Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 8

Batuol mamman complete novel - Chapter 8

Batuol mamman complete novel Chapter 8: Batuol mamman complete novel Chapter 8. Jiniya ce irin wadda aka kunna ranar tafiyarsu yau ma aka saki. Motoci…

3,353 words

Jiniya ce irin wadda aka kunna ranar tafiyarsu yau ma aka saki. Motoci manya na sojoji suka rinka shigowa barrack din a guje zuwa bangaren ofisoshin manyansu. A can aka bada cikakken rahoto game da mutuwar gabadaya sojoji da aka dauka a ranar tafiyarsu Zayyan daga Giginya Barrack da kuma halin da Hadir da Major suke ciki.

Wuri ba sai ya kaure da hayaniya ba, manyan sojoji ana ta shige da fice suna samun cikakkun bayanai. Tattaunawa ce tsakaninsu akan yadda ya kamata su bullowa lamarin. Masu aure cikin wadanda suka tafin wurin tara ne sauran duk samari. Wasu ma basu dade da zuwa barikin ba.

Matan wadanda suke asibiti dai babu yadda za'ayi a boye musu. Bisa wannan dalilin aka buga takarda mai dauke da bayanin halin da kowanne yake ciki za'a bawa matarsa.

***********

Mairama tana gidan Zainab taje kitso suna zaune daga bayan gidan wanda katanga ta karesu babu mai ganinsu. Sannan an dan zarta bangon gidajen ta barin hagu da dama domin ya zama kariya tsakaninsu da gidajen kusa dasu. Sai dai ba'a hade ginin ba zasu iya wucewa. Yawanci matan ke amfani da wannan wurin domin ayyukan da suka fi karfin cikin gidan kamar suya da babbar sallah.

Zainab tana yi mata kitson gefe Radhiya ce da Ibrahim an baza musu tarkacen wasa suna ta ihunsu irin na yara da duniya ta yiwa dadi.

"Ke yaushe zaki yi kitson ne?" Mairama ta tambayi Zainab

"Ai kallonki nake duk sati kitso, ni nan ina jiran muji kishin kishin din zasu dawo ne naje ayi min famin (perming ko saka relaxer). Ya tafi ya barni da kitson ya dawo ya tarar dashi. Hum'uhm"

Dariya Mairama tayi "nima da kika ga na nacewa kitson bana son haihuwa da kai a tsefe ne. Lokacin wannan yarinyar kan na kusa cizgewa don azaba"

Tafawa suka yi suna kyakyata dariya kowacce tana tuna nakuda da haihuwarta.

"Kin gansu tafiya daga wata uku an shiga na biyar ga ki haihuwa ko yau ko gobe" cewar Zainab da 'yar damuwa a fuskarta.

Wannan dadewar tasu ta dami matansu sosai. Kowacce dai tana kokarin daurewa ne don kada su rinka tadawa juna hankali. Amma a zahiri babu wadda bata kukan dare idan kewar mijinta da rashin sanin halin da suke ciki ya dameta.

Radhiya baki ya bude ba laifi don akwai surutu. Zaman da take yi dasu Zahra shi yake kara bude bakin. Ta dai fi likewa Awwab saboda yawo. Sai ya dauketa suyi ta karade barikin nan.

Yanzu ma 'yan takalmanta masu madauri aka sanya mata bayan an gama kitson tasa kuka ganin sun doshi gida "Ummi, Amma wawo" nufinta a kaita wurin Hamma su tafi yawo.

"Hajiyar gantali ni dai na gaji. Kiyi fatan daga islamiyya ya biyo sai ya kaiki wurin Mami"

Tana jin sunan Mami kuma kukan ya karkata tana kiranta. Tana ta bata baki yarinya taki shiru. Ba yadda ta iya dole ta kaita gidan. Mami tana cewa ta zauna tace gida zata tafi jikinta babu dadi. Radhiya harda yi mata bye bye tace idan Awwab ya dawo yazo ya karbar mata kaya don tasan yau ma ita kadai zata kwana Mami bazata bari a dawo da Radhiya ba.

Cikin dare bacci ya gagareta kamar yadda take ta fama 'yan kwanakin nan. Kullum cikin mafarkin Zayyan take, watarana ta tashi da kuka wani lokacin kuma idan mafarkin yayi dadi ta tashi da farinciki. Sai dai a can kasan zuciyarta tana fama da wani irin firgici wanda ta kasa gane dalilinsa.

Envelop din da ya bar mata ranar tafiyarsa ta dauko ta shafa amma har yau taki budewa. Tsoron me ya rubuta take yi, karshe ma dai ta fadawa kanta idan ya dawo ya karanta mata da kansa.

Haka ta cinye daren a tunani baccin da kyar ya dauketa. Bayan tayi asuba ma komawa tayi abinta ta kwanta. Wurin tara na safe ta ji bugu kamar za'a balle mata kofa. Haka ta taso da hijab a baibai saboda sauri ta bude tayi karo da Christie. Itama makociyarsu ce tare da mijinta akayi tafiyar.

"Mama Radhiya e bi like say your sister don die ooo. She just knack her head for ground after one officer wey I no know come give her letter"

Cikinta ne ya murde da tsoro ta bi bayan Christie da gidanta yake kallon na Zainab.

Mata ta ga sun zagaye Zainab ga Ibrahim yana ta tsala ihu. Ashe a kansa ma ta fada bayan ta karanta takardar Allah Yasa akwai mata a wajen suka dauke shi.

Da kyar Mairama ta durkusa a gabanta tana rike mata hannu "Zainab menene?"

Takardar ta iya mika mata kawai. Mairama tana karantawa itan ma sai kuka da tausayin Hadir. Christie ta cewa ta shiga da Zainab gida tana zuwa. Hankali a tashe tana baza sauri ta tafi gidan Mami don ta fada mata. A can ta tarar da wani mummunan tashin hankalin.

Mami ke kuka sosai tana ta hada kaya ta jibge akwatuna biyu a falon tana ta watsa kayanta da na su Fauziyya a ciki.

Gabadaya yaran suna gefe kowa yayi tsit harda Radhiya da ta ga babu mai kula ta. Awwab bai san me ya faru ba amma ganin mahaifiyarsa na hawaye shima yake tayata.

Mami na ganin Mairama taje ta rungumeta ta sake fashewa da kuka "Ummin Awwab na shiga uku, ina zan sanya kaina"

Duk ta gama tsorata ta daure tace "addu'a zakiyi Mami ba kuka ba, komai yayi zafi maganinsa Allah. Me ya faru?"

"Daddy ne..." sai ta mika mata takardar ta karanta da kanta.

Hawaye ne ya cigaba da zuba a fuskokinsu Mami tace "Katsina zan tafi yanzu. Sai naje na ajiye yaran in sanar dasu sai mu wuce Legas din"

Suna haka Zainab ta shigo ta goya Ibrahim da har yanzu yake kukan faduwarsu ta dazu tana jijjiga goyon tana kuka. Mairama ce tayi mata bayanin me ya sami Major kuma. Su uku suka hada kai suna ta kuka abin tausayi.

Kusan a tare Mami da Zainab su ka fuskanci Mairama "Zayyan fa?"

Dammm taji gabanta ya yanke ya fadi ta juya a guje ga nauyin ciki ga kafarta da take yawan rikewa ta nufi gidanta. Tsoronta daya kada itama anzo sanar da ita halin da Zayyan yake ciki ba'a sameta ba. Bata tarar da kowa ba ta tsaya tana ta haki tana jin kamar za ta amayar da abinda yake cikinta a lokacin. Da jan kafa ta koma gidan Mami sun gama shiri ita da yaran.

"Zainab, Mairama...Allah kadai yasan ranar sake haduwarmu. Komai nawa ya danganta da samun saukin Daddy"

"Babu komai, Allah Ya basu lafiya baki daya."

"Amin" suka amsa sannan Zainab ta kara da cewa itama zata je ta sanar da nata iyayen ne domin a aika Kano gidansu Hadir. Sannan a san yadda za'ayi a dawo dashi gida.

Ji suke kamar daga ranar sun rabu kenan suka yi ta kuka sosai. Radhiya da kyar aka rabata da Awwab ta makale masa wuya tana ta ihun Amma.

***********

Gidan iyayenta Zainab ta wuce cikin kasa da awa guda ta isa. Bayan ta yiwa mahafinta bayani a take ya taso babban wan ta ya bashi kudin mota yace ya wuce Kano gidansu Hadir ya sanar dasu.

Zainab na kuka tace masa su yaushe zasu tafi Lagos din.

"Zainab kinfi kowa sanin halin da nake ciki. Kudin da na bawa yayanki wallahi harda na cefanmu na yau da gobe ne. Kasuwar babu kudi yanzu sai nayi huluna biyar ba'a sayi ko daya ba"

Shiru tayi wani hawayen yana sauko mata. Ita ta sani kuma bata boyewa iyayenta talakawa ne fitik. A Kano ma iyayen Hadir ba wasu masu karfi bane. Sai dai sun fi nata sosai. Albashin Hadir shine yake turawa gida kuma a haka yake yiwa iyayenta ihsani lokaci zuwa lokaci. Zuciyarta ta gama tsinkewa da wannan bakon lamari a gefe guda kukan Ibrahim yaki tsagaitawa.

Mahaifiyarta ta karbe shi tana ta juya shi da shafa jikinsa ashe ya sami gocewar kashi ne a hannu sakamakon faduwar da Zainab tayi a kansa. Babanta ya karbe shi ya tabbatar hakan ne yace ta tashi su tafi gidan dori.

"Wayyo Allahna Baba. Da me zanji?" Ta kara rushewa da kuka.

"Zainab kamar baki da ilimin Tauhidi? Ki fawwalawa Allah ki yawaita addu'a. Daga gidan dorin zan wuce wurin kawunki ko Allah zai sa yana da abinda zai ranta min ko ni kadai ne sai na wuce Ikkon. Kinsan babu yadda za'ayi na barki kije ke kadai baki san ko ina ba ga yaro babu lafiya"

Kai ta gyada kawai suka tafi gidan dorin aka gyara masa hannun. Ibrahim ya zama abin tausayi don ya jigata ba kadan ba. Suna dawowa sai zazzabi da amai ya sarke shi ko hannu baya iya motsawa da kyau. Zainab tayi kuka har taji babu dadi.A rana daya rayuwar wannan baiwar Allah ta juye gabadaya. Miji yana asibiti a wata uwa duniya, amma babu kudin zuwa gareshi. Babanta yace su jira yayanta da yaje Kano ya dawo. Idan iyayensa sun dauko shi sai ta tafi can ko da yaya zai samu ya biya mata kudin mota. Yini kuka, kwana kuka haka ranar ta kasance mata.

***********

Gidansu Mami unguwa daya ne da na su Major Mustapha. Iyayensu maza su biyar ne a gidansu. Baban Major ne na biyu nata kuma auta. Da suka tashi aure sai suka zauna a gidajen da katanga kadai ke raba su.

Daga tasha bus ta hau zuwa unguwar tasu. Tana shiga layin ta hango babban wan iyayen nasu da suke kira Alh Baba. Yayi shigar mutumci da babbar riga da farin rawaninsa irin na malamai. Motarsa kirar Pigeout (pijo) zai shiga daya daga cikin yaransa zai kaishi unguwa ya hangota. Dakatawa yayi don ya tabbatar da wace ce saboda ita da Usainarta sai kayi musu farin sani kake iya tantance su.

Tana matsowa ya saki murmushi saboda daga yaranta ya ganeta masu kama da mahaifinsu "Mutanen Shehu saukar kenan?"

Daga ita har yaran sun durkusa da niyar gaishe shi kawai ta fashe da kuka. Yaran ya kalla yasan duk yadda akayi wani abu ya faru "Kai Muhammadu wuce ciki da kannenka" ya fadawa Awwab.

"Ke kuma muje" ya nuna mata hanyar gidansu Major.

Awwab kamar ya bita ganin tun a gida suke ta kuka amma tarbiyarsu tasa ya bi umarnin kakan nasu. Ciki suka shiga matan gidan suna ta murna ana tambayarsu mamansu suka ce tana wurin Alh Baba.

Basu sami baban Major ba sai Iya mahaifiyarsa. Alh Baba ya tura aka kira ragowar kannensa sannan suka bukaci jin dalilin zuwanta tana kuka. Duk sun sani cewa ya tafi Liberia tunda yazo yayi musu sallama. Tana kuka ta sanar dasu abinda takardar da aka bata ta kunsa. Gidan sai kuka tamkar ance ya riga ya rasu.

Bayan dawowar mahaifin Major iyayen su kayi zaman shawara. An daidaita magana akan cewa Alh Karami baban Mami da kuma yayan Major Mustapha da suke uwa daya uwa daya su ne zasu tafi.

Mami ta kasa daurewa tana kuka, Alh Baba ya dubeta "kiyi hakuri Hassana. Su dinmu dauko shi zasuyi a dawo dashi gida yayi jinyar a kusa. Legas tayi mana nisa. Idan munje da yawa bamu san ina zamu kwana ba"

Ba haka taso ba ko kadan amma bata da yadda zata yi. Tana ji tana gani asubar fari suka kama hanya a motar Alh Baba.

**********

Kwanaki biyar kenan da samun sakon da ya tada hankula a Giginya army barrack. Mairama ta rame sosai a 'yan kwanakin. Radhiya ma bata samun kulawa yadda ya kamata saboda tun ranar da suka tafi fargaba tasa ta fara nakuda a tsattsaye tana daurewa.

Rayuwa take yi mara dadi. Babu miji kuma babu wadanda suka zame mata tamkar 'yan uwa na jini. Tarin fargaba ne ya cika zuciyarta da kokonto. Ta damu tasan halin da su Hadir suke ciki ga kuma rashin sanin komai game da Zayyan ya sanya take jin kamar zata yi hauka.

A kwana na shida ciwo yaci karfinta ta daure taje ta buga kofar gidan Christie. Ita dinma duk zulumi da fargaba sun cinyeta tana ta ramewa. Tana ganin Mairama a haka tasan nakuda ce. Gida ta koma ta dauko zani ta saba Radhiya a baya sannan ta taimaka mata suka tafi asibitin sojojin inda take awo.

Ta kwashe kusan awa shida tana fama banda wanda tayi a cikin gidanta kafin Allah Yasa ta sauka lafiya ta haifi danta tamkar Zayyan yayi khaki don yafi Radhiya kama dashi sosai.

Likitocin sun bata kulawa yadda ya dace sannan aka kaita dakin da zata huta saboda wahalar da tasha. Christie tace mata zata je gida tayi girki ta kawo mata don taji kwari. Matar akwai kirki sosai ita ma. Radhiya ta sake dauka dama da tana ciki wurin haihuwa ta siyo mata fanke a 'yar kasuwar gefen asibitin taci ta koshi ta debo ruwa a famfon waje ta bata.

Suna fita ta sake daukan jaririn sai kawai tasa kuka. Yaron da tayi fatan zuwansa duniya mahaifinsa ya karbeshi yayi masa addu'a. Sai gashi ta haihu din a lokacin da bata da masaniyar halin da yake ciki. Karin kukanta yau ta haihu babu kowa nata sai Christie da ta tsaya mata tamkar 'yar uwa. Mami da Zainab suna can lalurar mazajensu ta saka su a gaba. Yanzu ita wa take dashi da zata tura a sanar da gidansu da gidan iyayen Zayyan. Tun tafiyarsa babu wanda ya tako ganinta cikin 'yan uwansa ko da wasa. Me ya ja mata nesanta da 'yan uwanta da na mijinta da rashin zama cikin mutanen da tasan sunyi tarayya a yare, addini da al'ada? Auren Soja ta bawa kanta amsa. Sojan ma Zayyan wanda idan za'a sake bata zabi tayi rantsuwa har ranta shi din a sojansa zata sake aure. Tana sonsa kuma tana alfahari da aikinsa kamar yadda yake yi shima.

Tunani ta zurfafa tana yi akan rashin sanin yaya zata yi labarin haihuwarta ya iske danginsu. Lokacin Radhiya shi yayi komai abinsa. Yanzu kuwa komai ya dawo gareta.

Kan jaririn ta shafa tana hawaye "Daadaa yaci burin ganin zuwanka duniya ko suna bai yarda mun zaba ba saboda yace yana son yayi yiwa jaririnsa huduba da kansa"

Yaro yana baccinsa cikin kwanciyar hankali ta kwantar dashi a gefenta daga jikin bango tana shafa shi a hankali.

"Sojana ka bar min amana mai nauyi. Baka fada min yaya zanyi ba idan baka dawo da wuri ba"

Kuka ta shiga rerawa a hankali tana jin wani matsanancin ciwon kai. Kwanciya ta gyara a gefen dan ta lumshe idanunta ta baiwa kofa baya.

Tana ji likitoci biyu suka shigo dukkansu sojoji da nos guda daya. Wanda ya karbi haihuwarta ya yiwa dayan bayanin cewa ta zubar da jini kuma jininta ya hau kada a sallameta sai gobe.

"Na fahimta Dr. Ina file din nata?" Ya tambayi Nos ta mika masa.

Zaro idanu yayi ya dago yana kallon wancan likitan.

"Matar Lt. Zayyan Tureta ce? Sune last week akace gabadaya unit dinsu...."

Wanda ya karbi haihuwar yayi saurin sa hannu akan lebensa yana magana a hankali harda juya harshe zuwa turanci a zatonsu bacci take, kuma kana yi mata kallo daya ka ga bafillatana wadda ake musu kallon basu da wani ilimin boko sai kiwon shanu.

"Shhh I don't think they know what has happened"

Mairama taji gabanta ya fadi wani abu yana mata yawo a jiki tun daga kai har tafin kafa, sai ta daure ko motsi bata yi ba. Nos din ta kalli bayanta da tausayawa a hankali tace.

"I pity their wives"

Basu san daga ina ba sai ganin Mairama suka yi rike da kafadun Nos din idanunta a rufe cikin karaji take tambayarta "what happened to my husband?"

Kallon kallo suke yi sai taji gabadaya duniyar tana son kife mata. Durkushewa tayi gwiwoyi a kasa tana kallonsu tamkar wadda ta sami tabin kwakwalwa.

"Don Allah don Annabi ku fada min gaskiya"

Tashinta yazo musu a bazata haka fahimtar turancinta shiyasa suka kasa bata amsa kai tsaye. Shirunsu kadai ya isheta amsar da take nema da yanayin da taga sun shiga na tausayinta da tsoron fada mata gaskiya.

"Kinga ki kwantar da hankalinki idan kinji sauki za'a fada miki komai"

Murmushi tayi mai sauti tana ja da baya da baya har ta kai jikin bango ga hawaye tana zubarwa kamar ruwan famfo "da hankalina fa, nasan abinda nake tunani hakane. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Ya Allah....ahhhh. ....kirjina..wayyo Allah.. Ka jikanka Sojana"

Likitan da yazo zai canji wancan aiki ya dan matso kadan "kizo ki zauna...uhmm"

Nos tace "Mairama"

"Ok Mairama ki zauna muyi magana kinji"

Jaririnta kawai ta dauka ta saka shi a kafada tana cigaba da kukanta tana cewa "tun yaushe ya rasu?"

Basu iya cewa komai ba tayi hanyar kofa suna kiranta taki tsayawa. Sai dai kafin ta fita jikinta ya soma rawa likitan da yafi kusa da ita yayi saurin karbe jaririn ta fara neman faduwa tana wata irin jijjiga ga jini ya balle mata.

Nos da daya likitan ne suka kamata aka dora akan gado suna neman ceto rayuwarta. [5/22, 10:51 PM] Sis Ruky: Daga tashar jirgin ruwa ta Apapa da ke dake Lagos su Zayyan zasu tashi a jirgin ruwa zuwa babban birnin Liberia wato Monrovia. Akan tekun Atlantika jirgin nasu ya dau hanya sai da suka wuce Benin republic wadda mu ka fi sani da Cotounou, sai Togo, Ghana, Cote d'voire sannan Allah Ya saukesu a kasar da rikici na cikin gida ya kaurewa tun shekarar 1989.

Motocin yaki aka turo domin daukarsu. Zayyan da Hadir zuwansu sansanin yaki irin wannan na farko kenan. Major Mustapha yazo ne a matsayin babban soja don ba wuri daya zasu zauna ba. Shi Computer Engineer ne saboda haka aikinsa yafi karfi ne daga bayan fage musamman da a wannan lokacin babu masu karatu irin nasa da yawa saboda karancin kayan aiki.

Cikin garuruwa ko kauyuka da rikicin yafi shafa ake watsa sojojin. Sune suke kwantar da tarzoma da fitina idan ta taso a tsakanin mazauna garin da kuma 'yan tawaye.

Ranar farko su Zayyan da sauran da su ka zo tare da yawansu basu iya rintsawa ba. Daki ne kato kowa da yalolowar katifarsa akan gadon karfe mai hawa biyu. Wasu kuma a kasa katifunsu suke saboda rashin wadatar gadajen. Zayyan da Hadir a kusa da juna suka shimfida katifun da aka basu. Shi dai tunanin Mairama da Radhiya yake yi. Ko me sukeyi a wannan lokaci? Tafiyar Radhiya ta kara kwari a kwanakin da suka shafe a kan ruwa? Idan ya koma zata yi masa kyuya? Gajeren tsaki yayi da wannan tunanin. Burinsa ace kowane mataki na rayuwar 'yarsa ya faru a kan idanunsa.

Hadir yace "kaima ka kasa bacci ko?"

"Yadda ka san nayi tsuntsuwa naje na gansu na dawo" yayi maganar cike da kewa.

Muskutawa Hadir yayi ya gyara kwanciyarsa. Shi kuma Zayyan yayi rub da ciki ya rike fuskarsa a tafukan hannunsa da ya tokare kansa dasu.

"Bansan yaya Zainab take yi da Ibrahim ba yanzu. Kusan wata guda yaron nan ba ya iya bacci sai akan kirjina"

Dariya Zayyan yayi "kace akwai daru, don ma bai kai Alheran rigima ba abin zai zo da sauki."

Wani cikin wadanda suka tarar a sansanin yana daga gefe yana jin hirarsu ya soma dariya "kusan kowa ranar farko sai yayi hirar gida"

Gwangwani ya dauka a kusa da shi ya bubbuga da hancin katuwar bindigarsa. Sai ga sojoji suna tashi zaune wasu akan gado wasu a katifa. Kalilan ne masu bacci. Mutumin yace "kunga yau anyi baki ku tashi mu san juna." Ya kalli bangaren da yawancin bakin nasu suke "babu wani abin debe kewa a wurin nan sai hira da muke samun yi da juna cikin dare"

Na kan gado na dirowa na kasa na matsawa sai gasu sunyi da'ira sun zagaye katifar wanda yayi maganar. Da gani zai girmi da yawansu. Kallonsa ya ga suna yi ya kada kafada.

"Ok, ok ni zan fara"

Ihu wasu suka fara su Zayyan dai abin duka sabo ya zame musu. Duk wata hayaniya sun saba da ita a irin training da suke zuwa. Amma wannan karon fa a filin yaki suke tare da sojojin wasu barracks din da basu taba haduwa ba. Muryar mutumin yaji ya soma magana.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull