeji sai sunyi kwanaki. Dalilin ma da suke tarewa gidan Mamin kenan.
Abu na taron mata tare su ukun da yaransu suka tafi asibiti. Ciki aka gano a jikin Mairama har wata uku. Kuka ta saka ganin Radhiya duka duka nawa take. Kuma ga kunyar ace yarinya bata shekara ba ta sake ciki. Su Zainab kuwa sai murna. Mami tace mata ya kamata kafin su Zayyan su dawo ta yaye Radhiya saboda cikin yana wahalar da ita ga tsotso. Da yake akwai kawaici a daren ta tafi ta barwa Mami ita sai kayanta da ta turo Awwab dasu.
Yadda Mami ke bawa Radhiya kulawa ya kara tabbatar musu da cewa zaman mutumci da amana ba sai da jini ba. Da ita da yaranta duk sun tare a jikin Radhiya an bar Mairama da uban laulayi sai Zainab dake sintirin zuwa wurinta.
A kwana na biyar su Zayyan su ka dawo. Sun sha wahala sosai sai dai kuma aiki ne na sabo. Da murnarsa ya shigo yana kiran 'yar soja Mairama tace masa tana gidan Major ta tafi yaye.
"Yaye Mairam? Ko shekara bata yi ba"
Hannunsa ta kama suka zauna ta dora kanta a kafadarsa "Sojana bani da lafiya ne"
Ya dago kan ta "na sani kuma asibiti zan kaiki, amma meyasa baki bari na dawo ba sai yaye?"
Baki ta tura masa "to ba..."
"Me?"
"Ciki" tace tana rufe fuska da tafukan hannayenta
Sungumarta Zayyan yayi yana murna "Mairam kice Tureta ya tureki a karo na biyu"
Salati ta hau yi tana mai jin kunyarsa shi kuwa ko a jikinsa. Dama ta samu sai sabon amarci don ma laulayin yana hana sakewa. Sai da Radhiya ta cika kwana goma sannan Mami ta dawo da ita da kaya da tarkacen wasa.
******
Bayan wata guda da yaye Radhiya wata litinin Mairama tana gyaran wake za ta yi alala da rana Zayyan ya shigo ba lokacin dawowarsa ba. Hannunta ta dauraye ta fito wurinsa.
"Sojana ya dai yau ka dawo da wuri"
Mikewa yayi akan doguwar kujera yana riko hannunta ta zauna a wurin da ya matsa mata.
"Me kike dafa mana ne?"
"Alala zanyi"
Hanci ya dage "Uhmm kayan bata ciki"
Hancin nasa ta riko tana dariya "nasan ba ka ci, banyi tsammanin dawowarka yanzu ba ne. Sai na canja abincin, waken...."
Kofar falon da taji ana bugawa da karfi kuma kamar muryar Zainab yasa bata gama fadin me tayi niyar fada ba. Da sauri ta bude kofar tayi baya a tsorace ganin Zainab tana rusa kuka kamar ranta zai fita ga Hadir a bayanta dauke da Ibrahim.
Hanya ta basu su ka wuce cikin falon Zayyan ya hada ido da Hadir yayi murmushin dole jikinsa a sanyaye yace "ka fada mata ne?"
Zainab kuka take har lokacin Mairama ta rude sai tambayarta take me ya faru. Hadir take kallo tana jiran bayani daga baya tace "ko dai aure za ka kara?"
"Wallahi dama auren ne Ummin Awwab da ya fiye min da wannan tashin hankalin"
Kanta ya sake shiga duhu "ba dai saki bane ko?"
"Liberia zai tafi"