Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 7

Batuol mamman complete novel - Chapter 7

Batuol mamman complete novel Chapter 7: Batuol mamman complete novel Chapter 7. Dif Mairama tayi sakon yana sauka a kwakwalwarta. Liberian da babu wanda…

3,320 words

Dif Mairama tayi sakon yana sauka a kwakwalwarta. Liberian da babu wanda yake cikin barikin da bai san tashin hankalin da suke ciki ba. Nigeria ta shiga cikin lamarin tana basu gudunmawar sojoji domin a kwantar da tarzoma. Dibansu akeyi lokaci lokaci ana turawa. Rawa taji jikinta yana yi ta kasa tsayuwa da kyau sai da Zayyan ya riketa ya zaunar da ita a kusa dashi.

Cikin tsantsar tashin hankali tace "da kai za'ayi tafiyar?"

Abinda ya dawo dashi gida da wuri kenan ya kasa fada mata. Kai ya gyada kawai ta kalli yadda Zainab ke kuka itama ta soma hawaye. Duk wata kalmar rarrashi da ban baki abokan sun lalubo domin kwantarwa matansu da hankali. Zainab ta fi gigicewa itama tana son Hadir fiye da zato da tsammani. Da kyar ya samu ta tashi su ka koma gidansu aka bar Zayyan da Mairama.

Ranar bata iya yin girkin ba jikinta yayi mugun sanyi. Abincin Radhiya ma sai shi yake bata. Ita kwanciya tayi a daki kawai tana zubar da hawaye. Bai ce mata komai ba sai cikin dare ya kwantar da ita a jikinsa yana rarrashi

"Mairam nayi zaton zaki bani goyon baya sosai har naje na dawo mu koma Kano"

"Yaushe zaku dawo?" Ta tambaye shi murya a dashe.

Tsokanarta ya fara yi don ta sake "tafiyar wata uku ce fa, zan dawo kafin ki haihu in Allah Ya yarda"

Sake shigewa jikinsa tayi yana jin cikinta da ya fara tasawa ya dora hannu a kai "Ashe haka ki ke so na ban sani ba?"

Shiru tayi ya cigaba da maganarsa shi kadai "a iya zamana dake Mairam bani da wani abu da zan fada akanki sai alkhairi. Duk abubuwan da na rasa a baya zuwanki ya wanke min kuncinsu. Shiyasa nake matukar son ki. Wannan tafiya da ina da yadda zanyi ko dai na tafi daku ko kuma na hakura ne. Ina rokonki da ki karfafa min gwiwa naji dadin bautawa kasata."

Wani irin abu take ji yana mata yawo a jikinta. Idan a da tana tunanin tana son mijinta to a yau sonsa yana neman ranta ne. Gani take kamar bazata iya jurar rashinsa a tare da ita ko da na kwana daya bane. Ashe baka sanin mahimmancin abun da ka ke dashi sai yayi nisa da kai. Bata san lokacin da bacci ya dauketa ba sai ajiyar zuciya da take ta saukewa.

Sai da ya tabbatar tayi bacci ya tashi ya dauro alwala. Yasan yaudarar kansa zaiyi idan yace zaiyi bacci a wannan daren. Nan da kwana biyar zasu bar kasar, zai bar iyalinsa wanda basu dogara da kowa ba sai Allah sai kuma shi da nauyinsu yake wuyansa. Yayi nafila raka'a goma tare da witri sannan ya zauna yana jero addu'o'i. Motsin Radhiya yaji yayi saurin fita da ita daga dakin don kada ta tashi Mairam yaje ya hada mata tea a feeder ta shanye. Yana jiran ta koma bacci yarinya ido ya soye ta fara kiriniya. Bata tafiya sai rarrafe da mikewa. Biye mata yayi suna wasan. Sai gabanin asuba ta bingire a jikinsa tayi bacci. Kan ta ya rinka shafawa baiyi zato ba sai hawaye ya ziraro masa ya goge da sauri yana baiwa zuciyarsa hakurin cewa wata uku a wurin Allah kamar kiftawar ido zasu zo su wuce.

**********

Gidan Hadir ma basuyi bacci ba don Zainab kwana tayi kuka. Mami da sauki tunda ba zuwan Major na farko wurin rikici ko yaki kenan ba. Sai dai itanma kukan tayi don ba'a sabo da rabuwa.

Washegari harabar gidajen nasu kaf babu wata hayaniyar kirki. Sojoji ashirin ne zasu tafi a cikin magidantan da suke wurin. Kowa yana gida tare da iyalinsa.

Bayan la'asar Zayyan ya dauki Mairam su ka je gidansu da gidan kawunansa da Mal Aminu ya fada musu zaiyi tafiya. Kowa yayi masa addua da fatan alkhairi ban da Jume da bata dena jin zafin rashin basu kudi ba. Duk da haka ya yi musu kyauta ita da su Maikudi tunda sunyi aure. Matan ma a ranar sai da ya kai musu ziyara.

Sukuku su Mairam su ka koma babu walwala a tare dasu ita da Zainab. Mami ce tayi musu fada akan idan sun cigaba da haka a wane yanayi suke so mazajensu su tafi. Sun ji maganarta don kowacce sai da tayi kokarin gyarawa. Mairam dambun nama ta yiwa Zayyan gari guda sai da ya dibarwa Hadir da Major. Ta kuma saki jiki tana bashi kulawa fiye da yadda ta saba.

Sauran kwana biyu su tafi tana goge masa khakinsa Radhiya ta fito daga daki da kafafunta a hankali saboda rashin kwarin tafiyar. Murna ta kama Zayyan ya sunkuceta yana sumbatar kumatunta.

" 'Yar soja ta girma, yau yawo zamu je tunda anyi kafa"

Kamar taji me yace ta rinka bangala dariya. Ajiyeta yayi zai chanja kaya su fita tasa masa kuka "Daaadaa" yaji tace tana dago masa hannuwa.

A nutse ya juyo ya tabbatar shi take kira. Har yanzu hannuwanta take miko masa "Daaadaa". Ya kalli Mairam ita ma mamakin yarinyar ya kamata. Awwab bashi da aiki sai koya mata Ummi da Daddy wai dole sai tayi magana. Yau gashi ta kira mahaifinta dadi yasa yaji idonsa na alamun zafin kwalla. Daukanta yayi ya shiga dakin su ka bar Mairam tana guga tana diga masa hawaye a kayansa.

Ranar ashirin da daya ga watan Mayu na 1993 ne Giginya Barrack dake cikin garin Sakkwato ta kwashi sojojinta za'a kaisu Lagos washegari su tashi zuwa Liberia ta ruwa. Daren ranar ya kasance dare na soyayya, jaddada alkawura da kuma sabunta matsayi a zukatan su Zayyan da iyalansu. Daga shi har Mairam babu wanda ya runtsa kuma hakan take a wurin Hadir da Zainab da Major kansa da Mami.

Komai Mairam ce ta yiwa Zayyan hatta abinci a baki take bashi. Tayi ta daurewa kada tayi kuka zuciyarta ta kasa daukan wannan lamari. Ko kadan baya son nuna mata damuwar da yake ciki shiyasa ya fake da yiwa Radhiya wasa.

Jiniya mai sanar da su fito ce tayi kara sai da cikin Mairama ya murda kawai ta fashe da kuka iya karfinta.

"Zayyan"

Tashi yayi ya rungumeta tsam a jikinsa "ashe kin iya fadin suna na"

"Ka ajiye aikin nan mu koma Nijar ko kiwo ka rinka yi"

Fuskarta ya zagaye a tsakiyar tafukan hannunsa.

"I love you Maryam Ali Gidado. Ki rike wannan a zuciyarki har na dawo. Nayi miki ajiya a kan mudubi idan na tafi ki duba"

Hade bakinsu yayi tamkar ranar su ka fara haduwa yana jin karar jiniyar a karo na biyu ya saketa ya dauki Radhiya.

"Ki tayani kula da Umminki da baby kinji mamana."

"Daaadaa" tace tana washe hakoranta biyu dimple dinta ya lotsa ciki sosai. Ita ma ya sumbaci kuncinta hagu da dama kafin Mairam ta farga ya fice daga gidan. [5/22, 10:51 PM] Sis Ruky: *********** Kyakkyawar kulawa da gyara Mairama take samu daga wurin Nene Marka. Ita da Zainab da Mami shakuwarsu sai gaba take kara yi. Idan kaga Awwab baya gidan to makaranta ce ta tsare shi ko dare ya tafi yayi bacci. Amma kullum yana wurin Mairama da kanwarsa Radhiya. Zahra da Fauziyya suna shan gori yayi ta cewa su Antinsu bata kawo baby ba har yanzu. Idan ya fadi haka Zahra sai tace ai nata cikin ya kusa fashewa ne su ma bazasu bari ya taba musu baby ba.

Zayyan ba karamin kewar matarsa yake ba. Ko yaya Nene ta dan bada wuri sai ya faki ido ya rungumeta yana fada mata yadda yake kewarta da matsuwa ayi arba'in dinnan kowa ya huta. Jaririyarsu Radhiya ta kara yin bulbul gwanin sha'awa. Idan kayi mata kallo daya sai ka rasa wa ta debo cikin iyayen. Bafillatanar mahaifiyarta ko sojan babanta da yake surki tsakanin mutanen Agadas da na Tureta. Yarinya ce mai matukar shiga rai musamman idan tayi murmushi gefen kumatunta na dama ya lotsa. Awwab har yatsa yake sakawa a wurin don kawai tayi masa murmushi.

Ranar da su ka cika wata biyu Zayyan ya kwashesu a motar haya sai Sumaila. Mairama bata taba tunanin zata yi kewar gidansu ba sai yanzu. Sun isa yamma likis 'yan uwa ana ta tururuwar ganinsu.

Malamijo yana jin isowarsu daga gona ya zari takalmansa ya yo gida. Fadi yake 'yarsa mai auren soja ce ta iso tare da jikarsa. Abin arziki kaza guda ya bayar irin 'yar sati goman nan aka yanka Yadikko ce da girki tayi musu shinkafa da miya.

Daki aka gyarawa Zayyan ya kwana. Da safe abin mamaki sai ga Salame wai bazata iya jiran su iso gidanta ba tana kewar Radhiya. Mairama taji dadi balle da ta ga yadda take haba haba da Radhiyan harda su goyo duk da ana hanata saboda nata cikin ya fara fitowa.

Zayyan dauke kai yayi saboda shige masa da take yi tana ta so ko magana yayi mata. Allah sai Ya dauke hankalin Mairama daga garesu bata kula ba.

Kwanansu biyu sannan su ka wuce Balan a karkashin karamar hukumar Gaya inda gidan Nene yake. Tana da kishiya guda daya mai yara shida. Maigidansu manomi ne babu wani kudi sai rufin asiri. Irin kyautar da Zayyan yayi mata Mairama kanta tayi mamaki. Nene Marka harda kuka tana masa godiya.

"Nene mune da godiya, Allah Ya saka da alkhairi. Idan ta sake haihuwa ke zaki dawo ko?"

Mairama ta tashi daga wurin da sauri saboda kunya. Nene tayi masa dakuwa tana murmushi "kuji min dan kaniya, wato a gaban nawa kake rashin kunya ko Zayyanu"

"Fada nayi fa saboda kada ace wata daban ce za ta zo." Tare su ka yi dariya don ta saba da barkwancin surikin nata.

Kofar dakin ta kalla ta tabbatar Mairama tana wurin kishiyarta sannan ta dan matso fuskarta babu alamun wasa "Zayyanu nasan kana sane da son da Salame take yi maka"

Gabansa ne ya fadi ya dago kai yana kallonta da kallon kofa "Nene ki bar zancen nan, yau ko Mairam zata fadi ta mutu bazan auri Salame ba. Matar da aure bai hanata nunawa mijin kanwarta soyayya ba"

"Tun yaushe ta fara son ka?"

"Kafin muyi aure...don Allah bana son kowa yaji. Ni dai babu abinda ya taba hadani da ita"

Hankalinta taji ya kwanta "nagode Zayyanu. Ka rike min amanar Mairama. Ga maraici ga rashin dangin uwa har yau mun rasa a wace rugar ma suke zaune. Duk tsiyar Malamijo yana ta kokarin nemansu domin ya faranta mata. Salame kuma ka barni da 'yar banza. Idan ta nemi tada muku hankali da kaina zan gyara mata zama don ba gagararmu tayi ba"

Kafin azahar sun koma Sumaila inda ta sake kwana biyu suka bar garin bayan ihsani mai tsoka da ya yiwa Malamijo da matan gidan. Mairama har mamakin ina ya sami kudi haka takeyi saboda ita tasan duka duka albashin nasu babu wata tsokar kirki.

Sun baro Sumaila tana sa ran za su wuce Sakkwato sai gani tayi sun shiga cikin Kano zuwa wata unguwa yana yiwa dreba kwatance. Gaban wani gida zubin zamani a wancan lokacin mai kyau da tsari tun a waje aka ajiye su. Mukulli ya dauko da ga aljihunsa ya bata yana dauke da Radhiya.

"Bude mana da sunan Allah"

Kallon tuhuma take masa yayi murmushi da ka yayi mata alamar ta bude. Ba musu ta bude yana cewa ta shiga da Bismillah. Farfajiyar gidan tana da dan girma daidai mota guda daya. Sai kuma ainihin ginin wanda flat ne gidan. Yana gaba tana biye dashi zuciyarta da tarin tambayoyi har ciki.

Wani korido su ka fara bi a karshensa kofa take inda suka tarar da katon falo ga kofofi a ciki. Daya bayan daya suke shiga yana mata bayanin. Kitchen, dakuna hudu, store da kuma bandakuna ko ina da fenti amma babu kaya. Daki daya ne aka shimfide da leda ga katifa sabuwa da filo biyu sai zanin gado a cikin ledarsa ko budewa ba'ayi ba.

"Sojana ina ne nan?"

"Mairam ga gidan mijinki na halak yau kin shigo"

"Gidanka ne nan?"

Takowa yayi gabanta ya hadeta da Radhiya ya kankame. "Gidanmu dai Mairam"

Zaunar da ita yayi ya mata bayanin kudin gadonsa da ya narkar a wannan gini domin inganta rayuwar iyalinsa. Ya zabi zuwa Kano saboda gujewa fitina daga bangaren su Jume. Dama yanzu matsanancin fushi suke yi dashi saboda an gama taron suna basu ga komai ba. Da Jume da tado zance yace gida dai shima na mahaifinsa ne, idan basa son ya rabesu a raba gado ko dakin mahaifiyarsa a bashi. Sunyi rigima ba kadan ba ya fito musu gar da gar dinsa a soja mara daukar raini ko kadan. Suna ji suna gani dole suka hakura da haram din da suka kwallafawa rai.

Addu'a ta rinka jerowa yana amsawa daga nan yace to fa ta shirya jiya da ya taho cikin Kano siyayya yayi musu yana so ko sati suyi a gidan kafin ya koma aiki.

Kitchen ta leka ya siyo karamin risho, tukwane biyu da yan kayan bukata. Wani sabon shafin amarci su ka bude a gidan ga diyarsu a gefe tana samun kulawa. Wasa-wasa kwanansu goma sha biyu sannan su ka fara shirin komawa Birnin Shehu. Duk yadda taso kuwa yaki kaita gidan Salame don baya kaunar duk wani dalili da zai sa su hadu.

**********

Watansu biyu da komawa Zainab ta haihu. Sai dai ita a gidan iyayenta ta zauna su Mairama da Mami ke zuwa kullum har akayi suna. Jariri yaci sunan kanin baban Hadir da ya rasu gabanin haihuwarsa Ibrahim.

Rayuwar wadannan bayin Allah haka ta cigaba da tafiya cikin so, yarda da aminci. A kowane mataki su na kokari wurin ganin sun tsayawa juna cikin dadi ko akasinsa. Da Salame ta haihu ya barta taje ta kwana hudu a Kano inda ta rinka fuskantar Gadara da wulakanci daga wurin yayarta ta. Da yake ta fara sabawa da wannan bakon hali sai ta daure zuciyarta don kada ayi batacciya. [5/22, 10:51 PM] Sis Ruky: BAYAN AWA TALATIN DA BIYU

Mutumin da ya kai rahoton karya ga rundunar su Zayyan shine durkushe a babban sansanin da su Major Mustapha suke. Kuka yake kamar karamin yaro ga sojoji sun tsare shi babu wasa a idanunsu.

"Ka tabbatar ba yaudararmu kazo sake yi ba?" Cewar Captain Jonah.

Mutumin ya daga idanunsa jajir ya sake maimaita musu cewa yan tawaye ne suka kamashi. Sunyi masa mugun duka sannan aka umarce shi da yaje ya san yadda yayi ya kawo sojojin Nigeria wannan wurin. Idan baiyi ba garinsu gabadaya zasu tasa. Tsoro ya sanya shi cika umarni. Amma suna zuwa da ya ga me ake yi ya gudu. Shine yazo nema musu agaji duk da yasan da wahala a samu mai rai cikinsu.

Yana rufe baki wani zuciya ta debe shi ya buga masa kasan bindiga a keya ya fadi sannan ya bishi ya rinka duka da kafcecen takalminsa. Da kyar aka rike shi kowa ya sani akwai kaninsa uwa daya uba daya a cikin wannan sansanin.

Motocinsu suka cika da makamai suka tafi tare da wannan mutumin. Daga nesa suke hango sauran hayaki ga kauri ya karade wurin. Dirgowa suka shiga yi daga motocin suna gudu har suka je wurin. Su din sojoji ne fa jaruman maza amma hankulansu sunyi mumminan tashi da ganin wannan kisan gilla da aka yiwa mutanensu. Binsu suka rinka yi daya bayan daya wadanda jikinsu yayi alamun harbi ne kawai likitocin cikinsu suna dubawa ko akwai masu rai. Basu yi dacen samun ko daya ba. Duk da haka shugaban tawagar yace su bazu cikin dajin babu mai tafiya sai sun tabbatar ba'a bar kowa ba.

Mutum biyu ne suka bi hanyar da su Zayyan suka wuce cikin sa'a sai gasu a bakin kwazazzabon da Major Mustapha da Lieutenant Hadir suka fada. Suna hangosu daya ya dira ciki dayan kuma yana daga waje ya fara kiran ga wasu gawarwarkin a nan. Sai dai me, yana juya Major Mustapha yaji yayi wani irin gurnani na azabar ciwo. Ya zubar da jini ba kadan ba wurin da kafar ta cire ya kumbura suntum ta soma yin kore. Ihu yasa yana kiran suyi sauri wannan yana da rai don bai ma gane shi ba.

Ya koma ya juya Hadir. Mamaki karo na biyu, shima da ransa saboda bugun zuciyarsa da yake a raunane amma baya motsa komai na jikinsa. Sauran sun zo an taru an fitar dasu cikin sauri suka isa sansanin inda aka wuce dasu bangaren kula da lafiya. Daki ne madaidaici da 'yan kayayyakin taimakon gaggawa da abinda ba'a rasa ba.

Komai cikin sauri ake gabatar dashi domin alamu sun nuna su biyun sun galabaita fiye da zato da tsammani. Anyi nasarar cirewa Hadir bullet a hannunsa sai dai buguwar da yayi wanda suke tsammani a kansa ne har yanzu bai motsa ko da yatsa ba. Babu kayan gwaje-gwaje sosai da zasu iya gano ainihin matsalarsa.

Major Mustapha shima an gyara wurin da kafarsa ta cire. Bayan allurai da ruwa da ake kara masa babban likitan Major Dalhatu ya tafi ofishin ogansu gaba daya a wurin. Izinin shiga ya nema ya tsaya a kame a gaban Colonel Fredrick Madueke.

"Sir they need medical attention more than we can provide"

Lt Col Madueke ya dago idanunsa sunyi ja kamar gauta. A yini daya sun rasa sojoji da dama wanda duka a karkashinsa suke a wannan tafiyar.

"I am trying to reach the HQ at Monrovia Captain . We need to fly them back to Lagos"

Captain Dalhatu ya juya ya fita bayan ya sara masa. Yasan Lt Col Madueke akwai tsantseni. Bazaiyi saken da rayuwar wadanda suka tsira zata salwanta ba a nashi bangaren.

Kwana daya, biyu, uku, hudu....shiru headquarter bata turo helicopter da suka roka domin a kai su Major airport din Monrovia ba. Lt Col Madueke kullum yana magana da headquarter sun ce suna jiran feedback daga Nigeria. Abu yaci tura suka debesu da kansu a motoci ga gargada da komai zuwa Monrovia din. Nan ma a basu dama ko izinin fitar dasu ya zama aiki. A haka sai da suka kwashe sati uku ana abu daya. Hadir yana nan jiya-e-yau. Major Mustapha kuwa ya farka amma azabar ciwon kafarsa tasa ya koma yana sumbatu. Dole yayi sambatu wurin ciwon nasa ya soma fitar da ruwa mai wari saboda kwayoyin cuta da suka shiga ga rashin kayan aiki. Anyi rigima harda nunawa juna bindiga tsakanin Capt Dalhatu da wani soja a headquarter din saboda rashin daukar patients dinsa da akayi. A haka sai manya masu mukami ko wanda yasan wani shine abin dubawa. Mu kasarmu har kullum wa ka sani wa ya sanka ce.

A rana ta ashirin da bakwai Allah Yayi aka dauki Major Mustapha da Lt Hadir zuwa Lagos. Yanayin da suke ciki suna bukatar taimako na gaggawa sosai. Kai tsaye aka wuce dasu 68 Nigerian Army Reference Hospital dake Yaba a Lagos.

An yiwa Hadir gwaje gwaje karshe dai likitoci sunce kawai a jira ko dai ya tashi ko kuma rai yayi halinsa. Idan da hali ana bukatar 'yan uwansa domin jinya da kuma fara biyan kudaden asibiti idan ana son su cigaba da aiki a kansa. Buguwar da yayi a kansa sai ya farfado zasu san ainihin iya damejin da tayi masa.

Major Mustapha kuwa aiki gagarumi yake bukata a rubabbiyar kafarsa. Ciwo wata guda ya ga izaya ra'ayil aini har yanzu bai san waye a kansa ba duk da ya farka. Dungulmin kafar ke fitar da tsutsa saboda rashin gatance musu da kasa tayi a lokacin da suke da bukata. Gasu da rauni ga rashin kayan aiki a inda suke. Anzo kasar tasu kuma asibiti na bukatar makudan kudade domin su yi masa aiki a yanke abinda yayi saura na kafar. Sojoji da basu kirguwa sun tafi da lafiya sun dawo gidajensu da nakasa ta har abada. Shima dai an bukaci a nemo nasa iyalin domin kulawa dashi da kuma kudin asibiti wanda gwamnati bazata iya daukar nauyi ba duk kuwa da cewa a kokarin bin umarninta suka riski kawunansu a wannan hali.

BOYAYYUN JARUMAI (NA SARAWA MATAN SOJOJI)

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull